Showing 87001 words to 90000 words out of 237425 words

Chapter 30 - ZAKI COMPLETE

tsorona daya kar korar da Mama Fulani ta ce zata min ta tabbata ga shi Aliy

un ma ya fusata wata kila shi ma korata zai yi. Idan ko har suka kore ya zama anyi ba ayi ba kenan, abunda na zo nema be samu ba.

“Karbi ki ci, na fada miki karki ji tsoro, babu abunda zai same ki”

Hawaye ne suka sauko min na kasa ce masa komai kuma

na kasa karbar naman.

“Kin fi son ki koma gidan nan?”

Na gyada masa kai sai yai murmushi

“Zan maida ke amman ba yanzu ba, Aliyu be isa ya bani umarni na bi ba, wani fadin rai nashi da hargaginsa na banza ba zai saka nai abunda zai dauka cewar t

soronsa na ke ba, ban san abunda kika yi daya saka Mama Fulani ta mareki ba, sai dai ina ganin kamar be dace tai miki hakan ba dan kawai kina aiki karkashinta”

Kasa nai da kaina na saka hannu na share hawayena, murya can kasa kasa na fara magana.

“Z

an jure komai za a min a ko'ina matukar hakan na nufin silar farincikina, samun lafiyar mahaifiyata shine farinciki a yanzu shine abunda na ke bukata kuma shine dalilin zuwana aiki a nan, ka kyale na wulakanta ta dake ni idan tana ra'ayi ta yi min abunda d

uk ta ga dama, zan jure har na cimma cikar burina”

“Zan taimake ki Ataa zan taimake ki mahaifiyarki ta samu lafiya”

Kallonta nai idonta na zubar da ruwan hawaye na ce.

“Bana bukatar taimakon kowa a yanzu, bana son kowa ya taimake ni na fi yarda d

a nai komai da kaina, da sunan taimako wani ya yaudare yaudarar da ta jefa mahaifiyata da ni a cikin wannan halin, ba zan sake yarda da taimakon kowa ba, matukar ba talaka ne dan'uwan ba”“Sannu bakuwa ya sunanki hala?”

“Aisha”

“Kai kai sunan Mamanmu

ne”

Ta nufi wata hanya da ke kamar corridor sai ta ga ta fito da gorar ruwa da kofi a hannu ta kawo gabana ta aje min.

“Ki fara shan ruwa kamin abinci ya zo”

“Na gode”

Na fada ba tare da na kalli ruwan ba, sai ta tashi ta fice daga falon ta ba

r ni nan zaune ina ta kallon yadda aka kawata ko'ina na falon. Wata budurwar ce ta shigo dauke da farantin nama da yaji a gafe ta aje mika min.

“Ga shi ki saka a baki bakuwar yaya”

Ta fada da kamar zolaya.

“Ina Kamal din yake?”

“Ya fita yanzu

amman ya ce mu kula masa da ke”

A yanzu ma murmushi take tana maganar ni kuma na mike tsaye ina kallon kofa na ce.

“Bari na leka gidan Mama Fulani kamin ya dawo”

“Okay kin santa ne?”

“Eh na santa”

Shine kawai abunda na fada mata na nufi kof

ar ina ta sauri na fito daga falon.

“Aa har kin fito?”

“Eh nan zan je gidan Mama Fulani na dawo”

Na bawa matar dazun amsa sai ta amsa da.

“Okay sai kin dawo”

Kamin na isa gate din gabana nata faduwa ina ganin kamar haduwa zan yi da Kamal ya

dawo ya hana ni fitar, ina samun nasarar ficewa daga gate din na tsallaka titi da sauri na buga gate din gidan Mama Fulani mai gadin ya bude min na shiga da sauri kamar wacce tai sata. Gadan gadan na doshi cikin gidan duk irin faduwar gaban da nake ji da

tsoro arba da Mama Fulani sai na danne shi na tura kofar falon na shiga da sallama. Tana tsaye tana magana da suka yan matan nan na dazun da suka zo baki da kuma yayanta ta juyo ta kalleni.

“Me kika dawo ki yi?”

Durkusawa nai daga inda nake tsaye ba

kin kofar na hade hannayena ina rikonta.

“Dan Allah dan girman Allah ki yi wallahi ban san ya kai ni asibiti ba, kuma ban ce ya kai ni ba, dan Allah karki kore ni”

“Da ya kai ki asibiti da kar ya kai ni uwarsu daya ubansu daya a gurina, amman tabbas

yau ba za ki kwana a gidan nan ba”

“Ki tausaya min dan Allah saboda Mama nake wannan aikin, bata da lafiya kudin maganinta nake nema”

“Ni nan da kika ganni ba ni da uwa da uba duka sun mutu marainiya ce ni, kara ke ma har da iyayenki a raye, wuce ki

je ki hada kayanki yanzu nan bana son ko minti talatin ki kara a gidan nan”

Ta fada cikin daga murya tana nuna min kofar fita. Siyama ta kalleta ta da tausayawa ta ce

“Mama ki yi mata hakuri idan ta sake sai ki koreta”

Sai Rukaiya tai karaf ta ce

.

“Wallahi ni bana ma son minti biyar ta kara a gidan nan wacan yarinyar da kike gani tun da ta zo kullum sai wani mummunan abu ya faru”

“Za ki wuce ko ba zaki wuce ba”

Mama Fulani ta daka min tsawar da ta sakani mikewa tsaye a razane na fice da

sauri. Garejin na dawo na zauna ina ta kuka mai karfi wai ko wani zai ji ya zo ya tambaya dalilin kukana yajd ya bata hakuri amman babu wanda ya zo har na ji muryarta tana kiran Zaharadden direba.

“Ki fito yanzu nan ko na shigo cikin na ci miki mutumci



Da sauri na tashi na dauki jakar tawa na nufi garden na dauko ragowar tufafin dana shanya tun rana na saka a ciki na dawo garejin na saka sauran da musasshiyar farfesun kazar dana shanya na saka cikin jakar da siyayar da Kamal yai min, sannan na saka

Hijab dina na fito ina hawaye na tsaya jikin garejin ina kallon kudin da take ba wa direban.

“Ka tabbatar ta shiga mota sannan na mika mata sauran kudi, idan an isa kaduna ta hau motar sokoto ai tasan gidan ubanta idan aka sauke ta a can”

“To Hajiya



Ya fada yana karbar kudin tare da zagaya wa wajen motar ya bude ya shiga.

“Zo ki wuce mun rabu da kaya”

“Kudin aikina fa?”

“Aikin da ko wata ba ki yi ba? Je ki turo ubanki ya zo ya dibar miki”

“Ubana baya duniya Hajiya, ya tafi idan zan k

i je zan je kowa zai je, amman Allah zai dibar min hakkina”

Shine kawai abunda na iya fada cikin kuka na nufi motar na bude na shiga, ina jinta tana ta zagina. Hawaye ne suke ta min zuba har muka isa tashar, a lokacin da direban yai farkin na bude zan f

ita sai na ji ya ce.

“Ki yi hakuri da rayuwa, haka take zuwa juyi juyi Allah ya sauwake mana talauci ni da ke mu daina zama karkashin kowa”

Da na kalleshi sai na ga hawaye a idonsa.

“Amin”

Na amsa sannan na sauka daga motar shi ma ya fito, sai

da yaje gurin yan Union ya hannata musu ni ya basu kudin motar zuwa kaduna da kuma kudin motar Kaduna to sokoto sannan ya ciro dubu biyu ya mika min.

“Gashi ki rike wannan Allah ya kai ki lafiya sai wata rana”

“Na gode”

Na karba da hannu biyu in

a ta hawaye kamar wacce akai wa ido dan hawayen kawai.

“Lafiya Mutuwa akai miki?”

Daya daga cikin mutanen ya tambaya. Sai na girgiza masa kai ina jan magina.

“Aa ba mutuwa akai min ba”

“To Allah ya sauwake”

“Amin”

Shi ya nuna min motar d

a zan shiga sannan ya bawa direban kudina da kuma kudin motar da zai saka ni ta Kaduna sannan na shiga na zauna muna jiran karin wasu mutum biyu. Ban dade da zaman ba aka kira sallah la'asar sai da aka kira sallar na tuna da cewar ban yi sallah azahar ba,

sauri na fita daga motar na nufi gefen masallacin nai alwala da butar su sannan na nufi wani dan daki dana hango mata na shiga na shiga ciki nai sallah, na fadawa Allah bukakata kuma na kai masa kukana na kuma roki mafita akan dukan lamura na. Ba bar tasha

r ba sai biyar da kwata sannan direbamu ya kama hanya.ALIYU POV.

Da mugun bachin rai ya fita daga asibitin yana cikin motarsa Momy ta kira shi ta fada masa cewar an sallami Rahma kuma ya zo ya tafi da ita, jin wannan labarin yasa ki sakewa daga bachin

ran da yake ciki sai ya dauki hanyar asibitin. Ko da y shiga ciki ya samu Momy da Mommy Rahma suna fita Rahma na zauna tare da kanenta guri daya fuskarta babu walwala, ganin Aliyu ya saka kanen nata suka tashi daga saman gadon suka dauki wasu kayan da za a

tafi da su suka fice. Da murmushi Aliyu yake kallonta amman ita ka kasa sakewa kamar ba ita aka sallama ba.

“Amman na ce idan mun wuta yau zuwa gobe za mu tafi da ita can sokoto ta samu kula kuma idan tana kusa da mu ita kanta zata fi walwala”

Momm

y Rahma ta fada har Aliyu ya bude ba ki zai yi magana sai Momy ta shiga kuma ta shanye duk wani abu da yake da niyar fada.

“Eh nima na yi wannan tunanin hakan zai fi, shi kanshi Dan wajen Fulani ai ba zai ki ba, Allah dai ya bata lafiya muma ai goben z

a mu koma”

Shiru yai be ce komai ba, saboda Momy ta saye bakinsa. Mommyn Rahma da Momy tare suka jera a gaba suna tafiya shi kuma ya jero shi da Rahma suka nufo gurin da ake aje motoci. Wata motar Mommyn Rahma da kanenta suka shiga Mommy kuma ta shiga g

idan baya Aliyu da Rahma suka shiga gaba. Sai da ya fara shiga har cikin gidan Mama Fulani ya sauke Momy har sisters dinsa suka fito suka ga Rahma ban da Mama Fulani da take jin sai dai Rahma ta fita daga motar taje ta gaisheta. Bayan Momy ta fita ya wuce

da Rahma gidansa, bata ce masa komai ba shi ma be ce mata ba har suka isa tana kao hannu ta bude motar sai ya rike dayan hannun wanda hakan yasa ta kalleshi.

“Rahma kamar ba ki murna da sallamar nan da aka miki?”

“Miye abun murna a gurin gawar da ak

a kai asibiti? Ai kasan daga asibitin sai kabari, ba warkewa nai gaba daya ba, to me zai saka ni murna?”

“Wani ya baki tabbacin cewa ba za ki warke ba? Ko kuwa kina da shaidar cewar mutuwa za ki yi saboda kina da wannan ciwon”

“Za ka iya bani tabbaci

n cewar zan warke na tashi kamar kai? Ko kuwa zaka ba ni tabbacin cewar wannan ciwon ba zai yi ajalina ba?”

Ta aika masa da tambaya cikin tambaya ba tare da ta bashi amsar tambayar da yai mata ba. Fita tai daga motar ya zagaya gefenta ya bude mata motar

ya fito da ita ta rumgumeta sai ta karasa fashewa da kukan da take ta kankame shi sosai tana shakar turaren jikinsa.

“Bana son na rayu da wani namijin baya kai Aliyu, ina son ka sosai, ko da bana aurenka ba zan iya jurar ka kula da wata macen kamar ya

dda kake kula da ni ba, ba zan bari son wata mace ya shiga zuciyarka ba dan Allah ka min alkawari ko bayan raina ba zaka auri wata ba”

“Mi zai saka na auri wata bayan kina raye? Ko wace ta cancanci wani gurbi a zuciyata bayan ke Rahma? Be kamata kina ir

in wadannan tunanin ba”

Akwai abubuwa da yawa da ba su kamata na aikata su ba Aliyu amman dole na aikata, a zuci tai wannan maganar tana nasalta yadda zata rayu ba tare da Aliyu ba na dan lokaci kamin da dawo masa kuma ta dawo da farincikinta da cikar b

urinta na haihuwa. Rikata Aliyu yai suka shiga cikin falon zuciyarsa cike da tausayinta duk kuwa da irin maganganun da tai masa dazun suna cikin ransa.

ZAKI

By Khadeeja Candy

28...

ATAA POV.

Misalin goma na dare muka isa Kaduna, a cikin tas

har direban ya sama min guri na kwana bayan na yi sallah, washe gari ma sai da na siya pure water sannan nai sallah asuba, bayan ruwan naira goma ban sake saka komai a bakina domin jin nai bana bukatar komai kuma bana jin yunwa, da asuba muka kamo hanyar s

okoto daga Kaduna, ina ta jin kamar zan yi amai a motar saboda kaurin mai da tafiya mai nisa wacce ban saba da ita ba. Ana gama sallah azahar muka shigo sokoto, ba dowowar dadi nai ba amman tuna cewar da mahaifiyata zan gana sai na ji sanyi, a wani bangare

n kuma ina ta zullumi da tunanin abunda zan fada mata domin na san ba zata ji dadi idan na fada mata an korono ba, gashi kuma ban samu kudi ba. A babbar tasha muka sauka na dauko jakata da dubu daya da dari biyar da sauran canjin da na siya ruwa da su ciki

n kudin da direban Mama Fulani ya ba ni. Sai da na kawo bakin titi sannan na tari napep na shiga na fada masa inda zai kawo ni. Daga tashar zuwa Clapperto road dari da hansi ya kawo ni na bashi kudinsa na fita zuciyarta cike da zullumi da tunanin karyar da

zanyi, har ina tunanin fara zuwa gidan Maman Salma sai kuma na wuce gidansu Farida kai tsaye. Wani dan karamin dakin kwano ne akai a gafen gidan wanda akai masa fuska daga can gabans ta yadda wanda yake cikin dakin baya ganin wanda zai zo wanda kuma zai z

o baya iya ganin na ciki. Ina ta mamakin miye a gurin domin ban san da dakim kwanon ba kamin na tafi,. Da sallama na shiga cikin gidan sai Farida ta fito waje da sauri tana washe hakora.

“Oyoyo Ataa”

Rumgume ni tai duk da ina cikin bacin rai hakan b

e hana ni murna ba na rumgumeta muna murna da ganin juna.

“Ina jin muryar na ce ke ce”

“Ni ce fatar na same ku lafiya”

“Lafiya kalau”

Na sake ta na nufi dan kitchen din da nasan na bar Nana a cikin kamin na karasa ta ce.

“Ai am maida Nana

dakin waje”

Cikin yanayin rashin jindadi ta fada fuskarta na nuna haka. Ban tambayi dalili ba sai dai naji faduwar gaba jin hakan, sai na juyo na fito daga gidan gaba daya na nufi inda kofar dakin kwanon take Farida na biye da ni a baya yanayinta kamar

mai jin tsoro. Mutuwar tsaye a bakin kofar dakin kwanon na saki jakar da ke hannuna ina kallon Nana da ke kwance kamar kare domin babu tsoka a jikinta sai ƙassa, kanta ba dankwali gashin kanta ya tsire an rufa mata wani zane dakin gana daya wari yake warin

kashi da fitsari, kallo take ba dan ta ganeni ba sai dan mutum take gani ban san lokacin da hawaye suka fara min zuba ba zuciyata ta rufe tai min wani irin mugun nauyi..

Daker na iya daga kafata na shiga cikin dakin hawaye na sauko min wasu na bin was

u. Kusa da ita na je na zauna ina kiran sunanta.

“Nana Nana Nana”

Shiru bata amsa min ba, sai kallona take kamar bata gane ba. Hijab dina na cire na na aje Farida na tsaye tana kallona har na janyota domin bana iya daukarta gaba daya bakin kofar dak

in na kawo ta na aje, na fito da komai na dakin na nemi tsohuwar tsintsiyar mu da naga a cikin kaya na share dakin, na dauki roba na shiga ciki na debo ruwa kasancewar cikin gidansu Farida a akwai rijiya, na dawo dakin na zuba ruwan na wanke na masa tas, d

uk abunda na ke Farida na tsaye tana kallona ta kasa komai, Hijab din nawa na saka na je gawon nama na siyo omo da kudin hannu na siyo fura da nono da madara na dawo, ko da na dawo Farida ta shige cikin gida, ni kuma na sake sakawa dakin omo na wanke shi y

a cire duk wani karni da warin da yake sannan na dauko turaren da Kamal ya siya min na saka duk da kasancewar na jiki ba hakan be hana dakin kamshi ba, zane da zane na hada na zagaye sannan na sake debo wasu ruwan na kai na jata a haka na kaita gurin na zu

ba mata ruwa nai mata wanka ko ina na jikinta sai da na wanke sannan na sake dawowa da ita a cikin tufafi na dauki wata riga da Aliyu ya bani na saka lokacin da nai rashin lafiya ta manya na saka mata na daura mata dankwalin sai na aje ta a waje saboda dak

in be gama budewa ba. Wasu ruwan na sake debowa na saka kayan ci abincin mu a gaba na wanke su ma sannan na dama mata furar na saka ludayi ina ta bata tana sha a hankali har ta sha ya iashe sai na debo mata ruwa na bata ta ta sha da yawa, sai ta sauke wani

irin ajiyar zuciya yana saka ni jin tausayinta fiye da da, sannan na dauke ta na maida ta dakin na fito na saka tufafinta a gaba na wanke su na shanya sannan na daw dakin kusa da ita na zauna ina ta kallonta kamar yadda ita ma take kallona irin kallo da k

e nuna bata gane ni ba, ko kuma bata san inda kanta yake ba kawai dai tana gani ne.

“Nana”

Bata amsa ni bata kuma daina kallona ba, hakan yasa na fashe da kuka na kama hannunta na rike, na dawo amman babu kudin maganin kuma n tararda ciwonta ya fi n

a da, sai dai ina tunanin dawowar tawa tai amfani domin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login