Showing 93001 words to 96000 words out of 237425 words
iya gane hanya ba amman an tura zuwa garin be san ina take ba,
maybe tai hadari ko ta gadu da wani abun be sani ba. Wannan tunanin ne ya hana shi bachi har asuba, for the first time yau ya kwanta gado daya da Rahma kuma rumgume da ita amman zuciyarsa tana gurin Ataa. Sai da yai sallah asuba sannan ya kwanta dakinsa s
hi kadai saboda nauyin da idonsa da kansa suke masa wai ko zai samu yin bachin da be yi ba jiya.
*** *** ***
A haka Mama Fulani ta kwana cikin rashin sakewa wanda ya bawa kowa mamaki ciki kuwa har da Momy da bata sake ganin walwalarta ba, ga
ba daya aka hadu dinning gurin cin abinci har Muhseen amman ban da Mama Fulani da ta gama shirya abinci ta koma dakinta tana karyawar.
“Husna kui yi ku gama mu shirya da wuri kusan 10 jirginmu zai tashi”
Momy ta fada tana mikewa tsaye ta daga dinning
din ta koma falo ta zauna tana kiran wayar Aliyu dan ta tambayi jikin matarsa. Muhseen ya kalli Maryam.
“Wai ina Mama?”
“A dakinta take karyawa wai bata jindadi”
“Ataa fa? Yau ba tai shara ba ban ma ta shigo ba, kuma tun jiya da dare na duba gan
ta a gareji ba ban ga kayanta ba”
“Mama ta maida ita gida”
Muhseen ya kalli Rukaiya da sauri wacce ke bashi amsar.
“Saboda me?”
“Ta gaji da ita, kuma abunda ya faru daman Mama ta ce ba zata kwanar mata a gida ba”
Sai a yanzu ya abunda Aliyu
yake tambayar Mama Fulani jiya har take ce masa bata san inda take ba. Jan kujerarsa yai baya ya nufi dakin Mama Fulani. Kishingide ya same ta tana cin fruit tana duba wayarta.
“Mama kin kori Ataa? Mi tai?”
“Ba tai komai ba, na gaji da aikinta kar
kuma ka sake min maganar abunda ya shafe ta last warning”
Ta fada masa sannan ta cigaba da abunda take, sai da yai kamar zai sake ce mata wani abu sai kuma yarfar da hannunsa ya juya cikin rashin jindadi ya fice daga dakin.
ALIYU POV.
Be fa
rka sai sha biyu saura na rana, ya dade kwance a saman gadon idonsa biyu yana kallon silin sannan ya unkura ya tashi zaune ya sauko da kafafunsa daga kan gadon, agogon dakin ya fara kallo yana ganin sha biyu ta kusa yai hanzarin mikewa tsaye ya fice daga d
akin zuwa dakin Rahma, be same ta a ciki ba sai yar takardar da ta bar masa saman gado.
_Kana bachi bana son na tashe ka, Mommy ta kirani zan je na same ta a gidansu sai mu wuce see you soon_
Yana gama karanta takardar ya cikawa bakinsa iska ya busa
r cike da rashin jindadin yadda yau Rahma tai masa, be taba damuwa da fita ba tare da ta tambayeshi ba sai yau, yana ganin kamar ta wulakanta shi. Hannu ya kai ya dauki wayarsa da ya bari a dakin jiya sai ya ga miss calls din Momy da Husna da Maryam misali
n tara da wani abu na safe kiran wayar yai sai ya ji bata shiga, hakan yasa ya kira wayar Maryam din sai ta shiga.
“Hello Ya Aliyu daman Momy ce ta ce na kira domin ta yi ta kira wayarka bata shiga”
“Ina Momy take?”
“Ta wuce tun ten suka tashi”
Ya kashe wayarsa yana fadin.
“Jirgi daya suka shiga da Rahma kenan”
Fitowa yai daga dakin zuwa dakinsa dan yin wanka ya shirya yaje gurin Mama Fulani, kamin ya shiga dakinsa ya kira wayar Nasir ring uku tai sannan Nasir ya daga.
“Na kira wayar
ka baka daga ba ya jikin Rahma?”
“Tana hanyar sokoto”
“What ta jin sauki ne ko kuma wani ciwon ne?”
“Sun sallame ta jiya, mahaifiyarta ta ce da ita za su je, and yau bata ma jira na tashi ba kuma bata tashe ni ba suka wuce”
“Kun samu matsala da
Rahma ne?”
“Ba wani matsala kawai dai na mata maganar Ataa ne kuma taga laifina, Wallahi Nasir tunanin yarinyar nan hana ni bachi yai, Mama ta koreta tun jiya yanzu ban san halin da take ciki ba”
“Garin ya miya faru?”
Aliyu ya labartawa Nasir abu
nda ya faru sannan ya dora da.
“Mama ba zata fada min inda zan same ta ba, domin jiya konda na baro gidan ranta a bace yake, amman yanzu ina son ka nema min jirgi zan je sokoto gobe, zan koma gidan nan na sake bincikawa”
“Ko ba ka je da kanka ba za
ka iya sakawa ayi maka Aliyu”
“Yeah ina son na je da kaina ko dan Rahma”
“Okay idan an gama komai zan sanar da kai”
Kai ya gyada kamar ance Nasir yana gabansa sannan ya kashe wayar.
Misalin biyu da rabi ya shiga part din Mama Fulani sai ya samu
bata nan Baby ce kawai a gidan ita bata dade da dawowa daga scul ba. A saman Sofa ya zauna ya kira Mama Fulani a waya ringing tai sai da ta kusa katsewa sannan ta daga.
“Mama na zo ba ki gida”
“Eh munje gurin kamu ni da su Maryam kuma za mu shoppin
g kamin mu dawo”
“Mama ina son magana da ke”
“Idan na dawo za mu yi”
“Yaushe za ku dawo sai da yamma”
Daga haka kai hanging wayar. Sannan ya nufi kitchen ya hadawa kansa Lipton ya sha ya fito shiga bangaren Ammy, a harabar gidan ya samu Batula
tana fira da wani saurayi tana ganinshi ta sha jinin jikinta saurayin kuma ya gaishe shi Aliyu ya amsa mishi ciki ciki sannan ya wuce falon Ammy. Sai da suka gaisa sannan take koro masa da zancen tafiyar Momy.
“Ko da suka wuce ina bachi, Ammy ba ki sa
n gidansu yarinyar nan Ataa ba?”
“Wallahi ban sani ba Aliyu, bata fada min ba nima dazun nake jin zancen tafiyarta gurin Muhseen yana tambaya wai ko na san inda take”
Aliyu yai shiru kamar be ji ba sai kuma ya mike tsaye yana saka hannayensa aljihu d
an be son Ammy taja zancen da tsawo.
“Zan leka office”
“To Allah ya tsare”
Ko da ya fito part din Ammy wayarsa na vibration kiran Nasir na shigowa picking yai yana bude motarsa ya shiga.
“Aliyu an samu jirgin da zai tashi da yamma nan zuwa Ke
bbi idan kana so, daga Kebbi sai ka shiga mota zuwa sokoto, domin gobe babu jirgi sai jibi shi ma kuma da safe zai tashi na san kuma ba son tafiyar safe kake ba”
“Karfe nawa jirgin zai tashi?”
“5 idan kana so sai a siya maka ticket”
“Siya min gani
nan zuwa office din ma”
“Okay sai na iso”
Yana kashe wayar ya shiga motarsa ya dauki hanyar kamfaninsu. Be bar kamfanin ba sai da ya rage minti talatin jirginsu ya tashi duk kuma jiran da yai na Mama Fulani ko zata dawo da wuri ne yai magana da ita
dan be gane wannan fushin da ta soma yi da shi ba. Amman hakan be samu ba sai dai a waya ya kirata ya fada mata zai je sokoto tai masa Allah ya tsare.
ATAA POV.
Ina ta tunanin samun mafita har garin Allah ya waye, ban samu bachi ba saboda tunani
da kuma nishin da Nana take yi. Bayan na gama sallah na dauki kofi naje na siyo mata koko da kosai da suga na saka mata na bata kokon kawai ta sha shima dan ina bata ne, ta ki ta ci kosan ni ma na kasa cin komai. Sai da na tabbatar ta koshi sannan na fito
da ita na gyara mata jikinta na sake gyara dakim na saka Hijab dina na nufi titi, Napep na tara na hau na kama hanyar gidansu Rahma, da kudirin da ke zuciyata duk da kasancewar na san bata nan ina son naje ne na bar wa mai gadinsu sako ya fada musu domin n
a san ba zai rasa number da yake kiransu ba. Bakim gate din gidan Mai Napep ya aje ni na bashi kudinsa sannan na buga gate din mai gadin ya leko ya ganni sai na ga yai murmushi.
“Ahh wannan na manta sunanki ke ce”
“Ni ce”
Na amsa masa cikin damuwa
. Sai ya bude min gate din na shiga ciki.
“Dan Allah so na ke ka kira matar gidan nan da mijinta a waya ka fada musu cewar akwai wata koda ta siyar idan suna so, ko kuma ka bani number wayarsu”
Ya daki kirji yana kallona
“Koda?”
“Eh”
“Ina ki
ka samu koda?”
Na yi shiru ban ce masa komai ba.
“Allah yasa ba taki ce ba, kin abunda kike kuwa?”
“Na sani ni dai ka kirasu kawai”
“Sai dai a kira matar a waya amman Alhaji yana nan cikin gidan ai jiya da dare ya dawo”
“Ba suna Abuja ba?”
“Eh shi jiya da dare ya dawo bari na miki sallama da shi”
Ya fada yana nufar cikin gidan. Ni dai ina tsaye kusa da gate din har ya shiga ciki sai na hango Aliyu ya fito sanye da Jallabiya daga can ya tsaya yana kallona kamin ya sauko ya doso inda nak
e tsaye.
“Za ki siyar da koda?”
Na gyada kai ina matsa yatsun hannuna.
“Waya ce miki muna bukatar koda?”
“Na san ai kodar matarka ta kone, dole wata za ku nema”
“Saboda mi za ki siyar da kodar ki?”
“Saboda na nema ma mahaifiyata lafiya”
“Idan kuma ke kika mutu fa ko kika samu matsala?”
“Kara ni na mutu ita ta rayu da ta muti ta barni, jiya ba tai bachi ba saboda azabar ciwo, bata iya tashi komai a inda take take yinsa bata gane kowa ni ma da nake yarta bata gane ni ba, kuma ba mu da
inda za mu babu wanda zai taimaka mana ina son mahaifiyata bana son ta mutu”
Na karasa cikin kuka mai karfi daman tun da na soma maganar hawaye ke sauko min. Shi ma hawayen na gani a idonsa sai yai saurin daga kansa sama ya zuba hannayensa aljihu.
ZAK
I
By Khadeeja Candy
29...
Dukawa nai a gurin saboda kukan da ya ci karfina. Sai ya bar ni a gurin ya nufi cikin gidan be dade ba sai ga shi ya fito rike da gorar ruwa da cup dayan hannunsa kuma rike da tissue, ya nufo inda nake, tissue ya fara ban
i ba tare da ya ce min komai ba, na karba na share hawayena sannan ya bude gorar ruwa ya zuba min a kofi ya miko min. Karba nai na sha rabin ruwan sai na risina na aje kofin kasa dana dago sai na ga ni yake kallo ba ko kyaftawa, dan kawar da fuskata nai in
a goge hancina.
“Ina Mamarki ta ke?”
“Tana can gida”
“Wane gida?”
“Gidansu kawata”
Shiru yai be ce komai ba har na wani lokaci idonsa na kaina ban san abunda yake kallo a jikina ba.
“Shigo ciki ki zauna kamin na shirya”
Yana fadar hak
an ya juya da zimmar komawa ciki sai kuma ya juyo ya kalleni ganin na tsaya a gurin na ki na bi bayansa.
“Ni ba zan shiga ciki ba”
Na fada ina turo baki ba tare da na kalleshi ba. Matsowa yai kusa da ni sosai kamar zai hade jikinmu gabana ya shiga fa
duwa kamshin turarensa ya cikani sai dan matsa baya na kalleshi ido ya zare min.
“Idan na ce ayi yi ake ba a min gardama, wuce ki shiga ciki”
Yadda yai maganar is like yana bani umarni ne kamar wani boss. Kara tubo masa baki nai na juya sai na ji an
fisgo ni da mugun karfi an juyo da ni.
“Wuce ki shiga na ce”
Ya fada cikin muryar dake nuna bacin ransa yana zare min ido.
“Bana shiga gidan da matan gidan ba sa nan”
Cikin daga murya na yi maganar har Mai gadinsa daya koma gurin gate ya zaun
a sai da ya kallemu. Matsowa yai da fuskarsa yana fitarda numfashi da karfi.
“Haka Muhseen yake miki ko? Shiyasa kike dauko ko wane namiji dan iska, mahaukaciya kawai”
Yana fadar hakan ya sake ni da karfi har yana ture baya kamar zan fadi, sannan ya
juya ya koma ciki ya bar ni a gurin tsaye. Juyowa nai na dawo gurin mai gadin na ce masa.
“Dan Allah ka kira matar gidan ka fada mata yanzu”
“Ba kun yi magana da shi ba?”
“Be ce min komai ba sai bakin fada, ni dai dan Allah ka kirata”
“Wallah
i Alhajin ne ba a iya masa yanzu zan iya kiranta ya zama ganin laifi”
Na marairaice masa fuska tare da dukawa kasa ina rokonsa.
“Ka taimaka min dan girman Allah, Wallahi ina cikin matsala sosai”
“Gaskiya tun da ya nuna ba ya ra'ayi kara ki hakur
a kawai, ko kuma na baki number ta kina da waya?”
“Ba ni da waya Wallahi amman dan Allah ka taimaka min”
“Zan kirata amman sai mai gidan ya fita, domin ni bana iya magana kadan idan kuma nai karai ya ji zai iya korata dan ya fada min baya son hayani”
“In tafi zaka kirata kenan?”
“Eh zan kirata In-Sha-Allah”
Daya bani tabbacin zai kirata ne yasa na taso na fito daga gidan, cikin rashin jindadin domin haka ta bata cin ma ruwa ba, daman nasan indai shi ne za ko zai siya sai ya wulakantani tunda
dan wulakanci ne. Har na kama hanya sai kuma ya juya na koma saboda bacin ran daya same ni gate din gidan na buga da karfi mai gadin ya sake leko ganina ya bude min karamar kofar.
“Dawowa kikai?”
“Eh”
Na fada da kamar Fada sannan na wuce zuwa bak
in kofar falon na taka na kai jikin kofar na buga kofar da karfin tsiya.
“Eh daman ai na san ba zaka siya ba, amman idan ta zalince ce kana so ko? Idan a hanya ka hadu da ni zaka iya sakawa a danne a min tiyata a cire a sakawa shegiyar matarka, mugu ka
wai duk halin da mahaifiyata ta shiga kai ne sanadi kuma ba zan taba yafe muku ba azzalumai masu.... ”
Ban karasa ba ya bude kofar falon sai nai shiru na kawarda fuskata ina hawaye. Farin jean ne jikinsa da bakar riga mai kwalliya sai fararen takalmi ha
nnunsa rike da waya da kuma keys din mota, kamshin turarensa duk ya cika gurin shi kuma ya min fadi a ido tsoronsa ya cika zuciya, ba kuma tsoro na kar ya dake ni ba, yana da wani irin kwarjinin da ke saka mutun tsoro na rashin dalili. Yana tsaye jikinnkof
ar daga ciki ni kuka ina daga waje kaina na wani gafen shi kuma idonsa a kaina kamar yana hararata kuma ba harararba. Juyowa nai na sauko daga gurin na nufi gate na fice abuna ba tare da na kara cewa komai ba, shi ma kuma be ce min ba, hanya na biyo ina ta
tunanina kala kala ciwon nana neman maganinta da kuma abunda mutumen nan da matarsa suka min. Da karfi aka faka mota gabana sai na ga an turo ganbun motar an bude shi, dana leka sai na ga Aliyu ne a ciki yana kallon wani gurin, ba zai iya cewa na shigo ba
saboda bakin girman kansa, idan ma na shiga ban san inda zai kai ni ba, sai akwai nai gaba abuna na barshi a gurin. Sai ya kara cin gabana da motar ba tare da ya min magana ba nima na kara yin gaba abuna, sai ya fito daga cikin motar ya biyo bayana ya fis
go kafadar hannuna ya dawo da ni ya saka ni da karfi a front seat ya rufe motar ya zagayo gefensa ya shiga ya hau titi ba tare daya kalleni ba.
“Wallahi ni ba zan yarda ka cutar da ni ba, wacan zalincin da kuka mana ya isa cin amanar da muka min kai da
Mama Fulani sai Allah ya saka min”
Na fada ina saka dayan hannuna na murza inda ya rikani cikin kukan dana fara tun a lokacin daya rikoni ya saka ni motar domin ba karamin riko yai min har yanzu ina jin ciwo a guri. Wayarsa ya ciro ya shiga wani guri ya
i dannen dannensa sai na ji karar kiran waya yana fita ta speakers din motar.
“Hello Ranka ya dade idan ka kira ta samu, idan ba ta samu ba sai dai mu kira mu gaishe ka”
“To ta samu Bukar kana ina?”
“Ina gida tare da iyalina”
“Ina da patient ne
ambulance nake so”
“Subhanallahi waye ba lafiya?”
“Baka santa ba”
“Wani guri zan saka a turo maka yanzu”
Sai yai shiru be ce komai ba, ni yake jira nai magana ni kuma ban sammaci hakan ba tun da naga ko kallona be yi ba.
“Ko ba ki ji ba?”
Ya fada still be kalleni.
“A Clapperto road house number 11 amman ta bayan gidan zaka shigo kananan gidanjen da suke nan”
“Okay”
Yana fadar hakan sai Aliyu ya katse kiran ya dauki wani farin Bluetooth ya saka a kunnesa ya kara gudun da yake. Ci
kin kannnen lokaci muka isa Clapperto road, wani abun mamaki har kofar gidansu Farida ya faka motarsa ina ta mamakin yadda akai ya san gurin kai tsaye ba tare daya tambaye ni ba. Fita nai daga motar na nufi dakin na kwano ba tare da rufe masa motarta ba. W
asu tufafin na canja mata na saka mata Hijab, sannan na zauna kusa da ita tana ta kallona kamar bata gane ni ba har yanzu. Ina jin lokacin da motar asibitin ta tsaya sai na ji muryar