Showing 72001 words to 75000 words out of 237425 words
motarsa aka bude masa gate ya fice daga gidan. Ni kuma na koma garejin na shimfida tabarmar ta na aje kayana na kwanta a gurin hankali ya fi natsuwa da nan din duk da a nan ma ina jin tsoro amman gwara nan
da can din. Ina kwance na ji ana kira na.
“Ataa”
Muryar Anty Rukaiya ce hakan yasa ni saurin amsawa na mike da sauri na nufi part din Mama Fulani, a bakin kofar falon na same ta tsaye.
“Ance ki je ki gyara part din Ya Muhseen ashe ba ki gyara shi
ba ko?”
“Wankin da aka saka ni yasa na manta”
“To yanzu an tuna miki”
Ta fada tana yatsina fuska, sannan ta kauce jikin kofar ni kuma na raba gefe na shiga na dauko tsintsiyar da mopper da robar da nake zuba ruwan mopping din ciki na hada komai sa
nnan na dauko na nufo part dinsa, ina isa bakin kofar na kai hannu na tura kofar falon na shiga na yi zaton ko baya ciki sai na same shi cikin falon a zaune yana video call da wata, ganina yasa ya katse video ya kalle ni fuska a hade wai shi har yanzu fush
i yake da ni, yana kallona nai saurin gaisheshi ina risinawa.
“Ina wuni”
“Ban sani ba, ba na ce karki sake min magana ba?”
“Yi hakuri”
“Fice ki ba ni guri”
“Mama Fulani ce ta na zo na gyara gurin”
Na fada ina dan turo baki idona na kokar
in cika da hawaye. Maida kansa yai gurin wayar ba tare da ya kula ni ba.
“Ya Muhseen kai hakuri ka daina fushi da ni ba zan sake boye maka komai ba daga yanzu”
Na fada cikin da damuwar yadda ya ke min tsakanin jiya da yau, domin har ga Allah na damu
da rashin kulani da yake yi. Kallona yai sai ya sakar min murmushi.
“Na ji”
“Na gode”
Na fada nima ina murmushi tare da daukar ruwan mopping din ma nufi bedroom dinsa. Shara na fara yi na kawo ta bakin kofar falon sannan na soma mopping, ina cik
in mopping din ya zo bakin kofa ya tsaya yana kallona wayarsa a hannunsa.
“Pretty karki sake wanka Garden kin ga ke macece ba namiji ba, i'm sorry dazun na kasa dauke idona akanki kina da kyau gaskiya ba zan boye miki ba kina da abun da ake so a jikin
mace kin san ni bana gani nai shiru, amman dai karki sake wanka a garden”
Kunya ce na ji ta rufe ni, ni har na manta da zancen ya ganni ina wanka dazun amman yanzu ya tuna min sai na ji babu dadi.
“Bana son wanka a bandakin mai gadin ne shiyasa”
“Be ma dace ki yi wanka a can ba, shi ma ai namiji ne, idan za ki yi wanka ko wani abu ki shiga bangaren Mama ki yi”
“Ai kasan Mama Fulani ba zata yarda ba, dukana ma za tai”
“To ki shiga bangaren Ammy ko kuma ki zo nan idan ina nan zan fita naje par
t din Mama Fulani har ki gama, amman karki sake wanka a garden”
“Tau”
Na fada a ladafce sai yai murmushi.
“Good girl”
“Aisha.... ”
Kamar daga sama na ji kiran da muryar Aliyu, yadda ya kiran sunan sai ka rantse da Allah shi ya rada min shi,
juyawa Ya Muhseen yai yana kallonsa ni kuma na saki mopper na nufo kofar dan ganin mai kiran duk kuwa da muryar mai kiran na karantar da cewar a hasale yake. Aliyu ne tsaye a kofar falon fuska a hade.
“Fito”
Ya fada a tsawace.
“Mama fulani ce ta
ce na gyara part din Ya Muhseen”
“Fito na ce kar na sake ganin kin zo nan”
Ta fada da kakkausar murya.
“Kamar ya?”
Ya Muhseen ya tambaya, sai Aliyu ya watsa nasa harara.
“Haka kawai zata zo nan ta kebe da kai da sunan wani sharan daki”
Z
AKI
By Khadeeja Candy
24...
Kadan-kadan yake tuka motar yana ta kallo har na soma tsarguwa na takure guri daya, sai yai murmushi ya kai hannunsa ya bude wani dan gurin ya dauko wata yar karamar kwalba mai kamshin gaske ya miko min turare a cikin
mai shegen kamshi na kamfanin Awwaba scent ya miko min.
“Wannan turaren tun da na siye shi ban yi amfani da shi ba, amman dai kanwata ta fada tace yana da kyau sosai”
Ina karbar turaren kamshi ya baibaiye tun kan na bude.
“Yana da dadi?”
Na g
yada masa kai alamar eh sai yai murmushi.
“Miyasa baki son yawan magana ne? Ni fa labari na ke son ki ba ni”
“Labarin me?”
Na tambaya ina dago kai na kalleshi sai ya sakar min murmushi.
“Mi ya kawo ki aikin garin Abuja, maman ki ta saka ki?”
“Aa ni na saka kaina, bata son zuwan nama ma”
“To miyasa kika zo? Kina ganin sha'awar Abuja ne?”
“Mutum ya taba sha'awar abunda be taba gani ba?”
Ya daga kafadunsa.
“Maybe kin san wani idan yana jin labarin gari sai yaji yana sha'awar zuwa
wata rana”
“Ban taba sha'awa ba, ban taba tunanin zuwa ba, ni da bani da lokacin fira ma wa zai ba ni labarin Abuja?”
“Kamar ya kina zuwa makaranta ne acan?”
“Aa na yi karatun primary daga bakin class 4 na daina zuwa har yau”
Kallon yai da mama
ki.
“Mi ya hana ki zuwa”
“Ba komai”
“Ba komai hakan nan kawai zaki ki zuwa makaranta? Ba ki son karatun ne?”
“Ina so”
Shiru yai ya cigaba da tukin can kuma ya kalleni ina ta wasa da kwalbar turaren daya ba ni ya ce.
“Gashin nan na ki na
son gyara kin taba gyara shi?”
“Eh ina wankewa”
“An taba wanke miki a shago?”
“Bari na biya da ke shagon da ake wankewa Ilham sai a wanke miki na ki”
“Da gaske?”
Na fada ina wara ido daman na dade ina sha'awar a wanke min gashi a shago.
“Yes yar fara”
Ya fada yana dariya ni kuma nai murmushi, ban kara ce masa komai ba shi ma be ce min sai dai ina lura da yadda yake ta kallona har muka isa gaban wani katafaren shago mai hotunan mata da gashi irin nawa su da kitso wasu kuma an gyara mus
u ya sauko har gadon bayansu. Sai da ya fara fita sannan ya zagayo ya bude min motar na sauko ina rike da turare sai ya mika hannunsa ya karba.
“Kawo a aje turare har mu dawo”
Ba musu na mika masa sai ya maida kwalbar cikin mota ya rufe motar sannan
na nuna min hanyar shagon da hannu.
“Muje”
Ni ce a gaba shi yana baya har isa bakin kofar shagon, sai ya kai hannu ya bude min kofar na shiga sannan ya shigo shi ma, dukan wadanda suke shagon kabilu ne ba hausawa ba, da yaren turanci yai magana da s
u sai wata ta zo taja hannuna ta kai ni wani kebantaccen daki mai kamar falo an gyara ko'ina kamar kana gida, kujera ta ja mi na zauna gaban wani katon madubi shi kuma ya zauna a kujerar dake bayana ya dauki magazine yana dubawa. Wani garin tawul ta dauko
ta dora min a wuya sannan ta cire dankwalin kaina tana fadin.
“Wow.....”
Har Kamal ya dago ya kalleni ta cikin madubi ni kuma nai murmushi sai shi ma ya mayar min. Sai da ta fara raba kaina gida hudu ta gyara ko wane bangare sannan ta saka na taso da
ga wannan kujerar na koma gurin wata na ta shafa mai.....
Mun kusan awa daya a shagon sannan aka kammala gyaran gashin, kamar wata ba indiya haka na fito gashin kaina ya kwanta irin yadda na indiyawa yake yi, yana ta sheki ni kaina sai da ya burge balle
kuma Kamal da ke ta kallona ba ko kyata ido. Wayarsa ya saka yana ta dauka ta hoto, ita kanta wace ta gyara min gashin sai da ta dauki hoto a wayarta, sannan ya biya kudi muka fito yan matan da ake ma gyaran gashin sai kallon nawa kan suke, domin kowa ya g
a nawa gashin yasan cewa nawa ne ba kamar su da ke sakawa fake ba. Wannan karon ma shi ya sake bude min motar na shiga ya rufe sannan ya zagaya ya shiga mazaunin direba ya tashi motar muka hau titi.
“Kina da kyau sosai Mamana”
Ya fada ba tare daya k
alleni ba, ni kuma na kalleshi ban ce komai ba ya maida dubana gurin titin.
“Har yanzu baki bani labarin dalilin zuwanki Abuja ba”
“Aiki na zo yi"
Na fada ina shafa gashin kaina da ke burgeni ina jin kamar ba nawa ba ne.
“Mu yan asalin yola
ne, fulanin yola ne mu, mahaifina ma'aikacin gobnati ne mai rufin asiri, a hannunsa na taso ina da yayye maza biyu da mace daya ni ne na hudu kuma ima da kanen biyu mata, a unguwar da nake zaune babban yayanmu da Matarsa ne a gidan da kuma Mahaifiyata da k
annena sai dai kowa bangarensa dabam, yayana dan majalisa ne a nan Abuja”
Na kalleshi.
“Ka ce min kai talaka ne ashe ba haka ba ne”
“Yes ni talaka ne kamin yanzu, a lokacin da muke yola mun sha wahalar rayuwa, domin mahaifinmu ya rasu a lokacin d
a muke da bukatarsa, karatu ya so ya lalace sanadin hakan, amman talakawan nan da nake fada min na unguwarmu su suka hada kudi suka komai na makaranta domin suna ganin kimar mahaifina sosai, dattijon arziki haka suke kiranshi, da taimakon da suka min na ka
wo a inda na ke a yanzu, kin ga ko ai dole na san darajar su”
Yana fadar hakan ya faka motarsa gefen titi ya juyo ya kalleni.
“Fada min ke fa?”
“Ni ba yar kowa ba ce, babana ya rasu ina da kane Lukman shi ma ya rasu, daga ni sai Mamana muka rage”
“Ayyah sorry"
Ya fada cikin yanayin da ke nuna tsantsar tausayinsa a kaina.
“Kika ce ke kika kawo kanki aiki a nan miyasa?”Ban boye masa komai ba face zancen cire kodar mahaifiyata shi ma saboda ina tsoron kar Mama Fulani ta ji ne ta koreni dan
sanan ba zata yarda cewar danta ya cirewa mahaifiyata koda ba, sai nai ma Kamal wata karyar da cewar ulcer ce take damun mahaifiyata na ke nema mata kudin magani, tsantsar tausayin da na gani a idon Kamal da fuskarsa ban taba ganinta a fuskar wani mai gani
n tausayina kamar haka ba. Da kansa y ciro tissue paper ta gaban motarsa ya miko min.
“Share hawayenki”
Na karba na share hawayen da suka ki su tsaya min saboda tuna da irin rayuwar da na baro da kuma kalubalen da ke gabana.
“Kin yi kokari sosai
Ataa kin zama jaruma, aiki a titi kula da mahaifiya ba abu ne mai sauki ba ko a gurin babba balle ke da ba zaki wuce 16 to 17 years ba, amman ina yan uwanki ba ki da kowa wanda zai iya kula da ku bayan rasuwar mahaifinku? Ya kamata ace sun kula da mulallin
ku ba su bar ku kuna ta bara ba”
“Ban san inda kowa nawa yake ba, mahaifina be taba firar kowa da ni ba, haka ma Mamana bata taba fada min wani abu daya shafi danginta ko dangin mahaifina ba, iyakar abunda na sani suna nijar”
Ajiyar zuciya ya sauke y
ana ta kallona sannan ya tashi motar ya hau titi muka cigaba da tafiyar, be sake ce min komai ba sai kallona yake har muka isa gida, a bakin gate din su Mama Fulani ya faka motarsa ya mika hannunsa baya ya dauko ledodin da aka saka masa a bayan mota ya mik
o min.
“Ungo wannan na ki ne”
Kin karba nai.
“Aa Mama Fulani zata iya min fada idan ta gani?”
“Ai ni na baki kuma yanzu da na aje motata a gida zan shigo cikin gidan a nan zan ci abinci rana”
Na saka hannu biyu na karba, sai ya saka hannun
sa aljihu yan bandir din dari biyu ya miko min.
“Ungo wannan ki aje mana, za mu fara tarawa kudin maganin Mama”
Kallonsa nai baki a sake sai nai saurin girgiza masa kai.
“Aa ba zan karba kudi ba, idan Mama Fulani ta gani dukana za tai kuma aikin
da nake saboda na tara kudin na ke za su iya idan na tara na wata uku”
“Ba za ki bari ta gani ba ai, boyewa za mu yi ki rika sakawa cikin kayanki, idan mun tara da yawa idan za ki je ganin gida sai a kaita asibitin ko?”
“Mama...”
“Ya isa, komai d
ai Mama Fulani zan mata magana ta daina takura miki”
“Aa dan Allah ka rufa min asiri wallahi zata iya dukana ma”
“To karba ki aje, karki bari ta gani sai ki boye abun ki ai”
Babu yadda na iya bayan karba domin ni ma kaina na san ina da bukatar kud
in, dan haka na saka hannu biyu na karba cikin tsoro da firgice har na manta ban masa godiya ba, shi ya fara fita cikin motar ya zagaya ya bude min ya fito sannan ya rufe motar, wani abun da ban sani ba ashe Aliyu yana tsaye bakin gate din yana kallonmu am
man ni ban lura da shi ba har sai da na ga Kamal yai murmushi ya daga masa hannu.
“Sannu dai Aliyu”
Sannan na koma cikin motar yaja abarsa zuwa gaban gate din gidansu ya danna horn aka bude masa ya shige ciki. Ina tsaye a inda ya aje ni ina kallon A
liyu da ke tsaye daf da gate din yana watso min wani kallo mai ban tsoro fuskarsa a hade kamar bakin hadari, tsakanin jiya da yau Allah ya saka min tsoronsa duk wani fitsara da nake jin zan iya masa sai na ji yai min kwarjini har na gagara karasa gurin gat
e din na shiga shi kuma yai tsaye a gurin yana ta kallona kamar daman can dan kallo kawai aka halliccesa. Ganin ba zan zo ba yasa ya juya ya koma cikin gidan, yana wani irin taku na masu karfi da kuzari. Sai na tabbatar ya shige ciki sannan na nufi gate di
n na tura kofar na shiga, sai na ganshi tsaye da alama ni yake jiran na shigo ni kuma nai tsaye a gurin dayan hannuna da kudin dayan kuma da ledodin.
ALIYU POV.
Tun ya bar gidan Mama Fulani ya saka samun sukuni da walwala a yadda yake, zuciyars
a na ta raya masa Muhseen zai iya cutar da Ataa, ya san Muhseen ba dan iska ba ne, amman ai ba a shaidun mutum a yanzu, kuma yadda Ataa take da kyau zai iya rudarsa ya jefata cikin wani halin, wanda yake da tabbacin shine silar komai tun da shi ne silar ci
re kodar mahaifiyarta har ta zo aiki a gidan, idan kuma wani abun ya same ta ai duk shine sila, dan haka ba zai bari rayuwarta ta lalace ba, ba zai taba yarda ta rika kebewa daga ita sai Muhseen ba, daman can tsakanin shi da Muhseen basu taba shan inuwa da
ya ba, saboda Muhseen yana jin haushin yadda yake da jin da nuna isa da dakama, shi kuma yana jin haushin yadda Muhseen yake da sakewa da mutane. Daga gidan Mama Fulani ya nufo gidansa cikin bacin rai, duk yadda yai kokarin ya kawar kar Rahma ta fahimci ya
na cikin damuwa sai ya kasa, in every minute sai ya ji kamar wani abun ne zai samu Ataa duk kuwa da yasan be barta mugun guri ba amman ya kasa natsuwa da zamanta a gidan tsakanin jiya zuwa yau.
Rahma kallonsa take har ya shigo cikin falon ya karaso kusa
da ita ya zauna yana matsa kansa alamar yana masa ciwo.
“Lafiya dai, na dauka sai nine zaka dawo gida idan mun ga Doc Perry?”
Kissing dinta yai sannan na kwantar da kansa jikin kujerar ya lumshe ido na wani lokacin sai kuma ya ciro wayarsa yai danne
danne ya tura mata. A take sakon ya shigo wayarta da sauri ta dauki wayar dake gefenta ta duba.
“Za mu iya bari zancen Doc Perry for now? Bana son zuwa gurinsa”
Kallonsa tai bayan ta gama karanta sakon.
“But why? Wata kila ma mafita ce ta zo man
a, waya sani ko waraka ce”
Dagowa yai ya zauna daidai yana kallonta.
“Rahma akwai abunda ban taba fada miki ba, ban so wannan maganar ta fito daga bakina ba, amman ban san iya lokacin da zan yi ta aje ta ba”
Kara matsawa tai kusa da shi da maida
hankalinta gurinsa tana kallonsa kunnuwanta cike da kwadayin jin ko mienene daman yau ta fahimci yana cikin damuwa.
“Minene Aliyu akwai wata matsala ne? Fada min”
Wani dogon numfashi yaja ya sauke ya shafa fuskarsa cikin yanayin da ke nuna yana cik
in damuwa, daman kuma a cikinta yake.
“Rahma ban sani ba ko zaki fahimta, ban san yadda za ki kalli abun ba, kuma ban san yadda za ki kalleni ba”
Saurin kama hannunsa tai.
“Fada min kawai Aliyu minene matsalar?”
“Rahma duka tsawon lokacin da m
uka dauka matsalar daga ni ne..”
Da sauri ta rufe bakinta sai kuma ta girgiza masa kai hawaye na cika idonta.
“Ba daga kai bane Aliyu sun ce ba mu da matsalar komai ba daga kowa ba ne, suna cewa za mu iya haihuwa a duk lokacin da Allah ya kaddara”
“Na boye miki ne saboda bana son ki damu, amman maganar gaskiya matsalar daga ni ne, a duk inda muka je ina sakawa likitocin