Showing 198001 words to 201000 words out of 237425 words
nufi dakinta, zazzabi ne ya rufe ta gaba daya yamma cin batai shi da dadi ba, da ada ne da yanzu ta fara kiran Momy da duk wani makusancin da labarta masa abun dadi da murna ya sa
mu amman yanzu babu wannan damar, da dare ma kasa runtsawa tai tana son ta kira Aliyu ta yi magana da shi amman tana jin nauyi saboda ta san yana tare da Ataa, kuma tai ta jiran ya kirata be kirata ba har garin Allah ya waye.
Misalin bakwai na safe ta
na zaune saman carpet din da tai sallah kasancewar jiya da yau ba ita ce da girki ba Ammy ce, Nana kuma ta kwana a bangaren Ammy, ban da Maryam da Rukaiya babu wanda ya san bata jindadi domin Muhseen be shigo gidan ba gaba daya tun da ya ga Ataa ta zo ya s
ake fita be dawo ba. Wayar Aliyu ringing biyu ya daga da far'asa yai mata sallama.
“Assalamu Alaikum”
Ta amsa mishi da muryar mai karantar da shi damuwarta.
“Aliyu kana tunanin ba zan yi farinciki da samun cikin ba shiyasa baka kira da kanka ka
fada min ba?”
“Wallahi ba haka ba ne Mama Nasir ne ya ce kar nai rashin kunya na bari zai kira ku ya fada muku amman ba dan wani abu ba”
“Aliyu yadda na ke son ka haihu ko da karuwa ce ta samu ciki da kai zan yi farinciki, saboda na ce bana son Ataa
ba shi yake nufin bana son abunda zata haifa maka ba, ita ma kuma da na san da zuwan wannan abun da ban aikata mata komai ba, ina jin kunyarta da na mahaifiyarta na abunda na aikata musu, amman Wallahi ba zan taba kin jininka ba ba zan taba tsana ki nuna k
yama a gurin abunda Ataa zata haifa maka ba, ko da ko ace gaskiyar wacece ita be bayyana ba”
Tana gama fadar hakan ya kashe wayar tana hawaye.
ALIYU POV.
Damuwa ce shimfide a fuskar Aliyu, yadda ya ji muryar Mama Fulani abun be masa dadi ba, y
adda baya son wani abu ya dami Momy haka baya son abunda ya taba Mama Fulani.
“Minene?”
“Mama ce, bata jidadin yadda na sanar da Nasir zancen samun cikinki ban sanar mata ba”
Ataa ta aje mug din dake hannunta na tea da ya hada mata tun da azuba t
ana kallonsa.
“Bata jidadin na samu cikin ba? Ko kuma saboda ni ce na samu cikin yasa ba ta jidadi ba?”
Matsowa yai da ita kusa da shi.
“Mama tana son cikin nan, ko da ko ke ko wata ce wadda ta fiki talauci, ko kuma wacce ta fiki arziki, saboda t
ana son farincikina, kuma tun kamin Momy ta fara damuwa da rashin haihuwa ta, ita ta fara min zancen karin aure kamin Momy, Mama Fulani bata son wani abun da zai taba ni ko kadan, shiyasa ko a wacan lokacin da na ake fada mata cewar ni ne da matsalar ba Ra
hma sai ta nuna damuwarta kuma ta nuna min na kara aure idan ban haihuwa sai a barwa Allah ko kuma a cigaba da neman magani”
“Kana da wata matsala ne?”
“Ba ni da wata matsala, Rahma ce mai matsala domin kwa haihuwa baya iya zama a cikin mahaifarta, a
mman sai na boye mata, da farko wace na ke ni d ita duka ba mu da matsala sai na biya likita kuma na roke shi ya fada mata haka, saboda kar damuwar tai mata yawa, ga ciwonta kuma idan ta ji bata iya haihuwa abun zai nata yawa, daga baya na maida abun kaina
na ce mata da kowa cewar ni ne mai matsala ba ita ba, saboda Nasir ya ba ni shawarar yin hakan”
“Amman Aliyu miye alakar da Mama Fulani? Na san Momy ce ta haife ka”
“Momy ce ta haife ni tabbas, amman a hannun Mama na girma, Mama Fulani da Momy amin
an juna ne tun a makaranta a lokacin Mama Fulani tana Yola kasancewar ta yar can, Momy kuma yar sokoto amman sai suka hadu a ABU zaria gurin karatu a daki daya suke komai tare suke kamar yadda na samu labari, Daddyn dan'uwan Momy ne Cousin brother dinta ne
ta gurin uwa, tun tana makaranta ta fada min wani lokacin a sokoto suke hutu ita da Mama Fulani, wani lokacin kuma a yola suke hutu gidansu Mama Fulani, after sun gama makaranta aka saka ranar aurenta da Daddy, a gurin bikinsu ne Abbah wanda yake kanen ga
Daddy ya ga Mama Fulani har ya fara sonta har Allah yai abun ita ya aureta, a sokoto suka zauna dukansu a wacan lokacin shiyasa a lokacin da Momy ta haife ni na isa yaye sai Mama Fulani ta yayeni, daga nan Daddyn ya samu aikin wannan kamfanin suka dawo a
nan Abuja sai ta dawo tare da ni, kawaici irin na Momy ya sa ta kasa cewa a bata danta domin har tsawon lokacin da na fara wayo Mama Fulani bata samu ciki ba, sai daga baya aka haifi Muhseen daga shi kuma sai ta dade kamin ta sake haihuwa wanda hakan yasa
Abbah ya auro Ammy, sai kuma haihuwar ta zo mata daga baya su kai ta yi tare da Ammy. Mama Fulani ta rike ni tsakani da Allah bata bari wani abun ya same ni ko nai kuka duk wani abun da nake so shi take min, kina da idonki idan wani abun ya shiga tsakanina
da Muhseen ni take ba gaskiya, ko da shi ne da gaskiyar, bata taba yarda yaranta su rainani shiyasa na taso bana sake musu fuska saboda kar su raina ni din, har abun ya zame min jiki, kowa a gidan yana saunata ko yin wani abu a gabana ciki har da shi Muhs
een din, hakan yasa ba mu jituwa da shi, ba ma san inuwa daya bama fahimtar junanmu, saboda shi yana ganin ina akan kuskure abubuwan da na ke yi ni ma kuma ina ganin yadda yake sakewa yana wasu abubuwan basa burgeni, a ciki kuwa har da tsanar talaka wanda
na samu asalinsa daga gurin Mama Fulani, ban taba daukar cewar abunda Momy da Muhseen suke nuna min abu ne mai kyau ba sai haduwa ta da ke”
Yayi shiru sannan ya rumgume ya sumbaci saman kanta.
“Na san ba za ki taba son Mama Fulani ba, amman zan jida
di idan kika aje kiyayyarta a zuciyarki ba tare da kin nuna mata a gabana ba, Mama Fulanu tana da muhimmanci da daraja da kima a gareni wanda Momy ma ba zata so ki wulakantata ba, Mama tana son cikin nan ko da ko bata so ki ba saboda cikin jikinki nawa ne,
tana jin kunyarki da mahaifiyarki da tasan da zuwan wannan abun tace da bata aikata miki komai ba”
“Miyasa sai ni Aliyu? Wata kila da asalina be bayyana ba, da har yanzu Mama Fulani ba zata ce tana jin kunyata ba, ko ba ni ba ko wane dan'adam mai daraj
a ne Aliyu, idan babu talaka wallahi masu kudin ba za su iya rayuwa ba, da babu talaka fada min wa zai zo gurinta nema har ta gane cewar tana da arzikin? Wa zai gina mata gidan da zata zauna? Wa zai tuka mata motar da zata hau? Wa zai mata wanki da guga da
gyaran gida ko na sani abun idan ya kama? Wanda ba shi da jinkai yake so da kauna da tausayi ba kyara da tsangwama ba, abun Alfarinka ne ace yau kana da abunda zaka iya dafawa ka bawa wani ko kuma ya taimaki wani a cikin taimakon da Allah yai maka, tarin
dukiya ba abun alfahari ba ne tarin imani da yawan taimako da kyakkyawan aiki shine abun tinkaho da bugun gaba, ranar lahira a wareka a bainar jama'a a karramaka akan aikin alherinka shine abun jindadi, ba a tsare ka ana tuhumwar ka da daga inda ka samo du
kiyarka ba kuma taya ka kashe ta? Wa ka zalinta da ita waya amfana da ita? Wani aiki kai ita saboda Allah? Aliyu ya zaja ji idan Allah ya tsayarda Mama Fulani a gabansa ya tuhumeta akan zalincin da tai na wani ko musgunawa saboda ita tana da dukiya shi ba
shi da ita ba? Wanda ya baka dukiyar da kansa ya tambayi ka dalilin wulakanta wani saboda abunda ya baka shi ya hana shi? Miyasa ba zaka fada mata gaskiya ka nuna nata abunda take ba daidai ba ne? Talaka kan kaurai zai dade da shiga mai kudi yana can yana
amsa tamaboyoyin dukiyarsa, ashe ko dukiya da zata saka ka fadin rai da wulakanta wasu ba abun tinkaho ba ce matukar ba ta taimakon bayin Allah ce da addininsa ba”
ATAA POV.
hawaye na ke yayinda na ke maganar ba da Mama Fulani kadai na ke ba, har da
Aliyu na ke domin shi ma rayuwarsa kenan kamin yanzu, da kuma duk wani mai halin irin nasa. Yadda na ga jikinsa yai sanyi sosai ya karantar da ji cewar sakona ya isa a inda nake son isar da shi domin hawaye na gani a idonta yana ta kallona.
“Na gode A
llah daya bani mata kamar ke, yarinya ce ke amman mai hankali da natsuwa da hangen nesa, ina son ki ina son abunda cikin cikinki”
Ya fada yana murmushi. Hannu na saka da kaina na share masa hawayen na rumgume shi da kaina ina jin wani irin dadi marar mi
saltuwa.
RAHMA POV.
Kamar yadda ta yanke shawara samun Daddy ta ta fada masa cewar zata koma dakin mijinta sai ta fara samun Mommy da zancen a lokacin Mommynta na jimmamin al'amarin da Daddyn Rahma ya fada mata a waya wanda ya hana shi dawowa.
A jiya kamar yadda yai alkwari.
“Mommy ba ki ce komai ba”
“Mi zan ce Rahma? Anya ma Aliyu zai kalleki ma yanzu kuwa?”
“Me kike nufi?”
“To ya samu wacce ta fiki komai”
Raham ta saki baki jin irin maganar da mahaifiyarta take da kanta.
“M
ommy ke da kanki kike fadin wannan maganar? Ko kin manta wacce Aliyu ya aura ne?”
Mommyn da juyar da fuska cikin damuwa.
“Bana son fada miki abunda zai zame miki tashin hankali ne”
“Minene dan Allah fada min”
“Kin san sarkin Agadaz wanda ya zo
?”
Rahma ta gyada kai cike da son sani.
“To kakanta ne, duk uwar dukiyar da muke tinkaho da ita ta gidansu ce, ke kiji wani al'amari”
Rahma ta girgiza kai.
“Mommyn kin gane me kike fada min kuwa?”
“Aifa sai ki yi, yanzu haka Daddynku na ca
n gurin sarki ya fada min ya sha kuka jiya har idonsa ya kumbura saboda Ataa ta fadawa Mai Martaba abunda mu kai musu”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u Innalillahi La'ilaha illallahu Muhammadu Rasulullah Sallalahu Alaihi Wassalam, jama'a Mommyn da gas
ke ko karya? Taya to taya how how how Mommy”
Ta fashe da kuka ta mikewa tsaye sai Mommyn tai saurin riketa.
“Ke ke saurara kwantar da hankali”
“Taya zan kwantar da hankalina Mommy fada min taya ya zama kakanta taya? Wallahi hakan ba zai yiyu ba, s
ai dai idan wata Wallahi ba ita ba”
Zaunar da ita Mommyn tai ta jera mata komai dalla dalla kamar yadda Daddynsu ya fada mata a waya domin ya fada mata cewar ba zai dawo da wuri ba sai Mai Martaba ya koma da ko rakiyarsa kawai zai yi Abuja ya dawo.
“Wayyo Allah na na shiga uku Mommy mutuwa zan yi yau, wayyo zuciyata wayyo kirjina wayyo raina”
Faduwa tai kasa tana da kuka da ihu kamar an mata mutuwa. Gaba daya yan'uwanta sai da suka taru a dakin suna ta jimamin al'amarin gaba daya abunda suke tunan
i Mai Martaba zai iya kwace duniyarsa daga hannun Daddyn gaba daya cikinsu ya duri ruwa. Haka Rahma ta kwana ta wuni tana da aikin kuka da tunani kala kala ada ya tsara yadda za tai zaman kishi da Ataa saboda tana yar talakawa to yanzu kuma ba ta san irin
zaman da zatai ba.
Washe garin ranar da Daddyn ya dawo duka suna zaune falonsa dukansu suna cikin damuwa har shi domin Mai Martaba ya kama hanyar zuwa jigawa tun jiya ba tare da shi ba, kuma be ce komai akan abunda Ataa ta fada am mata ba, shine abunda
yakr ta ba Daddyn Rahma tsoro.
“Ni wannan abun har mamaki yake ba ni, abu kamar a mafarki”
“Ai ba ki san a mafarki ba sai da yarinyar nan ta fara fadin abubuwa a gaban mai martaba kaina kamar ya tsare, kunya ta rufe ni ai ban san lokacin da fashe d
a kuka ba”
Cewar Daddyn Rahma bayan Mommyn ta fadi nata.
“Baku tunanin abun nan zai min yawa da kuke ta maganganun nan a gabana? Tun da na tashi lafiya bata isashe ni ba, ga auren da Aliyu yai yanzu kuma yarinyar nan azo ace wai cikin dukiyar gidans
u muke rawa da tumami, haba Daddyn haba ba a kyauta min ba”
Ta fashe da kuka, Ikram ta ce.
“Haba Rahma ya za ki yi da ikon Allah? Kullum idan ina fadar cewar abunda ake a gidan nan ba a kyautawa tun daga kan mijinta da kuke biyeta tana juya shi yadd
a ya zo da kuma yadda kuke yi ma mutane sai kuna ganin laifina kuna ganin ban kyauta ba ko kuma ni ban gane kan dawon garin ba, yanzu ai wa gari ya waye? Tsakani da Allah Rahma ciwon nan na ki tsoron Allah ya kamata ya Kara miki, ciwon kadai ya isa ya sak
a ki fahimcin cewar dukiyar ba komai ba ce tunda ta kasa baki dauwamammiyar lafiya ko ta hana ki ciwo ko mutuwa, wani yana can da talaucin amman lafiyarsa kalau hankalinsa kwance yana cikin farinciki”
Mommyn ta daka mata tsawa.
“Haba Ikram yar'uwark
i kike fadawa wannan maganar? Ba zaki barta ta ji da abunda yake damunta ba?”
Rahma ta mike tsaye tana hawaye ta nufi dakinta, saman gadon ta fada ta kwanta tana wani irin kuka kamar ranta zai fita, tana jin wayarta na ringing ta ki ta daga sai da ta sh
a kukanta ta koshi sannan ta shiga bathroom ta wanke fuskarka ta fito idonta sun yi ja sosai kanta har wani haukan ciwon yake. Wayar ta duba ganin number Aslamiya matar Nasir yasa ta kira ta tasan ba zai wuce ta labarta mata cewar ubangidan Daddyn kakan At
aa ne ba.
Sai dai a lokacin da ta dauki wayar bayan sun gaisa sai labarin ya sha banban ta labarta nata cewar Ataa na da ciki. Wani irin abu Rahma ta ji kamar tana zaune a saman kaya, ta mike tsaye sai ji tai dakin na juyawa mata bata san lokacin da wa
yar ta subuce daga hannunta ta fadi kasa ba, cikin jirin ta fara takawa ta nufi kofa tana fadin Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, so take ta fita taje gurin da sauran yan'uwanta suke kar ta rasa ranta a dakin ita kadai. Kamin ta kai kofar ta fadi kasa ta
kwala wani irin ihu sai numfashinta sama-sama. Jin ihunta yasa kowa ya taso da gudu suka nufo dakinta.
*Allah ka ba mu ikon yin domin ka. Bari domin ka, k'i domin ka, so domin ka. Wanda duk be ji tsoron hakkin wani ba kuma be ji tsoron Allah ba Wal
lahi ya yi aikin banza. Allah ka raba mu da aikin dana sani, ka doramu a daidai alfarmar Annabi Muhammadu Rasulullah Sallalahu Alaihi Wassalam*
6k Words
😲
Kun sha karatu har kun gaji.
*Littafina na kudi ne, biya duniya ko kuma inda mutum be da su
indai rubutun nan hakkina ne. *Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
*Ina mata son rage kiba? Ina mazan da kiba ta hana su sukuni? Ina masu jikin yai kyau kamar na yarinya? Ina masu fama
da kujera ko wani ta bo a fuska? Ina masu fama da hawan jini? Masu diabetic? Ag cera an gwada yayi an tantance ingancin babu shakku ko kadan. AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama w
adanda suke hana garkuwan jiki aiki yadda ya kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta.*
*Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su.
Haka ma cutukka irin wadanda suka shafi fatar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin ji
ki wajen kwanciya da iyali da kuma mata masu fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a
wannan number +60167474649 ko kuma ku ziyarci shafin mu http://agnutritioninternational.com.*
A lokacin da ya shiga wanka ni kuma sai na dauko tsintsiya na share dakin lokacin da na fito da sharar a falo sai gashi ya fito daure da tawul a jikina ya tsaya
bakin kofar dakin yana kallona. Nima kallonsa nai ganin be ce komai ba yasa na ce.
“Har ka gama wanka ne?”
Be ce min komai ba sai ma kara hade fuska da yai, tunani na tsaya na san dai kamin ya shiga wanka ban masa wani abun ba, kusan ma tun da aka da
ura mana aure Aliyu be