Showing 3001 words to 6000 words out of 20825 words

Chapter 2 - YAR QAUYE KO YAR BIRNI COMPLETE

gun kasuwa

Inasan dukiyata takaita gashi nasamu cikin sauqi

Lantana tace wlhi itace Larai nima yakubu yace inyadawo zaiban ita

Tace Allah ya kawo shi

Haya gagan dakeyi shiya fito dasu hassana da mairo matan qannan baban Nafisa

Kae Larai kina ca6awa yarinyarnan tana kawo miki azziqi dama nice inji hassana

Mairo tace bani ingani

Larai tace aiwannan dubun hannun Masu qashin harziqi take zuwa. Bakeba

Nan mairo taja gefe dan tasan Larai tas Ba mutuncine da itaba

Duk da Nafisa tabata muhimmin ku'di saida ta rankwasheta

Abin baqinciki sae yanzu zatayi sallar asuba

Nan Nafisa tashige gun babanta tana jiran Larai ta dama koko tafita talle Dan Allah Allah take tafita dan taqara ganin MARWAN da Amar

πŸ’—πŸ’“πŸ’—

'YAR QAUYE KO 'YAR BIRNIπŸ’—πŸ’“πŸ’—

Har Nafisa tasiyar da kokonta bataga Su MARWAN Ba

Ahanyarta tadawowa ne tayi tunanin shiga gun Hajjiya wato agidan megari

Da sallama tashiga

Hajjiya dake alwala ta'amsa mata cikin fara'a tace

Kaga nafisatu yau ansiyar da koko lpy ko

Tace eh nazoma ganin larabawan nanne

Hajjiya tace suwa kenan

Tace Su ambar

Yanzu Hajjiya tagane suwa take nufi

Yayi murmushi tace

Suna 'dakin Adamu

Da sauri tature tiran tallan tafallah da gudu 'dinkin Adamu

Hajjiya tabita da kallo tana addu'ar Allah yasa Amar yasota danko tunanin MARWAN batayiba

MARWAN da Adamu suna hirarsu ta'yan uwa

Amar na'dakin amma Sam yaqi kulasu wae adole fushi yake da MARWAN

Har fushin yashafi Adamu

Saiji kawae sukaji ana kwankwasa kofa

Adamu yace waye tace nice Nafisa

Tunanin Adamu ko Hajjiya CE taturota shiya shi cewa to kishigo

Tamur'da kofar taqi buduwa. Dole sanda yatashii yabu'de mata

Bajin ko 'dar taratsashi tahuce tazauna kan kafet Adamu yabita da kallo

Tace sannunku

Amar yace yauwa sannu Nafisat

Tace wae meyasa kuke canjamin suna ne.

Cikin 'dan waro ido ka'dan Amar yace

Waya canja miki suna

Tace kaga Hajjiya nacemin Nafisatu kae kace min Nafisat

Wannan tanuna MARWAN Wanda tunda tashigo yake kallan yana kissima abubuwa da dama acikin ranshi

Yana kirana da FEENAH

Amar yace to wanne ne aciki yafi miki da'di tace FEENAH

Yace gud kinza6i Wanda yadace tace

Yauwa nasan FEENAH yafi da'di yace hakane.

Yauwa baba Larai tadakeki kuwa

Tata6e baki tace rankwashina kawae tayi

Dan naci darajar kudin dakaban yace Allah.

Tace wlhi

Yace yanzu me kikazo yi tace nafito tallene shine da nasiyar nace sae nazo naganku

Yace ayya sannu FEENAH mungode sosae tayi dariya tace kaima kadena cewa Nafisat ne yace eh tunda naga kinfisan FEENAH tace to ai kae Nafisat yafi da'di abakinka yace ko tace eh yace to kinfisan ya MARWAN yakiraki da FEENAH tace eh dan abakinshi yafi da'di

Da sauri Amar da Adamu suka kalli MARWAN

Amar yace am sorry Yaya kakar6ita plx

Adamu yace wae ya'ayi kukasan Nafisa

Tace jiya suka sanni

MARWAN yaja tsaki

Quri Nafisa tayi mishi da ido tana cewa

Me yasa meka kake tsaki yadalla mata harara yace bansani Ba

Cikin rashin damuwa tace aidama kae da ganinka zakayi fa'da

Zaiyi magana Amar yayi saurin cewa tashi muje inrakaki takama baki tace yauzan zama abin kallo aqauyan nan

Yace meyasa

Tace saboda zanyi tafiya da balarabe

Dariya yayi yace to tashi muje tatashi sukafita.

MARWAN yaqayin tsaki Adamu yace yayane yayah yace

Kaduba shashanci irin na yarannan wae saidae Lalle na auri yarinyarnan

Cikin mamaki yace

Haryaushe kuka santa dahar zaima maganar auranta yace ohofah

Hajjiya ganin Amar da Nafisa sunfito sae abin yabata Shaw'awa tace yadae

Yace zan rakata gidane tace to saikadawo suka fita

Suna tafiya Nafisa tace gaskiya kanada Kirki yace ko

Tace eh

Yace kidena lefin da za'adinga dukanki kinji tace to dae dae nan suka iso

Yace toni natafi tace sae Naji banasan rabuwa dakai yace ko tace

Allah yace kinga dole murabu dan gobe ma zamu tafi

Ta waro ido tace zakuta gobe shikenan bazan qara ganinku ba yace eh

Tace dan Allah karkata kae

Yace dole natafi nafisat dan inada karatu.

Sae dae inzaki bimu

Tayi dariya tace

Yaushe zanbiku nabar babana

Kumama baba Larai bazata bariba

Yace to in babanki yace kibimu zaki bimu tace eh zanbiku amma sae dae inza kusani a makarantar boko

Kuma innaga babana ya warke

Yace OK nina tafi

Ta'daga mae hannu

Yatafi Yana murmushi

Koda Amar yatafi zuwa yayi ya'ibi ku'di tare da 'daukar mota

Ba'inda yasauka sae gidansu Nafisa

Yace ma babanta yazo yakae shi asibiti ne

Dan aduba lafiyar Sa

Baba yayarda Amar yatafi dashi

Lokacin Nafisa tafita tallan shinkafa da wake

Baba Larai kulewa 'daki tayi Dan acewarta Amar ba mutun bane

Sunji asibiti anduba baba antabbatar da ciwan da yake daminshi

Sunce hawan jinine amma bae shiga jikinsa sosae danhaka zasu bashi magani yasha natsawan wata 'daya

Nan Amar yakar6a mae maganin suka tawo

Akan tanyarsu tadawowan yasiyama baba katifa da kafet tare da situru.

Baba sae samishi albarka yake

Haka suka dawo gida

Yasa yara suka kwashe tarkacan 'dakin suka saka kafet da katifar. Sannan yamae da baba 'dakin

Yanata samae albarka

Yatafi

Nafisa CE Mae tafiya kan hanya tanata wawakenta tana tsalle tasan yau baba larae zata bata abinci taci San ranka dan tasae da shiinkafa da wake

Ke Nafisa ke Nafisa

Taji qawarta Fatsima na kiranta

Tatsaya tana dariya

Fatsima tace naganki sae murna kike ko kinsiyar da abinci ne tace eh nasan yau zanci abinci na qoshi

Tace hakane fah

Kinsan meye tace aa

Wae ya'u ne yake suna za'amana aure dashi

Tace Lalle kice zandinga zuwa gidanki muna shan hira tace

To aini bana sanshi kwata kwata

Tace to wakike so tace bakowa

Tace tab kinajin da'dinki ne shiyasa

Dae dae nan sukazo wuccewa ta wani lungu

Aifa sae sukaga

Lanta da yakubu saurayinta suna iskanci.

Kasan cewar Sam mutane basu damu da sama lungun idoba shiyasa har za'ayi abu alungun agama mutane basu ankare Ba

Yakubu yadanne lantana yata iskanci da ita.

Nafisa tace lantana me yakubu yake miki

Nan suka tsaya da jan kaya

Lantana tace bansani

Kuma wlhi kika fa'da sainaci ubanki kema Fatsima kifa'da kisani.

Fatsima tace saina fa'da 'din aini ba Nafisa bace nasan abunda kukeyi itace bata saniba

Tace to kifa'da inci uwarki

Tace kici uwarki Larai dae

Taja hannun Nafisa sukabar gun

Nafisat tace iskaci sukeyiko

Tace eh man

Nafisa tayi mamakin ganin 'dakin babanta fes tatan baye shi yagaya mata komae

Nan tahau murna

Su hassana da mairo ma suna santin 'dakin amma baba larai cewa tayi bazata shiga 'dakinba Dan 'danshan jinine Amar

Nafisa tace jikokin me garine fah Babah

Babanta yace shareta Nafisa

Larai tace eh tasherenin sae me kwa'dayayye kawae yace nine kwaa'dayayye tace kai'dinfa yace Lalle rashin mutunci nake yakai inda yakai

Tace har ya hucce

Yace wlhi Larai kikiyayi ranar dazan tashi

Tace ai'in Allah yayarda bazaka tashiba haka zaka qare rayuwarka

Bae kulata ba

Dan kallan mahau kaciya yake mata

Nafisa tace kayi hakuri baba yace Ba komae kidae kidinga min Addu'ar Allah yabani lpy tace to Allah......

Bata qarasaba taji am maka duka da takalmi abayanta.

Qara tasake tare da miqewa agigice

Baba Larai CE

Tace harda cewa yayi hakuri yarinya dake kin'iya makirki

Tace kiyi hakuri

Tace zoki 'dau cincin kifita

Nan ta'dauka tafita tana kuka

πŸ’—πŸ’“πŸ’—

Washe gari Su MARWAN sun gama shirinsu natafiya

Amar yace kakale baqo zaiyi halinsa tace wlhi bansan rabuwa daku

Yace to ya za'ayi dolene ai

Kinga ana leman yah MARWAN gun aiki.

Nikuma karatu

Tace to kugae damin da kowa.

Naha'dama Momyn taku kayanta suna mota

Amar yace kae matarnan yanzu zaki cikamana ciki da warin daddawa

Tace eh jiyama kacita ai yace inani inacin daddawa

Nan suka rabo cikin jin da'di

Akan hanyar sune Amar yayi parking kofar gidansu Nafisa

MARWAN yace lpy.

Yace kayi hakuri mushiga gidan kugaisa da baban nata tunda yanemi alfarmar hakan

Baice komae ba yafito daga mortar

Amar ya kunkusa kofar gida.

Nafisa na wanke wanke baba Larai tace ke jeki duba kiga waye

Tace to.

Ganin datayi Su MARWAN ne shiyasa koma da gidu cikin gidan

MARWAN yakalli Amar shima yakalle shi

Yace tunda takoma sae mushiga mutafi ko

Amar yace ila taje gayama....

Bae qarasaba sae gata

Tace ina kwananku

Amar ne ya am'sa

Yace kinfito kuma kinkoma da gudu tace

Naje gayama babane kunzo

Yace kushigo.

Nan suka shiga

Taje taci gaba da wanke wankenta

Baba Larai bata guduba wannan karan ba amma ta la6e kofar 'dakin tana sanjin me za'a fa'da

Baba ya musu sannu da zuwa

Suka gaida shi.

Yace nagode sosae da temakwanku garuni da 'diyata

MARWAN yace bakomae

Amar yace dama zamu koma gidane yanzu yace ayya kano ko yace eh

Yace yanzu ku yaran Abdallane suka eh

Yace ikwan Allah

Allah ya albarkaci rayuwarku

Ameen MARWAN yace

Baba yace yanzu yaushe zaku da'da dawowa Amar yace ai sae kunganmu kawae

Yace Allah yasa muqara ganin juna sukace Ameen

Baba ya tsaida kallanshi akan Amar yace dama inasan rokwan alfarma agunka. Yace to inaji.

Yace inbazan takura kaba inasan ka Auri Nafisa dan tunda naganka naji kashiga raina kae da 'dan uwanka.

Nasan Kaine zaka riqe Nafisa amana

πŸ’—πŸ’“πŸ’—

'YAR QAUYE KO 'YAR BIRNIπŸ’—πŸ’“πŸ’—

Tarine Yakama Amar bai shiryaba yayi saurin kallan MARWAN yaga yana murmushi alamar irin yashiga annu

Murmushi shimah yayi yace ai baba ya MARWAN yarigani shine yakesan Nafisa yanzuma munzo wajankane da magana

Tab....

MARWAN yace azuciyarsa amma Sam bae yarda ya'dago kansaba

Da murna baba yace ato aishi kenan wlhi nabaka Nafisa halak malak

Idan naji sauqi zanje gun megari da kaina

Amar yace basae kasha wahalaba zasuzo da Kansu

Yace to Allah ya kawosu

Yace Ameen

Nan Amar yace to zamutafi

Yace to Allah ya kiyaye hanya

Ya ajiyemae ku'di yana cewa kakula da shan maganin insha Allah zaka miqe

Yace to nagode sosae Allah yayi albarka

Yace amin

MARWAN yayi mamakin yanda dazasu fita yabi Nafisa dakallo

Itama tayi mamaki

Amar yayaficuta da hannu

Nan tsame hannunta

Tabiyosu

Kuda tafito wajan tuni MARWAN yashige Mota.

Amar yace zamutafi tace shikenan bazan qara ganinkuba

Yace aikinzama tamu tace meyasa kace haka

Yace haka kawae

Tace to yanzu yaushe zaku dawo

yace ila

In baba yagama yagama shan Magani

Tace to Allah yakiyaye

Taleqa cikin mutar tace ya MARWAN Allah yakiyaye

Da Saudi Amar yajata

Dan yasan ka'dan da aikin MARWAN ya falleta da mari Dan yacika yayi fam qiris yake jira ya fashe

yace munyi latti Nafisa

Tace to ai banyi sallamah da ya MARWAN Ba yace kunyi saikin gamu yafa'da yanamae shigewa motar yafigeta

Tabi motar da kallo Allah yasani bataso tafiyansu Ba.

Gashi taso MARWAN yayi mata magana dan tanajin da'din muryar shi sosae

Sam amota MARWAN bae kula Amar Ba

Todama Amar 'din yasan bazae kulashi Ba amma yana tsoran shurunsa

Sun isa gida lpy lau

Suka samu Momy da dady suna hira afalo zainab na game a laptop

Da gudu tazo tataresu tana cewa oyoyo ya MARWAN oyoyo ya Amar

Cikin fara'a sukace oyoyo my sis

Momy tace sannunku kunsha hanya

Amar yace wlhi

Dady yace to sannun Ku nasan kan kuqara zuwa garin sae kun'dau shekaru

Amar yakalli MARWAN qasa qasa yace

Ai dady zamu koma nanda wata 'daya

Cikin mamaki momy da dady suka kalli Amar dan sunsan koka'dan basasan zuwa qauyan

Momy tace to Allah dae yasa lpy

Yace lpy Momy alkairine

Yayane yayi mata a can

Momy takalli MARWAN tace wae haka

Gamamakin Amar sae yaji yace eh

Daka tsalle zainab tayi tana murya tace

Allah nagodema ma

Kae I luv u ya MARWAN naji 'dadi

Dady yace masha Allah 'yar gidan waye

Amar yace wae 'yar Malam shehu

Dady yace Malam shehu Malam kae ban ganeshi Ba

Yace yanadafa 'ya Nafisa amma mamanta tarasu tun tana qarama

Dogon tunani dady yayi can yagano Malam shehun yace nagane shi

To Allah yasa matar alkairice agaresa Amar yace amin

Momy da tasaki baki tace

Ikwan Allah yanzu MARWAN aure zaka qara ina soyayyar da kakema matarka

Amar yace kae Momy kibarshi man

Dady yace banda abinki ai so tsuntsune

Amar yayi dariya yace hakane dadyna

MARWAN ya'dau keey 'din motarshi yace Nina tafi

Dady yace to yaushe kakesan ayi bikin

Ya kalli Amar

Da sauri Amar yace nanda wata biyu yace

Yanaso ko

MARWAN baiyi magana Ba yafice

Momy tace nisae naga kamar matar bata shigeshi Ba

Dady yace inbata shige shiba yazaiyi yace yana Santa

Kawae halin miskilancin 'dannakine yatashi

Tace ina mamakin halin nan nashi ko nawa yayi oho

Dady yace Allah yakyauta

Amar najinsu yatashi yayi shashinsa yana cewa Momy kayanki namota Wanda Hajiya tabayar abaki

Sis kawomin abinci atare sukace to

to

Zainab na kitchen tana ha'dama Amar abinci

Allah Allah take tagama taje dan gulma nacinta

Ta'ajiye Mae abincin akan table

Yace yauwa sis

Tace ya Amar ya'akayi ya MARWAN yafa'da San wata yace

Duk shirinane

Nan yabata lbr tadinga dariya

MARWAN tuqi kawea yake amma tunanishi yazaiyi da auran Nafisa Allah yasani soyayyar matarsa ne kawae azuciyarsa

Amma tunda Amar ya matsa zai aureta kawae

intagirma tagane bayasanta tarabu dashii

Dan ra'ayin shi nazaman mata 'dayane

Yayi parking motarsa cikin gidansa yafito

Dagudu maryam tazo tarungume shi tana murna shima cikin 'doki yafara kissing dinta

Tajashi falo

Tace yanzu sae kafara wanka kaci abinci sae kaban lbr

Yazareta daga jikinshi yaqare mata kallo

Maryam bawata kyakkyawa bace amma kallo 'daya zaka mata gano Abu biyu atare da'ita

Nafarko tanada wayewa sosae

Nabiyu kallo daya zaka mata katabbatar da bata da kunya

Amma ga MARWAN duk duniya bamekyan marwan dakuma kunya

Bayan MARWAN ya gama kallanta Riga da wando ne tasa tayi kyauta sosae

Yamayar da kallansa kan falan

kaca kaca yake

yace wae my luv yaushe zaki fara tsaftace gidannan tayi shuru yaci gaba

Saiki tsaftace jikinki amma gidanki baxai sami wannan gatan ba πŸ’—πŸ’“πŸ’—

Tace haba hony daga dawowarka zaka faramin fa'da

Yace ok bazanyi miki magana akan gyaraba

Wlhi halin nan naki yana bani haushi

Tayi farii da ido tace yadena baka haushi honey

Su Habiba ne sukazo shiya gidan yayi datti

Kuma wlhi nagyara jiya yace

Tun jiya

Tace eh

Yace banga dalilinki nahanani kawo miki 'yar aikiba

Tace inaaaaaaa

banasan 'yar aiki sobuda 'yar aikin aunty Zakkiya ita ce tazama kishiyarta

Yayi murmushi

yana tuna kishi irin na maryam

Akwaita da kishi

Yace kina tsoran wata takwace miki nine

Tace kwarae

Ai duk macan da tayi gangancin sanka tota yaudari kanta

Ba'dan ka'dan ba

Yace danni nakine

Tace ato

Shiga yayi betroom. Yanda yayi zatan ganinsa hakako yagansa wato aburkice

saikace Ba mace agidan

Girgiza kae kawae yayi yafa'da toilet nanma takaici kamar ya kasheshi. Dakansa ya tsaftace toilet 'din yayi abin da zaeyi

tana kan gado tanajin

Shi

Yafito yace amma toilet 'dinnan yafi 4 days baiga wanki Ba

Tace tunda katafi

Dake ba shigarsa nakeyiba

Amma ai bae kae 4 days ba

Yana zaune a dining takwawo Mae abinci indomie ce da egg

Yana kallanta yakauda kae tace lpy

Yace ita tajawo hakan

Gsky bazanci Ba

A duniya baki da abinci sae indomie

Gashi itamma baki iyaba. Abu duk qarni

Cikin jin haushi tace

Nagajifa

Wae meyasa kowane lukaci kakesan kusheni

Komae nayi ban iyaba

Amma ai kasan bana girki agidanmu bare aiki

Amma kae ina qoqarin yima komae amma baka gani.....

Taja tsaki tabar gun

Tashi yayi ya'dau keey din mota ya fita

Dan yasan yanzu yana zuwa lallashinta sae tasashi yaci indomie shikuma Allah yasani ba zaeciba

Hotel yanufa yaci abincin da yakeso dama yasaba zuwa Dan 'yan hotel 'dinma sunsan shi

Sanda yagama yadawo gidan

Sam yanda yabar komae haka yazo ya ganshi yayi tsaki

Allah yasani MARWAN akwae shi dasan tsafta shiyasa duk ran weknd yake zama yagyara gidan

Har zae shiga 'dakinta saidae yafasa. Yashiga nasa.

Ya gyara kowane saqo da lungu na 'dakinsa

Ya tsaftace yadawo falo ya gyara shi

Tare dasa tuarare

Nan gidan yafito tsaf

Nan gidan ya 'dau kamshi

Kitchen yashiga shima yagyara shi sosae

MARWAN dama yasaba da wanke wanke maryam nan komae yafito tsaf

Ya qara yin wanka

Sannan yanufi 'dakin ginbiyar tasa

Tana zaune kan gado tana catin rannan 6ace

Kallo daya yayi mata

Yaga bazae iya jure fushinta ba

Nan yajawota jikinsa yana lallashinta

Dake itama ahannu take nan warware

Maryam tana harkar maganin mata sosae

Tabbas dashine takejan hankalin MARWAN yana jin da'dinta sosae amma baya gamsuwa da'ita

πŸ’—πŸ’“πŸ’—

'YAR QAUYE KO 'YAR BIRNIπŸ’—πŸ’“πŸ’—

Sam MARWAN ya manta da zancan wata Nafisa

Yana falan Momy sana hira tsakalin 'da da Uwa

Sae ga dady yafito

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login