Showing 1 words to 3000 words out of 31145 words

Chapter 1 - AISHATUL MUBEENA COMPLETE

13 Sep 2026

50

COPY N COMPILED BY

ESHAAT SMILER HOM OF

HAUSA NOVLS DOCUMNTS

WASAPP 08066360176 FOR MORE

AISHATUL MUBEENA 1-20

[12:12AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy:

◆◆◆

AISHATUL MUBEENA

◆◆◆

[1]-[5]

Na Miss hafcy

©ONLINE HAUSA WRITTERS

A fusace ya shigo gidan yana mita

"Haba!!

Mutum dame zeji? Da zafin talaucin dake damuna

ko kuwa da Rashin haihuwa,,Nagaji da wannan

rayuwar! "" Da sauri ta fito daga daki" Haba

malam ai talauci ba hauka bane kuma haihuwa aiy

ta Allah ce,,ka shigo gida bako salama kana

fadan wannan

maganganun ai komai yayi zafi

maganinsa Allah"" Ya dago a fusace ya kalleta

"ma'u kinga kimin shiru ki barni naji da abinda

nake ji ace yau duk wahalar dana sha a kasuwa

amma ba wani cinkin kirki dame zanji haba!

Haba!!"" Ma'u tace "Amma ai be kamata

wannn

maganar ta dinga fitowa daga bakin kaba,,Kasani

fa Allah yana cewa,, Acikin suratul baqarah Aya

ta 153 "" innalla ha ma^as -

sa biri n .""Ma'ana: Allah yana tareda masu

haquri"",, Ya juyo ya kalleta toh sarkin wa'azi,,

naji shikenan yanzu da ab

inda zan samu naci??

Tayi murmushi,,Dazu na sami 200 wankin

danayiwa talatu shine na yi mana danwake har

tumatir ma na bada aka siyo min"" Ya washe baki

yauwa mata ta gari nagode an gaishe ki,,Suka

shiga cikin dakin

Bayan ta zuba mai danwaken a plate

ya fara ci se

santi yake yi can ya kalleta yace "Duk sanda nake

cikin matsala in na tuna muna tare zan dawo na

ganki se naji wani dadi a raina,,saboda nasan

dole zaki faranta min rai" Tayi murmushi sannan

tace "malam kenan nima ai duk hakan take" Yac

e

"madalah ni yanzu matsala dayace take damuna

wanan rashin haihuwar dan na tabbata daga

gareni take mata nawa na aura bayanki amma har

yanzu ba wada ta taba ko bari"" Ta nisa "Malam

ba lallai bane hakan ne kawai dai mucigaba da

addua,,,Se kaga cikin

yardar Allah mun samu"

Yayi murmushi yace toh mata ta gari na gode

Allah ya amsa adduar mu tace "Amin malam"

Bako sallama ta banko dakin,,ma'u da sauri ta

tashi tana "Ahh iya ce? Sannu da zuwa,, iya ta

balla mata harara "Dallah yimin shiru se shegen

kinibibin tsiya ba wajen ki nazo ba wajen dana

nazo" Ma'u ta sunkuyar da kai bata qara magana

ba....Iya ta kalli Mal,, "Kai kuma mara zuciya

kawai kaqi rabuwa da wannan matar me baqar

kafa ta tsiya na gaji ace har yau banda jika,,nasa

ka auri mata ba

ta ko shekara ka saketa,, se

wannan mayar matar taka,Naga alama so kake na

mutu van sami jika ba "" Ta fashe da kuka,,Mal ya

kalleta "Haba inna,,Ya kikeso nayi? Da sauri ta

katse shi KA SAKI MATAR KA MAU SAKI 3! A

firgice ya juyo ya kalleta "Haba iya,

,ki tuna fa a

duk matan da nake aura ita ce kadai me rupa min

asiri take zaune dani a wannan quncin,Ga rashin

haihuwa amma kuma kice na saketa haba iya!,,

Iya ta juyo da mamaki "Auho lallai sule ka girma

ka isa har ina ma magana kana maida min,,ta

fa

she da kuka ace dan dana haifa shi muke

musayar yawu dashi na shiga uku ni tani!""Ya nisa

sannan yace "iya ba haka bane ba wlhy abinda

kika bukata ne bazab iya ba,"" Iya ta fusata "to

kaje wlhy matar nan ta qara wata3 bata sami ciki

ba se an raba aure

n nan,,,Tunda ban isa nasaka

abu ka yi ba,,"" Ta fice cike da fushi Ma'u datake

ta kuka ta juyo ta kalleshi "Bansan me nayiwa iya

ta tsane ni haka ba,,Har yau ta kasa gane cewa

haihuwa ta Allah ce"" Mal ya juyo ya kalleta "Kiyi

haquri ma'u na Insha Al

lah matsalarmu ta kusa

zuwa qarshe! Ma'u ta share hawayenta "Allah

yasa ameen" Ta dauke kwanukan dake dakin ta

fita dan wankesu shikuwa kishingida yayi akan yar

katifar dakin ina jinjina maganar iya

Share

Recent Posts

[12:13AM, 14/10/2016] Miss_Hafc

y:

◆◆◆

AISHATUL MUBEENA

◆◆◆

©ONLINE HAUSA WRITERS

NA MSS HAFCY

[6]-[10]

***ASALINSU****

Malam Sulaiman Abubakar me rariya Dan kasuwa

ne sana'arsa bata huce Ta saida rariya ba, yana

yin rariya ya kuma siyar a kasuwa sana'ar kuwa a

wajen babansa ya gad

a,Alhaji abubakar me rariya

marigayi,,,,

Alhaji Abubakar me rariya yanada mata biyu da

yaya guda 4 guda daya ta rasu,, Balki itace

matarsa ta farko wadda ta haifa masa yaya

biyu,,,Bashir da hauwa,Wanda dukansu sunyi aure

cikin rupin asiri, Se kuma ma

tarsa ta biyu Amina

(Tani) Masifafiyar mata ce ta gaske ga rashin

haquri Ta haifa masa yaya biyu Mal sule shine na

farko se kuma habiba wadda ta rasu tun tana

qarama,,,,,,,,,

Mal Sule matarsa daya wanda suke zaune a halin

yanzu, asmau ma'u wacce suka

yi auren soyayya

amma shiru kusan shekara 10 kenan suna tare

Amma ko batan wata bata taba yi ba,,,Hakan

yasa tani wadda suke cewa Iya ta takura masa

akan se ya qara aure,, mata aqala sunkai 5 ta

kawo masa in ya auri wanan ta fita se ta kuma

samo wata

yan mata da zawarori amma kuma

sam basa zama Kuma a cikinsu ba wadda ta taba

ko batan wata balle bari,,In suka gaji se su

tafii,Ga talauci ga rashin haihuwa da kansu su

suke neman saki, Wasu kuma in ya gaji da

halayarsu se ya sake su Iya tayi masifar

ta

gaji,,,Tayi neman malaman akan nemawa tilon

danta sule haihuwa amma har yanzu shiru

Ma'u matace me haqurin gaske da tawakali

tanada ilimin addini sosaii hakan yasa rashin

haihuwar sam be dame ta ba Duk da talauci irin

na mal sule amma Haka take h

aquri ta zauna

dashi wataran ma da en dabarunta take ciyar

dasu,Dan itama gidansu ba wasu masu arziki

bane,Ga miji shima ba wani me arziki ba dan da

sana'ar rariya kawai ya dogara ko noma ba yayi

saida gonar gadonsa yayi,,Suna zaune yau da ci

gobe ba

bu.

********CIGABAN LABARI******** Ma'u da

gudu ta fito daga daki tana kwarara amai a

rariyar tsakar gida,,daidai shigowar iya kenan,,iya

da sauri ta isa wajen ta "yar nan meya faru haka

me kika ci" Ma'u Tana huci tace " Wlhy tun da

safe nake jina wa

ni iri ga zazzabi dazu kuma

zuciyata ta fara tashi shine fa na fara jin amai

har nazo nayi" Iya ta dago kanta" Yaushe rabon

da kiga aladar ki? Ma'u tace "Watan daya huce

dai bangani ba""

Iya ta duba idonta sosai aikuwa se ta saketa ta

rangada guda ""

Ayiriyiri" Yarinya ki godewa Allah

ai alama ta tabbatar da cewa ciki gareki kai yau

ni nafi kowa murna ayiriririiriiiii"" Ma'u ta zaro

ido maganar iya se tazo mata kamar a mafarki ta

dago cikin dashashiyar murya tace "Iya ciki fa

kika ce?" Iya ta wash

e baki "Tabbas yar nan kiyi

murna fa"

Daidai lokacin mal sule ya shigo gidn dauke da

rariya a hannunsa ya tsaya turus ganin iya tasa

ma'u a gaba tana rangada guda ya matso yace

"Iya me ya faru ne" Iya ta kuma washe baki "Yaro

albishirin ka?"Da sauri

yace goro iya" Iya tace "to

matarka ciki gareta alama ta nuna!"

Mal sule ya yarda rariyar dake hannusa se ganni

Inna tai ya daga hannu sama yana godiya se

kuma hawaye,,Ma'u da take tsugune kuka ta fara

a hankali kukan murna! Yau dai Allah ya amshi

ad

du'arsu! Mal sule a fili yace "Allah nagode

maka,ya allah daka amshi addu'a ta, Ya Allah

kasa dan dake cikin matata ya zamo namiji! Allah

yasa namiji zata haifaa na samu magaji ameen!!

Ma"u da sauri ta share hawayenta ta kalleshi

"Haba malam Ai ba'a y

iwa Allah haka kai dai

kawai kayi fatan allah ya bamu nagari, inma

namiji ne inma mace !"

Ya juyo ya kalleta "A'a fa Ma'u ki banni na roqi

Allah ya ban namiji dan ni banida wani buri daya

huce na haifi da na miji ba mace ba!" Iya se a

lokacin tace "

fadi ka kara dana,me za'ayi da wata

mace? Ina laifin da na biyu ta haifo mace amma

wannan cikin Inshaa Allahu namiji ne ehe!"

Ma'u ta tashi ta girgiza kai alamar kalaman basu

mata dadi ba ta shige daki cike da farin ciki A

zuciyarta kuma mamakin furuc

in su Mal

take,tabar Mal da iya a tsakar gida suna ta Farin

ciki da anashuwar abinda ya faru! Iya tace "ka

dinga kula da ita bari naje na sanarwa da en uwa

da abokan arziqi wannan abin alherin,Ai banga ta

zama ba" Ta fice tana guda shima kuwa cewa

ya

yi "nima banga ta zama ba kuwa nima bari naje

na siyo mata kayan makulashe!

Share

Recent Posts

WA GARI YA WAYA? 2

WA GARI YA WAYA? 1

WA GARI YA WAYA?? 3

Comments

No comments yet. Why not make the first

one!

New Comment

[]

Name:

Comment:

(Some

BBCode tags are allowed)

Post Comment

options

Home

Guestbook

About Me

Feedback

Blogroll

Feed: RSS / Atom

Comment Feed: RSS / Atom

Get a

October 2016

October

13

Thursday

11:12 PM

Go to top

Visitor Counter : total-0060690

© 2016 Hafsat's M

obile Blog .

fmb_Powered by

Copyright 2016 mrs hafcy design by

muhammad abba gana (09039016969)

[12:14AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy:

◆◆◆

AISHATUL MUBEENA

◆◆◆

NA MSS HAFCY

®ONLINE HAUSA WRITERS

[15]-[20]

Ma'u tana zaune tana cin tuwo mirar kuka da

yajin

dadawar da mamanta ta aiko mata, gefe

guda kuma farfesu ne Goggo(k'anwar

babansu,wadda tazo mata zaman wanka) ta kawo

mata,suna zaune ita da goggon suna hira,Babyn

na hannun goggo,, Salamar Mal sukaji,ya shigo

fuska ba yabo ba falasa suka gaisa da go

ggo tace

"Ahh angon k'arni ne ke tafe ashe" be amsa mata

ba,tamai barka, ciki-ciki ya amsa sannan ta basu

waje

Ma'u da murmushi ta juyo ta kalleshi "Mal

kenan,inata cigiyarka kazo kaga kyauta da Allah

ya bamu,Yau dai Allah ya amshi addu'ar mu,se

mu

gode masa"a fusace ya kalleta "ke dallah

sauraramin! Kin tashi kin haifo wata mace,

zakimin dadin baki,bari kiji zuwan nan danayi abu

biyu ne ya kawo ni, ki saurara da kyau kiji""

Ma'u tace "Ikon Allah mal meya yayi zafi haka?

kuma ai bani ce ke bada

haihuwa ba,Allah ne ke

bayarwa" Ya katse ta"Abu na farko shine: kinga

wannan(ya fito da dari biyar 5) ita kadai zan bada

ayi hidimar suna da sauran abubuwa,Kaya kuwa

kinsan na gama siya dan haka kyasan yadda

kikayi,,Ragon dana siya ma,zuwa zanyi a caz

amin

aban tunkiya dan banga amfanin yankawa mace

rago ba! Abu na biyu, nazo muyi salama domin

tafiya zanyi bayan suna na dawo,Dafatan kin

gane?, Ma'u bata san sanda ta fashe da kuka ba,,

"Mal yanzu abinda kayi ya dace mal? Kayi mana

aladalci nida yar

ka? ,, Ya katse ta "kinga ni bance

kimin surutun banza ba,in kina da magana ki fada

da sauri, dan tafiya zanyi gidan iya yanzu,,Ma'u

ta cigaba da kuka bata bashi amsa ba

Yana k'ok'arin fita ne cikin dashashiyar murya

tace " Mal dan Allah ina neman alf

arma a

wajenka" ba tare da ya juyo ba yace "tame?" Ta

cigaba"Inaso kayi ma yarinyar nan huduba kamar

yadda Kowanne uba ya kamata yayiwa Dansa ko

yarsa,Sannan kuma inaso ka dauketa ta ji dimin

jinkin ka koda na minti 5 ne,,Ta fashe da kuka

Ya danyi ji

m sannan ya gyada kai,ya koma ya

zauna,Ya turbune fuska, ta dauko babyn, ta mik'a

masa ya karba yana gun-guni,, "Ai se ki fadi

sunan da zan samata," Ma'u ta juyo tace "Da

nazata ai kaine zaka zaba" a fusace yace "ke

bansan bata lokaci" cikin sanyin mu

rya tace

"AISHATUL MUBEENA"" Tsaki yayi ,toh shikenan,,

Ya mata hudubar,ta dan dade a hannunsa sannan

ya mik'a wa ma'u ta karba tana murmushin

yak'e,tace "nagode mal Allah ya kiyaye hanya"

yace ameen, yasa kai ya fita" Ma'u ta k'urawa

AISHATUL MUBEEN

A ido kawai se jin sabon

hawaye tayi na zuba,Tausayin Yarinyar duk ya

cika mata zuciya,,,Goggo ta shigo ta tadda ta

tana kuka,da sauri ta iso wajenta"Ma'u meya faru

kike kuka?" Ma'u ta share hawayenta "bakomai

goggo" Goggo tace "ban yadda ba,ki fada m

in

abinda ke damunki,ko wani wajen ke miki ciwo?"

ma'u tace "A'ah goggo kaina ne ke ciwo" goggo

tace "kuma shine kike kuka,bari na dauko miki

magani" ta tashi dan dauko mata maganin

Iya tashigo kamar yadda tasaba yau ma ba

sallama" ke ma'u dama nazo

fada miki sak'o ne,

mijinki yaban kudin,Shinkapa da kayan miya na

taron suna,Dan haka bazan baki kudin ba kuje ke

da daginki ku kashe a banza,dan haka ana gobe

suna kome ake buk'ata se kiyi magana,,""Ma'u ta

girgiza kai"A'ah iya ki barshi kawai,Ni baz

anyi

taron suna bama,Na hak'ura kawai Allah ya

rayata,Tunda bezo a al'k'urani ba dole se anyi

taron suna ba" Iya ta zaro ido ta dafe k'irji "Lallai

yar nan kin rik'a wato ni kike fadawa magana a

fakaice koh?" Se a lokacin goggo tasa baki " A'a

a'a Ta

ni karki soma,Yarinyar nan a kalamata ba

wanda yayi kama dana zagi ko kuma na bak'ar

magana, iya tace kwaji dashi dai dangin tsiya ta

fita tana masifa",Ma'u ta fashe da kuka "oh ni

asma'u ya zanyi? Da bak'in cikin mijina ko dana

uwarsa?

® OHW

AISHAT

UL MUBEENA 20-30

[12:15AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy:

◆◆◆

AISHATUL MUBEENA

◆◆◆

NA MSS HAFCY

®ONLINE HAUSA WRITERS

[20]-[25]

Goggo da sauri ta katse ta"karki soma fadan

wadanan maganganun Ma'u kinji,Kiyi hak'uri

komai lokaci ne" Ma'u tace toh goggo insha

Allah

bazan kuma damuwa ba,Zanta addu'a Allah ya

ganar da mal gaskia,,Goggo tace yauwa yar

albarka..

Yan uwa da abokan arzik'i sunata zuwa

barka,Yarinya tana ta samun kaya masu

kyau,,rannar suna kuwa duk da Ma'u tace bazata

yi taron suna ba mutane a

nzo dayawa...wata

mak'ociyarta wadda suke mutunci sosai khadija

shinkafa dafa duka ta yimata me dadi da

zobo,dayake mijinta nada hali,Ma'u tayi farin ciki

sosai da abinda khadija ta mata tayi ta

godiya,,,dangi aka zo anata kwashar girki ana

santi,had

a su Iya,don ita har diba tayi ta kai gida

kowa yaji sunan yarinyar AISHATUL MUBEENA Se

ya yaba sunan ,,,Liman ne ya yanka tunkiyar

suna, Iya kuwa ta tsaya tsayin daka akan naman

k'iri-k'iri ta hana dangin Ma'u da sauran mutane

taba naman,Daga ita se

yan'uwanta ne suka

sarafa naman,Wai kada su Ma'u su handame, ita

ma'u ma ko a jikinta...yarinya ta samu kaya kuwa

masha Allah daga ita har Ma'u itama tana samu

kudi da atamfofi,tayi mamaki sosai dan bata taba

zata zata samu abin alherin data samu ba

Bayan suna mal ya dawo,Ba yabo ba

falasa,Amma kuma sam yaqi yadda ya dauki

yarinyar koda wasa,Tun Ma'u tana damuwa har ta

dena,Ta cigaba da kula da yarta da ita kanta

bayan tayi arba'in ta zagaya dangi yawon arbain

shima da kyar ya barta,,Iya kuwa kul

lum cikin

tsangwamar AISHATUL MUBEENA take,Har yanzu

kuwa bata dauke ta ba,se dai ta kalleta daga nesa

BAYAN SHEKARA BIYU

Mal naezaune a kofar gida suna tadi shida wani

abokinsa sanda,Wasu mata suka nufo gidan su

3,A tare suka gaida Mal ya amsa yana

washe baki

daya daga cikinsu tace" Mune masu yak'i akan

cutar poliomyelitis wato cutar polio,Mun samu

labarin kana da ya shine zamuyi mata

rigakafi,"Mal ya kalleta "ke ni banda yaro a

gidana ku fice min daga nan shashasahai kawai"

Dayar tace "kaga ma

lam dan munzo mu taimake

ka kaida iyalinka,baka isa ka zage mu ba,ko

dayake naga alama kai jahili ne!" Ya juyo ya

kalleta" ke wallahi se na kwada miki mari,wa kike

cewa jahili?" Tsaki tayi "kai mana" Taja sauran

suka yi tafiyarsu ...yayin da suka bar

mal da

sanda suna ta balbalin masifa Ma'u duk taji

abinda ya faru,AISHATUL MUBEENA tana tsakar

gida abinta tana wasa, Ma'u kuma tana wanki a

tsakar gida, mamakin halin Mal kawai take...

Ya shigo yana balbalin masifa ko salama beyi ba,

ta kalle shi "M

al wannan yar muce fa, tana da

hakki akan mu,Ka tuna fa tunda muka haifi yar

nan bamu taba kaita asibiti ba,ko cuta tai se dai

inyi yan dubaru na,nice zuwa neman maganin

gargajiya,Amma kai ko da wasa baka taba nuna

damuwar ka ba,,,Sun biyo mu har gida

don su

mata rigakafin wannan muguwar cutar, sannin

kan kane wannan cuta nakasar da yayan mutane

take,akan me bazamu basu damaba? Basu nemi

ko biyar daga gare mu ba fa,Mal nagaji da wanna

halin naka nagaji!!! " ta fashe da kuka... Ya galla

mata harar

sannan yayi tsaki " Ma'u ki shiga

taitayin ki fa,Ya isheki abinda kike yi,rigakafin ne

nace baza'ayi ba!,Ai yata ce nina haife ta kuma

na isa da ita har dake!

Sh

[12:18AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy:

◆◆◆

AISHATUL MUBEENA

◆◆◆

NA MSS HAFCY

®ONLINE HAUSA WR

ITERS

[25]-[30]

Ma'u da sauri tadago kai ta kalleshi "au yarka?, se

yau kasan cewa yarkace,Kai yanzu baka ji kunyar

fada bama? Wallahi mal in baka canza halin ka ba

Allah se ya tambayeka,Allah wadaran wannan

mumunan halin naka!" Mal a fusace ya dago

ya

wankawa mata mari ji kake Tas!! Aishatul

mubeena se data tsorata ta fara rusa kuka itama,

Mal ya kalli ma'u ya cigaba"Naga alama kin fara

raina ni a gidan nan,Wato yanzu har ina fada kina

fada zan fara maganinki ne mara kunya kawai

wadda batada ta

rbiya"" Ya sa kai ya fita daga

cikin gidan a fusace......Ma'u ta share hawayenta

tace "Allah ga baiwar ka,Allah ka raya wanna

yarinyar ya Allah"" ta dauki aishatul mubeena ta

fara rarrashinta tana hawaye ahaka har aishatul

mubeena tayi bacci

To rayuw

a dai haka ta cigaba yau da dadi gobe

babu dadi,Ma'u kullum cikin hak'uri take da

mijinta da kuma uwar mijinta wanda suka zamo

mata matsala a rayuwarta

Yanzu dai shekarun AISHATUL MUBEENA 3 ta

taso yarinya kyakyawa san kowa k'in wanda ya

rasa,ga fari

n jini masha Allah,yara har fada ake

akan daukanta saboda kullum tsaf da ita,Har ta

fara magana sosai,abin mamaki kuwa itama

tsoron babanta ma take dan tun tana k'arama

tasaba tana zuwa wajenshi ze hantare ta hakan

yasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login