Showing 12001 words to 15000 words out of 31145 words
suna mata kirari ita kuma sai busa hanci
takeyi can tace "Sai ku shir
ya anjima za'ayi
assambili anan ne zaku tabbatar dacewa nice na
lashe gasar" Asiya ta tab'e baki "ba giringirin ba
dai tai mai!" Nafisa tsaki tayi ta juya ta mata
wani kallon raini sannan tace "ni bansan shishigi a
rayuwata ita gurguwar da kike shigew
a ai itama a
bayana take wallahi,dukanku nan sai da ku zama
'yan amshin shata dan nice gaba da ku akomai"
Mubeena murmushin takaici tayi ta sunkuyar da
kanta. Asiya a fusace ta tashi "keee!! Ba'a aibata
halitar Allah,ke in banda jahila/jahili ma wa ya
ke
yabon kansa? ,kuma da kike cewa gurguwa ai
Allah ne ya haliceta haka,, a haka yaso ya
ganta,kuma kema baki fi k'arfin Allah ya maida
ke haka ba,wai ke da me kike tak'ama ne? eh?
Nafisa a fusace tace "kut! Ke har kin isa ki zage
ni,"tayi wani kukan
kura zata wankawa Asiya
mari,da sauri Asiya ta rik'e hannunta cak! Tace
"karki kuskura ki taba min fuska,niba karya bace
irinki bana dambe,"tana gama fadan haka ta
zauna tabar Nafisa nata kumfar baki,,daidai nan
teachern su ya shigo ,yana shigowa a f
usace ya
kalli Nafisa "get out!!" Simi simi tabar ajin tana
gunguni. Malami suka dinga shiga aji-aji suna
cewa dalibai sufito za'ayi asambili na musaman
ba'a dad'e dalibai suka cika wajen assembly din
Nafisa kuwa sai wani tak'ama takeyi. Uncle
Hashim
dayake shine me kula da harkar gasar ya
fito ya fara jawabi kamar haka "Gud afternoon
students,,abinda yasa muka tara ku nan ba dan
komai ba dam mu fad'a muku sakamakon gasar
zanen iya makarantarmu da muka gabatar yau,, a
cikin mutane goma da suka yi
participating a
gasar mutum biyu zamu dauka wa'enda su kuma
zasu yi tasu gasar next week,a cikinsu kuma mu
dau wadda tazo ta d'aya dan ta wakilci
makarantarmu,, wanda yazo ta goma(10) shine:
Auwal Isah na tara(9 ) Jamila Muhd na 8 Iro
Faisal........
........,,.wadda tazo ta biyu....Nafisa
Jameel sai kuma zakaran wato wanda/wadda ta
lashe gasar ......(ya k'ara daga muryarsa)
AISHATUL....kan kace meye dalibai suka d'au ihu
suka k'arsawa masa "Mubeena Muhd Ameen.
[12:32AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [1
1:53AM, 18/03/2016] Hapsat:
◆◆◆
AISHATUL
MUBEENA
◆◆◆
©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [100]-[105] Umma
tace "Amin, wannan satin insha Allahu inason
muje k'auye wajen mama bata ji dadi ba ashe sai
jiya yaya Basiru yake fad'amin a waya" Mubeena
tace "ey
yah Allah sarki Mamana Allah ya bata
lafiya" Umma tace "Amin" . Abba ya dawo suka
fad'a masa niyyarsu ta ziyarta iyayen yarinyar
Abba yaji dadi kwarai ya k'ara musu dubu ashirin
(20) akai,, ya dau waya ya kira Ya Abdul "Abdul
Hafeez kana ina ne?" Ya A
bdul yace "ina dakina"
Abba yace "toh ka shirya yanzu zaka kai su
Ummanku unguwa kasan driver yayi bulaguro"
Yace "toh gashi nan". Ba dad'e ba kuwa sai gashi
bayan ya gaishesu gaba d'aya,Mubeena ma ta
gaishe shi ya amsa ba yabo ba falasa...Su Ya
Nana
ma sukace zasu bisu aikuwa suka shirya
abinsu, Mubeena kuwa hijab dinta ta d'auko ash
colour har k'asa tasa abinta hoda kawai ta shafa
sai farin man leb'e ..ta fito suka shiga mota, se
da suka fara zuwa wani babban mall suka siyo su
kayan abincine,ka
yan makulashe, kayan sawa,
daiper etc sun kashe kud'i dayawa ... dama
already Mubeena ta taho da wheel chair dinta da
take amfani da ita kan ta fara tafiya don ta bawa
yarinyar. Sai da suka fara zuwa gida su Asiya
suka dauko ta dan ta rakasu gidan,bas
u dad'e ba
kuwa sai gasu a gidan, k'aramin gida ne na k'asa
wasu wuraren na gidan ma duk ya rushe kana
ganin gida kasan na talakawa ne futuk.. Da
sallama suka shiga gidan a lokacin, wata
matashiyar mata ta amsa musu da fara'a,yayin
data aje tsintsiya
r datake shara da ita,,
"Sannunku da zuwa" ta fad'a tana fara'a, Umma,
Mubeena, Ya Nana, Husna da kuma Asiya, Ya
Abdul da Amir suna cikin mota su basu fito ba.
Matar ta shimfid'a musu tabarma suka zauzauna,
ta tashi ta nufi randar ruwa ta d'ebo musu r
uwa
a kwanon sha ta aje a gabansu, Sannan ta zauna
suka gaigaisa, matar tace "sai dai kuma ban gane
kuba, waccan kawai na gane(ta nuna Asiya) ko
yan gidansu ne?" Umma tayi murmushi sannan ta
fad'a mata dalilin zuwansu, matar sai hawaye
kawai tace "Na
gode kwarai Allah ya biyaku dama
in Allah ya kawo makashinka sai ya kawo me
ceton ka" Umma tace "gskiya ne, ina yarinyar"
Matar tace " YUSRA tana cikin d'aki ku shigo"
suka shiga dakin. A kwance suka tadda ita sai
kallonsu takeyi ta kalli Mamanta "Mam
a suwaye?"
Maman tayi murnushi "bak'i ne suka zo duba ki"
A tare su Mubeena suka had'a baki "ya jikinki?"
Tace "da sauk'i" Mubeena ta kura mata ido sai
hawaye sharr ta sunkuyar da kanta tana kuka a
hankali... ita kuwa Umma godewa Allah tayi da
banda
taimakon Allah ba da tuni itama suna cikin
wannan halin... Umma ta dage ta ce "Ina
mahaifinta?" Maman tayi murmushi takaici "Aiy
bama tare yanzu nan gidan iyayen mune da suka
mutu suka bar mana nida k'anina anan muke
zaune, tunda muka rabu da mahaifin
ta be kuma
waiwayar mu ba" ta fashe da kuka,, Umma ta
runtse ido sai hawaye, a zuciyarta tace "ashe
akwai masu hali irin nan Mal Sule a duniya? Allah
wadaran wannan mumuman hali tur dashi! Itama
da tuni fa tana cikin wannan hali kai dole ta
godewa Al
lah daya musan yamata da mafi alheri"
Umma ta share hawayenta tace " nima kinga 'yata
nan itama polio ne amma ita kafarta ce kawai"
Maman tace "Allah sarki ita yazo mata da sauk'i
ma". Nan da nan wasu maza suka fara shigowa da
kayayyakin da su Mubeena
suka siyo,, Maman
tsayawa tayi tana kallon ikon Allah ta kasa
magana ma saboda tsabar murna,, Umma ce ta
katse dacewa "gashi wannan kyautace daga
AISHATUL MUBEENA ga wannan daiper sai ku
dinga saka mata kinga kin huta da wanki kashi da
fitsari sai d
ai kawai ki cire a tsaftace, ga kayan
makulashe nan ana bata, ga Wheel chair nan
shima a dinga dora ta ana zagayawa da ita itama
ta zaga gari,, duk dai gasu duk naku ne
malakinku ne ga wannan(ta mik'a mata dubu
ashirin(20) da Abba ya bada) sak'o ne da
ga
Abbansu kwayi wani abun dasu, Allah ya k'ara
sauk'i" . Maman ta fashe da kukan murna "duk
mukadai? Allahu akbar ashe akwai mutane irinku
AISHATUL MUBEENA mun gode kwarai Allah ya
biyaki ya daukaki bansan dame zan gode muku
ba, bansan da wata kalma
zanyi amfani na gode
muku da ita ba, Allah ya biyaku, ya kare ku ya
biya muku buk'atunku duniya da lahira, Mubeena
da za'a sami mutane irinku da yan uwanku masu
wannan masifafiyar cuta ta polio basu wahala
ba,da basuyi bara akan titi ba, da kuma wasu
n su
basu rasa ransu ba saboda wannan cuta,," ta
k'ara fashewa da kuka. Mubeena ta k'araso
wajenta ta rungume ta tana kuka "Maman ki dena
kuka,a kullum raina yakan baci inda naga yan
uwana masu irin wannan cuta suna wahala ,
inason in taimakawa yan u
wa masu irin wannan
cutar mussaman ma wa'enda basu da bud'i
irinku,, kar ki gode min ki gode dan Allah"
Maman tace "Allah sarki Allah me baiwa" Yusra
dake kwance tace "mun gode Anty Mubeena".
*** ina gayyatar ku zuwa sabon group din dana
bude yau a f
acebook, masu yin facebook sai kuyi
searching "MISS HAFCY NOVELS" Nagode
Like · 2 ·
[11:53AM, 18/03/2016] Hapsat:
◆◆◆
AISHATUL
MUBEENA
◆◆◆
©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [95]-[100] Uncle
Hashim murmushi yayi yace "To kunyi gueesin
right" Nafisa kuw
a iya kulawa ta kulu batasan
sanda taji hawaye ba,dataga abin ya fara isarta
sai ta fara zage-zage "wallahi bazan yadda ba!
Wannan ma aiy sankai ne, aikin banza
kawai,kuma...bata k'arasa maganar ba taji saukar
mari a fuskarta ji kake tas! Kallo ya daw
o kan
Nafisa dake rik'e da kuncinta tana hawaye, sai a
lokacin suka gane ashe anty sa'adah (english
teacher dinsu) ce ta wanka mata mari,,wasu suka
hau yi mta dariya yayin dana kusa da ita sukai tsit
dan suna tsoranta. Anty sa'a taci gaba "ke waye
sa
'anki a cikinmu saboda tsabar rashin kunya mu
sa'aninki ne?" Uncle Hashim ya k'araso wajen
"bari ni da ita zanyi maganinta" ya kalli Nafisa
dake ta sheshekar kuka yace "shige muje" ba shiri
ta bishi Zuwa staff room...Dama lokacin tashi
yayi dan haka a
ka sallami dalibai. Mubeena ce
zaune ita da Asiya a bus stop din skul din,
Mubeena da Amir na jiran drivernsu yayin da
Asiya ke jiran skul bus din unguwarsu Asiya ta
kalli Mubeena "gaskiya Mubeena kin burgeni, ni
dama nasan ke zaki cinye,dama nice ke!
"
Mubeena tayi dariya "hmm Asiya kenan kema fa
kinada taki baiwar fa" Asiya tace "tame fa?"
Mubeena ta cigaba" na rubuta labarai mana
novels ni kome zaki min bazan iya rubuta
k'agaggen labari ba wallahi,ke kuwa fa kina iya
k'irkira ki rubatasu kala-k
ala" Asiya tayi dariya
"kema dai Mubeena nan abinda ni kadai nake
rawa ta nake kida na, in na rubuta da sisters dina
kawai nake bawa su karanta sai kuma ke"
Mubeena tayu murmushi "duk da haka' Asiya tace
"kodayake inmunyi candy inason na fara
publish
ing din wanda wasu danake rubutawa
wasu kuma na fara typing dinsu a whatsapp ko
facebook wato online writeups" Mubeena tayi
murmushi," lallai ashe kema kin kusa zama su'
Benaxir,Lubbatu,Chuchu,Ybk,Jabo,Faty
axland,etc danaji su Ya Nana na fadan su sun
a
rubuta online hausa novels ,,kinsan su Ya Nana
sun dage da karatun hausa novels,kullum zaki
gansu mak'ale da waya suna karatun littafi" Asiya
tayi dariya "lah ashe kema haka,wallahi nima
sisters dina haka kullum cikin karatu a whatsapp
har group ga
resu kala-kala na hausa novels"
Mubeena tace "aiy suna k'ok'ari". Drivern su yazo
suka wuce gida. Suna shiga gida Amir da gudu
yayi falo yana kiransu umma,suka firfito a tsorace
dan a zantonsu wani abun ne ya faru marar
dadi...Yayi wani tsalle ya kall
i umma "Yaya
Mubeena ce tazo ta d'aya(ya nuna yatsan sa guda
d'aya) Ummi ta wangale baki "Ai daman nasan a
rina! ina 'yar tawa take? Mubeena ta k'araso tana
murmushi "gani Ummina!" Ummi ta rungumeta
tana murna "Allah ya sanya Alheri" Mubeena ta
amsa,
Ameen ummina! Amma kinsan meye?
Ummi ta girgiza kai" next week zamu kuma yin
wata gasar da Nafisa Jameel wanna wadda nake
baku labarinta" Ummi tace "ai insha Allahu zaki
samu nasar 'yata zamu dage da addu'a" Umma
tace "kar kisa tsoro a ranki insha Al
lahu sai kin
cinye gasar nan" Mubeena tace "Ameen my
mother's" Umma ta cigaba "bari na kira Ameen
na sanar dashi wannan abun arzik'in" ta shiga
d'aki dan dauko wayarta. Murna wajen ya Ameen
ba'a magana sun dad'e suna waya yana bata
kwarin gwiwa akan
ta dage zatayi nasara insha
Allahu ta kuma dage da addu'ar daga k'arshe
sukai sallama ta mik'awa Umma wayarta.
Mubeena ce zaune akan carpet din falon Umma
abinci ne a gabanta amma ta kasa ci tayi tagumi
da alama akwai abunda take tunani, Umma ta
k'ar
aso wajen ta tace "Mubeena me ke damunki?
Kinsa abinci a gaba tun dazu kink'i ci? Mubeena
ta d'ago idonta sharkaf da hawaye tace "Umma
wallahi wani labari aka ban yau in na tuno duk sai
naji ba dadi" Umma ta kara matsowa kusa da ita
"na mene?" Mubeena
ta share hawayen nata
sannan taba umma labarin da Asiya ta bata na
yarinyar nan me cutar polio data ja mata
paralysed,, Umma itama sai ta fashe da kuka ta
tuno irin gwagwamayar data sha itama lokacin da
Mubeena na k'arama,, Mubeena ta katse mata
tun
anin da cewa "Umma wannan dubu hamsin
d'in dana samu a wajen musabak'ar nan nakeso
kiban muje dake muyi mata siyayya kayan abinci
da kayan sawa da kuma daiper size dinta,Atamfar
nan kuma abani guda biyu na kaiwa mamanta
d'aya sannan kuma aba Safi tell
a ta dinkawa
yarnyar, mu kai gidansu" Umma tayi murmushi
"Kaji d'iya ta kwarai Mubeena ke daban ce!
Kinada zuciya me kyau Mubeena a kullum godewa
Allah nake daya bani 'ya kamar ki, Mubeena Allah
ya shi miki albarka ya kuma albarkaci rayuwarki,"
Mubee
na ta ce "Amin Ummana nima ina alfahari
dake, Allah ya saka miki da alheri ya biya miki
duk bukatan ki duniya da lahira" Umma tace
"Amin nagode AISHATUL MUBEENA" amma sai ki
bari Abbanku ya dawo sai a sanar dashi koh?
Mubeena tace "gaskiya kam Allah y
a dawo dashi
lafiya"
Comment as:
Publish Preview
No comments:
Post a Comment
MissHafcy
View my complete profile
About Me
►
2017 (16)
▼ 2016 (34)
►
November (1)
▼ October (33)
WELCOME
ASMAUL HUSNA 6
ASMA'UL~HUSNA
ASMAUL~HUSNA 4
ASMAUL~HUSNA
3
ASMAUL HUSNA 2
ASMAUL HUSNA
AISHATUL MUBEENA 155-160
AISHATUL MUBEENA 145-155
AISHATUL MUBEENA 110-140
AISHATUL MUBEENA 85-105
AISHATUL MUBEENA 60-80
AISHATUL MUBEENA 45-60
AISHATUL MUBEENA 30-40
AISHATUL MUBEENA 20-30
AISHATUL MUBEENA 1-20
WANI HANIN END!
WANI HANIN 26-27
WANI HANIN 24-25
WANI HANIN 22-23
WANI HANIN 20-21
WANI HANIN 19-20
WANI HANIN 15,16,17&18
WANIN HANIN 12,13,&14
WANI HANIN 11
WANI HANIN 9&10
WANI HANIN 7&8
WANI HANIN 5&6
WANI HANIN 3&4
WANI HANIN 2
WANI HAN
IN 1
....
WANI HANIN
Blog Archive
Miss_Hafcy. Watermark theme. Powered by Blogger .
More
AISHATUL MUBEENA 110-140
[12:33AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:51AM, 18/03/2016] Hapsat:
◆◆◆
AISHATUL
MUBEENA
◆◆◆
©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS A tak'aice d
ai ansa
rannar Ya Ameen da Faty, da kuma Aisha( Ya
Nana) da Saifulah nan da wata biyu(2) ,, Su
Umma kuwa sai shirye shiryen biki sukeyi.. Ya
Abdul kuwa har ya gama karatunshi Abba ya
samar masa aiki har ya fara yi dan haka ma ba
kullum yake zama a gi
da ba. Baiwar Allah
Mubeena kuwa tacan duk ta damu dan ta dad'e
da gane cewa tana son ya Abdul ! amma sai take
ganin abun da kamar wuya, na farko dai Umma
tace mata Abba ne babanta to indai har kuwa
Abba ne babanta to ba aure a tsakaninsu saboda
want
a ne uba d'aya kuma ba aure a tsakaninsu
k'anwa da wa.!.na biyu kuwa, tasan halin ya
Abdul shida ko magana bata shiga tsakaninsu sai
ta k'ure,, in ba kwanan nan dayake d'an sakar
mata fuska,,kuma tasan ma baze rasa budurwa
wadda yake so ba,,,,yadda ya
ke d'in nan
tubarkalah gashi kuma d'an gayu,, doleh 'yan
mata suyi rububinsa... dan haka sai ta dinga
addu'ar Allah ya cire mata sanshi a zuciyarta,, a
kullum kuma tana k'ok'arin cire sanshi daga
zuciyarta,, dan a iya tunaninta ko da da aure a
tsakan
in su, in ba wani ikon Allan ba,to ko a
mafarki baza ta tab'a zama matarsa ba,, Ita dai
kullum addu'arta shine Allah ya bata miji na gari
ya kuma zab'a mata mafi alheri Yau saura befi
kwana biyar (5) suyi gasar ba,kuma dama sun
gama exams an basu hutu
, dan haka lokacin hutu
za'ayi gasar.. Mubeena na zaune a falo tana kallan
musab'akar alkur'ani da akasa a sunnah Tv,,
Umma ta fito daga d'aki cikin shirin fita unguwa,
Mubeena ta d'ago ta kalleta "Umma fita zaki yi
ne?" Umma tace "eh k'auye zani waje
n Mama"
Mubeena da sauri ta tashi "Umma dan Allah nazo
muje? Na dad'e banga Mama ba" Umma tace to
maza shirya muje,kafin rigimaman nan yazo(Amir)
dama neman dalilin k'in zuwa islamiya yake yi"
Mubeena tayi dariya sannan ta shiga dakinsu ta
dauko hija
b dinta ta bi bayan umma ,, suka yiwa
su Ummi sallama sannan suka nufi k'auye. Bayan
sun isa Mama tayi murna sosaii da ganin su,
bayan sun gaisa sun sha ruwa , Mubeena nakan
cinyar Mama suna wasan su na jika da kaka,
Mama ta kalli Umma," Ma'u kinsan I
YA ta samu
mutuwar b'arin jiki kuwa? Gaban Umma ya fad'i ,
"subhanalahi,wacca iyan??" ta fad'a had'e da
dafe k'irji, Mama tace " Iya dai surikarki, wallahi
abun tausayi kuje ki duba ta dan Allah kullum
fad'i take a kirawo mata ke da yarki ta nemi
gaf
arar ku . Umma tace "Allah sarki Iya, a ina
take zaune? Mama tace "inda dai kika santa tana
nan' Mubeena dake kwance akan cinyar Mama da
sauri ta taso ta tsutsura musu ido ,, ta kalli
Mama tace"Mama wacce ce Iya?" Mama na
k'ok'arin magana Umma ta daka
wa Mubeena
tsawa "bansani ba,dake muke magana,ban hanaki
sa min baki in ina magana ba?" Mubeena ta
sunkuyar da kanta , yayin da Mama tace "ke Ma'u
wai meyasa kike haka ne? Daga tambaya saiki
hayayak'o mata?" Umma tace "Mama haushi
taban ai manya na m
agana ta dinga sako baki,
bari na tashi naje na dubo ta"" ta tashi ta dauki
jakarta tana k'ok'arin saka takalminta, Mama ta
kalleta," Ma'u indai nina haifeki to ki tafi da
Mubeena" Umma ta juyo jiki ba kwari tace "to se
ki taso muje" bata jira amsar M
ubeena ba ta sakai
ta fita, Mubeena da sauri tasa hijab dinta tabi
bayanta. Har suka iso gidan Umma bata yiwa
Mubeena magana ba, da sallama suka shiga gidan
amma suka ji shiru,, sai da sukayi sallama yakai
guda hudu(4) sannan suka jiyo wata dashashiya
r
murya nacewa "Wa..alai..kum..us..salam...,k
u..shigo..mana,, Umma ta kad'a kai sannan ta
shiga dakin data juyo murya, Mubeena tabi
bayanta. Umma ta zaro ido saboda abinda ta
gani ya masifar tsorata ta, duniya kenan! ... IYA
ce kwance akan wata yaga
laliyar tabarma duk tayi
fitsari akai, dakin in banda zarni ba abinda yake
yi. Umma a firgice ta k'arasa wajen Mubeena ta
bi bayanta, Iya ta k'are musu kallo sannan tace
"Wannan kamar Ma'u nake gani kodai mafarki
nakeyi? Umma ta runtse idonta sai hawa
ye 'Nice
Iya!" Iya ta fashe da kuka "kece Ma'u ! ashe rai
kanga rai? Ina jikar tawa take?" Umma ta nuna
Mubeena