Showing 21001 words to 24000 words out of 31145 words
su duba
wannan d'in
shima. Suna zaune a aji suna class
work din maths Uncle Hashim yazo ya kira
Mubeena anan ya tabbatar mata da cewa itace ta
lashe gasar!! Wohoho murna wajen Mubeena
kamar me ta rasa ma me zatai dan murna.
Assamibili aka k'ara hadawa anan aka kirawo
M
ubeena gaban assambili aka sanar da sauran
dalibai itace ta cinye gasar kuma ita zata wakilci
makarantarsu a gasar da za'ayi nan da sati biyu2
dalibai aka d'au ihu ana Up Up Up Mubeena!!
Mubeena kuwa sai murmushi take tana godewa
Allah daya bata nasar
a... Nafisa dajin haka ihu ta
saki ,tana wani fizge fizge daga k'arshe ta tada
aljanun k'arya malamin islamic studies yasa
prefect mata suka d'auke ta zuwa staff room dan
yayi mata ruk'iya nan kuwa be san na k'arya ne
ba. Mubeena kuwa se murna ake mat
a malamai
kuwa sai wani nan-nan suke da ita kodayake
dama can malamai suna santa saboda
kwazonta...Nafisa kuwa da Ustaz(malamin
islamic) ya gane cewa na k'arya ne,dorina ya
dauko zabgegiya ya shiga lafta mata, bashiri ta
tashi tana kuka sharaf sharaf
tana bashi
hak'uri,dariya yayi sanan yace ta koma aji, aka
dinga mata ihu ana cewa me aljanun k'arya a
rannar tayi alkwarin baza ta sake dawowa
makarantar ba, dan abin kunya data aikita baza
su barta ta zauna a makarnatar lafiya ba. Yau Ya
Ameen ya
ze dawo murna a wajen 'yan gidan
kamar me,kowa ka gani yana cikin walwala hatta
Ya Abdul... Mubeena kuwa cewa tayi a bar mata
zata mai girki me dadi, dayake yanason abincin
gargajiya fankaso da tuwo ta yi masa da miyar
taushe dan ya fad'a mata a waya
ya dad'e be
cisu ba,, su ya Nana kuma suka yi masa kunun
aya da zob'o. Bayan yayi parking din motar shi
ya shigo gida Amir da gudu yazo ya rungume shi
yana masa oyoyo , su Mubeena suka fifito suna
masa sannu da zuwa shikuwa yana amsawa fuska
d'auke d
a murmushi..ya k'araso cikin gida Umma
da Ummi kuma na falo suna jiranshi suka yi masa
sannu da zuwa sa kuma ya hanya. Ya amsa da
"lafiya lau nagode,,kuma nayi missing dinku
sooooooo much" a tare suka ce "muma munyi
missing dinka". Bayan yayi wanka ya
yi sallah ya
dawo ya zauna Mubeena tace abincinsa na kan
dinning table( teburin cin abinci) yaje ya zauna
yana budewa ya fara "wow nasan wannan aikin
kine Mubeena", Ummi tace 'ai kuwa kamar
kasani,kayan shan ne su Nana sukayi yimaka" yayi
murmushi "a
mma kuwa nagode lovely sisters"
Bayan ya gama cin abincin su Ummi ke sanar
dashi Mubeena ce zata wakilci skul dinsu ba
k'aramin murna yayi ba,a rannar ta faranta masa
rai. Washe gari ya sami Umma yake fad'a mata
cewa iyayen Faty sun takura masa daya t
uro dan
nan da wata hudu (4) za'ayi bikin yarta kuma
sunaso a had'a da na Faty...shikuma yana kunyar
fad'awa Ummi da Abba,, Umma tayi murna dajin
haka, ta kuma yimasa alkwarin zata fad'awa
Abban sannan kuma indai ya shirya to ba
matsala. yayi mata go
diya ya tafi. Umma ta sami
Abba ta fada masa yaji dadin haka dama yana
shirin yi masa maganar auren dan a ganinsa
lokaci yayi daya kamata ya zama cikaken mutum
wato yayi aure...yace ta fad'awa ya Ameen d'in
ya kwantar da hankalinsa zasuje shida yan-
uwansa su nema masa auren insha Allahu..
[12:34AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:48AM, 18/03/2016] Hapsat:
◆◆◆
AISHATUL
MUBEENA
◆◆◆
©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [125]-[130] Wakilin
shugabanin da suka shirya gasa wanda yazo daga
birnin taraya Abuja wa
to MR MIKE da shugaban
k'ungiyar masu zanen dake kano ALHAJI AL-
AMIN BAWA sune suka fito dan fad'an result din
bayan manyan-manyan kwararru a harkar zane
sun duba sun fitar da sakamako, Alhaji Bawa shi
zai dinga kiran suna yayinda Mr Mike ze dinga
d
'aga zanen dan kowa ya gani. Bayan sun yi d'an
jawabansu, Alhaji Bawa ya fara magana kamar
haka:" zamu fara da na sha biyar (15)" nan ya
fara kiran sunaye yayin da Mr mike ke d'aga
zanen, sai kuma wanda aka kira ya fito bainar
jama'a. Sai mutane su ta
fa masa/mata . A haka
dai yana fad'a har yazo ta biyu. Wanda ya kira
dalibi Ahmad Huzaifa, aka d'aga zanen shi nan
mutane suka fara ihu sosaii dan zanen nashi yayi
bala'in kyau. Bayan nan yace yanzu za'a d'aga
zanen wanda/wadda ta yazo ta d'aya, mutan
e
kowa ya baza ido yana jiran ganin wani zane ne
wanda ya zarce had'ad'un zanen da'aka nuna, da
kuma wani tauraron ne ko kuma wata tauraruwar
ce ta samu nasarar lashe gasar? Mr Mike wani
had'ad'en ko nace gaba da had'ad'e zanen ya
d'aga sama, zane ne
wanda aka yishi akan al'adar
bahaushe wato , da farko dai , bukka aka zana
yar k'arama me bala'in kyau a gefen ta kuma
tabarmar kaba ce wanda aka zana akushi da
kwanon sha da kuma kwaryar akai, ga butar
alwala a gefe, a d'ayan bangaren kuma atamfa ce
aka zana da kuma dan kwali irin na da, sannan ga
murajani da dai sauran kayan hausawa na mata.
Zanen yayi bala'in kyau mutum in ya kalla sai ya
rantse hoto ne aka d'auka a camera saboda
tsabar tsaruwar da yayi. Nan da nan wajen ya
gauraye da ihu kow
a sai washe baki yake yi daga
masu cewa "wow!" Sai masu cewa 'masha Allah"
duk dai, Kowa burinsa be huce yaga wanda/
wadda yayi zanen ba. Yan jarida kuwa da sauran
mutane sai d'auka hoton zanen suke. Mubeena
kuwa suna hira da su Husna taga an d'aga za
nen
ta wani farin ciki taji wanda bata tab'a jinsa a
rayuwarta ba,, ta runtse idonta sai hawayen
murna, ta kuma k'i fadawa su Ya Abdul cewa
zanen tane, sukuwa suna gefe sai fama zuzuta
zanen suke,amma kowa a zuciyarshi, ji yake
kamar zanen Mubeena ne
. Alhaji Bawa ne ya
dakatar da mutane daga hayaniyae da suke
dakuma ihu, yayi gyran murya yace , "yanzu zan
kira wanda yayi wannan zane, ina me farin ciki
kirin AISHATUL MUBEENA Muhammad Ameen!".
Murna a wajen su Husna kamar me ,sai kallon
Mubeena su
ke suna k'ara kallonta, fuskarsu
d'auke da farin ciki, Mubeena kasa tashi tayi da
kyar suka lalab'eta ta tashi jiki ba kwari ta nufi
inda aka kirata. Mutane dake ta jiran fitowar ta,
sai hango ta sukai tana cangala kafarta dan
zuwan wajen, mamaki duk
ya cika su, amma
wannan ta ciri tuta ashe dama da nakasasu masu
irin talent irinta? Ihun mutane ya k'aru gaba
d'aya suka tashi suna kallonta yayin da 'yan jarida
suka cika wajen suna d'aukar ta hoto, da kuma
hoto mai motsi(video). Isarta keda wuya , M
r
Mike abinka da arne cak ya d'agata sama! Duk
k'ok'arin datake dan ta kwace amma ya rik'e ta
gam, cikin d'aga murya da hausar sa da wadda
bata fita sosai yace " wannan itace ta lashe
gasar, itace tazo ta d'aya!"
Like · 2 · Reply · Edit · 6 February
[11:50AM, 18/03/2016] Hapsat:
◆◆◆
AISHATUL
MUBEENA
◆◆◆
©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [115]-[120] Umma
tace "hakane Iya amma..." Iya ta katse ta
"dakata" ta janyo hannun Mubeena ta rik'e gam
sannan tace "Aihatul mubeena nice kakar ki, nice
na haifi
mahaifinki SULAIMAN, nida mahaifinki
mun kasance masu wata irin zuciya,masu butulci
kuma wa'enda basu da godiyar Allah,, nan da nan
ta fada mata komai tun daga auren Umma da
Mal Sule har rannar da suka rabu" Mubeena ta
fashe da kuka,kuka take sosaii
haka ma Umma.
Mubeena tana kuka tace "Umma dama na fad'a
miki, na fad'a miki cewa Abba ba shine mahaifina
ba!" Umma cikin tsawa tace " shine mahaifinki !
Abba shine mahaifinki! , shine yaso ki a lokacin
da Mal sule ya k'i ki har yake ik'irarin cewa ke
ba
'yarsa bace, shine ya ciyyar dake, ya tufatar
dake, ya baki ilimi, daidai da rana d'aya bai tab'a
nuna bambanci a tsakaninku ke da 'yan'yansa ba,,
sabanin Mal Sule da ya firta da bakinsa kar na
sake ko da wasa nace ke d'iyarsa ce , wanda
shine si
llar gurguncewa k'afarki, wanda besan cin
kiba, besan shan kiba, besan wahala kiba, besan
komai naki ba! Abu d'aya ne ya miki a rayuwa,
shine sillar zuwan ki duniya , amma bayan haka
ba abinda ya tsinana miki a rayuwa, wallahi kome
Mal sule ze miki ya
nzu in aka d'auke Silan zuwanki
duniya dayayi baze ko kusa yi miki abinda Dr
Muhammad ya miki ba,, Mal Sule ya amsa sunan
sa na cewa shine ubanki wanda ya haife ki kawai,
amma ko kusa baze amsa sunan , wanda yayi
wahala dake tun kina yar gwililuwa har
yanzu,
wanda ya ci dake, ya sha dake,ya tufatar dake,ya
baki ilimi ya kuma baki tarbiya, Shine ya cika
sharud'an zama uba wanda uban naki wanda ya
haife ki ya kasa cikawa!(Ta sassauta murya ta)
amma Mubeena kar abinda nida Iya muka fad'a
miki ya sa
ki tsani mahaifinki, ko kusa kar ki fara
domin in badan shiba baza kizo duniya ba!....ta
k'arasa maganar cikin sheshek'ar kuka. Kukan
Mubeena ya k'aru sosai, tama kasa magana, sai
sheshek'ar kukan data keyi,,, Umma ta kalli Iya
dake ta faman sharbar k
uka tace "Iya kiyi hak'uri
ban fad"i maganar ba dan ta b'ata miki rai,
gaskiya ce kawai na fad'a, Iya tace" baki b'ata
min rai ba Ma'u, gaskiya ke kike fad'i, nayi dana
sanin abinda na aikata a baya"" Ma'u tace "Iya
bakiyi mana komai ba Iya wannan mag
anar ta
huce saboda ni tun d'ad'ewa da kika nemi
gafarata na yafe miki, dama ko baki nemi na yafe
miki zan yafe miki dan wallahi ni tamkar Uwa na
d'auke ki!" Ga wannnan ta aje mata bandir din
yan dubu d'aya(1) sannan tace "gobe insha Allah
zan aiko m
iki da sauran abinda kike buk'ata,
kuma insha Allahu za mu dinga ziyartar ki akai-
akai. Iya ta rik'e hannunta " Ma'u tsaya na fad'a
miki wani abu,, yau tsawon shekaru goma(10)
kenan ban sa Sule a idona ba, tunda yazo yace
min ya tafi birni cirani na
nuna ban amince ba
amma sam ya k' jin maganata ya tafi ya barni, be
kuma waiwayata ba, ko yana da rai? Ko ya rasu?
Allahu a'alam,, amma dan Allah in Allah ya had'a
ku dan Allah ma'u ku yafe masa ke da Aiha
(Aisha), ki kuma ce nima na yafe masa, dan in
a ji
ajikina kwanan ya kusa k'are da k'yar na k'ara
kwana a duniya ,nima ku yafe min Allah ya had'a
fuskokin mu a aljana..." ta fashe da kuka,,,,jikin
Umma da Mubeena yayi sanyi sosaii Mubeena tayi
dauriyar cewa "ni na yafe miki Iya, kuma ki dena
amb
aton mutuwa insha Allahu zaki tashi, cuta ba
mutuwa bace! " Iya ta girgiza kai "kayya! Suka
mata sallama suna kuka tana kuka suka rabu. A
gidan Mama ne, Mama ta kwantar da murya
tayiwa Mubeena bayanin komai, Mubeena wani
sabon kukan ta sake Mama na ra
rashinta, taji
tausayin Ummanta sosaii sosaii ga wani sonta
dake k'aruwa a zuciyarta,, sannan kuma taji
tsanar Mal Sule a zuciyarta, ji take ba wanda ta
tsana sama dashi..godewa Allah tayi daya bata
uwa ta gari kamar Umma dan ita gani take tafi
kowa
dacen uwa a duniya! Haka suka koma gida
dukkansu ba farin ciki da walwala..
◆◆◆◆◆◆◆
Washe garin rana Allah yayi wa Iya cikawa,, su
Umma sunji mutuwarta sosaii a wannan dak'in
Allah yayi mata cikawa cikin dare. Da sassafe su
Umma suka tafi suna ta kuka
abun tausayi
mussaman ma Mubeena, da 'yan gidan suka tafi
gabad'aya har da Abba, dan shima yaji mutuwar
dan ya santa, lokacin da 'aka kwantar da
Mubeena a asibiti da cutar polio ta sameta,,sai
da suka fara sauka a gidan Mama sannan sukaje
gidan mari
gayiya Iya,, a lokacin ma ko wanka
ba'a yiwa gawar ba, Umma da taimakon Mubeena
su suka wanke gawar tas aka samata likafani aka
fita da ita ,maza suka sallaci gawar aka kaita
kuhewarta , Allahu akbar Allah kasa mu cika da
imani, ka bamu kyakyawan K'ar
she Ameen ya
Allah.. Ba wani zaman makoki akayi ba tunda wa
za'ayiwa gaisuwar? Dama Mal Sule ne kawai d'an
data haifa kuma baya nan bai san ta rasu bama,
'yayan mijnata kuwa Bashir da Hauwa sun dad'e
da dena kulata bama sa k'asar gabadaya. A 'yan-
uw
anta kuwa ita kad'ai tayi ragowa duk sun
rasu,, sai dai sauran dangi da ba'a rasa
ba..Masa'udu dama shi ake yiwa gaisuwar dan
shine ya kula da ita tun data sami rashin lafiyar
har ta warke, shima kuwa a rannar data rasu
admission dinsa ya fito yaci Ah
madu Bello
unibasiti zaria(ABU zaria) dan haka ya had'a
kayansa ya tafi Umma kuwa kud'i me yawa ta
bashi tace yayi harkar makaranta dashi ya yafi
yana ta godiya.
[12:35AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:46AM, 18/03/2016] Hapsat:
◆◆◆
AISHATUL
MUBEENA
◆◆◆
©
MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [135]-[140] Bayan an
dawo hutun tak'aitacen lokaci. Aysha Amatulah:
to barkan mu da dawowa. Hajiya Mubeena shin
wai ta yaya kika tsunduma cikin harkar zane-
zane? Mubeena: To agaskiya nidai na taso ne
kawai na gani in
ayi, a lokacin inga abu ya min
kyau sai na zana shi, cikin ikon Allah kuma sai
kiga zanen ya fita sosaii...lokacin da ina primary
kuma in kika duba littafai na na arts zaki ga inaci
sosaii, koda merit za'a bada ma a Art ni ake
bawa. Kuma akwai Yayana
Ya Ameen shine ya
cigaba da ban kwarin gwiwa har nazo matakin
danake yanzu. Aysha Amatullah: madalah, to
kafin ki fara wanan zane-zanen mene burinki a
rayuwa? Mubeena: Burin na da shine na zama
likita dan nima na bada gudunmawa ta wajen
yak'i da wann
an cutar sai kuma Allah beyi ba.
Aysha Amatullah: to Allah zaba mafi alheri, meye
ya fi b'ata miki rai da kuma abinda yafi faranta
miki rai? Mubeena: Abinda ya fi b'ata min rai
guda biyu ne na d'aya ya shafi personal life dina,
na biyun kuwa shine, id
an naga yan'uwana masu
wannan cuta ta polio suna bara ko kuma suna
cikin wani hali na rashin gata a gaskiya raina na
sosuwa kuma ina iya k'ok'ari na dan ganin na
taimake su. Sannan abinda yafi faranta min rai
shine, ina tuno irin nasororin dana samu a
rayuwa, sannan kuma ina ga masu irin cuta ta
wato polio basa fuskantar wani k'alubale a
rayuwa ,suna jin dadin rayuwarsu sannan suna
samin gata daga wajen iyayensu dama al'uma
baki d'aya, to nakan ji raina yayi fari . Aysha
Amatullah: Allah sarki, y
anzu zamu d'auki waya
guda biyu(2) duba da yanayin lokaci, zaku turo
sak'o ne ta wannan lambar 064**** sannan zaku
kira mu ta 064****. Mutane an kira an mata
fatan alheri, an kuma turo sak'oni ba adadi.
Aysha Amatulah:wani kira zaki yi ga iyaye da
ku
ma masu cutar polio? Mubeena: kiran da zanyi
shine dan Allah iyaye su dinga bada yayansu a
dinga musu d'igon rigakafi, sannan iyaye su dage
su dinga gano talent din da suke dashi su
k'arfafa musu gwiwa, bawai su dinga barinsu
suna bara ba, da sauransu
. Sannan irina masu
wannan cuta ta polio, ganin suna da nakasa kar
hakan yasa su fidda rai da rayuwa , su d'age suyi
karatu suma su zama wasu a dinga damawa
dasu, in hakan ya faru zan fi kowa farin ciki.
Aysha Amatullah: to duba da yanayin lokaci mene
sak'on ki na k'arshe? Mubeena: to Alhamdulilah
ba abinda zance sai in godewa Allah da kuma
iyayena nakan ji farin ciki sosaii in na tuno da
iyayena,yayena da k'anina, da sauran dangi.
Aysha Amatulah: to masu sauraron mu lokaci
yayi halinsa , anan za
mu k'ark'are wannan shirin,
Hajiya Mubeena muna godiya da kika amsa
gayyatar mu, da fatan duk sanda muka sake
neman ki zaki amsa kiranmu. Mubeena: to nima
nagode masu saurarona da kallona ina muku
fatan Alheri,(tayi murmushi) sai anjima. Ahaka aka
ga
ma shirin, ta fito driver yaja suka tafi.
*********** A yau ne aka d'aura auren Ameen
Muhammad Ameen da Fatima Adam, Aisha
Muhammad Ameen(Nana) da kuma Saifulahi
Abdalah. Ansha biki sosaii an kuma kashe kudi
dai-dai misali, Mubeena kuwa lemukan nan da
'aka
bata kyauta su ta bada akayi hidimar biki da su,
sannan katuwar jaka da calanda me sunayen Allah
ta musu a matsayin gudunmawa sun sha murna
tare da yi mata addu'ar Allah ya saka mata da
alheri. Bayan biki aka kai amarya Nana gidanta
dake Hotoro,
Sannan amaryar Ya Ameen Faty aka
kaita gidan ta dake Janbulo. A yau su Mubeena
sukayi final exam dinsu, sunsha kukan rabuwa da
dalibai, Mubeena da Asiya ma ansha kuka,
malamai sunyi bak'in cikin rabuwa da Mubeena
sosai , hadda masu kwala, bayan sunyi
sharing
contacts driver yazo ya d'auki Mubeena suka
koma gida, Mubeena cike da kewayar dalibai,
malamai dama makarantar baki d'aya. Yau ta
kama rannar lahadi kuma dama duk Lahadin
k'arshen wata sukan je shopping... Suna cikin
mota dan zuwa shopping
d'in Abba ne ke driving
dan yau yace sha'awar driving yake saboda ya
d'ad'e beyi ba, Umma na gaba, yayin da Husna,
Amir da Mubeena ke bayan mota Ummi kuwa taje
bikin 'yar aminiyata. Suna tafe cikin raha da
anashuwa. Can wata mota ta taho da gudun
gas
ke, dai-dai lokacin da wani datijjon mutum
yazo tsalaka titi, ai kuwa fuu motar ta bige shi,
bata ko tsaya ba drivern mota ya k'ara falawa da
gudu, cikin 'yan sakani aka dena hango motar sai
k'ura da motar ta tayar... shikuwa dattijon
mutumin nan yana
baje a titi jini sai zuba yake.
Abba da sauri ya fito daga motar yana salati
suma su Umma suka fito dan ganewa idonsu, a
firgice suka k'araso wajen da mutumin ke kwance
cikin jini, Umma da ta k'araso wajen da sauri,
dora idonta akan mutumin keda wuya
ta kwala