Showing 9001 words to 12000 words out of 31145 words

Chapter 4 - AISHATUL MUBEENA COMPLETE

13 Sep 2026

53

za'ayi a gidan nan" Nana tace

"Aikwa dai" Ya zauna akan kujera yana dana waya,

Nana ta kalleshi "yauwa na tuna,Ya ameen kasan

wata f

aty? " da mamaki yace "Yes nasanta" Nana

tace " A layin nan take?" Da sauri yace "A'ah a

unguwar nan dai suma suke,,me ya faru wai?"

Tace "Amma ni bansanta ba,Wani ta aiko da

sak'o dazu wai abaka,Am sorry mantawa nayi,,

da sauri yace "sak'on me? Fada

min" tace "bari

na dauko maka" yace "yauwa" ala-ala yake ta

kawo masa yaga ko mene ne Bata dade ba kuwa

sai gata da yar k'aramar jaka a hannunta ta mik'a

masa, cike da zumud'i ya karba yana washe baki,

,Mubeena kuwa bata ce musu komai ba shiru tayi

k

amar ma bata san abinda suke ba ,, Yana karba

ya fice abinshi ya nufi dakinshi. Kan gadonshi ya

baje da sauri ya dauko jakar yana bud'ewa wani

kati ya gani ya sha kwalliya cikin hanzari ya bude

ya fara karantawa kamar haka "" Remember the

good times w

e had spent together,And the

beautiful future we had dream of,,Darling i never

wanted to create a distance between us...please

let us bridges the gaps,,. Wani tsale murna yayi

ya rungume kati a fili yace "Bakomai my faty na

hak'ura!" Wayarsa ya dauko

yayi dailing number

ta,akace a kashe take,,Yayi tagumi yana sake

kalan katin shi abin mamaki yake basa ma ashe

dai abdul da gaske yake da yace da kanta zata

dawo su shirya!,, Wayarsa yagani tana ruri da

sauri ya dauka,, Ashe faty ce cike da murna Yake

tambayarta ta canza number ne tace masa eh,,

bayan sun gaisa tace "Kayi hak'uri ya ameen

rashin fahimta ne ya kawo hakan, amma yanzu na

gane komai,ina neman yafiyarka" yayi murmushi

"Bakomai faty darling Allah ya barmu tare

sweetheart" tace ameen de

ar suka cigaba da

hirarsu ta soyayya. Aishatul mubeena bayan ta

gama yiwa Amir assignment din ya tafi wajen su

umma,,ta juyo ta kalli nana, "Ya nana wacce

FATY wai" Nana tayi murmushi "inaga fa

budurwasa ce !Dan dama rannar na labe naji suna

hirarta

shi da ya abdul ""Mubeena bata san dalili

ba sai kawai taji gabanta ya fadi a sanyaye tace

"Amma nikuwa bai taba fada min ba" Nana ta

harareta da wasa "Ko ni dana girme ki be fada

min ba saike yarinya" mubeena tayi murmushi "To

yaya baba" nana tace "K

insan mu akwai san

girma" Mubeena tayi dariya ...Ta tashi ta shiga

cikin daki ta zauna jikin gado tayi tagumi Tana

tunane-tunane kala-kala a zuciyarta.. Umma ce

ta shigo dakin,,kusa da ita ta zauna a hankali ta

dube ta tace "me yafaru naga kin yi shir

u kina

tunani? Meke damunki?" Mubeena da sauri tace "

bakomai ummana kaina ne ke ciwo kawai" umma

tace "toh kuma ai se ki sha panadol,bari na

dauko miki magani kisha" Ta tashi ta dauko

mata,, ta k'arba da kyar ta sha maganin duk jinta

take wani iri,,

Ta d'an yi jim,Can ta tuno wani

abu da sauri ta kalli umma tace "umma dan Allah

wata tambaya zan miki amma dan Allah umma

kimin alkwarin zaki bani cikakiyar amsar"" umma

ta danyi jim sannan tace "inajinki indai inada

amsar insha Allahu zan baki ita"

Mubeena tayi

murmushi "yauwa ummana" sannan tace.. "Umma

DAN ALLAH WAYE MAHAIFINA? Gaban umma ya

fadi sosaii cikin dauriya tace "Wai ke mubeena

me ke damunki ne? Sau nawa kike tambayata

nace miki Abba ne babanki,Abba shine babanki

kar ki sake yi min

wannan tambayar tunda kinsan

amsar"" mubeena ta runtse idonta se

hawaye,cikin murya kuka tace "Umma Abba

bashine mahaifina ba, Na dade da sanin haka,"

Ummi cikin muryar masifa tace "to sai ki fada

min waye Mahaifin naki,tunda ni baki yadda dani

ba Mu

beena ta fashe da kuka "Umma ba haka

bane,Umma Dan Allah ki fada min,Kar kisa na

fara tunanin ko ni yar shege ce,,Ba ta hanyar

Aure aka haife ni ba!! Umma da sauri ta juyo

idanunta fal da hawaye tace "Auzubillahi" "ke ba

yar shege bace! Ke yar halak c

e! Idan bakyason

bacin raina to ko da wasa kar na kuma jin

maganar nan,,tana gama fadan hakan ta fice

daga dakin tana share hawayenta!

Comment as:

Subscribe to: Post Comments (Atom)

Saturday, 15 October 2016

Posted by MissHafcy at 08:00

AISHATUL MU

BEENA 85-105

[12:29AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy:

◆◆◆

AISHATUL MUBEENA

◆◆◆

©NA MISS HAFCY

®ONLINE HAUSA WRITERS [80]-[85] Mubeena

kuwa kukan ta ta cigaba dayi daga baya barci

b'arawo ya sace ta. Da asuba ta tashi tayi

sallolinta da kuma nafila,,Tana zauna

tana karatun

Alkur'ani har gari ya washe.. Bayan ta idar da

karatun ta tashi ta nufi dakin Umma,,zaune ta

tadda ita akan sallaya Tana addu'a,A bakin gado

ta zauna tana jiran Umman ta kamalla addu'oin

ta,, bayan Umma ta idar ta juyo ta kalli

mMubeena,

da sauri Mubeena ta k'ara duk'awa

k'asa ta gaishe ta cikin sanyin murya "Umma ina

kwana,kin tashi lafiya?" Umma tayi murmushi

"Lafiya lau Mubeena" Mubeena tace "Umma dama

ina neman yafiyarki naga jiya kamar na b'ata miki

rai,insha Allahu baza ki sake

jin maganar daga

bakina ba" Umma tace "Ban yi fushi ba

Mubeena,bakomai komai ya wuce" Mubeena ta

washe baki "yauwa Ummana nagode sosaii"

Umma tace "muje muyi karin kumalo(breakfast)"

Mubeena tace "Toh" Bayan sun gama cin

abincin,suna zaune ya Ameen y

a shigo sanye da

kayansa na pilot ya rik'e hular a hannunsa sai

murmushi yake yi, Har k'asa ya duk'a ya gaida

umma ta amsa da fara'arta,Mubeena ma ta

gaishe shi ya amsa. Bayan sun gama gaisawa ya

kalli Mubeena"Sis ni kinga yau zan koma aiki" ta

canza

fuska "Da gaske bro? ai nazata sai next

week" yayi dariya "Yauwa dan Allah inaso ki

maida hankali akan gasar zanen nan da za kuyi

kinsan Ran monday zaku fara,Ku goma(10 )Aka

zaba kuma a cikinku ne za'a zab'i ta d'aya( 1)

Please inaso ya zamana kece t

a dayar nan! Zaki

iya, ga wannan(ya mik'a mata leda) duk wani

items da zaki buk'ata a harkar zane yana ciki

inaso ki fara practice tun yau,,Please ki dage "

tayi murmushi "Toh bros nagode sosaii insha

Allahu zan fara daga yau mu dage addu'a,insha

All

ahu bazan baka kunya ba." Yayi murmushi

"Dats my sis,ki kuma sa a ranki zaki iya,indai kin

yadda da hakan to baza ki samu matsala ba insha

Allahu". Sai a lokacin umma tace "Gaskiyane Allah

ya bada sa'a" Dukansu suka ce "Amin."

Gabad'aynsu hadda Abba s

uka rako shi harabar

gida,Mubeena kuwa daurewa kawai tayi dan ji

take kamar tayi kuka idanunta sun yi rau-rau

alamar me shirin yin kuka, shikuwa sai k'ara

jadada mata yake akan ta dage sosai, itakuwa

tana cemasa "insha Allahu zata dage sosai" su

Abba

suka mai fatan alheri suka kuma mai

addu'ar Allah ya kiyaye hanya,sannan suka shige

ciki,suka barshi daga shi sai Mubeena datake jikin

motar tayi jim ta kasa magana ,daga baya ta

kalleshi tace "Yanzu bros sai yaushe? " yace

"Gaskiya for now bansani b

a" tace "Okay Allah ya

taimaka ya tsare ka Ameen,A dawo lafiya" yace

"Amin sis nagode" har ta tafi sai ta dawo da

sauri ta kalleshi "Ka gaida FATY in kunyi waya"

bata ko jira amsar shi ba ta shige ciki, shikuwa

mamaki yayi ,ko taya tasan faty budurwas

a ce ?

oho. Mota taja suka tafi.. Yau monday da sassafe

suka shirya itada Amir suka tafi skul,Dayake dama

can Husna da ya Nana sun fita aji a makaranta,su

sunyi candy last year kuma Abba yace sam be

yadda su fara unibasiti ba sai sunyi aure,Da kyar

d

a taimakon su umma ma ya barsu suka fara

zuwa Computer school. Tana zaune a kan bencin

ta ita da k'awarta Asiya suna hira,dayake lokacin

break ne,inda Mubeena ke bata labarin gasar

zanen da za'ayi,, Uncle hashim ya shigo nan take

ajin yayi tsit,suka t

ashi suka gaishe shi ya amsa

sannan yace duk wanda ya kira sunansu su same

su a Principals office, Ya fara kiran sunan kamar

haka: "Nafisa Jameel, Auwal Isah, AISHATUL

MUBEENA MUHAMMAD AMEEN,, Sai ku

biyoni,"Yana gama fadan haka ya fita,yayin da

yan

ajin kowa ya shiga fadan albarkacin

bakinsa,daga masu cewa laifi sukayi sai masu

cewa suspension za'a basu, duk dai, Ita kuwa

Mubeena sam bata damu ba dan tasan dalilin

kiran,Suka jera ita da Nafisa sai yatsine take ita

tana tak'ama an zo har aji an k

ira suna hada suna

ta. A office suka tadda malamai da sauran

Dalibai guda bakwai(7) suna jiransu,bayan sun

gaida sauran malaman uncle hashim ya fara

magana cikin harshen turanci kamar haka: "Mun

tara kune anan ba dan komai ba dan wata

gagarumar gasa

da gwamnatin taraya ta shirya

akan ZANE-ZANE,wato ART, ana neman kuma

mutum d'aya mace ko namiji wanda ze wakilci

kano baki daya,dan haka mukayi registar wannan

makaranta, da farko dai a cikinku ku goma nan

damuka zab'a, gobe zamu fara gasar mu a iya

makarantar mu kuma duk wanda ya cinye shine ze

wakilci makarantar mu a gasar da za'a yi da

sauran makarantu guda biyar(5) da gwamnati ta

tantance, idan Allah yasa wakilin makarantar mu

ya samu ya lashe gasar to shine ze wakilci kano

baki d'aya a gasa

r da za'ayi da sauran state

(jihohi) dake k'asar nan tamu Nigeria,,da fatan

kun gane?. Gaba ki d'aya suka ce "mun gane".

Principal ya kuma musu wani k'arin bayani tare

da yi musu fatan alheri daga baya aka salame su

kowa ya koma ajinsu Nafisa sai wani

iyayi take a

zuciyarta kuwa cewa take aiy tasan ita zata lashe

gasar. Suna shiga aji yan class suka fara

tambayarsu abinda ya faru Nafisa ta k'arfi ta

fada musu ,aikuwa suka d'au ihu "Se kinyi

wallahi!!,se kin cinye nafisa!, ita kuwa sai busa

hanci

take yi, cikin murya isa ta fara magana"

hmm ai ni dama sun ban mamaki,ai da basu b'ata

lokacinsu ba wajen cewa sai anyi gasa sun zab'i

gwani,suna b'ata lokacinsu ne amma kowa yasan

nice zan cinye,ko ya kuka ce friends?" Suka kuma

ihu "hakane Artist n

afeesa, sai kinje abuja kin

karbo mana award dinan!

Share

[12:30AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:53AM, 18/03/2016] Hapsat:

◆◆◆

AISHATUL

MUBEENA

◆◆◆

©MISS HAFCY

®ONLINE HAUSA WRITERS [95]-[100] Uncle

Hashim murmushi yayi yace "To kunyi gueesin

right" Na

fisa kuwa iya kulawa ta kulu batasan

sanda taji hawaye ba,dataga abin ya fara isarta

sai ta fara zage-zage "wallahi bazan yadda ba!

Wannan ma aiy sankai ne, aikin banza

kawai,kuma...bata k'arasa maganar ba taji saukar

mari a fuskarta ji kake tas! Kall

o ya dawo kan

Nafisa dake rik'e da kuncinta tana hawaye, sai a

lokacin suka gane ashe anty sa'adah (english

teacher dinsu) ce ta wanka mata mari,,wasu suka

hau yi mta dariya yayin dana kusa da ita sukai tsit

dan suna tsoranta. Anty sa'a taci gaba "ke

waye

sa'anki a cikinmu saboda tsabar rashin kunya mu

sa'aninki ne?" Uncle Hashim ya k'araso wajen

"bari ni da ita zanyi maganinta" ya kalli Nafisa

dake ta sheshekar kuka yace "shige muje" ba shiri

ta bishi Zuwa staff room...Dama lokacin tashi

yayi da

n haka aka sallami dalibai. Mubeena ce

zaune ita da Asiya a bus stop din skul din,

Mubeena da Amir na jiran drivernsu yayin da

Asiya ke jiran skul bus din unguwarsu Asiya ta

kalli Mubeena "gaskiya Mubeena kin burgeni, ni

dama nasan ke zaki cinye,dama

nice ke!"

Mubeena tayi dariya "hmm Asiya kenan kema fa

kinada taki baiwar fa" Asiya tace "tame fa?"

Mubeena ta cigaba" na rubuta labarai mana

novels ni kome zaki min bazan iya rubuta

k'agaggen labari ba wallahi,ke kuwa fa kina iya

k'irkira ki rubatas

u kala-kala" Asiya tayi dariya

"kema dai Mubeena nan abinda ni kadai nake

rawa ta nake kida na, in na rubuta da sisters dina

kawai nake bawa su karanta sai kuma ke"

Mubeena tayu murmushi "duk da haka' Asiya tace

"kodayake inmunyi candy inason na fara

publishing din wanda wasu danake rubutawa

wasu kuma na fara typing dinsu a whatsapp ko

facebook wato online writeups" Mubeena tayi

murmushi," lallai ashe kema kin kusa zama su'

Benaxir,Lubbatu,Chuchu,Ybk,Jabo,Faty

axland,etc danaji su Ya Nana na fada

n su suna

rubuta online hausa novels ,,kinsan su Ya Nana

sun dage da karatun hausa novels,kullum zaki

gansu mak'ale da waya suna karatun littafi" Asiya

tayi dariya "lah ashe kema haka,wallahi nima

sisters dina haka kullum cikin karatu a whatsapp

har

group garesu kala-kala na hausa novels"

Mubeena tace "aiy suna k'ok'ari". Drivern su yazo

suka wuce gida. Suna shiga gida Amir da gudu

yayi falo yana kiransu umma,suka firfito a tsorace

dan a zantonsu wani abun ne ya faru marar

dadi...Yayi wani tsalle

ya kalli umma "Yaya

Mubeena ce tazo ta d'aya(ya nuna yatsan sa guda

d'aya) Ummi ta wangale baki "Ai daman nasan a

rina! ina 'yar tawa take? Mubeena ta k'araso tana

murmushi "gani Ummina!" Ummi ta rungumeta

tana murna "Allah ya sanya Alheri" Mubeena t

a

amsa, Ameen ummina! Amma kinsan meye?

Ummi ta girgiza kai" next week zamu kuma yin

wata gasar da Nafisa Jameel wanna wadda nake

baku labarinta" Ummi tace "ai insha Allahu zaki

samu nasar 'yata zamu dage da addu'a" Umma

tace "kar kisa tsoro a ranki

insha Allahu sai kin

cinye gasar nan" Mubeena tace "Ameen my

mother's" Umma ta cigaba "bari na kira Ameen

na sanar dashi wannan abun arzik'in" ta shiga

d'aki dan dauko wayarta. Murna wajen ya Ameen

ba'a magana sun dad'e suna waya yana bata

kwarin gwi

wa akan ta dage zatayi nasara insha

Allahu ta kuma dage da addu'ar daga k'arshe

sukai sallama ta mik'awa Umma wayarta.

Mubeena ce zaune akan carpet din falon Umma

abinci ne a gabanta amma ta kasa ci tayi tagumi

da alama akwai abunda take tunani, Umma

ta

k'araso wajen ta tace "Mubeena me ke damunki?

Kinsa abinci a gaba tun dazu kink'i ci? Mubeena

ta d'ago idonta sharkaf da hawaye tace "Umma

wallahi wani labari aka ban yau in na tuno duk sai

naji ba dadi" Umma ta kara matsowa kusa da ita

"na mene?"

Mubeena ta share hawayen nata

sannan taba umma labarin da Asiya ta bata na

yarinyar nan me cutar polio data ja mata

paralysed,, Umma itama sai ta fashe da kuka ta

tuno irin gwagwamayar data sha itama lokacin da

Mubeena na k'arama,, Mubeena ta katse m

ata

tunanin da cewa "Umma wannan dubu hamsin

d'in dana samu a wajen musabak'ar nan nakeso

kiban muje dake muyi mata siyayya kayan abinci

da kayan sawa da kuma daiper size dinta,Atamfar

nan kuma abani guda biyu na kaiwa mamanta

d'aya sannan kuma aba S

afi tella ta dinkawa

yarnyar, mu kai gidansu" Umma tayi murmushi

"Kaji d'iya ta kwarai Mubeena ke daban ce!

Kinada zuciya me kyau Mubeena a kullum godewa

Allah nake daya bani 'ya kamar ki, Mubeena Allah

ya shi miki albarka ya kuma albarkaci rayuwarki,

"

Mubeena ta ce "Amin Ummana nima ina alfahari

dake, Allah ya saka miki da alheri ya biya miki

duk bukatan ki duniya da lahira" Umma tace

"Amin nagode AISHATUL MUBEENA" amma sai ki

bari Abbanku ya dawo sai a sanar dashi koh?

Mubeena tace "gaskiya kam

Allah ya dawo dashi

lafiya"

[11:55AM, 18/03/2016] Hapsat:

◆◆◆

AISHATUL

MUBEENA

◆◆◆

©MISS HAFCY

®ONLINE HAUSA WRITERS [90]-[95] Mubeena

tayi shiru can sai hawaye suka fara zirarowa,Asiya

a rude ta fara share mata hawayen "yi hak'uri

Aisha wallahi ba d

an na saki kuka nayi wannan

tambayar ba kawai dai..." Mubeena ta katse ta

"bake kika sani kuka ba Asiya... bari na fad'a

miki" Asiya tace "toh inaji" Mubeena ta

cigaba"cutar poliomyelitis (polio) ce ta maida ni

haka! Asiya ta zaro ido "polio??,da kina

k'arama

ba'a miki rigakafi ba? Mubeena ta share

hawayenta "eh,nidai kawai watarana na wayi gari

naga kafana ta dawo haka,ba zan iya tuna abinda

suka faru da ba,kuma banasan na tambayi Umma

tunda naga itama basan zancen take ba" Asiya

cikin sanyin mu

rya tace "Allah sarki,Allah ya

kiyaye gaba,ya kuma sauwak'e. Mubeena tace

"Amin". Asiya ta girgiza kai cike da takaici tace

"akwai wata yarinya a unguwar su cousins d'inmu

itama polio ne, itafa ya ja mata paralysed,ga

iyayenta talakawa ne,ko wheel cha

ir ba tada, a

k'asa zakiga sun shanya ta,tayi fitsari etc duk

anan sai dai su gyra,yarinyar 12years amma ta

k'ank'ance sai ki rantse bata fi 4-5years ba abun

tausayi,rannar danaje gidan dubu d'aya(1000) ne

a hannuna wallahi duka na basu naji tausayins

u

ita da iyayenta,har takai ta kawo daga karshe

maman bara takeyi saboda sukansu wani sa'in

abincin da zasu ci gagararsu yakeyi,sun ban

tausayi sosaii" ta k'arasa maganar tana kuka...

Mubeena itama sai ta fashe da kukan, zancen ya

matuk'ar bata tausa

yi,, ta dage tace "Allah

sarki,shi yasa nake godewa Allah kullum dakuma

iyayena,amma zaki gane gidan? Asiya tace "eh

zangane kusa da gidan su cousins d'inmu ne"

Mubeena tace "insha Allahu gobe zan zo ki

rakani" Asiya tace "to bakomai Allah ubangiji ya

kaimu" Mubeena tace "Amin." Akazo aka

kirasu,Nafisa sai wani iyayi akeyi,bayan an musu

bayanin komai aka raraba musu kayan da zasuyi

zanen akace kowa ya zana abu mai kyau amma

banda abu me rai,an basu minti talatin(30mint)

nan da nan suka fara. Mube

ena kuwa exactly

abunda ta zana jiya (har ya Abdul yace yayi kyau

daga k'arshe yace yanso tace ya dauka),ta zana

,tunda taji yace yayi kyau to tasan kuwa tabbas

yayi din da gaske,, dan haka ta k'ara zana irinshi

har yafi na jiya ma kyau... Lokaci ya c

ika,uncle

Hashim ne ya k'arbi zanen aka bawa masana

zanen da hukumar makarantar ta gayyato takanas

don su duba su kuma fad'i sakamakon tun daga

zanen daya zo na d'aya har zuwa na

k'arshe....Bayan sun dade suna duba suka fadawa

hukumar makarantar resu

lt din sannan suka tafi..

Uncle Hashim ne yazo yace musu su koma aji za'a

had'a assambili na mussaman wanda anan ne za'a

fad'i sakamakon. Nafisa tana shiga aji yan aji suka

hau tafi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login