Showing 15001 words to 18000 words out of 31145 words

Chapter 6 - AISHATUL MUBEENA COMPLETE

13 Sep 2026

58

"gata nan, tare muke ma" Iya ta k'ara

fashewa da kuka "zo nan 'yar jikalle ta, ni bansan

ma da wani ido zan kalle ki ba, randa aka haife ki

nida mahai....." Umma ta da sauri ta katse ta "Iya

komai ya wuce dan Allah a bar zancen nan baki

yimin komai ba ni kuma koda kin min ma na yafe

miki, garin yaya kika sami wannan ciwon?". Iya

tana kuka tace "rannar ina zaune ni kad'ai a daki

naji mag

e a gefena, kinsan dama ina tsoron mage

,to tun daga nan na tsorata sosai bakina ya juye

magana ma na kasa yi, hannuna ma na kasa

d'agawa balle na d'aga kafata,, Haka na kwana

ina kuka bame ceto na,, washe gari makota da

suka ji shiru suka zo suka bud

'e kofar aka fito

dani aka kaini asibiti anan akace mutuwar b'arin

jiki nasamu,,shine nake kwance anan masa'udu

(dan k'anwar iya) shine kawai yake kula dani,,, ta

sake fashewa da kuka,, Umma ta fashe da kuka

hakama Mubeena dama ga Mubeena da tausayi.

Iya ce ta katse musu kukan da cewa "Ma'u baki

fad'a wa jikartawa ni kakar ta bace ba? Dan daga

ganin alama bata san nice na....Umma ta katse ta

" Iya dan Allah ya isa haka, zancen nan ya wuce

banse tasan komai ba ai" Mubeena duk ta rikice

ta kasa gan

e maganar tasu, sun caja mata

kwakwalwa....Iya cikin dashashiyar murya tace

"Ma'u RANNAR WANKA BA'A BOYEN CIBI!

Like · 2 · Reply · Edit · 3 February

Khadija Muhamed

[11:52AM, 18/03/2016] Hapsat:

◆◆◆

AISHATUL

MUBEENA

◆◆◆

©MISS HAFCY

®ONLINE HAUSA WRITE

RS [105]-[110] Mubeena

ta shafa fuskarta" bakomai yusra Allah ya baki

lafiya" yusra ta rik'e hannunta "Amin",, sukai

musu sallama suka juya suka bar Maman nata

kukan murna k'aninta mu'az yazo shima murna

kamar me, ya dinga shiwa su Mubeena

albarka,,d

ama kudin reg din makaranta yake

nema ya cika dubu biyar(5000)amma ta gagara

sai gashi Allah ya share musu kukunsu. A mota ne

Umma ke ba ya Abdul labarin yarinya jaji

tausayinta sosaii shima ya kuma ji dad'i da'aka

musu wannnan taimakon..Suka aje Asiy

a a gida

suka mata godiya sannan suka koma gida. Kwanci

tashi ,gobe ne Mubeena da Nafisa zasuyi gasar

su, Mubeena tayi practice sosai, a rannar raba

dare tayi tana addu"ar Allah ya bata sa'a su

Umma ma haka duk 'yan gidan ma, Ya Abdul ma

yazo yayi ma

ta fatan alheri,dan yanzu ba laifi

yana sakar mata fuska. Da sassafe ta tashi ta yi

sallolinta sannan tayi zikirorinta ta shirya suka

huce makaranta...bayan an fito break 'yan class

sun zagaye Nafisa dake wa mickey mouse din

data zana musu fenti wai z

asu sa a wall bangon

class din ,bayan ta gama ta d'aga zanen "ya kuka

gani friends?" Suka hada baki "Woww..yayi kyau

sosaii amma da Mubeena ce ta zana munsan se

yafi haka kyau" Nafisa ta juyo a fusace "lallai ma,

in sha wahala in muku abu amma kuce da

wata

banza ce tayi sai yafi kyau?" D'aya daga cikinsu

tace "a'ah kinga kar ki sake ce mata banza "

Nafisa tace "an fad'a mata d'in, bari ku gani" nan

da nana ta warce zanen ta yayaga shi, sannan ta

fita daga ajin tana zage-zage,sukuwa dariya

sukayi

sukace "kanki kika cuta ai,wahalaliya kawai.

Mubeena ce da Nafisa zaune suna jiran akawo

musu abubuwan zanen, Uncle Hashim ya shigo ya

raraba musu sannan yace mutum d'aya ta biyo

shi saboda za'a raba musu aji gudun kar wani ya

kwafi na wani, caraf Naf

isa tace zata bishi ,hakan

kuwa akaiyi yabar Mubeena da anty Sa'a sannan

shi kuma suka tafi wani staff room d'in shi da

Nafisa. Cikin minti talatin suka kamala zanen

kowa yayi submitn,, suka koma aji ... aka bawa

wanda suka duba zanen kwanaki dan su d

uba

wannan d'in shima. Suna zaune a aji suna class

work din maths Uncle Hashim yazo ya kira

Mubeena anan ya tabbatar mata da cewa itace ta

lashe gasar!! Wohoho murna wajen Mubeena

kamar me ta rasa ma me zatai dan murna.

Assamibili aka k'ara hadawa an

an aka kirawo

Mubeena gaban assambili aka sanar da sauran

dalibai itace ta cinye gasar kuma ita zata wakilci

makarantarsu a gasar da za'ayi nan da sati biyu2

dalibai aka d'au ihu ana Up Up Up Mubeena!!

Mubeena kuwa sai murmushi take tana godewa

Allah

daya bata nasara... Nafisa dajin haka ihu ta

saki ,tana wani fizge fizge daga k'arshe ta tada

aljanun k'arya malamin islamic studies yasa

prefect mata suka d'auke ta zuwa staff room dan

yayi mata ruk'iya nan kuwa be san na k'arya ne

ba. Mubeena kuwa

se murna ake mata malamai

kuwa sai wani nan-nan suke da ita kodayake

dama can malamai suna santa saboda

kwazonta...Nafisa kuwa da Ustaz(malamin

islamic) ya gane cewa na k'arya ne,dorina ya

dauko zabgegiya ya shiga lafta mata, bashiri ta

tashi tana ku

ka sharaf sharaf tana bashi

hak'uri,dariya yayi sanan yace ta koma aji, aka

dinga mata ihu ana cewa me aljanun k'arya a

rannar tayi alkwarin baza ta sake dawowa

makarantar ba, dan abin kunya data aikita baza

su barta ta zauna a makarnatar lafiya ba. Y

au Ya

Ameen ya ze dawo murna a wajen 'yan gidan

kamar me,kowa ka gani yana cikin walwala hatta

Ya Abdul... Mubeena kuwa cewa tayi a bar mata

zata mai girki me dadi, dayake yanason abincin

gargajiya fankaso da tuwo ta yi masa da miyar

taushe dan ya fa

d'a mata a waya ya dad'e be

cisu ba,, su ya Nana kuma suka yi masa kunun

aya da zob'o. Bayan yayi parking din motar shi

ya shigo gida Amir da gudu yazo ya rungume shi

yana masa oyoyo , su Mubeena suka fifito suna

masa sannu da zuwa shikuwa yana amsawa

fuska

d'auke da murmushi..ya k'araso cikin gida Umma

da Ummi kuma na falo suna jiranshi suka yi masa

sannu da zuwa sa kuma ya hanya. Ya amsa da

"lafiya lau nagode,,kuma nayi missing dinku

sooooooo much" a tare suka ce "muma munyi

missing dinka". Bay

an yayi wanka yayi sallah ya

dawo ya zauna Mubeena tace abincinsa na kan

dinning table( teburin cin abinci) yaje ya zauna

yana budewa ya fara "wow nasan wannan aikin

kine Mubeena", Ummi tace 'ai kuwa kamar

kasani,kayan shan ne su Nana sukayi yimaka" y

ayi

murmushi "amma kuwa nagode lovely sisters"

Bayan ya gama cin abincin su Ummi ke sanar

dashi Mubeena ce zata wakilci skul dinsu ba

k'aramin murna yayi ba,a rannar ta faranta masa

rai. Washe gari ya sami Umma yake fad'a mata

cewa iyayen Faty sun ta

kura masa daya turo dan

nan da wata hudu (4) za'ayi bikin yarta kuma

sunaso a had'a da na Faty...shikuma yana kunyar

fad'awa Ummi da Abba,, Umma tayi murna dajin

haka, ta kuma yimasa alkwarin zata fad'awa

Abban sannan kuma indai ya shirya to ba

matsa

la. yayi mata godiya ya tafi. Umma ta sami

Abba ta fada masa yaji dadin haka dama yana

shirin yi masa maganar auren dan a ganinsa

lokaci yayi daya kamata ya zama cikaken mutum

wato yayi aure...yace ta fad'awa ya Ameen d'in

ya kwantar da hankalinsa zas

uje shida yan-

uwansa su nema masa auren insha Allahu..

[12:34AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:48AM, 18/03/2016] Hapsat:

◆◆◆

AISHATUL

MUBEENA

◆◆◆

©MISS HAFCY

®ONLINE HAUSA WRITERS [125]-[130] Wakilin

shugabanin da suka shirya gasa wanda yazo daga

birnin

taraya Abuja wato MR MIKE da shugaban

k'ungiyar masu zanen dake kano ALHAJI AL-

AMIN BAWA sune suka fito dan fad'an result din

bayan manyan-manyan kwararru a harkar zane

sun duba sun fitar da sakamako, Alhaji Bawa shi

zai dinga kiran suna yayinda Mr

Mike ze dinga

d'aga zanen dan kowa ya gani. Bayan sun yi d'an

jawabansu, Alhaji Bawa ya fara magana kamar

haka:" zamu fara da na sha biyar (15)" nan ya

fara kiran sunaye yayin da Mr mike ke d'aga

zanen, sai kuma wanda aka kira ya fito bainar

jama'a.

Sai mutane su tafa masa/mata . A haka

dai yana fad'a har yazo ta biyu. Wanda ya kira

dalibi Ahmad Huzaifa, aka d'aga zanen shi nan

mutane suka fara ihu sosaii dan zanen nashi yayi

bala'in kyau. Bayan nan yace yanzu za'a d'aga

zanen wanda/wadda ta yazo

ta d'aya, mutane

kowa ya baza ido yana jiran ganin wani zane ne

wanda ya zarce had'ad'un zanen da'aka nuna, da

kuma wani tauraron ne ko kuma wata tauraruwar

ce ta samu nasarar lashe gasar? Mr Mike wani

had'ad'en ko nace gaba da had'ad'e zanen ya

d'a

ga sama, zane ne wanda aka yishi akan al'adar

bahaushe wato , da farko dai , bukka aka zana

yar k'arama me bala'in kyau a gefen ta kuma

tabarmar kaba ce wanda aka zana akushi da

kwanon sha da kuma kwaryar akai, ga butar

alwala a gefe, a d'ayan bangare

n kuma atamfa ce

aka zana da kuma dan kwali irin na da, sannan ga

murajani da dai sauran kayan hausawa na mata.

Zanen yayi bala'in kyau mutum in ya kalla sai ya

rantse hoto ne aka d'auka a camera saboda

tsabar tsaruwar da yayi. Nan da nan wajen ya

ga

uraye da ihu kowa sai washe baki yake yi daga

masu cewa "wow!" Sai masu cewa 'masha Allah"

duk dai, Kowa burinsa be huce yaga wanda/

wadda yayi zanen ba. Yan jarida kuwa da sauran

mutane sai d'auka hoton zanen suke. Mubeena

kuwa suna hira da su Husna

taga an d'aga zanen

ta wani farin ciki taji wanda bata tab'a jinsa a

rayuwarta ba,, ta runtse idonta sai hawayen

murna, ta kuma k'i fadawa su Ya Abdul cewa

zanen tane, sukuwa suna gefe sai fama zuzuta

zanen suke,amma kowa a zuciyarshi, ji yake

kamar

zanen Mubeena ne. Alhaji Bawa ne ya

dakatar da mutane daga hayaniyae da suke

dakuma ihu, yayi gyran murya yace , "yanzu zan

kira wanda yayi wannan zane, ina me farin ciki

kirin AISHATUL MUBEENA Muhammad Ameen!".

Murna a wajen su Husna kamar me ,sai ka

llon

Mubeena suke suna k'ara kallonta, fuskarsu

d'auke da farin ciki, Mubeena kasa tashi tayi da

kyar suka lalab'eta ta tashi jiki ba kwari ta nufi

inda aka kirata. Mutane dake ta jiran fitowar ta,

sai hango ta sukai tana cangala kafarta dan

zuwan wa

jen, mamaki duk ya cika su, amma

wannan ta ciri tuta ashe dama da nakasasu masu

irin talent irinta? Ihun mutane ya k'aru gaba

d'aya suka tashi suna kallonta yayin da 'yan jarida

suka cika wajen suna d'aukar ta hoto, da kuma

hoto mai motsi(video). Isar

ta keda wuya , Mr

Mike abinka da arne cak ya d'agata sama! Duk

k'ok'arin datake dan ta kwace amma ya rik'e ta

gam, cikin d'aga murya da hausar sa da wadda

bata fita sosai yace " wannan itace ta lashe

gasar, itace tazo ta d'aya!"

Like · 2 · Reply · Ed

it · 6 February

[11:50AM, 18/03/2016] Hapsat:

◆◆◆

AISHATUL

MUBEENA

◆◆◆

©MISS HAFCY

®ONLINE HAUSA WRITERS [115]-[120] Umma

tace "hakane Iya amma..." Iya ta katse ta

"dakata" ta janyo hannun Mubeena ta rik'e gam

sannan tace "Aihatul mubeena nice kakar ki

, nice

na haifi mahaifinki SULAIMAN, nida mahaifinki

mun kasance masu wata irin zuciya,masu butulci

kuma wa'enda basu da godiyar Allah,, nan da nan

ta fada mata komai tun daga auren Umma da

Mal Sule har rannar da suka rabu" Mubeena ta

fashe da kuka,k

uka take sosaii haka ma Umma.

Mubeena tana kuka tace "Umma dama na fad'a

miki, na fad'a miki cewa Abba ba shine mahaifina

ba!" Umma cikin tsawa tace " shine mahaifinki !

Abba shine mahaifinki! , shine yaso ki a lokacin

da Mal sule ya k'i ki har yake i

k'irarin cewa ke ba

'yarsa bace, shine ya ciyyar dake, ya tufatar

dake, ya baki ilimi, daidai da rana d'aya bai tab'a

nuna bambanci a tsakaninku ke da 'yan'yansa ba,,

sabanin Mal Sule da ya firta da bakinsa kar na

sake ko da wasa nace ke d'iyarsa ce ,

wanda

shine sillar gurguncewa k'afarki, wanda besan cin

kiba, besan shan kiba, besan wahala kiba, besan

komai naki ba! Abu d'aya ne ya miki a rayuwa,

shine sillar zuwan ki duniya , amma bayan haka

ba abinda ya tsinana miki a rayuwa, wallahi kome

Mal

sule ze miki yanzu in aka d'auke Silan zuwanki

duniya dayayi baze ko kusa yi miki abinda Dr

Muhammad ya miki ba,, Mal Sule ya amsa sunan

sa na cewa shine ubanki wanda ya haife ki kawai,

amma ko kusa baze amsa sunan , wanda yayi

wahala dake tun kina y

ar gwililuwa har yanzu,

wanda ya ci dake, ya sha dake,ya tufatar dake,ya

baki ilimi ya kuma baki tarbiya, Shine ya cika

sharud'an zama uba wanda uban naki wanda ya

haife ki ya kasa cikawa!(Ta sassauta murya ta)

amma Mubeena kar abinda nida Iya muka fa

d'a

miki ya sa ki tsani mahaifinki, ko kusa kar ki fara

domin in badan shiba baza kizo duniya ba!....ta

k'arasa maganar cikin sheshek'ar kuka. Kukan

Mubeena ya k'aru sosai, tama kasa magana, sai

sheshek'ar kukan data keyi,,, Umma ta kalli Iya

dake ta

faman sharbar kuka tace "Iya kiyi hak'uri

ban fad"i maganar ba dan ta b'ata miki rai,

gaskiya ce kawai na fad'a, Iya tace" baki b'ata

min rai ba Ma'u, gaskiya ke kike fad'i, nayi dana

sanin abinda na aikata a baya"" Ma'u tace "Iya

bakiyi mana komai b

a Iya wannan maganar ta

huce saboda ni tun d'ad'ewa da kika nemi

gafarata na yafe miki, dama ko baki nemi na yafe

miki zan yafe miki dan wallahi ni tamkar Uwa na

d'auke ki!" Ga wannnan ta aje mata bandir din

yan dubu d'aya(1) sannan tace "gobe insha A

llah

zan aiko miki da sauran abinda kike buk'ata,

kuma insha Allahu za mu dinga ziyartar ki akai-

akai. Iya ta rik'e hannunta " Ma'u tsaya na fad'a

miki wani abu,, yau tsawon shekaru goma(10)

kenan ban sa Sule a idona ba, tunda yazo yace

min ya tafi

birni cirani na nuna ban amince ba

amma sam ya k' jin maganata ya tafi ya barni, be

kuma waiwayata ba, ko yana da rai? Ko ya rasu?

Allahu a'alam,, amma dan Allah in Allah ya had'a

ku dan Allah ma'u ku yafe masa ke da Aiha

(Aisha), ki kuma ce nima na y

afe masa, dan ina ji

ajikina kwanan ya kusa k'are da k'yar na k'ara

kwana a duniya ,nima ku yafe min Allah ya had'a

fuskokin mu a aljana..." ta fashe da kuka,,,,jikin

Umma da Mubeena yayi sanyi sosaii Mubeena tayi

dauriyar cewa "ni na yafe miki Iya, k

uma ki dena

ambaton mutuwa insha Allahu zaki tashi, cuta ba

mutuwa bace! " Iya ta girgiza kai "kayya! Suka

mata sallama suna kuka tana kuka suka rabu. A

gidan Mama ne, Mama ta kwantar da murya

tayiwa Mubeena bayanin komai, Mubeena wani

sabon kukan ta

sake Mama na rarashinta, taji

tausayin Ummanta sosaii sosaii ga wani sonta

dake k'aruwa a zuciyarta,, sannan kuma taji

tsanar Mal Sule a zuciyarta, ji take ba wanda ta

tsana sama dashi..godewa Allah tayi daya bata

uwa ta gari kamar Umma dan ita gani

take tafi

kowa dacen uwa a duniya! Haka suka koma gida

dukkansu ba farin ciki da walwala..

◆◆◆◆◆◆◆

Washe garin rana Allah yayi wa Iya cikawa,, su

Umma sunji mutuwarta sosaii a wannan dak'in

Allah yayi mata cikawa cikin dare. Da sassafe su

Umma suka t

afi suna ta kuka abun tausayi

mussaman ma Mubeena, da 'yan gidan suka tafi

gabad'aya har da Abba, dan shima yaji mutuwar

dan ya santa, lokacin da 'aka kwantar da

Mubeena a asibiti da cutar polio ta sameta,,sai

da suka fara sauka a gidan Mama sannan su

kaje

gidan marigayiya Iya,, a lokacin ma ko wanka

ba'a yiwa gawar ba, Umma da taimakon Mubeena

su suka wanke gawar tas aka samata likafani aka

fita da ita ,maza suka sallaci gawar aka kaita

kuhewarta , Allahu akbar Allah kasa mu cika da

imani, ka bam

u kyakyawan K'arshe Ameen ya

Allah.. Ba wani zaman makoki akayi ba tunda wa

za'ayiwa gaisuwar? Dama Mal Sule ne kawai d'an

data haifa kuma baya nan bai san ta rasu bama,

'yayan mijnata kuwa Bashir da Hauwa sun dad'e

da dena kulata bama sa k'asar gabad

aya. A 'yan-

uwanta kuwa ita kad'ai tayi ragowa duk sun

rasu,, sai dai sauran dangi da ba'a rasa

ba..Masa'udu dama shi ake yiwa gaisuwar dan

shine ya kula da ita tun data sami rashin lafiyar

har ta warke, shima kuwa a rannar data rasu

admission dinsa

ya fito yaci Ahmadu Bello

unibasiti zaria(ABU zaria) dan haka ya had'a

kayansa ya tafi Umma kuwa kud'i me yawa ta

bashi tace yayi harkar makaranta dashi ya yafi

yana ta godiya.

[12:35AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:46AM, 18/03/2016] Hapsat:

◆◆◆

AISHAT

UL

MUBEENA

◆◆◆

©MISS HAFCY

®ONLINE HAUSA WRITERS [135]-[140] Bayan an

dawo hutun tak'aitacen lokaci. Aysha Amatulah:

to barkan mu da dawowa. Hajiya Mubeena shin

wai ta yaya kika tsunduma cikin harkar zane-

zane? Mubeena: To agaskiya nidai na taso ne

kawai na gani inayi, a lokacin inga abu ya min

kyau sai na zana shi, cikin ikon Allah kuma sai

kiga zanen ya fita sosaii...lokacin da ina primary

kuma in kika duba littafai na na arts zaki ga inaci

sosaii, koda merit za'a bada ma a Art ni ake

bawa. Ku

ma akwai Yayana Ya Ameen shine ya

cigaba da ban kwarin gwiwa har nazo matakin

danake yanzu. Aysha Amatullah: madalah, to

kafin ki fara wanan zane-zanen mene burinki a

rayuwa? Mubeena: Burin na da shine na zama

likita dan nima na bada gudunmawa ta waje

n

yak'i da wannan cutar sai kuma Allah beyi ba.

Aysha Amatullah: to Allah zaba mafi alheri, meye

ya fi b'ata miki rai da kuma abinda yafi faranta

miki rai? Mubeena: Abinda ya fi b'ata min rai

guda biyu ne na d'aya ya shafi personal life dina,

na biyu

n kuwa shine, idan naga yan'uwana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login