Showing 24001 words to 27000 words out of 31145 words
/>
wani k'ara anan ta fad'i k'asa sumamiya!
Lik
[11:47AM, 18/03/2016] Hapsat:
◆◆◆
AISHATUL
MUBEENA
◆◆◆
©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [130]-[135] Nan take
wajen ya d'auka sai ihu akeyi su Husna dake gefe
sai dariya suke yi dan sunsan Mubeena
yau ta
shak'i haushi itada ko hannunta bata san wani
namiji ya tab'a, sai gashi yau k'aton arne ya
d'aga ta, shikuwa Ya Abdul ji yake kamar yaje ya
wankawa Mr Mike mari dan haushi. Da kyar ta
samu ya sauke ta k'asa, ai kuwa sai tabar
wajenshi ta kom
a d'ayan banganren, sai
d'aukanta hoto ake. Certificate aka bata ta,
sannan aka buk'aci ta sa hannu taje ta saka kuwa,
sannan aka mik'a mata shi, bayan nan aka shiga
raba kyautuka ga wanda suka yi participating
kyauta kuwa ta samu kala-kala, kamfaanin
wani
shahararen lemu ya bata da kuma sauran
participant's d'in kud'i da kuma lemuka, kyauta
dai iri-iri ta sha su wai kuma aka samun tab'i ne
dan ba'a bata babbar kyautar tata ba. Check na
miliyan d'aya(1) aka bata daga hukumar da suka
shirya gasar
sannan kuma k'ungiya masu zane
dake kano suka bata kudi naira dubu d'ari(100).
Mr Mike ne ya d'auko wasu sarkok'in medal's
guda uku(3) 'yan k'anana d'aya na gold d'aya na
silver na ukun kuma na bronze. Ta uku ya rataya
wa bronze medal aka fara tafi an
a d'aukan
hotuna, sannan ya kira Ahmad Huzaifa ya rataya
masa na silver, shima aka d'au tafi. Bayan nan
kuma wakilin gwamnati ya tabbatar mata da
cewa bayan ta kammala karatun sakandire
gwamntani zata d'auki nauyin ta taje tayi course
din zane a wata
makatantar zane-zane(art school)
dake amurka(America) Na gold din kuwa
Mubeena ya ratayawa nan waje ya k'ara d'aukan
ihu 'yan jarida nata d'aukan hoto da kuma hoto
mai motsi(video) domin a yawancin kafafen yad'a
labarai ta talabijin abin live ake nun
awa. Su Abba
dake zaune suna kallo LIVE murna a wajensu
kamar me, sun ma rasa me zasuyi saboda murna,
hak'k'ika wannan rana tana cikin rana mafi farin
ciki a rayuwarsu, mussaman ma Umma da
alk'warin da tayiwa Mal Sule ya cika yau, a
zuciyarta cewa ta
ke dama Mal Sule ya ji ko ya ga
wannan abin alherin. Bayan an kammala taro aka
rufe taro da add'ua, nan aka fara d'aukan hotuna
dasu Uncle Hashim da bakinsa ya kasa rufuwa
saboda farin ciki, su Ya Abdul ma haka, kana
ganinsu zaka gane irin halin da su
ke ciki. Zanen
kuwa tafiya Mr Mike zeyi dashi, inda za'a kai shi
wannan babban ART GALLERY dake Abuja. Su
Alhaji Bawa basu so hakan ba dan su sunfi san a
barshi a Art gallery din dake kano amma ba
yadda suka iya. Fitowar su Mubeena ke da wuya
wakilan
'yan jarida da gidajen radio sukawo mata
caa akanta, sai tambayoyi suke mata tama rasa
wadda zata amsa, can dai tace "Alhamdulilah ba
abinda zance sai godiya ga Allah da ya bani
nasara a wannan gasar, sannan ina godewa
iyayena da suka bani k'warin gw
iwa har nazo
matakin dana ke yanzu! Nagode.". Tana gama
fad'an hakan tayi hanyar motarsu. Zwan ta keda
wuya ta tadda wakilan wani shahararen gidan TV
suna jiranta, numfasawa tayi tace "wannan shine
anyi gudun gara an tadda zago". Nan suka shiga
yi ma
ta magiya akan suna so su tautana da ita
gobe, saboda gobe ne ta kama rannar masu
cutar polio da duniya wato (WORLD POLIO DAY)
wato ashirin da hud'u ga watan oktoba(24th
october) bata musu musu ba kuwa ta amsa sunyi
farin cika sosaii inda suka bata wa
ni kati na
gayyata. Farin ciki ya dawo sabo sanda suka
koma gida su Umma hadda kukan murna, Ya
Ameen dake can k'asar holland ya sami labari
daya duba news ya kira su aka sha murna,
makarantarsu kuwa dayake tana final year suka ce
sun d'auki nauyin ta
har ta gama su waec da
neco duk zasu biya mata, saboda ta fito da
sunan makarantarsu, bayan k'ananun kyaututuka
da suka bata. Yau ta kama 24th october(World
polio day), tun da safe ta ta shirya driver ya
kaita dan Ya Abdul ya tafi wajen aiki. Tana zu
wa
dama ita suka jira, aka shirya komai tazo ta zauna
akan kujerar da za'a tautauna da ita.(wasu
gidajen radio suma sun juno dan masu saurarun
radiyo suma suji) Me gabatarwa ta fara:
Assalamu alaikum warahamatul lahi ta'ala wa
barkatuhu masu kallo da
sauraranmu. Barkan mu
da sake saduwa a wannan shiri na mussaman da
muke gabatarwa duk a rannar polio ta duniya
duk shekara. A yau shirin namu yayi babban
kamu, domin yau zamu tautauna da AISHATUL
MUBEENA Muhammad Ameen, wadda itama ta
zamo polio vic
tim ta farko tada fara lashe gasar
zane-zane dake gabatarwa duk bayan shekara
hud'u a jihohi dama k'asa baki d'aya... Sunana
Aysha Amatullah wadda zan gabatar da shirin,
Hajiya Mubeena ko nace Artist Mubeena barka da
zuwa. Mubeena: Barka kadai. Aysha
Amatullah:
shin zamu iya jin tak'aitacen tarihin ki? Mubeena:
To Alhamdulilah, nidai sunana Aishatul Mubeena
Muhammad Ameen an haifeni a garin Kano na
taso a Kano, kuma a yanzu haka inada shekara
sha bakwai next year zan shiga sha takwas(18),
saboda
ban fara makaranta da wuri ba yanzu dai
ina ss3 a sakandire. Aysha Amatullah: Masha
Allahu, shin kina shekara nawa wannan cuta ta
sameki? Kuma mene ne dalili? Mubeena: A
gaskiya wannan cuta ta same ni ina 3-4 years,
dan dama kinsan a yara masu shekara
d'aya zuwa
biyar(1-5) tafi kamawa..kuma a gaskiya zan iya
cewa wannan cuta kaddara ce daga Allah, dama
can Allah ya riga ya rubuta cewa a haka zan
tashi, cutar zata same ni. Aysha Amatullah: to
madalah, wani kalubale kika ko kike fuskanta?
Mubeena:
Alhamdulilah a gaskiya nidai k'alubalen
dana fuskanta be huce lokacin da ina k'arama ba,
lokacin danake koyan tafiya, amma bayan haka
ban fuskanci wani k'alubale ba gaskiya. Aysha
Amatullah: to masu kallo da sauraranmu, kunji
yadda hirar mu ke kasance
wa, yanzu zamu je
hutun tak'aitacen lokaci
Share
Comment as:
Publish Preview
No comments:
Post a Comment
MissHafcy
View my complete profile
About Me
►
2017 (16)
▼ 2016 (34)
►
November (1)
▼ October (33)
WELCOME
ASMAUL HUSNA 6
ASMA'UL~HUSNA
ASMAUL~HUSNA 4
ASMAUL~HUSNA 3
ASMAUL HUSNA 2
ASMAUL HUSNA
AISHATUL MUBEENA 155-160
AISHATUL MUBEENA 145-155
AISHATUL MUBEENA 110-140
AISHATUL MUBEENA 85-105
AISHATUL MUBEENA 60-80
AISHATUL MUBEENA 45-60
AISHATUL MUBEENA 30-40
AISHATUL MUBEENA 2
0-30
AISHATUL MUBEENA 1-20
WANI HANIN END!
WANI HANIN 26-27
WANI HANIN 24-25
WANI HANIN 22-23
WANI HANIN 20-21
WANI HANIN 19-20
WANI HANIN 15,16,17&18
WANIN HANIN 12,13,&14
WANI HANIN 11
WANI HANIN 9&10
WANI HANIN 7&8
WANI HANIN 5&6
WANI HANI
N 3&4
WANI HANIN 2
WANI HANIN 1
....
WANI HANIN
Blog Archive
Miss_Hafcy. Watermark
AISHATUL MUBEENA 145-155
[12:37AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy:
◆◆◆
AISHATUL MUBEENA
◆◆◆
©MSS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [140]-[145] Abba
cikin rud'ewa ya d'auko wayarsa
yayi dailing
numbern drivern asibitin shi, ya mai kwatacen
inda accident d'in ya faru, yayinda ya d'auki
Umma ya sata a motar su, su Mubeena kuwa duk
sun rud'e. Sai da suka jira Motar asibiti tazo, da
taimakon mutanen wajen aka sa mutumin a Mota
suk
a bi bayan su Abba dan zuwa asibiti.
Emergency aka shige dasu, Umma kuwa bata
dad'e ba ta farfado dan haka aka kaita resting
room, shikuwa mutumin likitoci suka duk'ufa
akansa ana duba shi. Bayan Umma ta farfad'o ta
dawo dai-dai sai kuma kuka, kuka ta
ke sosaii
tama kasa magana, Abba dake gefenta sai
lalashinta yake, su Mubeena kuwa suna reception
suna jira. Abba cikin sanyin murya yace "Asma'u
wai meya faru ne? Kinada alak'a da mutumin nan
ne ko kuwa me? Daga ganin mutum sai ki yanke
jiki ki suma
, ke da kike da hawan jini, Allah ya
taimaka ma jininki be hau sosaii ba.....Asma'u
magana fa nake miki kin min shiru, kukan nan ba
abinda ze amfana miki dashi fa". Umma kasa
magana tayi kawai sai runtse idonta tayi tana
kuka a hankali, wata Nurse ta
shigo sanye da
kayan Nurses ta kalli Abba " Doctor, Dr.Faruk ya
gama dubashi mun samai bandage da komai,
yanzu ma mun canza masa daki, kuma da alama
ya dawo hayyacinsa ma, Abba ya kalleta "okay
nurse Sadik'a, muje d'akin naga jikin nashi"
zumbur Umma
ta mik'e tana k'ok'arin binshi,
Abba ya juyo da mamaki " Asma'u ina zaki?", ta
kalleshi "inda zaka je" murmushin tak'aici yayi,
sannan yace" to muje", yana gaba, tana binshi a
baya har suka isa zuwa d'akin mutumin. Yana
kwance idonshi na kan celling
sai zubar da
hawaye yake yi, Umma ta k'araso wajen sa a
nutse, tace "ya jiki?" yana had'a ido da ita ya
kauda kansa cikin muryar sa da bata fita yace "
Ma'u yau gizon naki da kike min hadda magana?
Kodai mafarki nakeyi? Ina ne nan?. Ma'u tayi wani
mu
rmushin tak'aici sannan tace "ba mafarki kake
ba, kuma ba gizo nake maka ba, kalle ni da kyau
kagani, nice dai Ma'u mahaifiyar nakashashiya,
nice dai Ma'u wadda ka tsana kake hantara
saboda kawai ta haifa maka d'iya mace kuma nice
dai Ma'u wadda ka wu
lak'anta daga k'arshe ka
sake ta, nice dai Ma'u tsohuwar Matar azzalumi
MALLAM SULE, ta fashe da kuka.. Abba ya dafa
kafad'arta yace "ya isa haka Asma'u muje gidan ki
d'an huta, anjima ma dawo muyi maganar (ya
kalli Mal Sule, Allah ya k'ara sauk'i) su
na k'ok'arin
fita ya kalleta yace, "and inaso ki share
hawayenki", ta kalleshi "toh" sannan ta share
hawayen, Abba yace to muje ta shige suka tafi.
Bayan sun shiga gida Umma kai tsaye dakin ta ta
shige ta kwanta, zuciyarta fal da tunane-tunane
kala-k
ala, Mubeena ta turo kofar d'akin ta shigo,
a kan gado ta tadda ta tayi tagumi, Mubeena ta
zauna a bakin gadon tace " Ummana wai meya ke
damun ki ? Waye wannan mutumin? Meya miki?
Har ganinsa ya sa ki suma? Umma ta juyo ta kali
Mubeena sannan ta dafa
kafad'arta tace "
Mubeena wannan mutumin bakowa bane illa
MAHAIFINKI Mal Sule! , Mubeena ta zaro ido
"mahaifina kuma?" Umma tace " tabbas"
Mubeena ta d'an yi jim sannan ta tashi da sauri
ta nufi d'akinta, tana zuwa ta haye kan gado ta
fashe da kuka,
a daren rannar kuwa gabad'ayan
daga ita har Umma kasa runtsawa sukayi.
Washegari........ Da sassafe suka tashi suka shirya
gabad'aya 'yan gidan suka d'unguma suka tafi
asibitin Abba, Mubeena cike da d'okin taje taga
wannan babanta da baya santa. A kwa
nce suka
tadda shi, yau ma kansa na kan celling sai
hawaye yake, daga ganin bayan damuwar dake
tatare dashi akwai zafin ciwo ma, yana kallonsu
ya kauda kai , Mubeena ta k'araso wajenshi da
sauri dan ya bata tausayi sosai, bakin gadon shi
taje ta zaun
a cikin sanyin murya tace "Baba ya
jiki??? *****ku yi hak'uri na rashin jina da kukayi
kwana biyu, wayata ce ta sami matsala shiyasa,
Nagode.***
[12:38AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy:
◆◆◆
AISHATUL MUBEENA
◆◆◆
[145]-[150]
©MISS HAFCY
®NWA
Ya juyo cike da m
amaki, cikin muryarsa da bata
fita yace "Allahu Akbar, Alhamdulilah ashe akwai
rannar da nima zanji d'an ko 'yar dana haifa ta
kirani da Baba?" Mubeena tace " ai dama can
kane bakso kaji ba da'ace kaso kaji da baka
wulak'antani nida mahaifiyata ba" ya
kauda kansa
"hak'ika nayi kuskure babba na kasance mutum
mara godiyar Allah, dan Adam butulu, ku yafe
min dan Allah" ya fashe da kuka.
Mubeena ta runtse ido sai hawaye ta kalleshi "ai
saika fara nemin gafarar Allah domin Allah
gafurur rahim ne" Abba
yace "Mal ya jiki?" Mal
Sule yace "jiki da sauk'i".
Mal Sule yace " ni naga rayuwa, naga sakayata,
Allah yaban 'ya mace amma fir nak'i gode masa
sai ma sab'o dana dinga yi kala-kala, ya kalli
Umma datayi shiru tana sauraransa, Bayan
rabuwar mu dake,
a k'auye duk inda na nemi
aura ba'a bani, saboda abinda na aikata ya baza
gari sosaii mutane sai suke kyamar hadda jini
dani,,, rannar sai na yanke shawarar komawa
birni wajen yayana Bashir, anan ya bani kudi da
d'an dama yace naje na ja jari, naje n
a sami d'an
k'aramin gida me d'aki biyu da bandaki na bud'e
shagon kayan masarufi na sami mata na aura,
amma shiru ba haihuwa data gaji tayi tafiyar ta, a
tak'aice dai wallahi sai dana auri mata sunkai
biyar(5) ciki harda masu ciki guda biyu2, wai dan
duk su haifi d'an a gidana na rene shi ya zama
d'ana, amma abin mamaki a cikinsu ba wadda ta
tab'a haifar cikin a raye a mace suke haifosu.
Daga baya auren ya gagara jari na ya cinye na
zamonto banda komai,na koma gidan yayan nawa
shima na tadda bas
a k'asar ma gabadaya,,,
rayuwa tamin zafi abincin da zanci gagara ta
yake, tun daga nan na fara nadamar abinda na
aikata, nakuma tabbatar da cewa hak'in ku ne ku
da Iya yake bina, na taho neman ku shine mota
ta kad'e ni kuka taimakeni" ya fashe da kuk
a.
Gabad'ayansu jikinsu yayi sanyi, kowa yayi shiru
Mubeena cema ke kuka a hankali, ya kalli
Mubeena 'yata ki yafeni, ki yafeni dan Allah kar
na mutu da hakk'in ki akaina na cuce ki, na cutar
da rayuwarki,(ya juya wajen Unma) Ma'u kema ki
yafeni dan
Allah, a lokacin da kike ce akwai
rannar da zanyi nadama bazata min amfani ba
ban yadda ba, sai gashi yau ga rannar nan tazo,
ki yafeni, kuma dan Allah ki kaini wajen Iyata
itama na rok'i gafararta, kar na mutu da hak'inta
akaina"
Umma tana hawaye ta
ce "bakomai na yafe maka ,
Allah ya yafe mana baki d'aya, Amma Iya babu,
Allah yai mata rasuwa, sai dai kan ta rasu tace ta
yafe maka" ya fashe da kuka " wayyo Allah na iya
ta rasu? Innalalhi waina ilaihi raju'un KAICONA!
Na cuci kaina,, Umma tace "ga
dai 'yarka kamar
yadda na fad"a maka zata zamanto abar
kwatance kuma duniya ta santa akan abin alheri
to Allah yayi, yanzu duk shafukan jaridar daka
duba zaka labarinta, gidan rediyo dana talabijin
dama..." Abba ya katse ta "ya isa haka ! Me ya
kawo
wannan zancen kuma, komai ya wuce
mubar maida hannun agogo baya".
Ya kwantar da murya yace "kuyi hak'uri kai kuma
tunda sun yafe maka har Iyan ma ta yafe maka,
ka gode Allah,k a kuma cigaba da nemi gafarar a
wajen Allah domin kamar yadda 'yarka ta fa
d'a
ma Allah gafurur rahim ne"" Allah ya sawwak'e,
mu bari mu tafi,(ya kallesu)"kuzo mu tafi"
Mubeena ta share hawayenta tace "ni ku barni
anan zanyi jinyarsa" da mamaki suka juyo "me?"
Tace "cewa nayi zanyi jinyarsa" Mal Sule yayi tari
"a'ah zan zau
na nan ma nagode d'iyar kirki, Allah
ya shi miki albarka, tace "amin, amma zan zauna
d'in anan,,da kyar ya rok'e ta ta hak'ura tace
zata bisu. Da kuma alk'warin kullum zasu dinga
zuwa suna duba shi.
Yau kimanin kwana biyar5 kenan da ganin Mal
Sule, a
ranna ta biyar d'in kuwa Allah yamai
cikawa sun sha kuka sosaii da sosaii mussaman
ma Mubeena data rasa Uba, haka dai suka sha
kukansu su gaji suka daina. Tare dayi masa
addu'oi kala-kala.
**********
Admission d'in Mubeena ya fito nan da wata
d'aya
zata tafi America.
Abba ne zaune a falonsa gefensa Ummi ce tana
karanta jarida,,ya d'an yi jim sannan yace "nikuwa
Hadiza wata shawara na yanke, amma bansani ba
ko ke zata miki,, Ummi tace "tame fa?" Abba
yayi gyran murya sannan yace
"Akan yarinyar
nan ne Mubeena kinsan admission
d'inta ya fito nan da wata d'aya1 zata tafi
America gashi shekara biyu 2 ne sai nake ganin
kamar be dace mu barta ta tafi ba muharami
ba,kuma kinsan ta isa aure shekara sha takwas da
d'ori ai ba kad'an bane, dan haka na
yanke wata
shawara......
Ummi ta gyra zama tace "gaskiya ne wannan,
amma shawarar me ka yanke?" Abba yayi
murmushi " ina so zan had'a ta aure da Abdul-
Hafeez ne!, kinga dama already an sa rannar
Husna sai a had'a a d'aura auren tare! Ummi da
mamak
i tace "gaskiya ne, amma a gaskiya sai a
kira su yaran aji ta bakinsu in sun amince falilahil
hamd in basu amice ba kuma shikenan sai asan
abin yi"
Abba yace " dad'i na dake garaje baki tsaya kinji
me zance ba kin tari numfashina, dama ya za'a yi
na
d"aura musu aure ba amincewarsu? Kuma
bazan musu auren dole ba, yanzu dai je ki kira
min 'yar uwarki Asma'u itama muji ta bakinta,
Ummi a sanyaye ta nufi part d'in Umma ta kira
ta suka nufo wajen Abba a jere.
Abba yayi mata(Umma) bayanin abin itama ta
yi
mamaki sosaii dan a ganinta Abdul ya wuce ajin
Mubeena amma dai sai tacewa Abba Allah zab'a
mafi alheri yaji dad'i sosaii.
Abba dakansa ya d'au waya ya kira Ya Abdul ya
kuma ce masa yazo yana son ganinsa, yace gashi
nan, sannan ya sa Umma ta kira
Mubeena suka
zauna suna jiran Ya Abdul. Mubeena cike da
fargabar ko wani laifin ta aikata..
Be dad'e ba ya shigo sanye da shadar light bleu,
Abba ya kalleshi " kai dai Abdul Hafeez har yanzu
baka girma ba?, kasa shadda manyan kayanmu
na hausawa, kuma
kana yawo kai a haka ba hula,
ina hularka? Ya sosa k'eya "tana daki wallahi ina
sauri ne dats y kaga na barta, yi hak'uri", Abba
yace bakomai zauna nan muyi magana.
Ya zauna, sai a lokacin ya lura da Mubeena dake
kan kujera kanta a sunkuye kallo d'ay
a yayi mata
ya kauda kai.
Abba ya fad'a musu hukuncin da ya yanke,dum!
Gabansu ya fad'i gabad'aya, Mubeena kuwa
murza idonta anya ba mafarki nake ba? Ta fad'a
a zuciyarta, shikuwa Ya Abdul suman zaune yayi
yama kasa magana, Abba dayaji shirun yayi ya
wa
yace "ya dai? Ya kukayi