Showing 123001 words to 126000 words out of 137264 words
akan wasu magunguna kuma zan hadaka da wani kakana likitan gargajiya ne akwai wani mutum da yataba zuwa da irin wannan matsalar shekaru uku da suka wucce yayi masa magani ya samu sauqi amma zaka zauna a g
urinsa harsai komai ya zama normal"
Baiyi musu ba saboda a yanda yakeji jiyake dama zaa iya kashe masa sha'awar gaba daya ya huta idan ya tuna bloody dinsa tanacan tana rayuwa da wani namijin kawai sai yaji zuciyarsa tana tafasa hawaye nabin kunci
nsa damma ya dage wajan addu'a da neman zabi da sauqi gurin ubangiji yana kuwa samun sauqin sosai duk da yasani son Umaimah bazai taba barin jininsa ba domin dashi aka halicceshi.
Hakan kuwa akayi ana sallamarsa daga asibiti yayima Daddy bayanin komai ya
bashi goyan baya har dashi suka tafi qauyen Ghabriel garin da kakan Dr Ammar yake suka samu karamci sosai sukayi masa bayani ya cajeshi tsaf sannan ya dorashi akan magani ya fada masa zaiyi wata biyu anan baija ba saboda bama ya buqatar zaman 9ja din kwat
a² yana karbar maganinsa yana warwarewa sosai.
Watan auren Umaimah da D.S bakwai lkcn tanada cikin wata biyar sosai d.s ya dauki so da qaunar duniya ya dorawa cikin jikinta bashi da mgn sai tasa a lkcn kuma tana 300 level a jami'a tare suke fitowa
kullum kowa yana yabawa soyayyarsu da kulawar da yake bata a lkcn ne kuma wata qaddarar ta fado rayuwar Ahlin Hameed Shuwa ranar wata juma'a Hajiya tana kitchen tana girki Nihal da Shurafah suna kitchen din suna wasansu saboda Maliha da Shuraif suna gdan
Aunty Zarah kawai sai aka kira Hajiya a waya bisa tsautsayi ta fita tabar yaran a kitchen fitarta keda wuya Gas din yayi wata bindaga gobara ta tashi ta kama wani bangare na gdan ihu Hajiya ta rinqayi tana salati daqyar yan kwanakwana suka kashe gobarar am
ma abubuwa da yawa sun qone a gdan harda asarar rayuka biyu Nihal da Shurafah.
Wannan mutuwa ta girgiza mutane sosai Daddy ne ya hana a fadawa Hameed ita kuwa Umaimah sai Mijinta aka fadawa shine yaje ya daukota ya kawota gdan tun daga qofar gdan
tasan wani abu ya faru gabanta ya yanke ya fadi tayi baya luuuuuu zata fadi yayi saurin tarota amma ta suma nan fa hankali ya dawo kanta ya dauketa shida Hajiyansa da aunty Zarah suka tafi Asibiti bayan wani dan lkc ta farfado tana tashi ta riqe hanunsa ta
fashe da kuka tace “don Allah Sulaiman kada kacemin Abdulhameed ya mutu zuciyata bugawa zatayi..." Rufe mata baki yayi yace “ai dama na sani nasan tunaninki kenan to ki kwantar da hankalinki bashine ya mutu ba..." katseshi tayi da cewa “to waye waye ya mu
tu D.S?" Share hawayen idonsa yayi yace “Nihal ce da..." Saikuma yayi shiru daya tuna irin son da takewa Shurafah kullum burinta akan Shurafah ya qare katse masa tunanin tayi da cewa “dawa kuma D. S?"
Janye hanunsa yayi daga nata ya fice daga dak
in da sauri Aunty Jameelah tace “kunyi Mata shuru ai dolene ta sani Umaimah hqr zamuyi Allah ya karbi rayuwar Nihal da Shurafah jiya da magaruba sakamakon gobara da sukayi a kitchen kiyi hqr Allah zai mayar miki da wadda tafita” ajiyar zuciya tayi tana kal
lon Aunty Jameelah tana furta “Innanillahi wa innah ilaihir raji'un” iyakar abinda take furtawa kenan har zuwa yamma da D.S ya dawo likitan ya sallameta suka tafi gdan rasuwar ta wucce akayi zaman uku da ita taso tayi kwana bakwai amma ya hanata yace ta da
wo ana gobe bakwai din.
Haka kuwa akayi ana gobe bakwai da kansa ya kawota tunda ta shigo unguwar taji gabanta yana faduwa hakadai ta daure ta rinqa yi masa yaqe suka fito yana riqe da hanunta saboda cikinta yayi nauyi da girma sosai kamar yakai w
ata tara bayan yanzu ne ya shiga na takwas tana daga qafarta daqyar suka shiga parlourn yanata zuba mata sannu yana riqe da jakarta dagowa sukayi a tare idonsu ya sarqe da juna taja
baya da sauri ta shige jikin D.S inda shikuma ya miqe da sauri yana nunata
da yatsa yana kallon cikinta yace “Blo... bloody ciki......."
*UMMUH HAIRAN CE...
✍
🏻
*
[2/2, 8:49 PM] UMMUH HAIRAN CE...
✍
🏻
: *_GU_*
Yana fadin haka ya nufi qofa da sauri ya fice daga dakin ko hanu
n da D.S yake miqa masa bai kulaba wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata ya kamata ya zaunar da ita yace “to ya isa haka kinsan banason kuka ko?" qoqarin tsayar da kukan ta farayi daqyar ta tsayar da kukan yayi murmushi ya miqe yace “zanje gda ke sai yau
she?" Qasa tayi da kanta tace “jibi" kallonta yayi da sauri yace “aa gobe dai" batayi masa musu ba ya juya ya fice bayan sun gaisa da mutanen dake dakin sai lkcn ta samu damar gaisawa da kowa ta miqe da qyar ta shiga dakin Hajiya ta kwanta tana tunanin Unc
le dinta zuciyarta na fada Mata ta tashi tabishi taje taga halin da yake ciki amma saita dake kawai tayi kwanciyarta har dare ya fara ta fita ta koma parlourn Aunty Zarah ce kawai saboda Aunty Jameelah tun uku ta tafi sai Hajiya Kaka da maqota dayake aikin
abincin sadakar duk kwangila suka bayar suna zaune har sha daya sannan kowa yaje ya kwanta itama kwanciyar tayi amma zuciyarta taqi hutawa koda D.S ya kirata ma daqyar ta daga tace masa bacci takeji sukayi sallama ta aje wayar tanata karanta wasiqar jaki
ranar daga ita har Hameed babu wanda ya rintsa shi gani yake Umaimah taci amanarsa data yarda wani ya kwanta da ita harma yayi mata ciki wannan ciki ya tsone masa ido da yasan mugun ganin da zaiyi kenan da bai dawo 9ja ba yanda yakejin ciwon abinda ya ga
ni a jikin Umaimah bayajin ciwon mutuwar yaran nasa haka saboda yasan su lkcnsu ne yayi amma ita ta manta da halaccin da
yayi mata taje ta bawa wani kanta yanzu abinda yakeji a jikinta shima Sulaiman abinda yakeji kenan?
Wani kishi ya taso masa daq
yar ya rinqa danne zuciyarsa da qarfin addu'a.
Washe gari akayi sadakar bakwai basu hadu da Hameed ba harta gama zamanta a gdan D.S yazo daukarta ta hado shirginta ta fito yana yana riqe da hanunta yana zuba mata zance tana dariya Hameed din ya shigo a mo
tarsa sabuwa dal yayi parking duk da batasan shi bane amma saida gabanta ya fadi ta kalli motar sosai jikinta yana bata na cikin motar ita yake kallo.
Ilai kuwa itadin ya zubawa ido yanajin wani abu yana tasowa qirjinsa zuciyarsa tana tafasa yanda
suketa dariyarsu da Sulaiman din yana jamata karan hanci har kuma dan jaraba irin tasa ya kasa daina kallonsu yana qara tsinewa Salma data zama sanadin rabashi da farin cikinsa qiri² Umaimansa tafi qarfinsa yanason yaga ya cireta a ransa amma ya kasa huku
nci ya yankewa zuciyarsa na barin qasar gaba daya dama ya samu aiki a World Bank of America da yace bazashi ba amma yanzu dole ya hada komatsansa ya tafi can qila ya samu sauqin rashinta saboda yasani Umaimah batada ta biyu a gurinsa har yau idan ya kwanta
tunanota yakeyi da irin sadaukarwarta ga farin cikinsa.
Buruka da yawa daya dauka akan rayuwarsa da bloody dinsa yanaji yana gani sunbi ruwa wai yau bloody dinsa ce da cikin wani a jikinta har tana ganinsa tana razana to meye ma ya razanata dashi
? Tambaya ce da bashi da amsarta tashin motarsu ne ya dawo dashi hayyacinsa ya buga kansa a sitiyarin motar tare da dukan qirjinsa yana kiran “ya rabbih" yana hawaye masu zafi yace “Allah Kaine ka halicci zuciyata da son baiwar nan taka Allah kasani bani n
a dorawa kaina ba kaine ka jarrabeni Allah ka ciremin ita a raina Allah meyasa kullum ina roqonka kamar baka amsawa Allah banaso ka kamani dason matar wani kafi kowa sanin banida qarfin raba zuciyata da ita a jinina take yawo" bude qofar motar da akayi ne
yasashi dagowa da idanunsa da har sun dafe saboda kunan zucci ya zubasu akan Yusuf yayi murmushi don yasan kukan me yake Hameed bashi da damuwar data wucce Umaimah a rayuwarsa gashi Umaimah tayi masa nisa.
Dafashi yayi yace “mutumin ya kamata ka c
ire bloody dinnan taka aranka ka nemi wata yar baby ks aura ka qarasa rayuwarka da ita" wani kallo ya watsa masa wanda ya tilasta masa rufe bakinsa jikinsa har tsuma yake saboda bala'i yace “waikai anyama kuwa kasan meye so a rayuwarka Yusuf to bari kaji i
dan baka sani ba ka sani inasonta kuma ina fatan na mutu da soyayyarta wlh nayiwa zuciyata alqawarin bazan sabawa farin cikinta ina sani ba Umaimah tana sona jiya nagano soyayya ta da
tausayina har yanzu a cikin idonta Maliha ta fadamin tun jiya take tamba
yarta Ina Ina me nakeyi har turowa tayi tazo taga lfyta Umaimah tana kishin ganin nayi tarayyah da wata mace saboda haka bazanyi ba har abada zan hqr na rinqa azumi har zuwa lkcn da Allah zai yankemin ya kawomin mafita amma bata hanyar aure ba na hqr da au
re har abada indai bada bloody bane kuma koda banda rabon sake aurenta inason na mutu da soyayyarta saboda itama nasan da tawa zata mutu wlh Yusuf na tsani mutumin nan da yake ganin kansa wai mijinta kayyy! kayyy!! kayyy!!! badai miji ba dan riqon qwarya w
ai harma ciki yayi mata kuma ma harta kusa haihuwa"
Ya mgnr yana dafe kansa yana jan zuciya yace “babu komai qaddara ce da kuma rabo wannan kadai ya isheni ishara" ajiyar zuciya Yusuf yayi cikin tausayin abokin nasa yace “kayita addu'a Allah yana
sane dakai zai kawo maka mafita yawwa kaji kuwa cewa matarka tana gdan mahaukata?" Dagowa yayi da sauri yace “wa kenan?" Murmushi yayi yace “matarka data rabaka da kowa kaqiji kaqi gani matarka data rabaka da farin cikinka jiya nake samun lbrn ta haukace s
ai tonawa kanta asiri take har tana fadin yanda tayi ta rabaka da Umaimah da bayan ka daketa ka saketa komawar da tayi akan a haukata Umaimah yanda bakai ba wani ma bazaiyi sha'awar rayuwa da ita ba taje ta hado abinta tazo tayi ita kuma Umaimah tayi aure
wannan dalilin da kuma addu'a sune suka mayar Mata da abinta kanta" qwafa yayi yace “narasa me muka tsarewa mutane kowa yake nufin mu da sharri Allah shine muka dogara dashi kuma shine abin dogaron bloody" yana mgnr yana dafe qirjinsa yace “bani maganina
nasha qirjina ciwo yakeyi"
Haka sukayi sallama Yusuf ya tafi kwanaki biyar tsakani ya gama dukkan shirye²nsa ranar daya cika sati da dawowa daga India ya shirya sai birnin California na qasar amurka inda suka bashi katafaran gdan zama da zundumemi
yar mota da matsayin me girma a world Bank.
*******
Sati hudu da rasuwar su Shurafah Umaimah ta haifo yaranta biyu mace da namiji kyawawan gaske farare tas masu kama da ubansu fari irin na fulanin Yola wai zokuga murna gurin D.S anyi yaya
shine yayi musu huduba da Zulaiha da Kabir aka mayarwa da Hajiya chibinar ta sannan yasa wa namijin sunan mahaifinsa aikuwa yaran sunga gata amma shi yayi musu inkiya da Nawwas da Nawwarah ranar suna tazo akasha bidiri abu gwanin sha'awa har kuka Umaima
h tayi saboda gatan data samu gurin danginta da dangin mijinta goga Hameed ma da Daddy ya tura masa hoton yaran yayi murna sosai yaji qaunarsu har cikin jininsa ya rinqajin dama shi ta haifawa yaran bayan taro ya watse da kwanaki uku suna kwance da Sulaima
n aka kirashi a waya ake fada masa anyi musu rasuwa a Adamawa qanin mahaifinsu ya rasu
yaji mutuwar sosai don zaune ya tashi ya hada kai da gwiwa daqyar ta lallabashi suka kwanta da asuba ya tashi ya shirya lkcn har qaninsa Nura yazo daukarsa zasuyi sammak
o itadai Umaimah hakanan tarinqa jin gabanta na faduwa daqyar ta bari yayi kissing yaran ya rungumeta a jikinsa ya fita har ya fita ya dawo ya kirata ya janyota jikinsa yace “amana nabar miki yarana ki rayu dasu cikin aminci inasonki Umaimatu".........
*UMMUH HAIRAN CE...
✍
🏻
*
[2/3, 8:45 AM] UMMUH HAIRAN CE...
✍
🏻
: *_GU_*
Duk da faduwar da gabanta yakeyi hakanan ta qwaqulo murmushin qarfafa gwiwa tace dashi “zaka dawo ka samemu cikin amincin Allah" yayi
murmushi tare da kissing din bakinta ya fita da sauri suka dauki hanyar Adamawa.
Ta jima a tsaye a gurin daya tafi ya barta tana jera masa addu'ar dawowa lfy kafin ta koma cikin gdan lkcn twins dinta sun tashi dake tanada meyi mata raino ta basu sukasha t
a miqa Mata su ita kuma ta kwanta har yanzu ciwon jikin haihuwar bai saketa ba sannan D.S ya kuma tara mata gajiya da D.S da Hameed batasan waye yafi wani jaraba ba sauqinta daya shi baya dadewa kuma penis dinsa batada girman ta Hameed amma jiya ta fada du
k da bai shigeta ba saida yasan yanda yayi ya samu gamsuwa da ita sosai.
Wajen qarfe daya taji wayarta tana ring ta shiga dakin da sauri ta daga ta kara a kunnenta tace “Allah ya taimaki mijina badai har kunje Yola ba naga tfyr da nisa sosai” ajiy
ar zuciya taji anyi gabanta ya yanke ya sake faduwa kafin tayi mgn aka
katseta da cewa “matarsa ce ke?" Cikin in...Ina da tashin hankali tace “a...eh ni... Ina matarsa ce" me mgnr ya kuma cewa “sun samu hatsari ne a hanyarsu ta zuwa Adamawa amma yanzu haka
suna asibitin qashi na dala shine yace a kiraki a fada miki” wani salati ta saki tace “way... wayyoh Allah... Ni Umaimatu amma dai bai mutu ba ko?"
Bata iya jiran amsar dazai bataba ta kashe wayar cikin tashin hankali ta durqushe a gurin qirjinta
yana tsananta bugu jikinta yana wata irin rawa daqyar ta iya sake daukar wayarta ta kira Daddy tana kuka tana cewa “Daddy Abu Nawwas Daddy karya mutu don Allah ya barni ka hanashi mutuwa Daddy..." Saurin katseta yayi da cewa “ya salam waye ya fada miki Uma
imatu bafa shi bane qaninsa ne" Allah sarki baiwar Allah sai kuwa ta sauke ajiyar zuciya tace “Allah na gde maka daba mijina bane" hawaye Daddy ya share cikin rawar murya yace “ki... Kiyi hqr haka Allah ya tsara miki ga Hajiya nan zuwa da yayarku Zahrah za
su tayaki zama kafin yaji sauqi a dawo dashi kada kice zaki fita daga gdan nan" yana fadin haka ya kashe wayar bata samu damar yin tunanin komai ba taji shigowar motoci gdan aikuwa batasan sanda ta zabura ta miqe tayi waje a guje ba ambulance tagani da qan
anun motoci uku tayi wajen ta tsaya tana rarraba idanu kamar mahaukaciya zuciyarta takasa tuna komai Daddy da Abba mahaifin Sulaiman taga sun fito sai wata motar Dawood ne yayan Sulaiman da Nazir qaninsa dayar kuma Hajiya Sa'adatu ce da qannansa mata biyu
sai ma'aikatan asibitin da suka fito suka bude ambulance din suka janyo wani dogon abu da mutum kwance akai jini sai diga yake ta qasan gadon daukar gawar.
Daddy yana qoqarin riqeta amma ina da tayi wata alkafura ta dira gabansu kafin su ankara ta
janye yadin da aka lullubeshi ta matsa ta qara kallon fuskarsa da gaske ba gizo ba Sulaiman ne kwance babu numfashi a jikinsa fuskarsa wasai da murmushin sa na rahama ta dafe qirjinta tare da furta Innanillahi wa innah ilaihirraji'un tayi baya luuuuuu ta
zube a qasa itama qanwar gawa da sauri Daddy da Hajiya sukayo kanta aka dauketa itama aka shiga da ita ciki aka kwantar da ita a gado babu irin ruwan da basu yayyafa Mata ba amma taqi dawowa hayyacinta hakanan aka kimtsa Sulaiman aka daukeshi aka kaishi gd
ansa na gsky zuciyoyi na kukan rashin managarcin mutum salihin bawa wanda bashi da tamka Hajiya Sa'adatu fadi takeyi.
“Wlh babana da nasan mutuwa zakayi da bazan takura maka kaje gaisuwar nan ba saida ka nunamin bakason tfyr na takura maka dake ka
idin dane me biyayya haka ka tafi yanzu ka mutu babana ka mutu kabar matarka abar qaunarka ka mutu kabar yayanka masu kwanaki goma sha daya a duniya ka mutu ka barni kabar yan'uwanka kabar abokanka kabar kowa babana wayyoni kaina wayyoh Umaimatu dole ki su
ma kinyi rashi Umaimatu wannan mutuwa takice ke akayiwa mutuwa kin rasa miji me sonki da qaunarki kin rasa miji me tausayinki dason farin cikinki Umaimatu Allah ya mayar miki da alkhairi Umaimatu na rasaki yanzu kenan na rasa sukura ta qwarai
wadda ta gina
min dana da tsarkakkakiyar soyayyah Allah na gde maka da baka dauki rayuwar Sulaiman ba saida ka cika masa burinsa na ganin yayansa"
Bayan ankai Sulaiman makwancinsa aka dauki Umaimah aka tafi da ita asibiti tashin hankalin dasu Daddy basu taba s
higa wannan karon shi suka shiga ba akan Umaimah yau shi suka shiga Umaimah ma da ciwon zuciya wannan wacce irin jarabta ce suke fuskanta ne.
Bata samu kanta ba saida tayi kwanaki bakwai saboda kumburar da zuciyarta tayi twins kuwa sai madara ake basu bay
an ta dawo hayyacinta mutuwar mijin nata ta dawo mata sabuwa tayi kuka kamar ranta zai fita tanajin dama ita ta mutu ta huta daqyar Hajiya ta shawo kanta da dadadan kalamai da misalai kwatankwacin nata da kuma irin nasarorin da zata iya riska a rayuwarta d
a wadannan kalaman Hajiya da Daddy sukayita kwantar mata da hankali amma duk sanda ta kalli Nawwas da Nawwarah sai tayi kuka saboda tunawa da kalmarsa ta qarshe yayana amanane a gareki inasonki Umaimah” wannan dalilin taci alwashin zata tsaya ta riqe masa
amanar yayansa koda kuwa zata mutu babu aure ita aurenma ya fita a ranta tama hqr dashi gara ta