Showing 84001 words to 87000 words out of 137264 words

Chapter 29 - GIDAN UNCLE COMPLETE

a lkcn

da yaso a hankali cikin kuka ta zube ta dora goshinta saman tiles din toilet din tace “Allah kaji qaina kabawa dan'uwana lfy Allah ka yafe masa zunubansa Allah kada ka kashe Uncle ka mayar min da Shurafah marainiya kamar ni Allah ka tausayawa bawanka me q

oqarin tsayawa akan dokokin ka Allah na sani qaddara ce da sharrin shaidan tasa Hameed watsi da umarninka wannan jarabta tayi masa yawa da wanne zaiji"

Ta jima a bathroom din sannan ta fito ta zauna kusa da Shurafah ta daukota ta sanya mata nono ta

kuma fashewa da kuka Aunty Jameelah ta dubeta da sauri tace “mene kuma na kuka Baby?"

Dagowa tayi tace “Aunty kinga Hameed fah yanda ya koma aunty anya Hameed zai koma normal kamar da?" Harara ta zabga mata tace “to meye damuwarki da komawarsa kam

ar da Umaimah na dauka ko babu komai tsakaninki da Hameed yafi qarfin wannan wulaqancin daga gareki Umaimah me Hameed yayi miki da zafi haka da zaki kwana ki tashi ki kasa tambayar iyayensa jikinsa kina ganin hakan daidaine a gurinki Umaimah kina tunanin D

addy da Hajiya basajin zafi da ciwon ko in kula din da kike nunawa dansu gudan jininsu akan laifin daba tursasa ki yayi ba kece kikaba da qofar da hakan ta faru Umaimah ko kina tunanin Daddy da Hajiya zasu soki fiye da son da sukewa dansu na cikinsu? Amsar

itace aa Umaimah qaramin misali yanzu ki duba ki gani shekara nawa kikayi kina wahala da Nihal da Maliha kwana nawa kikayi da haihuwar Shurafah amma soyayyar Shurafah ta disashe hasken soyayyar da kika dauki shekaru kina nunawa Nihal da Maliha saboda itad

in jininki ce da wani bangare na jikinki aka halicceta balle su da suka dauki shekara sama da talatin da biyar da dansu wacce soyayya zasu nuna miki data dara ta dansu? Ki fadamin ita Umaimah"

Ta qarashe mgnr tana matsawa kusa da yar uwar tata ta ka

mo hanunta tace “amma saboda tsabar rashin kunya da tsageranci da cin fuska kika iya duban tsabar idonsu kika iya furta musu bazaki qara zaman aure da dansu ba kuma kin tsaneshi hmn yarinya kiyi gaggawar sake tunaninki wlh mutanen nan basu cancanci wannan

sakayyar daga gareki ba Umaimah kinsani Hameed yana sonki bazai iya rayuwa babu keba kamar yanda yasha fadamin, ko kinsan yasha zuwa ya fadamin irin wulaqancin da kikeyi masa da tsanar da kike nuna masa Umaimah Hameed yasha zuwa har Damaturu yasani a gaba

ya rinqa yimin kuka yana fadamin zuciyarsa zafi take masa a duk lkcn da yaso ganinki ko yaso jin muryarki yazo gdan kikaqi yarda ku hadu ko ya kiraki a waya kikaqi amsawa Umaimah ko kinsan Hameed yasha fadamin sonki shine zai kasheshi ko kinsan a ranar da

abin ya faru yana fitowa daga gdan Daddy ya daga waya ya kirani yake fadamin zuciyarsa fashewa zatayi Ina bashi hqr naji ya saki wata qara tare da kiran sunanki shikenan har yau tsayin sati biyu da kwanaki uku baisan kansa ba"....

Ajiyar zuciya ta

kumayi kana ta dora da cewa “bakiyi kuka ba Umaimah sai ranar da kika daura aure da wani ba Hameed ba aka kaiki gdansa dare yayi ya shigo yayi mu'amalar aure dake minti biyu ya sauka ya bingire ya fara bacci bai farka ya sake nemanki ba saida safe ki neme

shi yace kin cika karuwanci da takura shi ya gaji to a sannan ne zaki fara kukan nadamar gujewa namiji daya tamkar da dubu namijin da mace da yawa take burin mallakar irinsa kuma namijin da bazaki qara samun irinsa ba a duniya ke bari nayi miki kalmar qars

he Umaimah wallahi tallahi billahillazi La'ilaha illah huwa bazaki iya zama da kowanne namiji ba sai Hameed shine ya fara saninki dashi kika saba kuma shine daidai dake saboda danshi kadai aka halicceki kamar yanda yasha fadamin"......

_Kuyi manege

da wannan_

🙈

*UMMUH HAIRAN CE...

✍

🏻

*

[1/22, 8:35 PM] UMMUH HAIRAN CE...

✍

🏻

: *GIDAN UNCLE*

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:

*PAGE FOURTY TWO*

Kuka ta sake saki me ciwo tana girgiz

awa Aunty Jameelah kai, sake Mata hanu tayi tace “bazanyi miki dole ba kamar yanda Daddy yayi alqawarin bazaiyi miki dole ki yarda ki auri Hameed ba amma ina tausayawa rayuwarki a gdan wani ba Hameed ba domin shine mahadinki shine abokin rayuwarki kuma shi

ne qaddararki ko ki yarda ko kada ki yarda Hameed nakine kema tasace kamar yanda yasha fadamin danshi kadai aka halicceki saboda haka kiyi gaggawar dawowa hayyacinki kafin kiyi abinda zai zame miki ciwo har qarshen rayuwarki”

Tana fadin haka ta dauk

e Shurafah a jikin Umaimah ta cire mata Pampers tayi mata tsarki karbarta Umaimah tayi ta fita zuwa dakin Hajiya ta bude ta shiga da sallamarta tasa kai ta shiga turus taja ta tsaya ganin Hajiya zaune gefen gado ta hada kai da gwiwa tanata gursheqen kuka

.

Jiki a matuqar sanyaye ta qarasa ta tsugunna a gabanta ta kwantar da kanta a cinyar Hajiya kawai itama ta saki kukan da sauri Hajiya dago tace.

“Ke meye hakan Umaimah?" Cikin kuka tace “kiyi hqr don Allah Hajiya insha Allahu Uncle zai samu lfy za

i warke kuma zaici gaba da rayuwa cikin farin ciki kamar baya don Allah Hajiya ki daina kukannan banaso ya kikeso muyi keda zaki rarrashemu" shafa bayanta Hajiya tayi tace “na fidda rai da rayuwar yaronnan Umaimah koda ya farfado idan yaji hukuncin da kika

yanke na bazaki qara rayuwa dashi ba zaiyi mutuwar dungurungum saboda nasani kece zuciyarsa Umaimah bazai iya rayuwa babu keba..."

Zamowa Hajiya tayi tayi knilling a gaban Umaimah ta ruqo hanunta tace “Don Allah badon niba Umaimah ki taimakeni ki

yarda ki rayu da dana kece cikon farin cikinsa Umaimah zan rasashi idan kikaqishi don....." Saurin rufewa Hajiya baki tayi cikin kuka tace.

“Kada ki qara hadani da Allah Hajiya ko baki hadani da Allah ba nasani kuma na amince Yayana Abdulhameed mah

adin rayuwata ne bazan iya rayuwa babu shiba bansan inason Uncle ba kuma bansan ciwonsa nawa ne ba sai yau dana ganshi Hajiya na shirya sake komawa qarqashin inuwar auran Uncle Hameed indai wannan shine zaisa yaci gaba da wanzuwa cikin farin ciki...."

Wata runguma Hajiya tayi mata tana kukan dariya tace “na gde miki yata Allah yayi muku albarka Allah yabawa dan'uwanki lfy kuci gaba da qawatamu da salon qaunarku mai ban sha'awa" murmushi tayi tace “ina Daddy Hajiya?" Ajiyar zuciya tayi tace “yana Riy

adh gurin Hameed shida Yusuf"

Sunkuyar da kanta tayi tare da qurawa Shurafah idon har yanzu idan ta kalli Shurafah sai taji tsanar Hameed a ranta amma tayi alqawarin kankareta a zuciyarta saboda cikar farin cikin iyayensu miqewa tayi a salube ta kw

antar da Shurafah tace “na kawo miki ita ta tayaki hira inason zuwa harami ne Hajiya" murmushi tayi ta matsa kusa da Shurafah tace “ja'ira mekan qwanqwalati bata da aiki sai bacci kamar kasa nidai bansan ina kika debo ragwanta ba iyayenki duk ba ragwaye ba

ne" murmushi Umaimah tayi tace “kun daifi kusa ta kwana tana maki waqa” itama dariya Hajiya tayi tace “to ya zanyi hausawa sunce abin cikin qwai yafi qwai dadi ai Allah ya taimaka saikun dawo”

Amsawa tayi da amin sannan ta fice taje ta tarar da Au

nty Jameelah har ta shirya suka fito da qafa suka tattaka har masallacin harami suka fara gabatar da ibadarsu kamar kowanne musulmi itadai Umaimah rasa abin da zata roqi Allah tayi banda abu uku yafiya, samun lfyr yayanta da kuma shiriyar yarta Shurafah ba

su sukabar harami ba saida sukayi sallar asuba da yake tun kwanaki sha biyar da haihuwarta ta tsarkaka sai ciwon dinkin da tasha da har yanzu bai warkeba har zuwa wannan lkcn dingisa qafarta takeyi bata taketa sosai ba.

Haka sukaci gaba da gabatar d

a ibadarsu cikin rashin nutsuwar zuciya saboda itadai Umaimah hankalin ta yaqi kwantawa saboda rashin sanin halin da Hameed din yake ciki ranar da sukayi sati biyu a qasar Saudia ne ranar Daddy ya samu Umaimah a dakinsu shida Hajiya ya dubeta yace.

“Uwar masu gida Hajiya ta sameni da wata mgn a baya kinyi furucin bazaki sake rayuwar aure da Hameed ba kuma yanzu naji kince kin janye hakane?"

Jinjina masa kai tayi cikin kunya yayi murmushi yace “amma dai ina fatan ba wanine ya takuraki ya canz

a miki raayi ba?" Sake daga masa kai tayi yayi ajiyar zuciya yace “naji dadin hakan kuma nayi farin ciki da faruwar hakan Umaimah Allah yayi muku albarka ya shiga cikin lamarinku a gobe idan Allah ya kaimu zanje harami a mayar muku da auranku jibi saiku wu

cce Istanbul zuwa lkcn da zaku dawo komai yayi Normal da izinin Allah"

Dagowa tayi da sauri tace “aa Daddy nikam na fasa zuwa Istanbul dinnan ba" kallonta yayi da sauri yace “meyasa?" Qasa tayi da kanta tace “Daddy hankalina bazai kwanta ba ana zuwa

yawon shaqatawa ne saboda nishadi toni nawa farin cikin yana asibiti baisan wake akansa ba wlh Daddy koda na tafi hankalina bazai taba kwanciya ba kayimin hqr bazan iya tafiya bansan halin da Abdulhameed yake ciki ba"........

*UMMUH HAIRAN

CE...

✍

🏻

*

[1/23, 4:34 PM] UMMUH HAIRAN CE...

✍

🏻

: *G.U*

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:

Ajiyar numfashi Daddy yayi cike da jin dadi ya miqe yace “shikenan ki zauna Baby bazan miki dole ba a

mma kinsan bazaku zauna anan ba tunda kun gama umararku zaku koma gda duk halin da ake ciki ma rinqa waya saboda makarantar ki kuma ma jikin Hameed da sauqi tunda yanzu numfashin sa yana fita sosai kuma wasu bangarori na jikinsa suna motsawa ba kamar baya

ba"

Ficewa yayi ita kuma ta miqe ta haye gado ta kwanta inda Hajiya ta dauki Shurafah suka fice.

A washe garin ranar aka sake daura auranta da Hameed itadai a ranar yini tayi zuciyarta babu dadi hakanan bata farin ciki da auran nasu duk da ita kan

ta tasani yaudarar kanta ta rinqayi a baya da takejin kamar zata iya cireshi a ranta, kwana hudu suka qara a qasar Saudia suka dauko hanyar 9ja badan tanaso ba saidon batason yin musu da iyayen nasu musamman Daddy daya matsa akan sai sun tafi kwana uku ta

huta Aunty Jameelah ta kama hanyar gdanta ita kuma ta shirya domin fara halattar makaranta micro biology take karanta kuma tanajin dadin course din sosai da yake Umaimah bamai hayaniya bace yasa ko qawa batayi a skul din ba daga ita sai Shurafah dinta suke

harkokinsu yarinyar tayi qiba sosai tayi wayo cikin wata biyun idan ka ganta zaka dauka tayi wata hudu yarinya kyakkyawa abarso ga kowa ga Umaimah da sanin darajar kwalliya wa yaro kullum cikin ado Shurafah take hakan yaja Mata farin jini gurin yammatan d

epartment din nasu kowa Shurafah hakan yanasa Umaimah taji dadi aranta Saudat Alfah itama sabuwar daluba ce matashiya meji da gayu da tsayuwar naira a jikinta tunda ta shigo makarantar Allah ya hada jininta da Umaimah itama sanadin Shurafah Saudat Alfah it

ama matar aure ce da yaranta biyu tana auran wani custom tun Umaimah na janyewa abotar tasu harta saki jiki suka zama abokai sosai ita Saudat namiji take goyo Sudais kusan saanni ne da Shurafah.

Semester ta fara nisa sosai su Umaimah yan makaranta

itadai karatun kawai tasa a gabanta amma rabin hankalinta yana wajen su Daddy da kullum sukayi waya saidai yace musu jiki yana kyau sosai a haka har suka cinye semester sukayi hutu a cikin hutun ta takurawa Daddy kan cewa tanaso taje ta gano jikin Hameed

Daddy yaso hanata zuwan amma yanda yaga ta damune yashi dole ya qyaleta dake ya dawo dazai tafi suka tafi tare.

Kai tsaye asibitin da yake suka nufa suka shiga dakin tana rungume da Shurafah tunda suka shigo ya Hameed dake zaune jingine da matashin

kai ya ya zubawa Umaimah ido ya kasa ko qiftawa sai yawo yake da idanunshi akanta kamar wanda ya warke daga ciwon makanta ajiyar zuciya ya sauke ta dago kanta da tayi qasa dashi tun kallon farko da sukayima juna idonsu ya qara sarqewa da juna a hankali ya

daga hanunsa ya miqa mata alamun yana buqatar tabashi wani abu.

Cikin sassarfa ta qarasa gabansa ta dora masa Shurafah a jikinsa ya qurawa yarinyar da itama shidin take kallo ta qura masa ido sai bangale masa baki takeyi shima murmushin shima yayi m

ata tare da dagowa ya dubi Umaimah da taketa kallonsa ya rame sosai hancine kawai da ido sai dan qaramin bakinsa da yake motsawa a hankali alamun magana yakeson yi mata amma muryarsa bata fita sosai.

Shigowar Daddy da likitocin ne yasata neman guri kusa d

ashi ta zauna a sanyaye taji ya ruqo hanunta ta dago da sauri suka hada ido ya lumshe nasa a hankali ya bude tare da cewa “Kina kulamin da Shurafah yanda ya kamata kuwa?"

Yayi mgnr da murya me rauni a salube ta jinjina masa kai ya janye hanunsa dag

a nata tare da cigaba da kallon yarinyar yanajin qaunar da baitabaji akan sauran yayansa ba game da yarinyar dagata yayi a hankali ya dorata a qirjinsa.

*UMMUH HAIRAN CE...

✍

🏻

*

[1/23, 8:05 PM] UMMUH HAIRAN CE...

✍

🏻

: *G.U*

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:

Likitan ne ya dubi Daddy sukayi larabcinsu ya miqawa Hameed hanu sukayi musabiha suka juya suka fita Daddy ya dubesu yace “zuwa sati idan ka qara warware

wa saimu tafi gda ko babana?" Lumshe idonsa yayi ya bude Daddy yayi murmushi yace “gadai Umaimah tazo ta kawo maka Shurafah nima hankalina ya kwanta yanzu zamu iya tafiya"

Daddy ne ya taimaka masa ya miqe kasancewar komai a asibitin ake masa babu ab

inda suka dauka sai kayansa yana rungume da Shurafah Daddy yana riqe dashi haka suka fita motar asibitin ta daukesu zuwa masaukinsu dakin da Daddy ya

kamawa Umaimah nan yakaiwa Hameed kayansa ya juya ya fita ya barsu su biyu zama yayi a gefen gadon yana bi

nta da shu'umin kallonsa me kashe mata jiki bata iya ce masa komai ba sai neman guri da tayi ta zauna a saman resting chair din dake gefen gadon ajiyar zuciya ya sauke tare da kawar da kansa daga kanta yace.

“Ina buqatar zan kwanta na huta” da sauri

ta dubeshi ya sake kawar dakai yace “ina nufin Ina buqatar privacy zaki iya fita kice da Daddy ya kama maki wani dakin" dagowa tayi zatayi mgn yayi saurin daga mata hanu yace “banason surutu kuma banason takura kitashi kije ki kwanta dare yayi"

Ji

kinta a mugun sanyaye ta miqe ta nufi gadon idanunta ya ciko da hawaye ta sunkuya zata dauki Shurafah ya daka mata wata tsawa data sata saurin yin baya yace “get out for my room" da sauri ta juya ta nufi qofar dakin ta bude a tsorace ta fice daga dakin.

Miqewa yayi ya kwantar da Shurafah dake bacci yasha magungunansa ya kwanta tare da janyo yartasa a jikinsa da haka bacci ya daukesa.

Umaimah kam a tsayawa tayi jikin qofar dakin zuciyarta nayi mata wani zafi da ciwon irin korar da yayi mata takeji wa

i ta fice masa daga dakin wasu hawaye ne masu zafi suka ziraro mata ta zauna a parlourn saman carpet zuciyarta nayi mata suya wannan ko wanne sabon wulaqancin rashin lfyr tasa tazo masa da ita oho.

Da wannan tunanin ta kwanta saman carpet din bacci

ya dauketa da asuba ya farka yayi alwala yayi sallah yana zaune saman sallaya ta bude qofar ta shigo ta saida gabanta ya fadi data ganshi zaune yana lazumi kamar wacce qwai ya fashewa a ciki ta nufi bathroom din ta dauro alwala ta juya ta fita zuwa parlour

n ta tayar da sallah tana idarwa yana fitowa yana cilla Shurafah sama yana cafewa ya zauna saman kujerar yana yima yarinyar wasa cikin faduwar gaba tace masa.

“Ina kwana" kallonta yayi kallo irin na rainin wayo yaci gaba da yima yarsa wasa shiru tay

i masa taci gaba da azkar dinta kamar daga sama taji muryarsa yana cewa “wato da nace kije ki fadawa Daddy bana buqatarki a kusa dani ya nema miki dakin da zaki zauna kafin mu koma gda shine saboda ban isa ba kika kwana anan ko? To bazan hanaki kwana anan

ba tunda haka kika zaba amma kisani kada ki kuskura ki shigomin daki da dare ranki baci zaiyi"

Harya gama mgnr batace masa qala ba sai hawayen da take zubarwa a rayuwarta babu abinda yake mata ciwo irin jizgi da wulaqanci bata jurewa hakan ko kadan

.

Bai sake bi ta kanta ba ya tashi ya miqa mata Shurafah yace “yarinyata me hqr ya kamata a bata abincinta taci" yana fadin haka yasa hanunsa ya zare hijjab din jikinta ya zuge zif din ya sanya hanunsa ya dago qosasshen breast din nata yayi ajiyar zuciya

tare da hadiye wani yawu ya saita bakin Shurafah yasa mata ta kuwa kama da sauri harda sanya hanunta ta dafe.

Miqewa yayi ya shige dakin saboda wani yar da yakeji a jikinsa ya fada bathroom da sauri ya sakarwa kansa ruwa ya fito ya dauki wani magani

da Dr Maheelr ya bashi wanda yake taimaka masa wajan control din feelings dinsa sosai yasha ya koma ya kwanta tare da jan blanket sanyi Umaimah takeji sosai saboda weather din sanyin Saudi akwai shiga jiki amma tsoron ta tashi ta shiga dakin take ta dauko

rigar sanyinta saboda ta lura ya qaro rashin mutunci sosai hakanan ta zauna data gaji ta dauki pillows din kujerar ta kwantar da Shurafah itama ta kwanta.

Ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login