Showing 27001 words to 30000 words out of 34067 words
yayi dai dai sai a kara mata”.
Dr Khalid ya ce ”To muje lab a gwada” za su lab din sai ga su Mama sun karaso.
Bayan an gwada jinin Dr Nura din aka samu yayi dai dai dana Khadeejatu nan aka dibi leda biyu aka karawa Khadeejatu din aka kaita dakin hutu.
A lokacin su Hafsa da su Mami sun karaso inda Hafsa da taji labarin ta ringa kuka ita a tunanin ta ma Khadeejatu din ta mutu.
*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* ............
*Ta ku ce har kullum*
_Addeejerh😘_
✨✨✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨✨✨
*LABARI/RUBUTAWA*
*KHADIJA ADAM IDRIS*
( _Shalelen kainuwa_ )
*MARUBUCIYAR*
👩❤️👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩❤️👨
*AND NOW*
✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨
*___________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*__________________________________*
ALHAMDULILLAH!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah kasa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai.
Sadaukarwa
Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana.
Amin
_ALKALAMIN DA_ _BAYA RUBUTA_ _SHIRME🤟👌_
49~50
Nura da kyar ya bar asibitin dan sai da Mama ta ce ya tafi saboda kayanshi da ya baci da jini gashi farin kaya.
Ya na zuwa gidan ya ga ba motar Zainab babu alamunta kawai ya girgiza kanshi su ka shiga side din Khadeejatu shida Maryam.
Maryam su na shiga ta gyara falon ta goge jinin da ya zuzzuba nan ta feffesa freshner tuni gida ya dau kamshi.
Kana ta shiga kitchen da sauri-sauri ta dafa abinci mai sauki wato jalof din taliya sai kunun gyada da tayi dan ta san Khadeejatu naso Allah kuma ya taimaka da akwai gyadar kunun.
Bayan ta hada basket din ta fito da shi falo Nura shima a lokacin har yayi wanka ya shirya ya na saka hula a kanshi ya cewa Maryam “lil sis ina fatan dai kin gama?”.
Maryam ta ce “Ehhh Yaya” Nura yayi murmushi ya ce “Sannu da aiki Allah maki albarka ya nunan Bikin ki da Barrister”.
Maryam tayi mutmushi ta na rufe fuskarta .
Nura yayi dariya ya ce “kyadai ji dashi dauko basket din mu tafi”.
Maryam tana murmushi ta yafa mayafinta ta dau basket din suka fito ya rufe kofar da mukulli.
Su na karasawa asibitin su ka nufi dakin da aka kwantar da Khadeejatun Aminity 2.
Nura da ke gaba ya tura kofar dakin kiiii bakinsu dauke da sallama su ka shiga dakin .
Mami ce kawai a akan Khadeejatu da take ta kuka fadi take cikin kuka ta ce “Shikenan cikin nawa ya zube yanzu bazan haihuwa ba wannan rayuwa ina zata damu wayyo Yaya cikina”.
Da hanzari Dr ya karasa jikin gadon ya na fadin ”Ta farka ne? ya ke tambayar Mami.
Cikin damuwa Mami ta juya ta kalleshi ta na fadin “Ga tanan ta farka sai surutai take nayi lallashin duniya ta kiyin shiru ko idonta taki budewa” ta karasa zance tana matsawa baya.
Shafa kanshi Nura yayi , Mami tayi kamar bata ganshi ba ta ce ”rarrashe ta ko kai ta saurare ka”.
Cike da kunya ya kama hannun Khadeejatun ya ce “Khadeeja kiyi hakuri dan Allah kiyi hakuri cikin ki nanan tunda nan ma ina jiyosu su na ball sojojina kenan”.
Cikin dashewar murya Khadeejatu ta ce “Ba wani Yaya ni na san ya zube”magana ta ke still idonta a rufe.
Dr Nura ya riko hannunta da ba canular ya dora mata akan cikin ta ya na murmushi ya ce “Kindai ji cikin na nan ko? ya na dariya ya karasa maganar.
Murmushi tayi sai a lokacin ta yarda ta bude idonta dariya Nura ya kyalkyale da ya ce “Ya jikin rigimammiyar matata”.
Chuno baki Khadeejstu tayi ta ce “Da sauki daga yau na gama shan yoghurt”.
Mami ganin ya kamata ta basu guri ta tafi gurinsu Umma Hafsa ma na waje ta na waya.
Bayan fitar Mami Dr Nura ya zuba ma Khadeejatun kunun gyadar da Maryam ta hada mata kuma ba laifi tasha da yawa.
Sai da su Umma su ka dawo dakin sannan Dr Nura ya wuce office dinshi shigar shi office din kenan yaji anyi Knocking cikin muryar shi mai sanyi ya ce “Come in”.
Tura kofar akayi Dr Khalid ne bakinshi dauke da sallama ya shigo Dr Nura na murmushi ya amsa mashi sallamar da yayi.
Shima Dr Khalid ya mayar mashi da murmushi ya zauna a kujerar da ake ganin likta ya na dariya ya ce ”Kaga mai mata biyu Zainab da Khadeeja kuma Abban unborn mai zuwa insha Allah”.
Dariya Nura yayi yace “Wannan kirarin duk ni kadai” nikam in tambaye ka mene ya kawo zubar da jinin da Khadeeja tayi har ya na kokarin salwantar da abun da ke cikin ta?”.
Ehmmmm Dr Khalid yayi gyaran murya ya ce “To a iya binciken da mu ka yi poison ta sha, kuma poison din da alamu a abu mai ruwa ta sha”
A zabure Dr Nura ya tashi ya ce “kanaso kace mun a cikin yoghurt din da ta sha ne da poison a ciki ina da sake” kawai ya bude kofa ya fice ba tare da ya saurari kiran da Dr Khalid ke mashi ba.
Inda suke parking motoci ya nufa inda ya bawa motarshi wuta inda ya budawa Dr Khalid da wani Dr kura.
Dr Nura na tuki zuciyarshi na tafarfasa duk idanuwanshi sun ka'da.
A kofar wani police station yayi parking ya na shiga ya nufi police din da su ke tsaye a bayan kanta.
Nan suka gaisa ya masu bayanin abinda ke faru nan su ka hadashi da police guda biyu.
Nan su ka nufi gurin da ya siyi yoghurt din inda shi ne kadai ya shiga gurin saboda bayason a tada hayaniya.
Ya na shiga ya fara baza idanuwa wanda kallo daya za kai mashi ka san ba a cikin nutsuwarsa ya ke ba.
Nan inda idanuwanshi ya sauka a kan wanda ya sai yoghurt din a gurinshi.
Nan ya nufeshi sai da ya gama sallamar customer dinshi sannan Dr Nura ya ce “Mashi dan uwa in ba damuwa dan Allah ina son muyi magana da kai”.
Mai siyar da Yoghurt din ya ce ”B damuwa nan su ka fita waje su na fita su ka fara magana aiko nan police din su ka kamashi su ka sa a mota sai police station din.
Su na zuwa police station din nan aka ce Nura ya bada bayanin ya akayi tun farko nan Nura yayi bayanin duk abinda ya faru tun daga lokacin da Khadeeja ta kirashi.
Bayan DPO ya gama jjn bayanan duk abinda Dr Nura yayi sai ya kalli mai siyar da yoghurt din ya ce “Kai kuma mai zaka ce?”
Nan mai sai da yoghurt ya ce ”Wallahi tallahi yalllabai ni ba abun da na zuba mashi a yoghurt ya ma zan aikata haka mai ya mun da zan mashi wannan abu abinda yau mu ka fara ganin juna ma”.
Nura ne ya ce “To in bakai ka zuba ba to wane zai zuba?”.
DPO ne ya katse Dr Nura ta hanyar cewa “Malam Nura ka bi komai a hankali za'ayi bincike ne zamu gano gaskiya ina fatan da akwai ragowar yoghurt din da aka saka poison din ?to indai da ragowa za aje ayi test a ga koma me ne da lokacin da aka saka poison din mu kuma san time din da ka koma gida”.
Nura ya kalli DPO din ya ce “Eh akwai ragowarshi dan kadan irin na kasan robar nan za a iya test din dashi”.
DPO ya cire glsss din idanuwanshi ya ce “Okay tohm yanzu kaje gida ka dauko shi mu kuma zamu cigaba da rikeshi har sai anga mai ne result din test din”.
Dr Nura ya ce ”Toh yallabai bari naje gidan na dauko .
Bayan Nura ya karasa gidan nan ya dau robar yoghurt din.
Bayan anyi test din result ya nuna awanni daya ne da sanda ya koma gidan da kuma lokacin da aka saka poison din.
Bayan dogon nazari da DPO yayi sai ya fuskacin Dr Nura ya ce ”Amma Dr lokacin da ka tsiya ina ka fara zuwa?”
Dr Nura ya gyara zama ya ce “Ban tsaya ko ina ba sai gidana ”.
DPO ya jijjiga kanshi sannan ya ce “To a gidan wane da wane a zaune”.
Dr Nura ya ce “Mata na ne guda biyu”.
DPO ya ce “A bangare daya su ke tare ko kuwa ko wacce da bangarenta?, Dr Nura ya amsa mashi da bangaren su daban daban, DPO ya ce “Da kaje ka zauna a gidan? ko kuma dada fita kayi?”.
Ajiyar Zuciya Dr Nura yayi kana yayi gyaran Murya ya ce “Ehh toh na fita amma ba nisa nayi ba dan iya kata kofar gida inda nayi parking motata dan ina da niyar sake fita dalilin da yasa ma ban fice ba inaso in dan gyara abu ne a motar to naje kuma zan dau kayan gyaran sai na ga amaryar tawa kwance cikin jini”.
Sai da DPO yayi dan rubuce rubuce sannan ya dago kanshi ya ce ”A gaskiya yanzu mu na bukatar ganin daya matartaka wato uwargidan”.
Dr Nura ya ce “Okay ba matsala yallabai insha Allah zan kawota” nan dai su ka yi sallama .
Asibiti Dr Nura ya koma nan su Umma da duk hankalinsu ya tashi nan ya sanar dasu abinda ke faruwa nan dai su kai fatan alheri sai da ya tambayesu ko su na bukatar wani abu su ka ce basu bukatar komai nan ya tafi a cewar sai dare zai dawo.
Dr gida ya koma inda Allah ya taimake shi Zainab ta dawo nan yaje gurinta da siyasa da wayo yace mata tazo ta rakashi unguwa ita kuma shasha sai ta amince har ta na yake baki nan su ka fice a kofar police station ya yi parking a firgice Zainab ta kalleshi ta ce “Ahhh lafiya kuma naga ka kawo mu police station?”.
Dr ya shafa gyararren gemun shi ya ce “Gurin abokina nazo kafin muje inda zaki rakani”.
Wata karkarfar ajiyar zuciya Zainab ta saki jin abinda Dr yace nan Dr ya ke mamaki mai ya faru tayi wannan ajiyar zuciya haka.
Amma sai ya kawar da wannan tunanin yace mata su shiga ta futa direct Office din DPO su ka je.
Nan akayi ram da ita aka sananar da ita dalilin zuwan nata nan ta ringa rantsuwa ta na magiya akan ita ba ruwanta ba a abinda ta sani ita bama tasan Khadeeja din bata da lafiya ba
A na cikin haka ne sai Mama ta kira taji ko ya ake ciki nan Dr Nura ya sanar da ita komai tace yayi hakuri kawai ya barwa Allah duk wanda yayi ba dai dai ba kanshi............✍🏻✍🏻
*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* ..........✍🏻
*Ta ku ce har kullum*
_Addeejerh😍_.
✨✨✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨✨✨
*LABARI/RUBUTAWA*
*KHADIJA ADAM IDRIS*
( _Shalelen kainuwa_ )
*MARUBUCIYAR*
👩❤️👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩❤️👨
*AND NOW*
✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨
*___________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*__________________________________*
ALHAMDULILLAH!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah kasa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai.
Sadaukarwa
Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana.
Amin
_ALKALAMIN DA_ _BAYA RUBUTA_ _SHIRME🤟👌_
51~52
Nan a police station din Dr Nura ya sanar da DPO mai mahaifiyar shi tace da DPO din yaki kawai dai sai ya hakura nan a ka sallami mai siyar da yoghurt nan shi kuma ya sa Zainab a gaba su ka tafi.
Ai tunda su ka hau titi Zainab ta ringa fada mashi maganganu shi dai ya mata banza bai kulata ba.
Bayan ya sauketa kawai ya wuce asibitin ya na shiga dakin nasu Mama ta fuskanci akwai matsala dan fuskarshi duk ba annuri jijiyar kanshi duk sun firfito.
Ba laifi Dr Nura an danyi hira dashi sai wajen 11 ya bar asibitin.
Ya na komawa gida sai ya nufi bangaren Zainab nan yayi ta knocking amma shiru Zainab din ko ta na jin duk bugun da ya ke kawai ba zata bude ba ne.
Haka Dr Nura ya karaci bugunshi har ya hakura ya je ya bude side din Khadeejatu ya shiga.
*Bayan kwana biyu*
Kwanan Khadeejatu biyu a asibiti yau laraba aka sallamo ta da yamma nan Mama ta wuni ita da Mami dan Umma gida ta wuce sai daf da magariba su Mami su ka tafi inda aka bar Hafsa da Maryam su zasu dan zauna mata na dan kwanaki.
*Washegari*
Zainab ce da Safiyya a falo su na hira Zainab ta gyatsine baki ta ce ”Rabu da wannan tsinannen cikin duk irin karfin maganin nan cikin da ya ke tsinanne ne yaki barewa”.
Cikin masifa Nura da shigowarshi kenan cikin bacin rai ya kalli Zainab ya na nuna ta da yatsa ya ce “Yanzu ke zainab kece dama sanadin son hallakar mun da gudun jini ko da yake ba wani abu bane yasa ki yin hakan ba sai jahillaci da bakin hassada”.
Cikin rashin mutunci Zainab ta dakatar dashi ta hanyar fadin ”Ehhh din nidin ce ko da uwar uban da zaka yi ciki ne na dau alkawarin cewa bazai zo duniya ba......” cikin kunar rai Nura ya kikkifawa Zainab mari har sau hudu wanda shi ne yayi sanadiyar makalewar maganar da ta ke.
A hargitse Zainab ta dago kanta ta na kallon Nura cike da mamaki ta na dafe da kuncinta.
Nura wanda idanuwanshi su ka kada su ka yi jajur kamar garwashi ya maida kallonshi ga Safiyya ya daka mata harara cike da tsantsar tsana ya daka mata tsawa ya ce “Bakar munafuka algunguma tashi ki bar mun gida karki kuskura in sake ganinki a cikin gidana”.
Ai a tsorace Safiyya ta wawuri dan kwalinta da yagololon mayafinta ta suri jakarta ta fice a guje dan ba karamin tsorata tayi da Dr Nura ba.
Bayan fitar Safiyya ne ya maida kallonshi gurin Zainab dake dafe da duka kuncinta biyu yayi kwafa ya fice.
Ya na shiga Bangaren Khadeejatu ya tarar da su Maryam su na zaune a falo su na kallo ko ta kansu bai bi ba ya wuce corridon da zai sadashi da dakunansu.
Da kallo Maryam da Hafsa su ka bishi da kallo cikin hadin baki Khadeejatu da Hafsa su kace “Toh Yaya ko mai ya faru”.
Maryam ta tabe baki ta ce ”Zai wuce wanchan matar tashi....”ai bata karasa ba sai ga Zainab ta shigo kamar an jefota tana fadin ”Har ma ni za'a mara akan wannan cikin to billahil lazi yau sai na barar da shegen cikin da ake abubuwan akan shi ta dunkule hannunta inda ta nufi Khadeejatu da ta mike tsaye ta saici cikin ta ai nan Maryam ta fizgota ta rirrike mata hannaye.
Inda Hafsa ta kama Khadeejatu da ke kuka cikin kukan take fadin ”Wai ni mai na maki ne da kikeson ganin bayana”.
Cikin karaji Zainab dake ta fizge fizgen kwacewa daga rikon da Maryam ta mata ta dallawa Khadeejatu harara ta ce ”Ke kika janyowa kanki da har kika yi gigin auren mijina”.
Nura ne ya fito falon jin hayaniyar da yayi Zainab ya gani su hafsa sun rirriketa kamar wacce ta ci memory lolx, .
Cikin kumfar baki ya ce “Ke wai Zainab baki da hankaline?” ya kalli su Maryam ya ce ”Ku cikata ta zubar da cikin kuma wallahi Zainab muddin kika taba Khadeeja kisa a ranki a bakin auren ki baza ki taba dawowa ba kuma.
Bayan sun cikata ta kasa aikata komai in banda muzurai da ta ke tayi.
__________
*Bayan wasu watanni*
Khadeejatu kwance a kan gadon Mama wanda tunda cikinta ya kai wata takwas Mama taje ta dauko Khadeejatun ta dawo da ita gida.
Khadeejatu dake kwance shememe da katon cikinta da za kayi tunanin yan biyu ne ko uku dan girmashin ya zarce misali a ce da daya ne gashi scanning din duniya da aka yi da guda daya ne.
Wani irin ciwon mara ne ya ziyar Khadeejatu nan ta fara ciccije baki ga bayan ta ya rike wanda tun jiya da daddare take jin irin wannan yana yin.
Nan ta ringa murkusutsu ta na ciccije baki cikin karfin hali ta fara bin bango har ta samu ta bude kofar dakin ta fice a falo ta tarar da Mama zaune tana kallo taga Khadeejatu ta fito Mama ta na murmushi ta ce ”Har kin fito ne”.
Khadeejatu ita ma tana murmushi ta dagawa Mama kai ta na cewa ”Eh” Mama ta samu kujera 2 sitter ta zauna da dabara ta zauna .
Nan mama ta ringa mata sannu sannu cewa take “Khadeeja Allah dai ya raba ku lafiya” a hankali khadeejatu ta amsa da ”Amin”.
Nan suke ta yar hirarsu Mama ce ta ce “Khadeeja lafiya naga kina ta ciccije baki kodai haihuwar ce?”.
Wani irin murdawa da marar Khadeeja tayi ne ya sa ta ma kasawa bawa Mama amsa sai girgiza kai da ta ke yi.
Da sauri Mama ta mike ta karasa gurinta ta kama ta tana mata sannu da karfi ta kwalawa maryam kira da ke kitchen ta na yanka salad jin kiran da Maman ta ke mata ne ya sa ta saurin fitowa.
A firgice Maryam ta kalli Mama ta ce “Lafiya? ko haihuwar ce?”.
Mama ta kalleta ta ce “Ehh dauko mayafin ki da key din motarki ki dauko akwati”.
Ko amsawa batai ba da gudu ta nufi dakinta nan ta dauko akwatin da mayafin nata ta daukowa Mama hijabi.
Sai da ta fara kai kayan tazo ta taimakawa Mama su ka kamata su ka kaita mota.
Nan Maryam ta jasu sai asibitin nan da Dr Nura ke aiki