Showing 9001 words to 12000 words out of 34067 words

Chapter 4 - KHADEEJATU COMPLETE

halin Yaya Nura yake ba"


Lallabawa Mama tayi tashi zaune ta jingina a jikin Allon gadon ta kalli Maryam ta ce ”Wane irin Zargi kikeyi Maryam?".


**********

”Haba ku kuwa Yayan nan yaushe zaku shiryu ne kuyi hankali dazu muna zaune da Ummanku Hajiya Kubra tazo da yarta duk fuskarta a kumbure tana ta masifa yarinyar tace wai haka kawai suna fada Khadeejatu tazo ta shiga fadan shine tawa yarta jini da majina" cikin fada Mamin Hafsa take maganar.


Khadeejatu ce ta ce ”Toh....toh" Mami ta ce “Dallah chan ku rufen baki ku bace mun da gani tun kafin na sassaba mu ku wallahi Allah".


Su na tutturo baki gaba su ka tashi.


************


Tass tasss tasss kakeji Maryam ce ta fallawa Zainab mari zafafa guda uku da har sai da wayar dake hannun Zainab ta fadi a kasa .



Tasss ta sake faula mata wani marin wani irin gigitaccen ihu Zainab ta saki tana kuka



Maryam ta nuna Zainab da hannu tana hararar ta ta ce “Kinyi na farko kin yi na biyu da har zaki sake tunkarar uwata da nufin rashin kunya nasan baki taba tunanin zanzo ba to wallahi kika kuskura kika yi na uku wallahi sai na maki dan iskan duka da sai dai azo a samu gawar ki in kunne yaji jiki ya tsira".



Ta na gama fadar abunda zata fada tasa kai ta fice.



Gwalolo Zainab ta bita da kallo .



______________



*BAYAN SHEKARA BIYU*


A cikin wannan shekara biyun nan ne abubuwa da yawa sun faru su Khadeejatu sun gama makarantar sakandiri a halin yanzu an kawo kudin auren Khadeejatu in da zata auri wani Yusuf wanda suka hadu dashi a gidan bikin yar uwarsu Hafsa yayan Amaryar ne cousin gurin Hafsa dan yayar Mamin ta.


“Hafsa dan Allah ki taya ni zabar kayan da zansa in Yaya Yusuf zai zo anjima duk na hargitsa kaya na"


“Kinga kisa wanchan leshin namu brown mai ratsin orange" cewar Hafsa tana nuna mata leshin da Hannu.


Khadeejatu ta durkusa ta dauka leshin fuskarta dauke ta murmushi ta kalli Hafsa tace ”Wallahi yayi ni nama manta dashi ke yanzu wanne zaki saka?, kinsan yace zai kaimu shopping"


Hafsa ta ce “Nima bari kawai nasa irin shi muyi anko"


Khadeejatu ta ce “Yauwa haka ko za'ayi"


*************


Khadeejatu ce a kwance wajen sha biyu na dare bata yi bacci ba Hafsa kuwa tuni ta wuce Gusau lol,


Khadeejatu idonta kirr akan cilin din dakinsu ta na ta tunanin masoyinta Yusuf.


Wayarta ce da Yusuf din ya siya musu ta fara ringing da sauri ta duba taga ansa Yaya Yusuf har ta katse bata daga ba ita nan wai irin jan ajin nan na yanmata lol,


Wani kiran ne ya sake shigowa sai a lokacin ta daga chan yusuf ya ce


“Assalamu Alaikum ya ma'abociyar kyau da cikar kamala da fatan na same ki lafiya?"


Wani yarrr khadeejatu taji a jikinta duk tsigar jikinta tashi ta rasa mai yasa duk sanda ya mata magana take jin hakan.



Sun dau wani guntun lokaci ba wanda yace da dan uwanshi ci kanka
Chan Yusuf ya katse shiru ta hanyar cewa “Naji kinyi shiru Nanata"



Sai da Khadeejatu tayi wata sanyayyar ajiyar zuciya sannan ta amsa “Wa'alaikums salam Ya yusuf lafiya kalau ina fatan haka kaima".



*************


“Dan Allah Safiyya kiyi sauri kizo ki taimakan wani irin nake ji pls kozo na rage zafi" Zainab ke maganar tana wani irin nishi .


Daga ita sai guntuwar rigar bacci hannunta na ta yawo a kan dukiyar fulaninta da ko bra bata sa ba.



( waiyazubillah Allah ka kare mu daga sharri aika zunubi , Allah ka kare mana gabannin mu daga aikata Alfasha Amin ya rabbil Alamin.)



Ba ayi ko minti ishirin ba sai ga Saffiya ta karaso Zainab na ganinta tayi sauri ta kamo ta , taja ta daki nan ta tsige rigar barcin jikinta.


Ta cirewa Safiyya kayanta gaba daya nan su ka fara aikata Alfasha waiyazubillah..............🖊️✍🏻









*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* ...........✍🏻✍🏻








Taku ce har kullum
_Addeejerh❤️_


✨✨✨✨✨✨✨

*KHADEEJATU*

✨✨✨✨✨✨✨



*LABARI/RUBUTAWA*



*KHADIJA ADAM* *IDRIS*
( _Shalelen kainuwa_ )


*MARUBUCIYAR*



👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨

*AND NOW*

✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨


*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

ALHAMDULILLAH!!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah ka sa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai .




Sadaukarwa

Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana

Amin.



17~18

Su na gama aikata badalar su ko wanka ba suyi ba su ka dafa indomie su ka baje su ka ci su ka bingire bacci (waiyazubillah zama da janaba).


*************

Hafsa ce ta shigo dakin ta tana fadin “Dan Allah Khadeejatu ki zo muje chemist a maki Allura kinki gashi jikin ki yayi......"


Abun da ta gani shi ya makalar da maganar da take da karfi ta kwalla kara tana fadin “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun".


Mami ce ta shigo da sauri har ta na tuntube gurin Khadeejatu ta nufa ta fara jijjigata tana fadin “Innalillahi ki tashi Khadeejatu" amma ina ko motsi bata yi.



Da gudu Hafsa ta fita ba ko dan kwali a kanta baram ta fada gidansu Khadeejatu ba sallama ta fara kiran Umma!! Umma!! Umma!!.


Da sauri Umma ta fito a hargitse ta kalli Hafsa ta ce “Lafiya zaki zo kina mun kiran mafarauta? kinga ma yadda kika fito".


Kama Hannun Mami Hafsa tayi jikinta sai kyarma yake cikin rawar baki ta ce ”Khadeejatu!! Khadeejatu!! Umma" lu tayi kamar zata fadi.


Da sauri umma ta kamo ta tana jijjiga ta tace “Mai ya faru da Khadeejatu din?".

Kasa magana Hafsa tayi nuna hanyar futa take yi kamata Umma tayi ta rufe gidan su ka fice sai gidan su Hafsa.


Su na zuwa su ka tarar Mamin sai yayyafawa Khadeejatu ruwa take bata farfado ba .


Da sauri Umma ta karasa gurin Khadeejatu tana ta salati ( ita ba ta yarda da da abun yan fari ba)dora kan Khadeejatu tayi a cinyarta ta cire mata hijab din da tayi sallah ta zuge mata zip din rigarta ta fara mata fiffita da hijabin amma ina.


Mami ta kalli Hafsa da ke ta kuka ta ce “Yi maza ki samo mana adaidaita kawai mu wuce asibiti".

Da sauri taje ta samo mai adaidaitar har kofar gida su Umma suka dauko Khadeejatu.


Hafsa tana ta kuka haka da dauko hijabi tasa ta dau wayarta ta rufo gidan su ka wuce Asibitin.



Su na karasawa asibitin da sauri likitocin sun ka karbe ta gani halin da take ciki.


Hafsa sai zurga take ta na kuka tafiya tayi tafiya wajen awa daya sai a lokacin lokitocin su ka fito.


Da sauri su Mami su ka nufe likitan a tare su ka hada baki wajen fadin ”Doctor ya ake ciki ta farfado?".


Doctorn ya kallesu ya ce “Ku buyo ni Office" ya nufi Office ya na sharce gumin fuskar shi da hankachief Dr Musab kenan.


Su na shiga Office din su ka zazzauna.


Kallon su yayi sai da ya numfasa sannan ya ce “Hajiya sai dai hakuri"


Da sauri Hafsa ta mike tana fadin ”Innalillahi wain'na ilaihir rajiun ta mutu ko na shiga uku" ta kwallara kara.


Kamo ta Umma tayi ta zaunar .

Likitan ya ce ”A'a yan mata ba haka nake ba Zazzabi ne take mai zafin gaske da har yasa ta suma sai kuma Ulcer da ya dan kamata bawani matsala amma da ta farka amai zata yi saboda mun mata wata Allura ".


Mami ta ce “Tom Doctor mungode Allah saka da Alkhairi"


Doctor ya na cire glass din idon shi ya ce “Amin Allah bata lafiya"


“Amin Amin mungode" sai a lokacin Umma tayi magana


Sallama su kai mashi su ka fita dakin da aka kwantar da ita su ka shiga.


Da sauri Hafsa ta karasa jikin gadon ta kama hannun Khadeejatu fuskarta tayi fayau kamar wacce ta shekara tana ciwo da sauri tasa hannu ta goge hawayen da ya zubo mata.


**********

Hafsa ce ta fito daga toilet Ya yusuf ta gani su Umma sun tafi gida ya na zaune a gefen Khadeejatu dake ta baccin ta.


Karasowo gurin shi Hafsa tayi ta ce “Ya yusuf sannu da zuwa"


Yusuf ya kalleta yayi murmushi ya ce “Lafiya kalau kanwata ya mai jikin?"

Hafsa ta ce “Da sauki ta zauna a gefen gadon gurin kafafun Khadeejatu"


Yusuf ya ce “Allah kara sauki"

Hafsa ta ce ”Amin Amin".



_Bayan minti goma_


Khadeejatu ta fara motsi da sauri Hafsa ta karasa gurinta ta na mata sannu daga kai Khaddejatu tayi ta na bin Hafsa da kallo.


Taimaka mata tayi ta jingina da filo a hankalin Khadeejatu ta bude baki kenan zatai magana sai ga amai.


Da sauri Hafsa ta kamata har saida ta gama aman wani koren amai tayi da sauri Hafsa taje kiran doctorn dan ya Yusuf ya fita karbo masu abinci karta farka ba abun da zata ci .


Doctorn ne yazo ya ga Khadeejatun ya yi examining dinta ya fita wata nurse ce ta taimakawa Hafsa suka gyara ta......................✍🏻🖊️









*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* ...............✍🏻✍🏻




_Sanarwa_

Sabon littafi na da zan fara nan gaba zai zama na kudi sunanshi *KUNCIN RAYUWA*




Taku ce har kullum
Addeejerh


09012671608

✨✨✨✨✨✨✨

*KHADEEJATU*

✨✨✨✨✨✨✨



*LABARI/RUBUTAWA*



*KHADIJA ADAM* *IDRIS*
( _Shalelen kainuwa_ )


*MARUBUCIYAR*



👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA👩‍❤️‍👨*

*AND* *NOW*

✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨


*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

ALHAMDULILLAH!!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na KHADEEJATU Allah ka sa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai .




Sadaukarwa

Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana

Amin.




19~20

Rufe idanuwanta Khadeejatu tayi ta koma ta kwanta tana ta sakin ajiyar zuciya.



Kiiiiii Ya yusuf ya turo kofar ya shigo hannunsa rike da ledoji yayi sallama Hafsa ce ta amsa.


Shiko tunda ya shigo idonsa na kan Khadeejatu.



Karasawa gurin gadon yayi ya zauna akan kujerar dake gefe yana kallon Khadeejatu ya ce “Hafsa " ta ce “Na'am" ya ce ”Zo ki karba ki ajiye har yanzu bata farka ba ne?" ya kalli Hafsa.


Hafsa bayan ta ajiye kayan ta ce “A'a ta tashi, har aman ma tayi wani irin kore dashi"



Khadeejatu ta da take saurararsu ta dallawa Hafsa harara.


Hafsa ma galla mata hararar tayi ta ce ”Uwar masifa baki ma da lafiya sai kinyi masifa"


“Kaiii ya ishe ni ko ina sai kun nuna halin ku ke Hafsa kamar bakye akace kina ta kuka ba” Yusuf ne yake maganar turo baki Hafsan tayi taje chan kan couch ta zauna murmushi kawai Yusuf yayi ya maida duban shi gurin khadeejatu ita ma ta juyar da kanta tana kallon bango.


Dariya ya kyalkyale da danshi dariya suke bashi cikin dariya ya ce “Sweetheart ba ma magana?"


Khadeejatu ta ce ”Uhumm" yayi murmushi ya ce “Shikenan bari na tashi na tafi tunda ba'a son gani na".


Da sauri khadeejatu ta juyo ta na kallonshi fuskarta dauke da murmushi ta ce “Ya Yusuf ina wuni "


Wani irin niimtaccen kallo yayi mata mai nuna shaukin so a tsakanin masoya ya ce “Lafiya kalau ya jikin?"


A hankali khadeejatu ta bude dan mitsitsin bakinta mai matukar kyau a hankali ta ce “Da sauki".


Yusuf ya shafa sumar kanshi ya ce “Masha Allah haka akeso tashi ki ci abinci"


Kallon Hafsa yayi dake chatting ya ce “Hafsa zoki hada mata tea ga kayan tea nan na kawo ga chips nan sai ku ci akwai fried rice ma".


Cikin nutsuwa Hafsaa ta ce “Toh Yaya Yusuf ( wannan tarbiyar su Mami ne sam basa raina na gaba dasu) ta na tashi.


Tea mai kauri ta hadawa Khadeejatu ta mika mata ta zuba chips din ta hau kan gadon su ka fara ci ita ta na ci ta na chatting.


Yusuf ne ya dallawa Hafsa harara ita ba ma tasan ya na yi ba cikin tsawa ya ce ”Hafsa miko mun wayar nan ku dai baku son cin abincin sai afkin chatting".


Hafsa ce ta fara fadin “Yaya dan Allah na dena......"cikin fada Yusuf ya ce “Baza ki bani bane kinsan dai bana son musu ko"


Badan taso ba ta mikawa khadeejatu wayar ta mika mashi.

*************

*Washegari*


“Hmmm ai Suwaiba yadda kika ji na fada maki hakan ne ya faru "cewar Mama


Umma ta gyara Zama ta ce “Yaya Sadiya baki tunanin ko juyar masa da kaii taje akayi ba".


Mama ta ce “Naka nima yanzu nake zato shiyasa ma nace zan maki maganar da har gida ma zanso sai kuma aka kwantar da khadeejatu".


Umma ta ce ”Yaya Sadiya karki damu zanwa Abban Khadeejatu magana a kai duk yadda akayi zan kira ki in sanar maki ko ma nazo har gida"


Mama ta ce “Tom Nagode sosai bari mu koma ciki Maryam ta taho mu tafi gida"


______________

“Wai ina ruwanka dani ne Nura sai kaji inda zanje ajiye ni kayi ko kaii ubanane da har sai kaji ina zanje ".


Nura ne ya ce ”Allah baki hakuri "duk yayi kashin wuya yayi baki duk ya rame idanuwansa duk sun fito.

Ko kara kallon inda yake ba ta yi ba ta fice.


************


Zainab na tafe a hanya tana jin kida wayarta ta fara ruri ta na dubawa ta ga an sa Alhaji Bala.


Dagawa tayi ta kara kunnenta cikin kashe murya ta ce ”My Alhaji gani nan fa a hanya na kusa zuwa hotel din".


Tana karasawa hotel din tayi parking ta shiga direct daki da ya fada mata ta nufa tana murda handle din ya bude.


Wani dattijo ne a zaune akan couch ya na latsa wayarshi.


Tana karasawa gurinshi ta dena kan cinyar shi ta na sakala hannu ta a wuyan shi.......................✍🏻🖊️










*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* ................✍🏻✍🏻










Taku ce har kullum
Addeejerh

09012671608



✨✨✨✨✨✨✨

*KHADEEJATU*

✨✨✨✨✨✨✨



*LABARI/RUBUTAWA*



*KHADIJA* *ADAM* *IDRIS*
( _Shalelen kainuwa_ )


*MARUBUCIYAR*



👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨

*AND NOW*

✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨


*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

ALHAMDULILLAH!!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah ka sa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai .




Sadaukarwa

Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana

Amin.


*JUMA'AT MUBARAK* 🕋 *MUSULIMS* _Allah_ _sada mu da Alkhairan_ _da ke cikin wannan rana_ _mai albarka_ , *Amin* .



21~22


*Bayan kwana biyu*

Alhamdulillah Khadeejatu ta samu sauki sosai an sallamo su soyayyar ita da Ya Yusuf baa cewa komai ko Yaushe su manne da juna a waya ko yazo gida.


”Dan Allah Zainab ki taimaka ki bani hakki na ina cutawa kinji dan Allah" Nura ne yake rokar Zainab.


“Dallah chan malam ni ka takura mun naki na baka an fada ma ni inji ce ".


Nura bai kara ce mata komai ba ya fice yana tafe kamar zai fadi kitchen ya nufa ya dauko lemon tsami a fridge wajen guda uku ya matse a cikin cup ya shanye dakin shi ya nufa.


Ya na shiga ya kwanta a kan gado ruf da ciki zirrrr sai ga hawaye ya na zubowa ta idonshi.


*Bayan sati hudu*

“Mama Yanzu gidan Ya Nuran zaki je?" cewar Maryam.

Mama ta na zira Hijab ta ce ”Ehh mana gwara naje na kai mashi wannan rubutun tunda jiya Suwaiba ta aiko su Khadeejatu gwara a kai dan malamin yace sai yayi wata daya da sati uku ya na sha".

Maryam ta ce “Hakane Allah yasa a dace ".

Mama ta ce “Amin Amin" ta dau galan din rubutun ta fita.

Sanda Mama ta isa gidan ta tarar Zainab bata nan sai Nuran shi kadai sai birgima yake.

Ungurnu ta jika ta bashi nan yadan ji dama dama .

Mama takalleshi a hankali ta ce ”Nura ".

Amsa mata yayi ya ce “Na'am Mama".

Nuna mashi galan din rubutu tayi ta ce “Ka ga wannan inaso safe da dare kasha kofi daya ina so ka fara a daren yau karka kuskura ka bari matarka ta sani kasan inda zaka ajiye".

Cikin ladabi ya ce “Tom Mama zanyi yadda kika ce nagode".

Mama ta ce “Yanzu ina matar taka take?"

Nura na shafa kanshi ya ce “Tun jiya bata nan"

Bude baki Mama tayi Amma bata ce komai kawai ta ce “Allah ya kyauta ni kaga zan wuce gida na baro Maryam" ta mike tsaye.

Shima Nura mikewa yayi ya ce “Mama bari na sauke ki a gida"

Da sauri Mama ta ce “A'a kayi zamanka kai da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login