Showing 33001 words to 34067 words out of 34067 words

Chapter 12 - KHADEEJATU COMPLETE

na shiga ya tarar da Khadeejatu ta hada kaii da gwuiwa su Hassan na yan wasannin su ba ruwansu.


Zama yayi a gefenta cikin sanyi Murya ya ce ”Khadeejatu ta dago kanta ta kalleshi duk idanuwanta sun kada”.


Kama hannunta yayi ya na murzawa ya kalleta idon su cikin na juna ya ce “Mene kuma kike kuka Nana Khadeeja haka Allah ya tsara mana bamu da tsimi bamu da dabara hausawa dama sunce _duk abinda ka_ _shuka...shi_ _zaka girba_ dan haka karki damu abinda tayi shi yake bibiyarta.


Khadeejatu tana hawaye ta daga mashi kaiiii...........



Bayan Dr Nura ya gama sanar da Mama duk abubuwan da su ka faru.


Sai da ta jijjiga kanta irin nasu na manya bayan dogon nazarin da tayi ta ce “Hmm biri yayi kama da mutum amma duk abinda tayi dan kanta sai dai muce Allah ya kyauta dan ni ta dauren jijiyoyin jikina na rasa mai zance.


Nura ya ce “Wallahi nima haka Mama duk abun ya dauren kai sai dai muce Allah kare mu da karewarshi”.


Mama ta amsa da Amin ta gyara zama ta ce ”Toh ya diyartawa? da fitinannun yaran nan”.


Nura yayi murmushi ya ce ”Su nan lafiya ita kam Khadeeja tun da abun nan ya faru ta daga hankalinta”.


Mama ta kalleshi ta ce “Toh ita Khadeeja me na damuwa ita fa ta jawa kanta ”.

*BAYAN* *SHEKARA GOMA*


Wata yar karamar yarinya ce a wani katon compound mai cike da shuke shuke da flowers tana gudu sai kuka take a kalla zatai shekara hudu a duniya.


Wani haddadden falo ta shigo tana kwala kiran Daddy!!! Dadddy!!!


Wani matashin mutum ne ya ke saukowa daga staircase .


Wannan yarinyar dake kuka da gudu ta nufeshi ta rungume shi tana kuka.


Tsugunawa yayi ya dauketa ya na cilla ta sama ya ce ”Mai ya faru da Suhaiman Daddy ne? naji ta na kuka tana kiran Daddy wane ya taba mun Baby na?”.


Suhaima ta chuno baki ta ce ”Ba su Yaya Hassan bane yace wai bazan yi ball dasu ba inje wai muyi wasa dasu Yaya Basma da Yaya Noor kuma ni ball din nake son yi” ta karasa maganar ta na marairaice fuska.


Nura shima ya marairaice fuska ya na tabe baki ya ce ”Kassh amma su Yaya Hassan ba su kyauta ba amma muje gurinsu dole Baby na tayi Ball”.


Ni kam Shalele sai da na karewa wannan mutumin kallo sai naga wai ashe Dr Nura ne lolx, naga yayi wani bulbul dashi ya na kyalli lolx😂.


Wata matashiyar matace ta ke saukowa ita ma daga stairs din tasha bubun na wata dakarkiyar shadda kalar Blue tasha paint work kalar pink and blue tayi dauri ta na Zahrah buhari sai tashin kamshi take irin matan manya nan haka ta ringa saukowa kamar ta na tausayin kasa.



Jin karar takalmin matar nan yasa Nura juyawa ya na wani irin murmushi mai tsuma zuciyar wanda ake yiwa ya ce “Wow My Nana Khadeeja kinga yada kika yi kyau”


Khadeejatu ta jujjuya kwayoyin idanuwanta tace “Da gaske Yaya?”.


Nura ya ce ”Sosai ma Suhaima ta kalli Kgadeejatu ta tabe baki ta ce ”Yen yen batai chauba nidai”.

Khadeejatu ta dungurewa Suhaima din kaiii ta ce ”Naji aji banyi kyau din ba chocolate din ne dai komai abunki bazan baki ba duk wanda kikasha bai ishe ki ba”.


Suhaima ta boye kanta a kirjin Nura shi kam Nura ya kyalkyale da dariya.


Kama hannu Khadeejatu yayi su ka fice compound din inda yaran su ke ball din dole Suhaima dan rigimarta sai da ta shiga ball din nasu su ma su Basma da Noor su ka shiga bayan sun gama assigntment dinsu aka buga ball din dasu abun nasu gwanin sha'awa.


Garden su Khadeejatu su ka je ta zauna akan grasscarpet din Nura ya dora kanshi a kan cinyarta ya kwanta ta na shafa gashin kanshi su na hirar su irin ta masoya cike da tsantsar so .



Khadeejatu da Nura yaransu bakwai bayan *Hassan* da *Hussaini* sai ta haifi namiji *Rais* bayan shi sai ta haifi mace da namiji *Suhailat* da *Suhail* daga su again kuma sai ta sake Haifar twins duka mata *Basma* da *Noor* sai kuma ta haifi auta *Suhaima*.


Hafsa ma yaranta biyar suna zaune lafiya da mijinta Shamsu .


Sai Maryam ita ma tayi aurenta da mijinta Abdulmajid su na zaune lafiya cike da soyayyar juna sun samu karuwar yara shida inda ita ma sai da ta haifi twins har sau biyu.

*SAFFIYA*

Safiyya ta samu wani dan dattijo tsohon dan siyasa matan shi uku inda ita ta shiga a ta hudu ta hadu da jarababbun kishiyoyi ta je gurin boka kenan akan kishiyoyi a hanyarta na dawowa ne ta gamu da hatsarin mota inda a take ta mutu dan kwakwalwarta ta ma sai da ta fito kayan cikinta su ka fito waiyazubillah.



A wannan Shekarun Khadeejatu Dr ya samo mata admission a jami'ar *Bayero University Kano* inda ta karanci bangaren Medicine har ta kammala inda ta fito da first class.


Nan Dr ya gina masu wani tanfatsetsen asibiti shi da ita inda a ka sawa asibitin suna *KHADNUR* *SPECIALIST* *HOSPITAL*.................



*TAMMAT BI* *HAMDULILLAH!!!!!!!!!*
_Komai yayi farko zaiyi karshe._



*ALHAMDULILLAH!!! ALHAMDULILLAH!!!ALHAMDULILLAH!!!*

_Allah nagode ma da ka bani ikon kammala wannan littafin nawa da ya samu karbuwa gurin masoya hakika naji dadin haka._


_Anan na kawo karshen wannan littafin nawa mai_ _suna_ *KHADEEJATU* _kuskuren da nayi Allah ya yafe mun , fadakarwar da nayi Allah bani lada, Allah sa Alumma su amfana.
_


_GODIYA_

Maman Yusrah
Mom ihsannnn
Am his
Khadeey fashion
KhadNur
Mom Mus'ab&Zarah
Mom Haneef
Ummu Rufaida
Eyshart
Mommny Ithmad
Ummu Shaddad
Ya Hamida
Meerah
Nanwara
Haleeemat Muhammad
~B.B
Zainab Sa'id
Deejert
Princess
Ummu Huzaifa
Mommny Nanah
Khadeeja Sulaiman Garba
Khadeejart
Mum Huzaifa (Ummin Kurfi)
Fatymah Kusa
RuqAyyah
~R~B~J
Khadijatijjaniibrahim6@g
Maryam Na'ala
Zabs 4 real
Ummu Muhammad
Maman Siyama
Mummcyn Khadeey
Mmn Heedayah
Omar Hafsy
Mmn Abdussamad
Firdausi sani
Anty Maryam
Ummu Manal
Batool Jarmah
Mmn Adnan/Yusrah
Mom Sultanah
Zynab Abubakar
Aisha Khalil.



_Gaskiya bansan da bakin da zan gode maku ba_ _masoya_ *KHADEEJATU* _bisa namijin kokarin da kuka yi wajen bani hadin kai , kana kuma da kwarin gwuiwa wato_ _wajen yi sharhi(comments)hakika ina matukar godiya sosai Allah bar kauna son so_ _fisabilillah_ ❤️💃



_JINJINA A GAREKU_

Mom Islam
Maryam Dangi
Mum fuad
Ummu Dahirah
Maman Noor
Aunty Fauzah yar Amana
Aunty Haupha.


*Ban manta daku ba kuma daukacin 11stars🌟💫✨❤️💃son so fisabilillah.*


_Jinjina ta musssam a gareku_

Mom Islam
Maryam dangi

_Bazan taba mantawa da namijin kokarin da kuka yimun har na kammala littafin nan nawa._


_Sai mun hadu a littafina_ _na gaba wato_ *KUNCIN* *RAYUWA* _True life story_(Paid book)



*Ta ku ce har kullum*
~_Addeejerh_~ 😍


*BISSALAM* 👏🏻👏🏻👏🏻

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login