Showing 24001 words to 27000 words out of 34067 words

Chapter 9 - KHADEEJATU COMPLETE

cire hular kanshi ya ajiye akan kujera


Ya kalli Khadeejatu ya ce “Kinga wallahi na manta ban fada maki ba akwai inverter zo ki ga yadda ake kunnawa” yayi gaba ta bishi a baya.



Bayan ya kunna inverter din ya kalli khadeejatu ya ce “Bari in shiga ciki in dan watsa ruwa wannan ledar fruit ne a ciki ki yayyanka”.


Khadeejatu ta amsa da “Toh a fito lafiya” ya ce “Allah yasa” ya nufi daki ita kuma ta dauki ledar ta tafi kitchen ta wanke kayan fruits din ta yayyanka su a wani bowl mai dan karan kyau wanda kodan kyanshi zaka so kaci abunda ke ciki................



_________

*Bayan kwana uku*


Yau da wuri Dr ya fita asibiti bayan ya fita ne Khadeejatu ta fara gyara gidan dakinshi ta shiga domin gyarawa duk da wani baci yayi ba ta kara dan gyara gadon ta share tayi mopping.


Ta shiga toilet din nashi nan ta tarar da ya jika underwears dinshi a bokiti ta wanke su tas bayan gama ta shanya su a abun shanyan da ke toilet din ta wanke toilet din fes ta feshe shi da freshner.


Turaren wuta ta sanya a d'akin nasa ta fito ta nan ma ta sanyawa parlorn turaren shi , ko ina sai tashin k'amshi ya ke yi , wanka ta shiga tana fitowa ta nufi dressing mirror ta shafa mai da su kwalacca tuni kamshi turarrurukan ya gauraye dakin bayan ta gama shafe-shafenta ta sanya wata burmemiyar abaya kalar blue-black ta dan shafa powder sai dan whit lips da ta sawa pink leben ta ta zizara kwalli a idonta ta nade kanta da dankwalin rigar fes ta fito parlor ta fita ta kunna television ."



Tashar MBC action ta kai jita yi bata san yin kallon sai ta dauko wayar ta , number Ummanta ta kira har tayi ringing ta gama ba daga ba sai ta sake kira kamar farko ba a daga ba a ranta tace ko bata kusa ne nan sai tayi dialing number Mamin Hafsa taci sa'a ita Mamin ta daga nan suka gaisa nan Mami ta ke tambayar duk suna lafiya inda Khadeejatu tace lafiyar su kalau nan suka danyi hira nan Mami ta da da yi mata nasiha akan tayi hak'uri da zaman aure daga nan su ka yi sallama , su na gama wayar da Mami sai ga Umma na kira Khadeejatu bata daga har sai da ta gama ringing sannan ita ta kira Umman daman taki dagawa ne kar ta cinye mata kati bayan Umma ta daga suka gaisawa ita ma dai Umma fada take mata da nasihan sosai sukai hira da ga bisani sukai sallama.



knocking taji ana yi cikin sanyin jiki ta mik'e ta murd'a handle d'in k'ofar , Maryam ta gani cikin murna suka rungume juna , suna shiga Maryam ta tuntsire da dariya ,Khadejatu ce ta cuno baki ta ce ”To menene abin dariya kuma daga shigowar ki ?" Maryam ta sake tuntsirewa da dariya sannan ta ce ”Naga amarya guda da binjimemiyar riga” Khadeejatu ta kalle ta ta ce to mai kike son nasa?” Maryam ta janyo travelling bag din da ta shigo da ta zuge din english wears ne makil a ciki fara fito da kayan tayi masu bala'in kyau da su Maryam ta daddaga mata wata riga ta daga mai k'aramin hannu tsakiyar kirjin a bude sai skirt shi kuma mai flawoyi tsahon shi iya cinya zaro ido Khadeejatu tayi ta ce “kina nufin wannan kayan zansa a jikina?".



Maryam tace “Eh mana ya kamata ki waye ki kama mijin ki hannu biyu kina shigar daukar hankalin wanda ko wane na namiji lafiyayye ya ganki ki sai ya motsa gaki da kira mai kyau dirarrariyar mace da ke, kinsan fa kananan kaya ba karamin taka muhimmiyar rawa sukeyi ba dariya Khadeejatu tasa ta na kara daga kayan ."



Banko kofar da akai ne su ka maida kallonsu gurin kofar Zainab ce ta shigo falon sai gyatsine gyatsine take cikin masifa Khadeejatu ta kalli Zainab ta ce ”Ya haka zaki banko mun kofa ki shigo mana batare da sallama ba cikin masifa Zainab ta ce ”Dan uwarki bazan yi sallamar sai inga abunda zakiyi ......... tass Khadeejatu ta dauke da mari ta na huci ta nuna Zainab din da yatsa tace wasa iya wasa banda tsikalin uwar miji karki kuskura ki sake sako iyaye na a maganar ki nice abokiyar karawar ki basu ....... Kukan kura Zainab tayi ta cakumo Khadeejatu nan suka fara dambe ita ma Maryam nan ta shiga fadan dama tana kule da Zainab din.




Dambe su ke yi sosai inda Khadeejatu ta fasawa Zainab baki sai da su ka mata likis........................✍🏼✍🏼







*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* ............✍🏼✍🏼






*Ta ku ce har kullum*
_Addeejerh❤️_

✨✨✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨✨✨


*LABARI/RUBUTAWA*


*KHADIJA ADAM IDRIS*
( _Shalelen kainuwa_ )


*MARUBUCIYAR*


👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨


*AND NOW*


✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨

*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*__________________________________*


ALHAMDULILLAH!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah kasa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai.


Sadaukarwa

Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana.

Amin


_ALKALAMIN DA_ _BAYA RUBUTA_ _SHIRME🤟👌_


Juma'at mubarak🕋🕌Muslim Ummah Allah bamu Albarkacin wannan ranar mai falala Amin.


Wannan page din na kune commenters kuyi yadda kukeso dashi😘😘☺️son so fisabilillahi💃❤️.

45~46



Zainab ce zaune ta na waya tana fadin ”Ai wallahi tally bata daki banza ba sai na rama ko ba dade ko ba jima har ni zata fasawa baki fuskata duk ta kumbura shima dan iska wai ni duk ya dorawa laifin”, niko shalele nace kurin gida amanar Inna lolx😁


*Bayan wasu yan* *kwanaki*


Bayan Dr Nura ya gama kwanakin shi a bangaren Zainab a daddafe yau zai dawo gurin Khadeejatu.

*Da daddare*

Khadeejatu ce a gaban mudubi bayan ta fito daga wanka hannunta rike da karamin towel ta na goge gashinta da ta wanke.


Tasa dryer ta busar da gashin nata ta shafa mashi mai ta yi parking nashi da red ribbom.

Da sauri sauri ta shafawa jikinta turaruka da su humrori masu balai'n kamshi.


Wardrobe dinta ta bude wajen english wears dinta ta fara dubawa duk ta rasa wacce zatasa dan ita kunya ma takeji dan duk kayan da Maryam ta kawo mata bana arziki duk ta ma rasa wanne zata sa.


Nan ta dauko wata red gown mara hannu an mata tsaga tun daga cinya har kasa.


Nan Khadeejatu ta dafe goshinta tana fadin “Kashhh ita ma dai irin haka take amma gwara ita dai”.


Ta sa rigar ta kalli kanta a jikin mudubi duk ta kama ta hips dinta bam kirjinta kamar zai fasa rigar ya fito.


Ta kara kallon kanta a fili ta ce “Anya kuwa zan iya fita da rigar nan ko nan da falo ne”.


Zani ta daura akan rigar tasa hijab ta shimfida sallaya ta tada sallar isha .



Ta na idarwa taji ana knocking ba makawa ta san Dr ne .


Ba tare da ta cire hijab din ba taje ta bude kofar da sallama ya shigo ta mashi sannu da zuwa ya amsa ya na tambayarta ya gida.


Ta karbi briefcasse din shi, kan kujera ya fada ya na lumshe idanunsa.


Khadeejatu ba tace mashi komai ta kai briefcase din dakin shi ta ajiye ta dawo still ya na nan yadda ta barshi.


A hankali cikin nutsuwa ta ce “YaYa", ya bude idanuwanshi da su ka kada ya ce “Na'am ya akai?”.


Khadeejatu tana wasa da hannunta ta ce “Dama nace abinci nan zan kawo ma ko zakaje kan dinning din?”.


Mikewa Dr Nura yayi ya na shafa kanshi ya ce “Bari in fara watsa ruwa dan duk a gajiye nake yau din kaina har ciwo ya ke”.


Cikin tausayawa da nuna kulawa ta ce “Ayyah sannu Allah baka lafiya, bari inje in hada ma ruwan wankan”.


Ta nufi hanyar dakinshi ya bita a baya suna shiga ya zauna a gefen gado .


Tsugunawa Khadeejatu tayi cikin nutsuwa ta fara cire mashi safar kafarshi a ranshi ya na jin wata kaunar yarinyar tabbas mahaifiyar shi batai masa zaben tumin dare ba ta katse mashi tunanin da yake ta hanyanr cire mai riga ta barshi da iya singlet sai dogon wando da ke jikin shi.


Sai ta shiga toilet nan ta fara hada ruwan ta na cikin hada ruwan taji shigowar shi da sauri ta dago daga shi sai boxer tai maza ta dauke kanta .


Ta dan kalleshi ta ce “Na gama hada ruwan ya ce “To ai sai ki karasa ladanki ki mun wankan” ya karasa maganar ya na dariya.


Da sauri khadeejatu ta zazzaro ido ta ce “tabbb bazan iya ba” ta karasa zance ta na fita a guje.


Dariya ya kyalkyale da irin wacce shi kanshi bai zata ya iya ba ya na wankan ya na murmushi.


Bayan ya fito daga wankan ya dan shafa mai ya sa gajeren wando three quater falo ya fita inda ya tarar da ita tana kallo .


Nan su ka ci abinci bayan sun danyi kallo su ka kwanta inda suka luluka duniyar ma'aurata.


________


Nura ne ya sauke Khadeejatu a gidansu za taje ta wa su Maryam wuni shi kuma ya wuce aiki sun sha hira.



Da daddare Dr ya zo daukar ta nan ya tarar da Mama da Maryam a falo su na ta hirarsu irin ta ya da uwa nan shima su ka hadu su na ta hirarsu abun sha'awa.



Nan Dr dai yaga shiru ba khadeejatu ba alamun ta ya kalli Maryam ya ce “Ina Khadeejan ne ta fito mu tafi dare yayi”.



Mama ta kalleshi ta ce “Bacci ta ke ne sai dai a taso ta dan tun wajen uku take bacci sai dai ta tashi tai sallah nace nikam baccin nan kona lafiya ne”(Mama na fatan Allah sa zaton da take ya zama gaske)


Nura ya ce “To ikon Allah kuma bata bacci irin haka bari in taso ta mu tafi ”


Mama ta ce “Da dai yafi dan dare yayi” sai da yaci abinci sanan sukai wa su Mama sallama su ka tafi.


Su na hawa kan titi Khadeejatu ta ce “Dan Allah Yaya ina son shan farar kasa”


Cike da mamaki ya ce “Farar kasa kuma mai zaki da ita?”.


Cikin murna Khadejatu ta ce ”Sha zanyi mana”.


Nura ya ce “What!! kasar zaki sha nidai bazan siya ba ina ma zan samu gurin da ake siyarwa”.



Cikin fushi da kunkuni Khadeejatu ta ce “To nidai shi nake so in ba zaka siya ba shikenan”.


Ya yi dariya ya ce “Mai da wukar matata mafadaciya, yanzu ina zan samu ?”.


Khadeejatu ta ce ”A hanya mana”, aiko a wani shagon iyamura su ka siya .



Su na tafe a hanya sai da tasha wajen kwallo hudu a haka ma Dr ne ya hana ta sha...........................









*Kuyi hakuri pls fans banjjn dadi ne gashi week din duk am busy* *amma duk da ba na posting weekend zan maku muyi covering* 😘😘 *son so fisabilillahi* 💋💋.






*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* ...........✍🏻






*Ta ku ce har kullum*
_Addeejerh😘_ .


✨✨✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨✨✨


*LABARI/RUBUTAWA*


*KHADIJA ADAM IDRIS*
( _Shalelen kainuwa_ )


*MARUBUCIYAR*


👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨


*AND NOW*


✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨

*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*__________________________________*


ALHAMDULILLAH!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah kasa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai.


Sadaukarwa

Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana.

Amin


_ALKALAMIN DA_ _BAYA RUBUTA_ _SHIRME🤟👌_



47~48

*Bayan wata uku*

Khadeejatu ce zaune kasan capet cikinta sai qara yake saboda wata yunwa da take jinta,dan rabon da ta sa wani abu a cikinta tun safe gashi yanzu kusan karfe uku har da kusan rabi,shima ba wani abu taci ba yought ne wanda a yanzu shine ya zame nata abinci bata iya cin komai sai shi dan duk abinda ta ci sai tayi amansa.


Kara duba fridge dinta ta yi wai cike da mamaki tace da gaske yanzu youghurt din ya qare na shanye shi?ita kadai tai murmushi,ka
na ta sa hannu ta shafa dan qaramin cikinta wanda a iya yanzu ita kanta ya shiga ranta,jin cikin ya cigaba da kara ne ya sa ta mikewa domin zuwa wajen Zainab dan tasan ita ba zata rasa ba,wane tunanin tayi sai kuma ta girgiza kai ta ce “kai gwara kawai na kira Yaya tunda ya kusa dawo wa gida ya tawo min da shi ”nan ta mike ta nufi dakinta dan wayar na chan.


A daidai wannan lokacin ne Zainab ta shigo side din khadeejatu ta tarar bata falon direct sai tayi hanyar dakunanta ta tazo dab da dakin khadeejatu din ta ji khadeejatun ta na waya jin wayar da ta ke yi ne yasa Zainab saurin kama kugu a zuciyarta ta ke cewa shegiya mai kinibibin tsiya cikin da ko wata biyar cikakke bai ba har kin fara wani tsurfa ta munafurci ta na gama zancen zucin da take ta ma bar side din ta koma nata .


Zainab na komawa side din tayi maza ta nufi kitchen dinta ta bude fridge ta dauko yoghurt dama tasan wanda ake siyowa Khadeejatun dan tare ya ke siyo masu.


Da gudu ta je dakinta ta dauko wani kullin wani farin gari wanda dama ya dade a gurinta dan tayi wa kanta alkawarin in har tana raye sai ta barar da cikin Khadeejatu a huta da kinibibin da take bude robar yoghurt din tayi ta zuba maganin ta ringa jijjigawa kana ta mayar da murfin ta rufe ta goge ko ina ba zaka taba cewa an bude shiba.


Ba ayi minti 30 ba da kiran Dr da Khadeejatu ba sai gashi a na knocking jin ana Knocking da sauri Zainab ta daga labulen falon ta da za a iya gano gate din.


Nura ta gani ya shigo hannunsa sa rike da robar yoghurt daya a hannun shi dayan hannun kuma wata leda ce bata tantance mai ne a cikin ledar amma ga alamun jarkoki ta ga ya shige side din khadeejatu ba'ayi minti uku ba sai gashi ta ga ya fice.


Ai da sauri ta fito tasha hijabi tasa robar yoghurt din a cikin hijabin cikin sanda ta shiga bangaren Khadeejatu Allah ya taimake ta kofar a bude ta ke ta shiga falon ba kowa sai yoghurt da ledar da Dr ya shigo dashi.


a sauri ta chanja yoghurt din da baya cikin ledar sai ta dauke shi ta ajiye wanda tazo dashi.


Ta na ajiyewa cikin sauri ta fice daga falon da sauri sauri ta shige part din ta tana sauke ajiyar zuciya sai kuma ta sheke da wata shegiyar dariya a fili ta ce “Zaki ci ubanki ne”.


Khadeejatu bayan ta fito daga wankan da tayi dan tunda ta samu cikin nan a rana sai tayi wanka sau wajen shida ta shirya ta fito falon nan ta tarar da yoghurt din da Dr ya shigo dashi ita tana wanka ba ma tasan ya shigo ba.


Ai Khadeejatu ganin yoghurt din nan yawunta ya tsinke da sauri ta dauki yoghurt din da ke ajiye daban ko neman kofi bata yi ba ta bude yoghurt din ta fara kwankwada bata ajiye robar ba sai da ta ga babu komai .


Mikewa tsaye tayi zata koma daki kenan kawai taji kanta ya fara juyawa da sauri ta dafe bango ta rike kanta nan taji mararta ta kulle ta karfi ta kwallara kara.



Zamewa tayi a kasa kan tiles ai nan take jini ya balle mata .


Nura da ya shigo domin daukar kayan gyaran mota ya ga Khadeejatu kwance cikin jini .


A rikice ya karasa gurinta ya na fadin “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun!!” nan ya ringa jijjiga ta ya na cewa Khadeejatu mai ya faru nan ta bude baki zatai magana amma ta kasa suuuu sai ta sume, sunkumarta Dr yayi da sauri ya fita bakin gate mai gadi na tambayarshi lafiya amma ko saurarar shi beyi ba ya fita dama a waje yayi parking.


A sit din baya ya sata da hanzari ya koma mazaunin direba inda ya fafari motar kamar zai tashi sama.


A minti sha biyar Dr ya karasa asibitin da yake aiki nan ya sake sunkumarta ya yi cikin asibitin nan Nurses su ka karbeta nan likitoci su ka dukufa a kanta inda yaso ya shiga doctors din abokanan aikin shi su ka ce a'a dan baya cikin nutsuwar shi .



Nan yayi ta zagaye nan ya tuno bari ya kira Mama ya sanar da ita nan ya duba ya ga ya baro wayar tashi a gida lokacin da ya ga halin da Khadeejatu ta ke ya ajiye wayar .


Nan ya karbi wayar wata Nurse ya kira Maman ya sanar da ita.


Dr Nura na tsaye sai ga Dr Kalid ya fito ya na goge gumi da handkachirf din shi da sauri Dr Nura ya tare shi ya na fadin “Ya aka yi? cikin ya zube ko ?nan yayi ta jero mashi tambayoyi.


Nan Dr Khalid ya kama shi ya zaunar dashi a kujerun dake gurin cikin kwantar da hankali Dr Khalid ya ce “Calm down Dr Alhamdulillah cikin bai zube ba amma a gaskiya ta zubar da jini sosai ana bukatar a kara mata jinin”.


Dr Nura ya ce ”To aje a gwada nawan in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login