Showing 30001 words to 31895 words out of 31895 words
mike yana nufan toilet hadi da watsa ruwa koyaji sanyi a zuciyar sa. Tsawon dare ya raba yana sallan nafila don dama wannan sababbiyar sace.
******
Rungume Ummien nata Diyana tayi tana kissing din kumcinta hadi da cewa"Ummi na na tafi sai na dawo! Daga mata hannu Ummi tayi tana rufe mata murfin moton da ta shiga hadi da mata a sauka lafiya...A haka suka rabu da Ummie Diyana tana daukar hanyar zuwa
garin Bauchi... Wanda anan kam gida Bauchi Tuni Momyn Abbas ta shirya komai don taryar diyan nata ,ko nace yar kawarta aminiya da zata taho mata daga mai duguri wato Diyana .
Sanye yake cikin shigarsa ta suit wanda yayi matukar amsan jikin sa ,rungume m
omyn tashi yayi ta baya yana murmushi hadi da dora kansa bisa kafadan ta .
Juyowa tayi tana murmushi hadi da fadin Aa Abbas har ka shirya badai tafiyan ba...Gashi Diyana tana hanya ta kusa karakowa ,kuma naga yau fa
tarewan matar Anwar ,a gani na da k
a tsaya ka hakura xuwa gobe sai kaje ganin Yar fulanin .
Kallon Momyn nashi yayi kamin yayi dan murmushin saman la66a yana cewa "Aa Momy inaso naje yau din ,kinga diyana a gidanan zata sauka komun dare na dawo xan ganta haka Anwar kinga gasu Sadeeq can
suna tare da sauran Abokai ,kuma fah Momy yace ba rugar dashi zaije idan an kawo matar maje mu ganta dashi duka ,kinga har naje na dawo sannan...
Saima na sauka garin Zaria kinga dama can zaa kai Amaryan tasa.
Nisawa Momyn tashi tayi kamin tace tom a
llah tsare kaji kayi driving da lura banason wannan gudun da kukeyi bakaiba ba Abokannaka ba .
Dariya yayi yana dan sosa kyeya kana yace tom Momy yana ficewa daga kitchen din da Momy kemawa Diyana diffrent dishes na saukan ta .
Tana aikin ne wata ma
'aikaciyarta ta zo ta amsheta nan tayo waje hadi da zama a falon nata ,a hankali ta daga wayar ta tana karawa saman kunnen ta daalama kira takeyi.
Assalmu alaikum uwar ango lallai komai lokacine gashi tamu tazo ayirriiii....abunda Momyn Abbs tace kenan
kamin taji amsa daga dayan bangaren .
Nisawa Hajiya Haula tayi tana sakim murmushin bakin ciki kamin tace " aa ni ai har yanxu momyn Abbas ina a smatsayina na uwan Anwar ban ajiye suruka ba har yanxu kam don ban ga taba .
Nisawa momyn Abbas tayi kamin
tace Hjy Haula hakuri zamuyi ,wlh matan wani bata auren mijin da bana ta ba ,bakisan zazzafan rabon dake a wannan auren nasu ba , Muyi hakuri mudai namu kawai muyi masu addu'ar zama lfy...
Nisawa Hjy Haula tayi kaman wata ta fadaku tana cewa" shikenan H
ajiya yaushe zaki shigo ne??
Inshaallh zuwa la'asar ina nan shigowa naji ance bakiyi taro ba ,kuma Zanyi bakuwa sai karfe 4pm zan shigo inshaallh.
Tom allah y kaimu lfy..
A haka sukayi sallama kamin Hjy Haula ta aika wata maaikaciyarta ta sanar m
a security tahowan Momyn Abbas su barta ta shigo ,don kowa a dangin Alh jalingo yazo sawa take a koresu ta hanyar cewa ta hana kowa ya shigo baxatayi taro ba .
Hakan yasa Duk dangi aka nufi Gidan Grndma wato hjy Yalwa mahaifiyar Alh jalingo da ita kam y
ar tsohuwa farin ciki a wurin ta bai misaltuwa a yau da ranta wai zataga Auren Jikan nata mafi soyuwa a ranta . Hakan yasa gidan Hjy Yalwa y cika da dangi da yan uwa har da bare ma...domun ko biki ne akeyi kaman a yau aka daura auren Anwar da Shatu....Duk
girman harabar gidannan babu masaka tsinke yayan Hjy Yalwa na kasashe da garuruwa duk sun hallara .
Don dole Anwar ya taho Bauchi badon yaso ba don damun hjy Yalwa da iyayen nahi da suka taho....su Sadeeq kam baki yaki rufuwa yau suke ango...Sam Anwar y
aki yarda yaje rugar Surbajo acewan shi shufa batason karnin nono ne ,hakan yasa manyan shakikan Abokan sa tafiya dan dauko Amarya Shatu ,haka wasu daga cikin dangi ciki har da Mama Rahamatu duk sun nufi rugar Surbajo dauko amarya ,wasu kuma sun nufi Gidan
Anwar na na barikin sojoji inda xaaa sauke amaryan...
Tun da Su Hameeda suka isa barikin sojojin da shigar su gidan Anwar sukayi arba da Zabeena dama kam ba shiri ne suke ba ,sosai Hameeda ta tsani Zabeena tun da tana zuwa gidan Hjy Haula badon kowa ba
sai don Anwar da nasu yazo daya ,ita kuma Hameeda yarinyar Hajiya Rukayya ne ,wato kanwar mahaifin Anwar .
Harara suka hau aika mawa juna kamin su saki buda don suk cikar su kusan su bakwai yammata ne ,su suka fara isowa barack din ,suna shewa hadi da
fadin yau leutanant Anwar lokaci yayi yau muke ango cewan Hameeda tana kara kama hamci hadi da rangada buda... Sauran masuka hau shewa maasu budan nayi don sun fahimci Hameeda habaici takeyi .
Sum_sum cike da tukuki Zabeena ta wuce dakin da ta banb
ake ,niko maman teddy nace zan gani ko zata fita takoma gidan uban ta yau ,don amarya dai ta zo gidan mijin ta sai ta bata sararari su gurji amarci ...don na kosa naga yanda zaman tasu zai kaya tsakanin shatu da Anwar .
Ganin ta shige daki yasa hameeda
bin kowani daki tana shiga hadi da fitowa ... Wani kayataccen daki ta gani da yafi kowanne kyau komai nashi golden da milk har funitures din bedroom din haka yake...
Don dama ta amshe keys din dakunan a hannun Anwar tun kamin su taho...ganin kayan sa t
ayi a dakin ,aiko nan ta kwashe su tass tana sakawa a dakin da yace mata na shatun ne ,Kayan shatun kuma tana dawo dasu dakin anwar din .
*******
Bangaren Teemah kuwa tunda lbrn Auren Anwar yazo kunnen ta ta kwanta ciwo ,wanda batayi karfi da jikin t
a ba sai da tajiyo yai ne tarewan sa da matar sa ,da kuma jin ashe yar kauyen bafullatana ya aura ,hakan ya sanyaya zuciyar ta ,tana cewa tabbas yanxu ne xasu fara takun saka tsakanin ta da wannan gajar bafullatanan ,don ta lashi takobin auren Anwar koda d
a boka ne da malam . Tirkashi...!!!
Bangaren kuwa Amarya shatu ,koda su Mama Rahamatu sukaje rugar sam basu hanasu yin al'adar su ba ,komai nata har kwallaiya ta fulanin su sukayi mata cikin blue din saki ,mai ado da jan zare ...sun rufa mata mayafin j
ikin sakin....sosai Shatu tayi kyau na kurewa ,dangi kam su Mama rahamatu komai za ayi tana tare da Amarya a buka ,har aka kammala komai ,iyaye sukayi mata nasiha sosaoi. A wannamn lokacin ne zuciyar umman shatun ya karye sai da ta zubda kwallah sosao sann
an tayi mata nasiha ,hadi da amsan lil Zahra da cewa sai ta kwana biyu a dakin mijin ta zaa'a kawo mata .
Anan ne Shatu ta hau kuka badon komai ba don rabuwa da lil zahra koba komai tasaba da yar nata sosai...duk da dama va ita take shayar da ita ba.
Umman ne mai kulawa da ita dama .
A hakan ne bakiya da masoya kowa na tafo albarkatun bakin sa ,aka shiga da amarya moto wanda tun da take a tarihin rayuwar ta bata ta6a shiga ba ,taso tayi kauyanci amma babu bakin yi don tana cikin damuwa..
A hakq mo
ton su tafara tafiya don barin kauyen....koda akazo wuce rugar su Hardo hawayen ta ne ya karu don sai da ta hango shi ya zabga tagumi da alama shima dana sani yakeyi...
Tana wannan tunanin ne taji an daki moton su da sanda fadi yake munafukai ina zaku ka
imun mata ku fito mun da shatu na...!!!
Allah da ikon sa a cikin moto cin har na angwayen babu wanda ya tsaya ,kuma abunka ga wayayyun mutane koda suka fice daga rugar babu wanda yayi mgnan ko tambyar waye wannan din?.
Itakam Shattu kuka takeyi sosai
Hjy rahamatu tana rarrashin ta ,don duk maganan da hardo yakeyi da fulatancu ta jiyo shi . Cewa yake bazai rabu da shatu ba ko ina taje sai ya biyota...Zai iya komai akan Matar shi shifa bai saki Shatu ba hushin zuciya ce ta debeshi .....
Nikam nace ai
kin gama ai ya riga da yagama yanxu kam shatu ta jarumin sojan mu Anwar ne ko ya kuke ce mosoyan shatu...?
******
Kamin bakwai na dare kowa ya watse yabar gidan Amaryan mu shatu sai Zabeena kadai da ta kulle dakin ta ba asan ma da ita ciki ba.
Tan
a zaune tana tunanin abubuwan da zata dauka akan shatum ne tsawon lokaci har 9pm sai taji motsin shigowar angwaye....
Mikewa tayi tana la6ewa don jin komai na abun da zasuce ,amma sai muryar Anwar taji a miskilance yana fadin ,tom nagode zaku iya tafiya
".
Hhhh kujimun dan rainin hankali ,bamuga amaryar bane kake sa ran tafiyaru ko yaya kai muke jira ka fito mana da amarya mu ganta ! Cewan Ibrahim wanda sauran nan suka amsa da kwarai kuwa ciki harda Sadeeq .
To kujira na fito maku da ita ,ni kunga m
a tafiyata bedroom dina nayi ,yana fadin haka ya nufi hanyar da zai sada shi da bedroom din shi kai tsaye...
Lallai wannan dan rainin hankali ne ma ,kazo ka amsa kazan amarcin cewan Sadeeq yana dariya...banza ya musu yana shigewa ,yyn da Sadeeq din yace
gashinan mun ajiye maka a gaida amarya aji mana da ita sosao plz..dariya duka suka saka kamin su juya suna ficewa daga falon .
Shikam Anwar Ranshi duk wani irin yakejin zuciyar shi ,yarasa meke damun shi ,a hankali yafara tunano da sinfurin kalolun aza
btarwan da yace zaiyi
akan wannan yarinya yana cije la66an sa hadi da lasansu yana girgixa kai...
Babban rigar sa yafara cirewa na danyar gexna milk kamin ya fara cire wristwatch na hannun shi a saman mirrow ,mmki ne ya kamashi dago idon sa da yayi kw
atsam yaga Shatu a saman gadon shi an rufe mata fuska da mayafi da kayan ta na fulani...Bude idon shi yakara yana mutsikasu yana mai fadin No ba itace ba ,kodai tunanin Azaban da zai mata ne yasa shi saboda kosawa yake ganin hazo hazon ta haka ... Cike da
rashin tsoro ya sauke hularsa yana nufar gadon da cewa indai ko itace aka ajiyemun ita a bed sai naaaaaaaaa....................
Topah dama hausawa na cewa laifin dadi karewa gashi a yanxu labarin take yanxu xamu fara...
Anan na kawo karsh
en free page na wannan littafi ,idan kin ga wani page na yawo bayan wannan tom na sata ne kar ki karanta kawai rintse idon ki ki wuce ,kar kuci hakki,babu abu mafi muni da yakai mutum yaci hakkin da banasa ba...
_*Idan kina bukatar karanta cigaban labar
in nan zaki iya mgn ta wannan number 08081202932....ta hanyar turo da kudin ki kaman haka Vip payment 500....Normal payment 200...Special payment 1k ,iya kudin ka iya shagalinka
💃💃
...zaku iya turo da katin MTN ko kuma ku tura ta wannan account din Farida
Hashim Stanbic bank 0028799846....sai ki turo mun da shaidar biyanki ta wannan number 08081202932....yan niger zaku biya 500f ne kacal katin airtel zaku na iya tuntu6an wannan number mutanen niger +22797780373*_
_Share and share and share fisabillah_
*Mmn teddy
🧸
*