Showing 1 words to 3000 words out of 31402 words
[10/16, 8:01 PM]
®```NWA```
_written by_
*_Zee Mmn khady_*
1to2 ```Page```
kuka take kamar zata cire ranta, idanunta sun kad'a sunyi jawur saboda tsananin kuka, fuskarta tayi face-face da hawaye, zaune take
cikin d'akin kan tabarmar kaba, jikinta wata atamface Riga da zani, simple da ganin atamfar kasan tad'an kwana biyu saboda farin data d'an yi Alamar kod'ewa, sai wani madai-daicin hijabi data sanya, shima dai dagani kasan ba sabo bane, amma kuma wankakke n
e, duk kayan jikinta basu tare da datti.
"Haba laraba kiyi ha'kuri ki daina kukan nan, sabi'u dai yariga ya mutu kuma kinsan kukannan naki baze dawo dashiba, Addu'a kawai yanzu yake bu'kata daga gareki, ta dafa kafad'arta kiyi hakuri dan Allah ki daina
kukan nan.
Sai lokacin Balaraba ta kalli wacce keta faman rarrashinta tace "Haba indo dole inyi kuka, kukan nan danike shi kad'ai ze ragemin rad'adi da ba'kin cikin danake tartare dashi, (tacigaba da kukanta,)
Indo tana matu'kar tausayama halin da '
kawarta take ciki, itama wasu guntayen hawaye ta zubar sannnan ta'kara matsaowa kusa da 'kawarta ta dafa kafadarta da hannu guda,
gudan hannun kuma tana goge mata hawayen dake kwarara daga idonta, tace
"Tabbass nasan rabuwa da masoyi akwai ciwo,
baranta kuma rabuwa ta har abada, Amma dole kiyi ha'kuri ki d'auki wannan a matsayin jarabawa ce daga ubangiji.
Laraba ta fashe da wani sabon kuka, tace indo bazaki ta6a gane halin ba'kin cikin danake cikiba, ki duba kiga irin soyayyar da muka shimfid'a
nida Iro acikin 'kauyennan muna burge Kowa, amma lokaci guda ana saura sati d'aya bikinmu yaje wanki rafi yafad'a ruwa sai dai gawarsa aka fiddo, tafashe da wani sabon kuka, indo ma kukan take, amma hakan be hanata rarrashin 'kawar tata ba.
Cikin shesh
shekar kuka tacigaba da cewa "yanzu kuma :yau an wayi gari sabi'u shima ya mutu kamar yanda Iro ya mutu, wannan wane irin iftila'i ne yafad'amin.
Assalamu Alaikum, inna ce tashigo da sallama, indo ta amsa mata sannan tashigo d'akin, ta cire ijabinta ta
rataye kan 'kyauren d'akin sannan takai dubanta ga Balaraba wacce taketa faman kuka indo kuma na rarrashinta wacce itama kallo d'aya zakayimata Kazan kukan tayi.
Indo takai dubanta ga inna dake shirin zama kan kujera tace "lnna har kun dawo?
"Har
na dawo indo ay anriga anrufoshi sai dai muyi mashi addu'ar samun rahamar ubangiji, sabi'u kam yayi mutuwar ban mamaki, duk da ba mamaki cikin lamarin ubangiji, amma mutane da dama sunce lafiya lao ya kwanta, kawai aka wayi gari ya mutu, wasu siraran hawa
ye suka zubo daga idon inna dan tana tausayama tilon yarta, wacce tayi rashin masoyi a karo na biyu.
Laraba ta fashe da wani irin kuka, ta taso daga inda take tafad'a jikin inna tana kuka, "shikenan inna yanzu narasa sabi'u wayyo nashiga ukku, sabi'u m
iyasa kamin haka saida kabari na sha'ku dakai sannan zaka tafi ka barni, innalillahi,wa'inna,ilaihirraji'un, ta fad'a kawai sai ji sukayi tayi shiru ba Alamar numfashi tattare da ita, duka jikinta ya saki
Nan inna tashiga wani irin rud'ani tana girgizat
a tana kiran sunanta, "fatima..... Fatima innnalillahi nashiga ukku,
Indo dake tsaye hankalinta duk ya tashi tarasa inda zata sa kanta da gudu tafita daga gidan tana neman taimako.
"Dan Allah Hashim ka taima mani kada ta mutu, wanda takira da hash
im yace "wacece zata mutu, bata bashi amsaba tacigaba da kuka tana cewa ka taimakeni, mutuwa zatayi, dan Allah, da gudu takoma cikin gidan.
Har yanzu laraba na rungume jikin inna ba Alamar numfashi tattare da ita, inna kuma sai kuka take tana kiran suna
nta.
Da gudu hashimu yanufi gidan me gari ya aro baro,
Kofar gida ya ajiye baron, sannan yashigo gidan da taimakon, indo da lnna aka dora Laraba kan baron, Hashim ne ke tura baron da gudu.
Lnna da indo suna biye dashi hankalinsu tashe suka nufi 'ka
ramar asibitin dake 'kauyen.
Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 8:02 PM]
```NWA```
_written by_
*_Zee Mmn khady_*
3to4```Page```
Sannu Laraba sannnu kinji, kallo kawai take bin mutanen dake gu
rin dashi, idanunta suka ciko da hawaye, Inna tasa gefen mayafinta tana goge mata.
Sai da musalin 'karfe biyar na yamma aka sallamesu daga asibiti, bayan 'karin ruwan da aka sanya mata ya 'Kare,
Indo kuwa duk abinnan tana tare dasu sai gab da magrib i
nna ta umarceta data koma gida kada anemeta,
haka ta wuce tana me tausayama halin da 'kawarta ta tsinci kanta.
Hashim kuwa tinda akaje asibitin yaketa hidima da Laraba dan kusan duk kud'in da aka kashe shine yabiya, yana mutu'kar tausaya ma Laraba,
Shima sai lokacin yabar gidan yanama Laraba fatan samun lafiya, inna kuwa godiya kawai take mashi dan ya taimakesu ba kad'anba, dan in baccin shi da batasan inda zata samu kud'in da zata biya na magani da 'karin ruwan da akayima Laraba ba.
°°°°°°°°
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*_BAYAN SATI BIYU_*
Zaune take kan guntuwar tabarmar da aka shimfid'a kan shararren gidansu na 'kasa, ta tasa kwanon abinci gabanta, ita bata ciba kuma bata maida ta rufe ba, ta zubama abincin ido tana kallo, wasu zafafan ha
waye suka zubo daga idonta, tasa hannu ta goge.
"Yanzu Laraba bazaki cire damuwarnan daga cikin ranki ba, kiyi ha'kuri ki d'auki kaddara, kin riga kinsan dukkan me rai mamacine, muma nan mutuwa jiranta muke ko yau ko gobe ko jibi koma yanzu,
Dan Al
lah kisama ranki ruwan sanyi.
Wasu siraran hawaye suka zubo daga idanunta tace na ha'kura inna.... Na ha'kura..... Ki tayani da addu'a Allah yayemin damuwar dake tattare dani.
Inna ta tausayama Laraba har cikin ranta, tace "Allah yaye maki Laraba, Al
lah sa maki 'ha'kuri da dangana.
Tace Ameen tare da share hawayen dasuka zubo daga idanunta.
Da 'kyar inna ta rarrasheta taci abincin, Wanda taci be wuce loma hud'uba, dan ma lnna ta matsa mata ta d'ora da fura rabin cup, sannan taji d'an 'karfi-'kar
fi.
Da sallama ya shigo gidan, ya dur'kusa har 'kasa ya gaida inna, cikin far'a ta Amsa "Hashim kaine sannu da zuwa, ta d'auko wata guntuwar tabarma ta shimfid'a mashi ya zauna, tunda ya shigo idanunshi na 'kan Laraba wacce duk tabi ta rame ta fita hayy
acinta,
Saida ta lura da yanda yake kallonta sannan tace mashi "ina wuni, ya amsa da "Lafiya lao Laraba ya jikin naki?
"Da sauki, "Allah 'kara sauki, tace "Ameen.
Sannan ta tashi tanufi randa ta ebi ruwa cikin wani madai-daicin bokiti tashiga keway
e dan tawatsama jikinta taji sanyi.
Tunda ta tashi yake binta da kallo, cikin zuciyarshi yana cewa
_"Na dad'e ina son Laraba dan dai wasu sun rigani ne yasa na ha'kura, amma yanzu bazanyi sake da wannan damar ta wuceniba, 'kila dama rabonace shiyasa A
llah ya kashe lro da Sabi'u_.
Inna ce ta katse mashi tunani "Hashim ya mutanen gidan naku?, yayi saurin dawowa daga dogon tunanin dayake yace "suna lafiya sunce agaisheku, daga gurin aike nake nace bari in biyo inga jikin Laraba, inna taji dad'i har cik
in ranta yanda Hashim ke nuna kulawa ga 'yarta, tace "jiki Alhmdlh, yace "Allah 'kara sau'ki tace Ameen.
Nan dai suka 'dan ta6a fira kafin yayi mata sallama, ya ajiye wata ba'kar leda yace "ga wannan aba Laraba, inna tace "a'a Hashim hada hidima kuma,
yace "ba kome inna Allah sauwa'ke nina wuce, tace to Angode Allah bada lada, yace Ameen.
Bayan fitarsa ne, Indo tashigo, lokacin Laraba tagama wanka tana shafa mai, inna na Nuna mata abinda Hashim ya kawo mata, balangu ne lafiyayye hanta tafi yawa aciki
, sai 'kananan robar yourghut guda ukku,.
Bayan inna tafita waje, Indo ta kalli Laraba tace, "gsky Laraba Hashim yanada wata manufa acikin ransa dangane dake, dan ni nasan ba a banza yake maki wannan hidimar ba,
Laraba ta kalleta cike da nuna rashin
sanin inda maganarta ta dosa, tace "Ban ganeba wace manufa kuma? Indo tayi murmushi tace "gani nake kamar 'Hashim sonki yake.. .
Wani mummuman Fad'uwar gaba Laraba taji, dan yanzu ko kad'an bataso taji an anbaci kalmar wani na sonta.
Tace Dan Allah
indo mubar wannan maganar Hashim ba sona yakeba, inajin kawai dai yana tausayi na ne, amma babu wata soyayya dayakemin, murmushi kawai indo tayi, dan bata so suna kace-nace da 'kawar tata.
Ranar dai indo ta d'ebema Laraba kewa dan fira suka sha sosai, h
ar fita sukayi suka d'an zaga gari,
Tinda suka fita mutane ketayima Laraba ta'axiyya, indo ce ke amsawa dan bata son abinda ze daga hankalin 'kawar ta.
Sai bayan la'asar indo taraka Laraba har 'kofar gidansu saida taga shigewarta sannan itama ta wuc
e gidansu.
Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 8:10 PM]
😭
*_ALHINI_*
😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
®```NWA```
_written by_
*_Zee Mmn khady_*
😘
5
⃣
to6
⃣
```Page```
🖊
K
wanaki sun ja lokaci na tafiya, yau an wayi gari sabi,u nada wata ukku da sati biyu da rasuwa,
Alhmdulillahi Laraba ta saki jikinta, ba kamar da ba, kuma jikinta ya goge yayi sumut,
6angaren Hashim kuwa kullum soyayyar Laraba 'kara ha66aka take aci
kin zuciyarsa, har yakai da yakasa sukuni, hakan yasa ya yanke shawarar zuwa gidan yayarsa, ya fad'a mata halin dayake ciki, kuma ya ro'keta taje gidansu Laraba ta gabatar dashi amatsayin me neman Laraba da Aure.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Laraba ce tafito cikin shirinta, atamfa ce jikinta d'inkin doguwar riga, kalar ruwan 'kasa duk da atamfar ba sabuwa bace amma ta masifar yimata kyau, abinka ga farar mace, kowane kaya tasa kyau yakeyimata, wani 'karamin hijab ta sanya shima 'kalar ruwan 'k
asa tayi kyau abinta, duk da ta taso 'kauye bazaka kalleta ka kirata 'yar 'kauyeba, saboda bata irin shigar nan da 'yan 'kauye keyi na zani daban riga daban, ita tanasa kayanta complete, sannan kuma bata fiye sa gyale ba, yawanci kullum zaka ganta da hijab
d'inta, gata da nutsuwa da kamun kai, shiyasa duk mutanen 'kauyen take burgesu.
Kitchen ta iske mahaifiyarta tana faman girka masu abincin rana, tace "Inna zan d'an fita,
Inna ta kalleta tace "ina kuma zaki Laraba,?
"Inna inaso zanje gid
ansu indo ne naji kwana biyu ban gantaba,
To shikenan Laraba kije Allah kiyaye hanya, tace "Ameen, sannan ta fice daga gidan.
Inna kuwa har cikin ranta taji dad'in yanda d'iyarta ta saki jiki, dan rabon datace zata fita tun da rasuwar masoyinta sa
bi'u.
Cikin nutsuwa take tafiyarta, kanta sadde dan batason yawan kallon da mutane suke mata.
Dai-dai santar dazata sadata da gidan su indo ne taji kamar ana kiranta, waigowa tayi dan ganin me kiranta,
Cikin nutsuwa ya iso inda take fuskarsa d'au
ke da murmushi, yace "Laraba kina lafiya, tace "Lafiya lao Haruna,
ya'kara fad'ad'a murmushinsa yace "Laraba ashe kina ganuwa, itama mumushin tayi tace wace ni ince bani ganuwa,
yace ay naga tun rasuwar sabi'u rabon da inganki sai yau tace kaidai
bari Haruna, wallhi fitar ce yanzu kwata-kwata tayimin wahala yauma dan naga kwana biyu banga mutumniyarba shiyasa nace bari inzo inga ko lafiya, Haruna yayi murmushi yace "gaskiya ne 'kara da kika fito, nikau wallahi 'kawancenku yana birgeni keda lndo, du
k 'kauyennan ba Wanda besanku tare ba.
Murmushi kawai tayi tace "Haruna kenan, yace "Allah kuwa, duk 'kauyennan kuna burge mutane da dama kuma gashi kunsha bam-bam da 'yan matan 'kauyen, gurin nutsuwa da kamun kai.
Tace "to mungode da wannan yabo dam
uka samu daga gareku, ni zan wuce kaga rana na 'karayi baniso in wuce azahar ban koma gida ba,
Yace "to Amma idan bazaki damuba inaso zamuyi wata magana dake, tace "ina sauraronka Amma Allah sa bazata d'auki lokaci ba.
Yace "inshaAllahu bazata d'auki l
okaciba duk da bansan yanda zaki ji ba indan kikaji maganar dazan fad'a,
bejira tafad'i wani abuba ya'kara gyara tsayuwarsa yace "watako Laraba a gaskiya na dad'e ina Sonki cikin zuciyata, ganin sabi'u yarigani ne kuma gashi har maganarsa takai ga iyaye
yasa na ha'kura ban bayyana kainaba, amma yanzu tunda ta Allah ta kasance shine nace bari nazo da 'ko'kon barata ko Allah zesa a ki 'kar6eni in maye gurbin sabi'u a cikin zuciyarki.
Tunda ya furta kalmar so, Laraba taji gabanta yayi wani mummunan fad'uw
a, da kyar ta tattaro nutsuwarta, batare da ta kallesa ba tace "naji duka bayaninka amma inso kabani likaci inyi shawara.
Yace "nabaki kwana biyu ko wace shawara kika Yanke zanji, tace "Allah kaimu yace "Ameen.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
°
Da sallama tashiga gidansu lndo, innar indo ta iske tsakar gida tana wanke-wanke, ta dur'kusa har 'kasa ta gaisheta, "inna ina wuni, cikin fara'a ta amsa
"lafiya lao Laraba yau kece a gidan namu, tayi murmushi tace "nice inna, indo nanan kuwa? "Tanana
n da yanzu ma take cemin zata gidanku, ki isa mana.
Cike da murna indo ta tarbeta, 'kawata sannu da zuwa, wlh shirinnan da kika ga inayi gidanku zani, Laraba tace "sai kuma gani nazo, lndo tayi dariya tace "ay naji dad'in zuwanki, dama jiya Hashim yazo
gidannan yabani sa'ko gurinki, Laraba cikin halin rashin damuwa da maganar da lndo zata fad'a mata tace sa'ko kuma, lndo tace kwarai ko, dan abinda na dad'e ina gaya maki ne ya tabbata, Hashim dai yace inmi'ka 'ko'kon bararsa gareki, yace wlh ba wasa yakeb
a sonki yake, kuma baza'a d'auki lokaciba yakeso ayi aurenku.
Laraba tayi murmushi tace "yanzu ma kan hanya Haruna yatsareni da surutu waishi a dole yana sona, lndo tayi murmushi tace "inkon Allah, to yanzu yazamuyi kenan? Laraba tace "yafa zamuyi addu'
a zamuyi Allah za6amin abinda yafi Alkhairi, indo tace hakane Allah shige mana gaba, Laraba ta amsa da "Ameen.
Ranar gidansu indo Laraba ta wuni, sai bayan la'asar takoma gida.
Zaune ta iske innarta cikin inuwar bedi tana hutawa, d'aki tawuce tacire
hijabinta sannan tadawo ta zauna kusa da innar, tace inna sannu da hutawa, tace "yauwa har kin dawo, tace nadawo innna.
Inna ta kallata tace bayan tafiyarki, saratu yayar Hashim tazo gidannan, wai Hashim ya turota yana sonki idan anbashi dama kuma kin
amice Aurenki zeyi, cike da kunya Laraba ta sadda kanta 'kasa ta gayama inna yanda sukayi da lndo, sannan kuma ta gayamata shima Haruna yana sonta, inna tace "to dukansu dai basuda makusa amma ni aganina Hashim kamar zefi, kuma idan kikayi la'akari da hidi
mar daya dad'e yanayimaki idan kika gujeshi yanzu kamar munyi butulci ne.
Laraba tace "inna nidai duk Wanda kika za6amin shine za6ina, fatana kawai kitayani addu'a Allah za6amin abinda yafi Alkhairi.
Inna tace "Ameen.
🖊
Zee Elkaseem
Mmn
khady
💋
[10/16, 8:10 PM]
😭
*_ALHINI_*
😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
®```NWA```
_written by_
*_Zee Mmn khady_*
😘
7
⃣
to8
⃣
```Page```
🖊
Soyayya me 'karfi ta 'kulle tsakanin Lar
aba da Hashim duk 'kauyen mutane sun gama sanin Hashim ne ze Auri Laraba.
Haruna kuwa hakuri Laraba tabashi akan soyayyar daya nema daga gareta, bata za6e Shiba,
A ranshi yaji ba dad'i amma sai ya nuna bedamuba, yayi mata fatan Alkhairi.
°°°°°°°°
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Inna na zaune gidin bedi tana tsintar wake wanda zasuyi sanwar rana, tajiyo sallamar mal Lawal, Wanda ya kasance 'kanine ga mahaifin Laraba, da fara'a inna ta amsa sallamar "a'a mal Lawal ne sannu da zuwa, jiki na 'kyarma
taje ta d'auko tabarma ta shimfid'a mashi.
Mal Lawal mutum ne d'an bala'i bayada mutunci ko kad'an shiyasa lnna ke binsa ahankali dan tasan duk garin Laraba batada mahaifin daya wuceshi,
Yayinda shikuma yake amfani da wannan damar yanayimasu yanda
yaga dama.
Laraba ma masifar tsoronsa takeyi, hakan yasa tanajin shigowarsa gabanta yayi mummunan fad'uwa dan tasan akwai abinda yakawo shi,
Zuwa tayi har gabansa ta dur'kusa ta gaisheshi, cike da gadara da nuna isa ya amsa, sannan ta mi'ke taje t
a d'auki tukunyar 'kasar data kasance ta ebar ruwansu, ta yafo gyalenta tazo gaban inna tace "inna zanje d'ibar ruwa, inna ta kalleta, tariga tasan dalilinta na son tafita, saboda haka bata hanataba, tace to Allah bada sa'a tace "Ameen sannan tafice.
K
amar jiran fitarta yakeyi, ya maida hankalinsa ga inna yafara magana cikin bala'i da d'aga murya,
"Hinde dama gurinki nazo, watako banida daraja a idonku dan baku d'aukeni bakin komeba keda d'iyarki, shine har yarinyar nan tana soyayya da wani ba'a san
ar daniba dan an d'aukeni mahaukaci Wanda besan abinda yakeyiba.
Tunda yafara masifarsa lnna bata d'aga kai ta kalleshiba, saida yagama, sannan tace "Allah baka ha'kuri, dama wallahi yau nayi niyyar inzo dakaina har gida ingaya maka.
Ya tari numf
ashinta cikin masifa, yace "sai kuma gani nazo, to duk da bakison sanyani cikin Al'amarinki baki isa ki rabani da Laraba ba, saboda Laraba batada Uban da ya wuceni duk fad'in 'kauyennan.
"To duk da baki tura shi Hashimun gurinaba yaje ya sameni munyi ma
gana, kuma yatura magabatanshi mun tsaida maganar aurenshi da Laraba nan da sati ukku idan Allah ya kaimu.
Inna tace "Allah kaimu Allah sa muna raye, ta tashi tashige d'aki tana matsar kwalla, kusan duk randa mal Lawal yazo gidan sai inna ta zubar da ha
waye.
Nan yagama zamanshi yanata zazzaga masifa marar dalili, ta inda yake shiga ba tanan yake fitaba, lnna kuwa tana d'aki tana jinshi har yagaji ya'karama rigarsa iska.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Zaune suke kan wani dutse 'kafafun
su na cikin ruwa, da Alama sunajin dad'in yanayin gurin, Hashim ya kalli Laraba yace "Am Laraba na manta ban sanar dakeba, jiya baffanki yasameni yace intura magabata na, yanzu haka kafin infito nabaro su baba bala