Showing 21001 words to 24000 words out of 31402 words
ta 6ata yaran mutane.
Wani irin takaici da ba'kin ciki da kishi suka taru suke rufe Mukhtar dan jin labarin da Sadiq
yafad'a saboda haka ido rufe ya tunkareshi kamar wani tsohon mayunwacin zakin daya kwana beciba.......
4
⃣
9
⃣
to5
⃣
0
⃣
Very
🔜💃🏻
🖊
Zee Elkaseem
Mmn khady
💋
[10/16, 8:12 PM]
😭
_*ALHINI*_
😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
®```NWA```
_Written by_
_*Zee Mmn khady*_
😘
4
⃣
9
⃣
to5
⃣
0
⃣
🖊
A zuciye mukhtar yakaima Sadiq wani wawan naushi a fuska, take gancinsa yafara zubar da jini, cikin 'kankanin lokaci jini ya
6ata mashi tsadaddiyar shaddarsa wacce tasha d'inkin computer, ganin jinin dake zuba daga hancin Sadiq besa Mukhtar ya saurara mashi daga dukan dayake mashi ba, cigaba yayi da dukanshi ta ko'ina, sannan yacimashi kwala ya tadashi tsaye ya angizashi, cikin
fushi da d'aga murya yace "kafita daga gidannan tun kafin inzama ajalinka, mugu azzalumi barin irinka cikin Al'umma had'arine.
Duk abinnan da Mukhtar yayima Sadiq beyi 'ko'karin hanashiba, kuma be kare kanshi daga dukan dayayi mashiba, badan beda 'karfi
n daze ramaba, dan a girme sadiq yakai d'aya da rabin mukhtar, dan acewarshi duk abinda Mukhtar yayimashi ya can-canci hakan.
Jidda ce taga abin na yayanta yayi yawa dan dukan sad'iq yake kamar baze barshi da rai ba, ta kalli Hajiya tace "dan Allah kiha
nashi kada ya kasheshi,
Bata jira hajiyaba tanufi gurin tari'ke hannun mukhtar tana cewa "dan Allah yaya kayi ha'kuri ka 'kyaleshi tunda Allah be bashi ikon aiwatar da kome kan Fatimar ba.
Ganin beda niyyar sauronta yasa ta kama hannunshi tari'ke tana
bashi ha'kuri a zuciye ya hankad'ar da ita tafad'i zaune tafashe da wani irin kuka.
Ganin abin na Mukhtar bana hankali bane yasa Hajiya tazo ta kamashi, tace "kai mukhatar ka daina dukanshi nace, be saurari hajiyaba sai 'ko'karin tura Sadiq waje yake, y
ana cewa "kafita kabar gidannan ban 'kaunar ganinka, wallahi idan ina ganinka zan iya illataka dan ban had'a fatimana da kowaba.
A fusace Hajiya ta fincikoshi, cikin fushi take magana "wai kai Mukhtar wane irin mutum ne, yaushe kafara rainani da inama m
agana baka saurarena.
Wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonshi, baya yayi yasamu guri ya zauna kan d'aya daga kujerun falon yana cika yana batsewa, jiyake dama Hajiya tabarshi da sai yakusa halaka sadiq.
Fatima kuwa tunda suka shigo gidan taga hali
n data iskesu hankalinta yatashi, bata 'kara shiga wani tashin hankalinba saida taga yanda Mukhtar ke dukan Sadiq gashi harya fitar mai da jini amma be daina dukansaba.
*_Innalillahi'wa,inna'ilaihirraji'un_* tashiga furtawa, tana kuka kamar zata cire ra
nta, jidda ce takamata tace "ki daina kuka fatima ki godema Allah daya tseratar dake da mutuncin ki,
Cikin dusashshiyar murya Alamar tayi kuka tagaji tace "jidda dole inyi kuka, duk halin damuwar da kuka shiga nice na jefaku, sannan abinda mukhtar yayi y
anzu duk saboda ni yakeyi, wayyo Allah na ina zani da Alhaki, nazama butulu, na guji mutanen dasukayimin hallaci a rayuwa, mutanen dasuka sharemin hawayen da 'kanin mahaifina yakasa sharemin,
Zuwa tayi gaban Hajiya ta dur'kusa gwiwa biyu, tana kuka tace
"dan Allah Hajiya Ku yafemin nasan nashiga rayuwarku na jefaku cikin damuwa.
Cike da damuwa da tausayi Hajiya takama hannun fatima ta zaunar da ita kan kujera tana gogemata hawayen dake zuba Daga idonta.
.
Hajiya takai dubanta ga Mukhtar Wanda ket
a cika yana batsewa, tace "ba haka akeyiba kawai ka kama mutum kayita duka har ka jimasa ciwo, duk da abinda yafad'i yana aikatawa ai bekai ga aikatashi ga ita fatimar ba,
Kuma tunda kaga yakawota har gida ina tunanin akwai dalilin sayasa yakawota.
Sa
nnan ta maida dubanta ga Sadiq tace ina jinka yaro, cike da nadama Sadiq yafara magana,cikin muryar tausayi da nadamar abubuwan daya aikata a baya.
_ ```na kasance ni 'kadai iyayena suka haifa, kuma iyayen nawa sun kasance masu tarin dukiya, tun ina 'kara
mi suke nunamin tsantsar so da 'kauna, hakan yasa natashi banajin magana ko kad'an kuma duk abinda naga dama shi nakeyi, tun ina secondary school nake 6ata yaran mutane, ta hanyar yimasu fyade idan sun'ki amincewa, a lokacin nama fi so inyi fyaden dan nafi
jin dad'in hakan, kuma idan aka ganeni aka kawo 'karata babana sai yakama fad'a yace anjamin sharri dan ana ba'kin ciki da dukiyar da Allah yayi Mashi, kuma yabani shi amatsayin d'a d'aya tilo haka yake fatattakar mutane, wasu su fita suna kuka wasu kuma
suje suna Allah ya isa, ana cikin wannan halinne mamana da babana sukayi tafiya, kan hanyarsu ta dawowa suakayi had'ari suduka suka mutu, nayi kukan rashin iyayena sosai, bayan kome ya lafa aka raba gado aka bani, kasancewar bani ganin Kowa da gashin arzi'
ki yasa ba wanda yayi gigin cewa ze ri'kemin dukiyata, cikin dangin mamana, kona baba na, haka nacigaba da bushasha, har basamu yarana wad'anda sune ke d'aukomin 'yan mata ina keta masu haddi ta 'karfin tsiya```
Wasu hawaye masu zafi suka zubo daga idan
unshi, yace amma sanadin zuwan fatima gareni yasa natuba na daina wannan mummunar d'abi'ar danikeyi, kuma inaso dan Allah fatima ki yafemin, yafad'a yana kallonta.
Mukhtar be tausayama sadiq ba ko kad'an illah wani irin haushi daya 'kara bashi yace "dal
lah Malam kafita kabar gidannan munji duk bayaninka Allah shiryeka, bani son ganinka cikin gidannan kuma bani bu'katar jin muryar ka.
Cikin fad'a Hajiya ke magana, dan mukhtar yafara 6ata mata rai tace "wai kai wane irin mutum ne, mutum yazo har gida ya
ro'ki yafiya amma kakama cimasa mutunci, ay inajin koda kafirine yazo neman gafara gareka zaka gafarta mashi kodan yasan musulunci akwai Alfarma acikinsa, barantana d'an uwanka musulmi, Allah yana son masu yafiya ga junansu, wai Mukhtar ina iliminka yake,?
Kuma kafin wannan ma ay komiye fatima itace babbar mai laifi, da bata fitaba da duk haka be faruba.
Sadiq yace "ni najin dad'in fitar tata dan tazama sanadin shiriyata, fatana shine tace ta yafemin, yafad'a yana zubar da hawaye...
Cikin muryar k
uka fatima take magana "tabbas kome yafaru nice na jawo, dan daban fitaba da hakan bata faruba,
Ta kalli sadiq tace nayafema, Allah 'kara shiryaka, kuma naji dad'i dana zama sanadin shiriyarka.
Tana gama fad'in haka Sadiq yami'ke yace nagode Hajiya sai
anjimanku, yafice daga gidan.
Fatima kuwa durkusawa tayi tsakiyar falon tana kuka, tana ro'kon Hajiya da jidda da mukhtar su yafemata,
Mukhtar har cikin ranshi yakejin kukanta, baze iya juraba saboda haka barin d'akin yayi zuciyarshi na tafarfasa.
5
⃣
1
⃣
to5
⃣
2
⃣
Very
🔜💃🏻
*_'kya'k'kyawar gaisuwa ga 'kanwata, NASIBAT ELKASEEM_*
_Love u my sister_
😘
🖊
Zee Elkaseem
Mmn khady
💋
[10/16, 8:12 PM]
😭
_*ALHIN
I*_
😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
®```NWA```
_Written by_
_*Zee Mmn khady*_
😘
5
⃣
1
⃣
to5
⃣
2
⃣
🖊
washe gari bayan kome ya lafa, da misalin 'karfe tara da rabi na safe,
Zaune suke a general falo, bayan sun kammala kalacin safe, Kowa yayi shiru
, amma akwai abinda yake sa'kawa cikin zuciyarshi, yayinda Fatima takan goge guntayen hawayen dakan zubo mata daga idanunta akai-akai.
Mukhtar yana lura da halin datake ciki saboda haka hankalinshi duk yana gurinta, fatanshi Hajiya ta wuce d'akinta ya r
arrashi fatimarsa ya kwantar mata da hankali, dan idan akwai abinda yafi tsana a duniya shine 6acin ran hajiyarsa sannan kuma yaga fatimarsa cikin damuwa.
Hajiyace ta maido da kowanensu daga duniyar tunanin daya Lula, yayinda ta kalli Fatima tace "Fatim
a inaso ki nutsu ki kwantar da hankalinki ki fad'amin gaskiyar dalilin dayasa kikayi 'ko'karin guduwa daga hannunmu wanda hakan yajefamu cikin matsanancin tashin hankali.
Shuru tayi na d'an wasu mintoci bakajin kome sai sheshshekar kukanta, sannan tafar
a magana cikin sarkewar murya tace "da farko inaso in ro'keku yafiya akan halin damuwar dana jefaku na 'ko'korin guduwa danayi,
Bawai nayi hakan bane dan kun gaza da ri'kon da kukemaniba, ba kuma dan na raina hallacin da kukayimani bane, a'a nayi hakane
saboda baniso in sakamaku da sharri akan Alkhairin da kukayimani.
Sannan inaso Ku gafarceni akan 6oye maku wasu abubuwa da dama danayi dangane da labarina, yau inaso zan sanar daku kome bakin gaskiyata, dan baniso nazama sanadin rushewar farin cikinku.
*_HAKA LARABA TA KWASHE LABARINTA KAF TA FA'DA MASU BATARE DATA 6OYE MASU KOME BA_*
Bayan tagama basu labarinta ne tacigaba da cewa "muddin na yarda da auren mukhtar nasan shima 'karshen rayuwarsa yazo, nasan shima ze mutune kamar yanda maza ukku suk
a mutu sanadiyyar aurena, a 'kauyenmu' yayinda na hud'unsu yasha ba'kar azaba har yarabu dani ranar dana tare gidanshi, shima na tabbata kwanasa ne be 'kareba da yanzu shima sai labari.
Jidda wacce tunda Fatima tafara bada labarinta take kuka tace "Fati
ma duk wanda yamutu kwanansa ne suka 'kare kuma inshaAllah yayana ze aureki kuma ze zauna dake ba abinda ze faru daku.
Hajiyama saida ta goge guntayen hawaye dan tausayin da Fatima ta bata, tace ki kwantar da hankalinki Fatima ni nayi Al'kawarin zama d
ake kuma inshaAllah ko miye ze rabu dake, kuma aurenki da Mukhtar ba fashi muddin kuna son junanku.
Wani sanyi Fatima taji har cikin ranta, dan son mukhtar ya dad'e da d'arsuwa a zuciyarta.
Shima mukhtar haka yaji,
Cike da farin ciki yace "Hajiya i
naga Al'amarin Fatima kamar hada iska cikinsa, saboda haka inaso zan kaita gurin wani friend d'ina wanda shida babanshi sun 'kware gurin magance irin wannan matsalar ta hanyar amfani da ayoyin Allah da kuma magungunan musulunci wanda babu shirka a cikinsa.
Cike da jin dad'in yanda d'anta keson taimako Hajiya tace "to Allah taimaka Allah sa a dace.
Su duka suka amsa da Ameen.
Sannan jidda takama hannun Fatima suka nufi d'akinsu, kai tsaye toilet suka shiga suka d'auro alwala suka kabbara sallar nafila
da niyyar Allah yayema Fatima lalurar dake tattare da ita.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Washe gari da musalin 'karfe goma na safe sun fito cikin shiri, jidda da faima suna sanye da riga da wando na fakistan sannan suka d'ora hijabansu,
sunyi kyau abinsu, Mukhtar kuma cikin shigar manyan kaya shadda ash colour sai ba'kin takalmi sai 'kamshin turarensa daya buge ko'ina,
Har mota Hajiya tayi masu rakiya, suka shiga me gadi ya bud'e masu get suka d'au hanya.
Mintuna talatin suka sada
su da gidan mal bature, shine mutumin daya 'kware gurin magance matsalar jinnu ko asiri ko sihiri, ta hanyar amfani da ayar Allah batare da an kauce hanya ba.
Suna Isa Mukhtar yayima abokinshi waya me suna Usman ya sanar dashi isowarsu,
Da far'a
ya fito ya tarbesu, sannan yayimasu iso,
Bayan sun shiga sun gaggaisa Mukhtar ya sanar dashi abinda ke tafe dasu, duk da dai kamar 'karin bayanine yake mashi dan sun riga sun gama maganar kome ta waya, har Usman d'in ya Sanar da babanshi zuwansu.
Nan
ya nunamashi Fatima matsayin wacce za'ayima maganin, Fatima wacce tunda sukazo kanta ke sadde 'kasa Usman yakira sunanta "Fatima, sai lokacin
tad'ago ta kalleshi, suna had'a ido gabanta yayi mummnar fad'uwa wanda ita kanta batasan dalilin hakan ba.
Cewa
yayi su biyoshi zuwa gurin babnshi, haka suka bishi Fatima jikinta sai 6ari yake kamar wacce ake girgizawa....
5
⃣
3
⃣
to5
⃣
4
⃣
very
🔜💃🏻
🖊
Zee Elkaseem
Mmn khady
💋
[10/16, 8:12 PM]
😭
_*ALHINI*_
😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
®```NWA```
_Written by_
_*Zee Mmn khady*_
😘
5
⃣
3
⃣
to5
⃣
4
⃣
🖊
Bakin 'kofar d'akin Fatima ta toge ta'ki shiga, mukhtar ya kalleta yace "muje mana Fatima ko wani abu kk jira, banza
tayi ta 'kyaleshi ta tsaya gurin batada niyyar matsawa ciki, saima 'kokarin komawa da baya take.
Jidda da tayi gaba harta shiga inda malam yake saida ta waigo taga Fatima da mukhtar basu shigoba, dawowa tayi dan ganin ko lafiya, nan ta iske mukhatar na
fama da ita akan ta shiga d'akin ta 'kiya.
"Haba Fatima ki shigo mana' gurinfa maganinne mukazo nasan kinfi kowa son rabuwa da lalurar dake tattare dake, jidda tafad'a cikin rarrashi.
Ganin Fatima batada niyyar tanka mata kuma batada niyyar shigowa y
asa jidda kama hannunta da niyyar tashigo da ita.
Saukar wani lafiyayyen mari jidda tayi a kumatunta, Wanda saida ta gigice saboda tsananin zafin marin, takai dubanta ga Fatima wacce ke cika tana batsewa tace "me nayimaki zaki mareni.
Cikin wata gur6
atacciyar murya Fatima tafara magana, wacce ko alama ba muryarta bace dan muryar tafi kama data maza, "an mareki d'in tafad'a tana wani irin huci, "ke har kin isa ki shigar dani gurin dabanyi niyyaba.
Mukhtar naganin haka yasan ba Fatima bace, saboda ha
ka ya kalli jidda yace "maza kiramin Usman ya taimakamin dan wannan abin nayine.
Jiki na 'kyarma jidda tatafi kiran Usman, abin kamar jira tana fita kokowa ta kaure tsakanin Fatima da Mukhtar, dan niyyar guduwa tayi shikuma ya ri'keta.
Saida Usman ya
zo da taimakonshi aka shiga da ita inda malam yake.
Suna shiga tafasa wata uwar 'kara wacce duk illahirin mutanen dake gurin saida suka firgita, banda Malam wanda dama yasaba ganin irin haka.
Fad'uwa tayi 'kasa bakinta na fitar da wani irin kumfa, M
alam yataso ya tsaya gabanta yace "waye kai, ko wacece? Shiru Fatima tayi sai wani gurnani takeyi, Malam ya'kara magana karo na biyu nan ma shuru tayi, wani ruwa ya d'auko ya karanta wasu addu'oi yatofa aciki ya watsa mata, wata irin 'kara tasaki firgigi t
atashi zata gudu kamar wacce aka watsama garwashin wuta, mallam ya daka mata tsawa yace "koma ki zauna, ba musu ta zauna tanata wani layi kamar wacce tasha ta bugu.
Sannan yace ina jinka waye? Cikin muryar daba ta Fatima ba take magana tace "nine, hakan
yasa Malam yagane namijine yace "Kaine wah?
Yace "nine masoyinta.
"Masoyinta kamar ya?
"Me shirin aurenta
"Me shirin aurenta kome shirin cutar da ita.
"Niba cutarta zanyiba, dan na dad'e ina dakon soyayarta tun tana cikin tsumma nake tare da ita ina
rainonta da niyyar idan ta girma in aureta.
"Kasan dai babu aure tsakanin mutum da aljan saboda haka kayi gaggawar barin jikinta.
"Bazan iyaba ina sonta.
"Kafita da arzi'ki kokuma in fidda kai da tsiya.
"Bazan fitaba ko zaka kasheni.
Haka akayita da
ga tsakanin aljani da Malam, 'karshe dai mallam yayita karanto ayoyi yana tofa mata, tashiga birgima tana ihu, hakan besa mallam ya daina karanto ayoyin Allah yana tofa mata ba.
.
Kusan awa d'aya da rabi ana abu guda, sannan daga 'karshe Fatima ta fas
a wata uwar 'kara tafad'i 'kasa war-was,
Wani abin al'ajbi dai-dai wannan lokacin kuma wannan 'katon ramin wanda laraba tayi niyyar fad'awa a 'kauyensu lokacin da mukhtar ya tsinceta, yakama da wuta,
Ashe dama nan ne mazaunin wannan Aljanin da yake j
ikin Fatima.
Mallam ya kalkesu yace Alhmdulillahi kome ya wuce, babu sauran wani jinnu a jikinta zaku iya tafiya gida, cike da tsoro jidda ta kalli malam tace "mallam a haka zamu tafi da ita bata fa farfad'o ba, mallam yace "kada ku damu zata tashi wann
an nannauyan baccin dole tayishi, ga wannan garin habbatussauda ne tar'ika amfani dashi tana zubawa a abinci ko cikin abinsha, kamar kunu ko koko, ko tea, sannan ya mi'ko wani maganin yace wannan 'kuma haya'kin shaid'anune, tarika turarashi kullum kafin ta
kwanta, sannan ta ri'ke addu'oi da azkar da salatin annabi, Allah sauwa'ke, suduka suka amsa da "Ameen.
Sun kar6i maganin sukayi godiya,mukhtar ya ajiyema mallam kud'i me tarin yawa yace "mallam ga sadaka, mallam yace Allah ya kar6a.
Haka mukhtar
da jidda suka kama Fatima wacce batasan inda kanta yakeba, suka sakata mota,
Har gurin mota Usman yazo sukayi bankwana yaimasu Allah kiyaye tare dayima Fatima fatan samun lafiya me d'orewa.
Tunda suka tafi a mota jidda ke faman kuka dan fatima ta ma
sifar bata tausayi, Mukhtar kanshi 'karfin hali yake gurin driving dan duk illahirin jikinshi kyarma yake, haka suka iso gida bakin get sukayi horn megadi yabud'e masu get suka shige.
Suna shiga jidda tabud'e motar tafita, cikin gida tayi tana kuka, Haj
iya dake zaune falo tayi uban tagumi tana tunaninsu, tajiyo sallamar jidda, kafin tayi magana jidda tafad'a jikinta tana kuka,
Cikin tashin hankali Hajiya ke tambayar jidda "ina fatimar meya faru da ita?
Sallamar Mukhtar tajiyo, yashigo falon d'auke da
fatima kamar wata jaririya,
Shimfid'ar da ita yayi tsakiyar falon sannan yasamu guri ya zauna suka zubama sarautar Allah ido.....
5
⃣
5
⃣
to5
⃣
6
⃣
Very
🔜💃🏻
🖊
Zee Elkaseem
Mmn khady
💋
[10/16, 8:12 PM]
😭
_*ALHINI*_
😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
®```NWA```
_Written by_
_*Zee Mmn khady*_
😘
5
⃣
5
⃣
to5
⃣
6
⃣
🖊
*_BAYAN WATA BIYU_*
Fatima ta samu lafiya, kuma acikin 'yan kwanakinne soyayyarta da mukhtar t
ayi 'karfi wanda sukayi tsananin shakuwa, da so da 'kaunar juna.
Wata rana suna zaune a falo su duka kamar yanda suka saba idan sun gama cin abinci, Hajiya ta kalli fatima tace "yakamata kibada izini aje 'kauyenku gurin baffa Lawal Neman aurenki,
*'Rassss* Fatima taji gabanta yayi mummunar fad'uwa, lokaci guda tanemi nutsuwarta ta rasa dan ko kad'an bataso ayimataaganar 'kauyensu dan yariga yafitar mata arai, garin da aka 'kuntata mata aka muzantata, garin data wayi Gari yunwa da 'kishirwa sun
kusa halakata saboda tsana da tsangwama da suka nuna mata.
Hannu tasa ta goge hawayen dasuka 6ata mata fuska, Hajiya tace "ki saurareni fatima, kinsan indai mace na