Showing 18001 words to 21000 words out of 31402 words
fahimci inda zancensu ya dosa,
A gida kuwa da misalin 'karfe ukku da minti sha shidda na dare jidda ta farka zata shiga toilet sai taga bataga Fatima ba, hakan yasa tayi tunanain ko tana
toilet d'in ta dad'e tana jiran fitowarta amma kusan minti goma shiru saboda haka saukowa tayi daga kan gadon da niyyar ta duba toilet d'in.
Abinda idanunta yafara karo dashi shine ya d'aga mata hankali, kayan baccin Fatima yadde a 'kasa, bata tsaya d'
auka ba ta tura 'kofar kewayen, nan ma ba Laraba, cikin tashin hankali tayo baya sai tayi karo da wadrop bud'e tayi sauri dubawa cikin wadrop d'in saitaga kaya yamutse da Alama an d'auki wani abu aciki, nan tashiga matsanancin tashin hankali lokacin data t
a6a kofar fita daga d'akin tajita bud'e.
Cikin tsananin tashin hankali tanufi d'akin hajiyarta ta sanar da'ita abinda ke faruwa,
Mukhtar ma an tasoshi an fad'a mashi halin da ake ciki, cikin tashin hankali yafito, haka suka shiga duba ko'ina na gida
n Amma ba Alamar Fatima, an tambayi me gadi yace shikam bega fitar Kowa a gidan ba.
Lokacin idan hankalinsu yayi dubu tashe yake, mukhtar d'akinsa yanufa ya d'auko key d'in motarsa yacema Hajiya "Zan fita in duba ko Allah zesa in ganta.
Lokacin itak
uma jidda ta d'auko wayarta dan ta lura duk inda Fatima take ta tafi da waya dan ta duba bata gantaba, lokacin ta lalubo sunan sister Fatima, sunan data sanyama Laraba kenan ta danna mata kira.
Dadai lokacin da wad'annan mutanen guda biyu suka tashi d
aga 'kofar kangon gidan da Fatima ke la6e a ciki guda na cewa "baba yakamata fa mu'kara gaba ko mun samu, ya duba agogon hannunshi yace 'karfe ukku da rabi kada gari ya waye mamu anan, kasan oga mayen mata ne duk ranar dabamu samo mashiba bamuda jin dad'i,
d'ayan wanda tun farko yace yagaji da sana'ar yace "waallahi ni abin na oga yana bani mamaki, ga yan mata nan karuwai masu Neman mazan da kansu meyasa baya ri'ka d'aukosu yabiya bukatarsa yabiyasu 'kud'insu hankalinshi kwance suma hankalinsu kwance, gudan
yace "kai dai banzane baka ta6a ganewa, ai a cewar oga duk macen data kai kanta ga naminiji batada wani fa'ida yafison wacce za'a d'auko Mashi ya mata fyad'e, yafi jin dad'in hakan dan duk wacce aka kawo tana tirjewa yasan ba 'yar iska bace, ko ka manta l
okacin damuka kawo mashi wata yarinya tanata ihu tana zillewa, ta d'auka yankata za'ayi koda tagane ba yankata za'ayiba, tagane manufarsa kawai sai tace "dakasan wannan ne da baka sa nayi wahalar hawayena ba, kawai mallam bissmillah, yana ganin haka yace a
fita da ita, wallahi beyi amfani da itaba, dan ya lura sana'arta ce.
Zasu tafi kenan wayar fatima tashiga ruri lokacin, kiran jidda ya shigo, cikin tsananin tsoro da kad'uwa ta sa hannu ta danne wayar, harta tsinke bata d'aukaba sai kuma aka 'kara kira
karo na biyu, tayi ko'karin takashe wayar baki d'aya amma sai ta kasa saboda tsananin rud'ewa.
Da sauri wad'annan mazan suka shigo cikin kangon gida suna dubawa dan jin waya nata ringing, lokacin kuwa Fatima tagama sadaukar da rayuwarta, cikin sa'a kuw
a suka ganta basuyi wata-wata ba suka sungumeta, guda ya d'orata kan kafad'arsa tanata ihu tana dukansa tana yagunsa, hadama cizo amma ko a jikinsa, ganin zata tona masu asiri yasa gudan ya fiddo wani salatif ya toshe mata baki.
Tafiya marar nisa ta sad
asu da inda suka ajiye motarsu wata bakar Hummer jeef mai ba'kin glass suka jefata ciki, sannan sukaja motar, tafiya mai nisa sukayi wacce fatimar batasan inda sukeba, bata iya ganin kome, saboda duhun dare ga kuma ba'kin glass d'in motar.
Bakin wani
'katon gida wanda zamu iya kira aljannar duniya saboda 'kyawunsa, sukayi horn me gadi ya bud'e masu get suka shiga, wani had'adden bedroom suka jefata kan gado sannna suka kware salatif d'inda ke bakinta, saboda tsananin azaba saida tafasa 'kara.
Haka s
uka fita suka barta sukaja 'kofar, itakuma banda kuka ba abinda takeyi.
'Karar bud'e d'akin yasa ta d'ago kanta wani 'katon mutum tagani, dogo ne fari me dogon hanci da manyan idanuwa, ga bakinshi ma barakallahu babbane, ga 'kiba dake gareshi kamar basa
mude.
Tsayawa yayi ya 'karema Fatima kallo, sannan ya matso yana lasar baki kamar tsohon maye, yace "kai amma yau nayi dace tunda ake kawomin 'yan mata ba'a ta6a kawomin 'kya'kyawa kamarkiba, yasa hannu ya cire hijabin dake jikinta, ganin surar jikinta
yasashi 'kara rikicewa dan rigar datasa tad'an kameta, ga kanta ba d'an kwali, yayi dariya yace amma kinada ala'ka da india ko? Wannan 'kya'kyawan gashi haka, yakai hannu yana shafa kanta, itakuma kuka kawai take takasa ta6uka kome, a zuciyarta sai addu'a
take Allah kada yaba wannan mutumin ikon aikata abinda yake nufi akanta.
Haka yacigaba da shafata yana latsata, inbanda kuka ba abinda take, nan yashiga 'kokarin rabata da 'kayan jikinta, tasa hannu ta rirri'ke koda yaga zata kawo mashi gardama sai ya n
unamata 'karfi lokaci guda ya rabata da rigarta, jikinta yarage daga ita sai bes, sai wando lagis data Sanya lokacin dazata fito, ganinta haka da bayyanar 'kya'ky'kawar surarta ya'kara rikitashi, ya fita hayyacinshi gaba d'aya ya rungomota jikinshi....
_*Ina barar addu'arku masoyana a duk inda kuke, shekaran jiya anyima babana theatre Emergency, amma yaji sauki, kutayani addu'a Allah 'kara Mashi lafiya da duk musulmi baki d'aya*_
👏🏻😭
🖊
Zee Elkaseem
Mmn khady
💋
[10/16, 8:12 PM]
😭
_*ALHINI*_
😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
®```NWA```
_Written by_
_*Zee Mmn khady*_
😘
4
⃣
3
⃣
to4
⃣
4
⃣
🖊
kuka Fatima tashiga yi ganin yana neman keta mata haddi, tana cewa "dan Alla
h kayi ha'kuri kada ka cuceni kada ka 6ata min rayuwa, tana fad'ar haka tana wani irin kuka me tsuma zuciyar me sauraro, amma mutuminnan ko ajikinsa, dan ko kad'an bata bashi tausayiba illah 'kara kwad'aituwa dayayi da ita.
'Ko'karin rabata da sauran ka
yan dasuka rage jikinta yakeyi, itakuma banda addu'a ba abinda takeyi, dan batada wani sauran kuzari tattare da ita.
A 6angaren Mukhtar kuwa yasha yawo har kusan 'karfe biyar na asuba amma bega Alamar zega laraba ba, be 'kara shiga tsananin tashin hanka
liba saida yafara jiyo kiraye-kirayen sallar asuba,
haka yakoma gida zuciyarshi cike da takaici da ba'kin cikin rabuwa da masoyiyarshi.
Yana shiga gidan a falo ya iske Hajiya da jidda sun buga uban tagumi, suna tunanin ko yaga fatimar,.....
Ganin shi
gowarshi shi d'aya batare da laraba ba yasa jidda saurin tashi cikin muryar kuka tace "yaya baka gantaba? Innalillahi munshiga ukku, ta fashe da wani sabon kuka.
Jiki sanyaye mukhatar yasamu guri ya zauna.
Sai lokacin Hajiya ta kalleshi jiki a sanyaye
tace "Mukhtar Yaya ba'a gantaba ko?
Wata nannauyar ajiyar zuciya yayi sannan ya d'ago da idanunshi wad'anda suka kad'a sukayi ja saboda tsabar damuwa, yace "Hajiya Fatima ta su6ucemin shikenan Hajiya narasa Fatima, lokacin wasu zafafan hawaye suka zubo
daga
idanunshi, yace "Hajiya me mukayima Fatima ta gujemu? Me tanema a gidannan tarasa?.
Lokacin wani irin tausayin Mukhtar tashige hajiya, a zuciyarta tace tabbas mukhtar yana cikin halin damuwa, dan na lura da yanda ya gama dam'ka duk illahirin soyay
yarshi ga Fatima, a Zahiri kuwa cewa tayi "inshaAllah duk inda Fatima take zata dawo garemu, kudai kucigaba da Addu'a Allah tsareta a duk inda take,
Lokacin jidda ta fashe da wani sabon kuka tana cewa "ya Allah ka bayyanamin 'yar'uwata a duk inda take, A
llah kareta da duk wani mugun abu.
Sai da sukaji an kabbara sallah a masallacin kusa dasu sannan kowanensu yatashi yanufi sashensa dan gabatar da sallah, mukhtar kuwa koda yayi Alwala masallaci ya wuce zuciyarshi cunkushe da ba'kin ciki da takaicin hali
n daze tsinci kanshi inhar yarasa Fatima.
A 6angaren laraba kuwa haka mutumin yari'ka jagulata amma har yanzu Allah be bashi ikon cimma burinshiba na keta mata haddi,
Amma duk illahirin jikinta yagama jagulata, hannu yakai yana kokarin ida rabata da
bes d'in jikinta wacce ita kad'ai tarage sai lagis d'inda tasa hannu ta rirri'ke lokacin dataji yana Neman rabata dashi,
Wani irin 'karfi yazo mata a lokacin hannuwanta tasa duka biyun ta d'ora kan 'kirjin mutumin Wanda gaba d'aya yayimata rumfa dashi
, ta turashi iya 'karfinta.
Jiyayi kamar wasu 'katti goma sun angizashi, yayi baya,yafad'i 'kasa, lokacin kuma Fatima ta taso mashi hai'kan kamar wata tsohuwar damisa, lokaci guda duk wani haske na fuskarta ya dishe, idanunta suka canja launi zuwa ja, t
ayo kan mutumin hai'kan, a tsorace yatashi yafara ja da baya, dan ya masifar tsorata dan yanda take tunkaroshi.
Saida ya dangane da bangon d'akin lokacin yashiga laluben 'kofa dan tsira da rayuwarshi, amma kafin yayi yun'kurin bud'e dakin yafita ta
kaimashi wani wawan bugu da hannunta d'aya, wani irin duhu yaga ya gifta mashi, kanshi ya bugu da bangon d'akin, take yafashe jini yafara ambaliya, yana wanke mashi jiki, a tsorace yafasa wata uwar 'kara yana Neman taimako,
da gudu yaranshi suka nufo
d'akin dan jin ogansu yana neman taimako, suka shiga tura 'kofar amma ko kad'an ta'ki bud'ewa, da sauri guda yanufi wani d'aki ya d'auko wani makullin ya bud'e, da sauri suka nufi inda ogan nasu yake kwance yana maida numfashi sama-sama ga jini duk ya gama
wanke mashi jikinshi, suka d'agoshi suna fad'in "oga lafiya meke faruwa? cikin dusashshiyar murya ya nuna Laraba, yace "ita....itac...itace... Nan kafin yagama fad'a masu yafad'i sumamme.
A harzuke suka nufi Fatima wacce hankalinta yayi masifar tashi d
a ganin halin da mutumin dayayi niyyar yimata fyad'e yake ciki, dan ita bata San meya faru da itaba, tun lokacin da mutumin yanemi ida rabata da kayan jikinta.
Amma me kafin su 'karaso gareta sai ji sukayi an d'aukesu da wasu mahaukatan marurruka, kowa
nensu ya dafe kunci yana duba d'an uwansa, kafin suyi wata magana aka rufesu da duka ta ko'ina, nan suka shiga ihu suna neman taimako, amma ba wanda ke jinsu, dan dama haka gidan yake ihunka banza ne, dan da haka ogansu ke samun damar keta haddin 'ya'yan m
utane batare da anji koda ihunsuba.
Saida suka daku sukayi li'kis sannan aka 'kyalesu,
Fatima kuwa banda kuka ba abinda takeyi, dan ita kanta abin ya tsoratata yabata mamaki dan ganin yanda mutanen keshan jibga batare da su duka sunga me dukan nasu ba
,
Lokacin jikinta yashiga 'kyarma takama kuka tana 'yarfa hannuwa tana kiran innalillahi,
Hanyar guduwa tashiga nema dan tsira da rayuwarta, lokacin idonta yakai kan 'kofa dake bud'e tun lokacinda yaran oga suka shigo dasukaji yana neman taimako.
Bata tsaya d'aukar kayan taba tanufi 'kofar tashiga falon d'akin tari'ka shiga 'kofofi na gidan, tashiga nan tafita nan amma har yanzu Allah besa taga 'kofar da zata sadata da wajen gidan ba, 'karshe ma idan tashiga wata 'kofar sai taga ta 'kara maidota c
ikin gidan.
Haka tayita zagayen gidan, har 'karfe bakwai da kimanin minti sha shidda na safe, lokacinne kuma oga ya farfad'o daga doguwar sumar dayayi, yayi saurin kai dubanshi gurin da laraba take amma be gantaba, cikin tsananin rud'ewa ya kai dubanshi
ga yaranshi dake kwance suma basu san inda kansu yakeba, lokacin ya ta'kar'kara yatashi yakai masu duka, "kutashi kai dan uwarku ku tashi ina yarinyar nan take, a firgice suka kai dubansu ga ko'ina na d'akin basu gantaba.
Cikin d'aga murya oga yake mag
ana, kuyi sauri ku nemomin ita, kada ku kuskura tabar gidannan, da sauri suka tashi suka shiga zagaya gidan suna nemanta, dan sun tambayi me gadi yakuma tabbatar masu da bata fitaba, aiko suna cikin dubawa sukayi kici6is da ita a cikin wani korido, wata 'k
ara ta fasa tayi baya, kafin tayi wani yun'kuri har sun cafkota.
Cikin gidan suka koma da ita, wannan karon wani d'akin suka kaita ba wanda suka fara ajiyeta da farko ba.
Wata igiya suka sa suka d'ad'd'aureta, sannan sukaja 'kofar d'akin sukasa key s
uka kulle.
Banda kuka ba abinda Fatima keyi, wannan karon tariga ta gama sadau'kar da rayuwarta,
Bayan kamar awa d'aya da d'auretane, taji ana murd'a kofar, takai dubanta ga 'kofar dan ganin me shigowa.
Oga ne yashigo cikin shigar ba'ka'ken jack
et da wando sai wani ba'kin 'katon glass dake fuskarshi me suna no respect
😎
.
sai yaranshi guda biyu suma cikin 'kananan kaya suna take mashi baya.
Bakin 'kofa yaran suka tsaya, kowane gefe guda yayinda sukasa 'kofar tsakiya,
Shikum oga ya ida shi
gowa d'akin inda fatima take d'aure yanufa yashiga zagayata yana tafa hannuwa, itakuma sai binshi take da ido duk illahirin jikinta 'kyarma yake,
Wani shu'umin murmushi yayi yace.......
4
⃣
5
⃣
to4
⃣
6
⃣
Very
🔜💃🏻
🖊
Zee Elkaseem
Mmn kh
ady
💋
[10/16, 8:12 PM]
😭
_*ALHINI*_
😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
®```NWA```
_Written by_
_*Zee Mmn khady*_
😘
4
⃣
7
⃣
to4
⃣
8
⃣
🖊
Cigaba yayi da kallonta, sannan yace "A gask
iya na kwad'aitu da kyakkyawar surar da Allah yayimaki, kuma iya tsawon rayuwata ban ta6a d'ora idona kan wata mace ba tabani sha'awa in kyaleta batare dana biya bu'katataba, amma ke sai gashi na kasa aiwatar da kome a kanki.
"Ianso zan miki wasu 'yan t
amaboyoyi yanzu, ki tabbatar da kin bani amsarsu iyakar gaskiyarki, hakan zesa in fiddaki daga gidannan da kaina batare da wani abu yafaru dakeba.
Binshi kawai takeyi da ido, dan ita ahalin yanzu tariga ta sadaukar da rayuwarta, kuma yanzu take danasani
n gudowa datayi daga hannun mutanen dasukayi
mata halacci, yanzu batasan halin da guduwarta ya jefasu cikiba, tabbas ko ba'a fad'aba tasan idan hankalinsu yayi dubu yatashi, ba kamar masoyinta Mukhtar Wanda ya d'auki son duniya ya d'ora mata, a zuciyarta t
ace _(ya Allah ka fitar dani daga hannun wannan mugun mutumin, Allah ka maidani gurin masoyina abin 'kaunata Mukhtar)_.
Wata uwar tsawa ya daka mata, wacce tayi saurin maidota daga duniyar tunanin data afka, yace "miye sunanki?
Jiki na 'kyarma ta kall
eshi idanunta na zubar da hawayen nadama tace
"Sunana Fatima...
Murmushi yayi sannan ya maiamaita sunan fatima koh? Ya'kara tambayarta, ta d'aga Mashi kai alamar eh.
Yayi shuru na kimanin mintuna biyu sannan ya'kara jeho mata wata tambayar,
"Fatima
ke mutum ce ko Aljan?
Tace "ni mutum ce.
"Amma ke matsafiyace,
Jiki na 'kyarma ta girgiza kai tace
"Ni ba matsafiya bace ban ta6a tsafiba.
Shuru yayi na wani d'an lokaci sannan yace "to fatima abinda yafaru jiya miye kikayi idan kince keba Aljana ba
ce, cikin muryar kuka tace "minayi,? Wallahi banyi kome ba.
Cikin takaici ya kalleta yatuno da irin 'karfin data nuna mashi jiya lokacin dayake 'ko'karin yimata fyade, da ciwon data jimashi, yashafa kanshi inda ta dokeshi gurin ya fashe, take wani irin
mugun tsoronta ya dirar mashi a zuciya, ya maida kallonshi gareta yace "yanzu zaki iya gane gida?
Kai kawai ta d'aga mashi alamar "eh badan tasa ran ze maidata gidan ba.
Hannu yasa ya kwanceta daga d'aurin da sukayimata, sannan yace "zaki iya shiga toi
let ki watsa ruwa ki canja kaya ni zan maidaki gidanku da kaina, dan barin irinki suna zuwa hannun masu irin halinmu babban had'arine.
Be jira abunda zata fad'aba yafita daga d'akin yaranshi suka take mashi baya.
Tana ganin yafita jiki na 'kyarma taj
e ta kulle d'akin hada sa key da sakata, sannan tafad'a toilet tahad'a ruwan d'umi tayi wanka, tad'an gasa jikinta dan duk illahirin jikin ciwo yake mata, sannan ta d'auro Alwala tafito tasa kayanta sannan ta d'ora hijab ta kabbara sallah, dan bata manta d
a batayi sallar asuba ba.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Zaune suke jugum-jugum kowanensu yabuga uban tagumi bakajin kome sai sheshekar kukan jidda, dan tunda aka tabbatar da 6atan fatima jidda ke kuka, idanunta sun kumbura ga matsanancin ciw
on kai dake damunta sakamakon kukan datake ba 'ka'k'kautawa.
Mukhtar ma kukan yake kamar mace, kokuma 'karamin yaro, sun tasa hajiya gaba, wacce itama duk illahirin jikinta mace yake, dan ta d'auki fatima kamar 'yar data Haifa da cikinta saboda haka dol
e taji 6atanta har cikin ranta, amma ganin yanda yaranta suka d'aga hankalinsu yasata daurewa tari'ka rarrashinsu.
Suna cikin wannan zaman ne megadi yashigo da sallama, bayan Hajiya ta masa sallamar yace Hajiya sallama ake a waje, cikin damuwa Hajiya ke
tambayarshi "wanene me sallamar, yace "eh to Hajiya gaskiya ban shedashiba amma yace maganace me mahimmaci ke tafe dashi idan da hali yanaso ayimashi iso yashigo,
Hajiya tace "OK shigo dashi.
Bayan fitar me gadi da kamar minti biyar saigashi yashigo,
cikin shigar manyan kaya shaddace jikinsa, light blue, sai hularsa light blue, sai takalmi ba'ki, kallo d'aya zakayimashi ka gane mutum ne wanda naira ta zauna mawa...
Bayan yasamu gu ya zauna yafara magana "ni sunana sadiq kuma ni d'an cikin garinnan
ne, idan bazaku damuba inaso insan yara nawane a gidannan, ma'ana 'ya'ya nawa kuke dasu.....
Wani 'kululun ba'kin ciki ya tsayama mukhtar a wuya, a fusace ya kalli mutumin yace "wannan wane irin rainin wayone zakazo kana mana tamabayar da bata shafekaba
,
Sadiq yabud'e baki zeyi magana kenan sukaji tafiyar mutum ana shigowa gidan, da sauri suka kai dubansu gurin....
Da gudu jidda ta tashi taje ta rungumeta tana kuka, tana cewa "sister ina kika shige kika barmu cikin tashin hankali, fatima kasa furta
kome tayi sai hawaye datake zubarwa, cike da murna da fargaba Hajiya tazo takama hannun Laraba tashigo da ita falon, mukhtar kuwa kasa furta kome yayi, illah bin fatima da yayi da ido.
Maganar Sadiq ce tadawo da hankalinsu gareshi, yayinda yake sanar da
su abinda yafaru tsakaninshi da Fatima, be 6oye masu kome ba ya sanar dasu gaskiyarshi, dan yariga ya tuba daga mummunar d'abi'ar dayake