Showing 9001 words to 12000 words out of 31402 words

Chapter 4 - ALHINI complete.

San daga inda take fitowaba ana cewa,

"Yaro kayi ta barka, ashe kana son rayuwarka, aka sake bushewa da wata d

ariya, sannan sukaji d'if kamar anyi ruwa an d'auke.

Wani matsanauncin tsoro Yakama Laraba dan jin wani sabon Al'amari, da gudu tanufi habu wanda shima jikinsa mazari kawai yake saboda tsananin tsoro tafd'a jikinsa ta 'kan'kameshi.

Cike da tsoro hab

u ya finciketa daga jikinsa, yajata kiiiiii, ya turata waje yace "kije nace nasakeki *Saki ukku* ya maida 'Kofa ya rufe.

Laraba ta shiga bugun 'kyauren gidan, tana cewa "Dan Allah habu ka taimakeni ka barni in kwana gobe sai intafi, haka ta rin'ka magi

ya amma bataji Habu yayi maganaba, hakan yasa ta kalli gabas ta kalli yamma kudu da arewa, ba Alamar haske, garin yayi duhu dind'um bakajin kome sai kukan tsintsaye, take wani mugun tsoro ya dira a zuciyarta.

[24/08 2:38 pm] Zee Elkaseem: Wani irin haske

ta hango daga nesa yana nufo inda take, tin tana kallonsa nesa da ita har yazo gab da ita,

Wani irin matsanancin tsoro ya'kara kamata,

Wata irin 'kara ta fasa sannan ta ranta a na kare

🏃🏻

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Inna na kwance d'ak

i, kan guntuwar tabarmarta sai juyi take bacci ya gagari idonta, ba abinda take sai tinanin kowane hali 'yarta take ciki,

Wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonta, tasa hannu ta goge,

Lokacin kuma taji Uciyarta tayimata nauyi kamar an d'ora mata wani

katon dutse, lokaci guda taji yun'kurin amai, aiko tatashi zaune tafara amai, babban tashin hankalin da inna tagani duk yun'kurin datayi maimakon taga aman abida taci, jini ne take amayowa hadda gundarinsa,

Cikin 'kan-kanin lokaci ta galaibaita tafita

hayyacinta,

Da gudu Laraba tashigo gidan, wata irin 'kara tasaki dan ganin halin da inna take ciki, sauri ta 'karaso gareta, takamata tana kuka tana kiran sunanata, inna....inna...inna... Da 'kyar inna ta iya d'aga ido ta kalleta tace "Laraba nasan taw

a ta 'kare amma bazan gusheba inamaki addu'ar Allah fiddaki daga mawuyacin halin da kike ciki.

Fad'uwa tayi rai yayi halinsa, ```Allahu akbar inna tarigamu gidan gaskiya```

Wata uwar 'kara Laraba tasaki, dan ganin inna ba Alamar numfashi tattare da

ita,

Wani irin duhu taga ya gufta mata, kokacin kuma kanta yayi wata irin sarawa, jiri ya ibeta ta fad'i kasa sumammiya,....

🖊

Zee Elkaseem

Mmn khady

💋

[10/16, 8:10 PM]



😭



*_ALHINI_*

😭

🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇

®```NWA```

_written by_

*_Zee Mmn khady_*

😘

2

⃣

3

⃣

to2

⃣

4

⃣

🖊

washe gari tunda asuba Habu yanufi gidan iyayenshi, yana isa innarshi taganshi da uban rauni a kai, ga jikinshi jage-jage da jini, dan be canja

kayaba haka ya kwana, wani uban salati ta buga tace "Habu lafiya meya faru dakai, ina Larabar,? Lokaci d'aya ta jero mashi wad'annan tambayoyin, Habu bayaso ya fad'i gaskiyar Al'amarin abinda yafaru dashi saboda besan wani halin fad'in ze jefa laraba ba, s

aboda haka shiru yayima innar tashi.

Innar taga bayada niyyar bata amsar tambayoyin datayi mashi, kawai saita d'ora hannu a kai tafashe da kuka, wanda yin hakan ya jawo da hankalin mutanen gidan garesu, duk akayo d'akinta ana tambayarta lafiya meya faru

, dayake gidan irin gidan yawa ne,

Ganin habu dasukayi zaune ga jini duk ya 6ata jikinsa yasa suka ba kansu amsa, tabbass koba tambaya sun san larabace ta tasarma kasheshi Allah beyiba dayake yanada sauran shan ruwa.

Wata mata cikin mutanen dake tsai

-tsaye Bakin 'kofar d'akin tace "ina kabaro amaryar angon Laraba?

cike da takaici habu ya kallesu yace "Laraba na gidansu na saketa,

Wani uban salati matan suka d'auka lokaci guda, sukace "yo habu ya akayi haka tafaru?

Be basu amsaba illah fita da

yayi yabar gidan dan bayaso ana can-cana maganar.

Wata tsohuwar mata ta kalli innar Habu tace "Wallahi atika kinyi ta barka, dan wannan maganin da 'yar me ganye tabada tace ki binne a gidan, amma da badan haka ba da yanzu habu sai dai wani bashiba.

I

nnar habu tayi murmushin takaici tace "Hmmm Wanda beji bari ba ay yaji hoho, cikin gidanan waye be ba Habu shawarar kada ya auri Laraba ba amma yakafe, ay dama me rabon shan duka bayajin kwa6a, bata jiran me sauran matan zasu fad'aba tashige d'aki tana mat

sar kwalla.

Ganin haka yasa kowace takama gabanta, suna fad'in albarkacin bakinsu,

Abinka ga matan 'kauye kad'an suke jira su 'kara, kafin kace me labari ya bud'e gari.

Mutanen gari anata yayatawa, Laraba takusa kashe Habu Allah ya taimakeshi ya sa

keta.

Aiko labari yakaima mal Lawal, a fusace yanufi gidansu Laraba da niyyar yaci masu mutunci itada uwarta wacce ke d'aure mata gindi tana kashe mutane.

Bako sallama ya bankad'a 'kyauren gidan yashiga,

Laraba yagani ta had'a kai da gwiwa tana kuk

a, gefe kuma ga innarta kwance cikin jini.

"Ke.....ya daka mata tsawa, da sauri ta d'ago da fuskarta ta kalleshi, saitaji wata dama-dama a ranta, tunda tariga tasan inna tamutu, kuma batasan wa zata gaya mawaba, tunda mutane yanzu da sun ganta guduwa su

ke.

Da sauri ta taso tazo gabanshi ta dur'kusa, yanzu kam idonta ba hawaye ko kad'an dan tayi kuka har hawayenta sun 'kafe, tace "dan Allah baffa Lawal ka taimakeni inna ta mutu, tun jiya da dare, ban san yazanyiba, shiyasa ban fitaba dan nasan duk ind

a na nufa ba wanda ze saurareni,

Wata irin dariya mal Lawal yayi sannan ya kalli Laraba yace, "watako maitar taki har takai ga uwar data haifeki, to wallahi ki shiga hankalinki, danni idan kikace zaki cinyeni sai inci ubanki, 'yar iska kawai, yakai mat

a wani hauri har saida ta fad'i, sannan yafita yabar gidan.

Zuwa yayi yasanar da mutane, innar Laraba ta mutu, amma kowa sai yace Allah ji'kanta, da ance suzo ayimata sutura akaita makwancinta sai kaga mutum yafara zame-zame Alamar dai baya zuwa.

Hak

a akayita fama da muatanen Gari, karshe dai saida me gari yasa Baki, yasa liman da wasu tsirarun mutane akaje akayima innar

Laraba wanka akayimata sutura aka kaita makwancinta,

Kuka kau Laraba yanzu ta daina na hawaye, sai dai na zuci, dan zuciyarta t

ariga tagama soyewa, tasaba da ba'kin ciki da takaici.



*_BAYAN KWANA BAKWAI_*

Yanzu Laraba ita kad'ai ke kwana gidansu babu me ra6arta, ga yunwa dan ba wanda kebata koda sauran abinci, idan kuma tafita dan tasiyo abinda zataci dataje shago sai

muatane sukama gudu, haka zata dawo gida takama kuka, abin dai gwanin ban tausayi, duk ta rame ta kod'e idanun nan sun kara fitowa sunyi zuru-zuru, ga wani ciwon ciki datake fama dashi sakamakon yunwar datake fama da ita,

Ruwa kawai take banka ma cikin

ta koda yaushe, to yanzu ma idan tasha ruwan sai ya 'kulle mata ciki tayita amai,

Yau dai tagaji da bala'in datake ciki, saboda haka tayi niyyar zuwa gidan baffa Lawal dan ya taimaka mata.

🖊

Zee Elkaseem

Mmn khady

💋

[10/16, 8:11 PM]



😭

*_ALHINI_*

😭

🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇

®```NWA```

_written by_

*_Zee Mmn khady_*

😘

2

⃣

5

⃣

to2

⃣

6

⃣

🖊

Baffa Lawal ne cikin gonarshi yanata noma, yanayi yana 'yar wa'ka irin ta

mutanen 'kauye, abin yayi masa dad'i har gyad'a kai yakeyi, zuwa can kuma sai yatashi yanufi inda ya ajiye kayansa ya fiddo da wata 'yar madai-daiciyar radio, yasanya sabbin batura ya 'kunna, ya kuwa yi sa'a gidan redio an sanyo wa'kar d'an kwairo, aiko s

ai ya rataye redion jikin bedi yana ji yana aikinsa,

Befi minti shidda da kunna red'ion ba sai yaji d'if redion ta d'auke, ya d'ago kansa ya duba bega kowaba, yaje ya ta6a redion sai yaji kashe take, nan ya sake kunnawa ya maida yarataye ya juya ze cig

aba da aykinsa sai yaji an 'kara kashewa, yana juyowa wa ze gani,

Laraba ce tsaye jikin bedin tana yimashi wani mugun kallo,

Cike da masifa da bala'i baffa Lawal ya tunkarota na niyyar ya wanka mata mari, amma kafin yayi wani Abu sai jin saukar mari y

ayi, a fuskar shi.

Cike da tsoro yakai dubansa ga Laraba, wacce tana dai tsaye inda take ko motsi batayiba, wani wawan mari aka 'kara d'aukeshi dashi, lokaci guda kuma aka rufeshi da duka ta ko'ina, Laraba dai na tsaye har yanzu bata motsa ba,

Haka

akayita jibgar mal Lawal saida ya daku sannan aka 'kyaleshi, wata irin mahaukaciyar dariya Laraba ta she'ke da it'a sannan ta 6ace, mal Lawal yashiga rud'ani, hankalinsa yayi matu'kar tashi, jikinsa yakama 6ari, aiko da sauri ya tattare 'yan kayanshi yanuf

i gida,

Ganin ya shigo hajaran-majaran yasa matarshi tamabyarshi, "mal lafiya, meya faru naga ka dawo tun 'yanzu gashi ko azahar batayiba,

Mal Lawal bayaso yafad'i gaskiyar Al'amari dan kada mutane suyi Mashi dariya, sai cewa yayi "gajiya nayi kuma j

ikina ba dad'i d'an dafamin ruwan d'umi inyi wanka, cike da mamaki matar tace "ruwan dumi kuma malam

🤔

, kaida idan kadawo daga gona kake son ka watsa ruwan sanyi amma yau ruwan d'umi kake nema,

Aiko nan yarufeta da bala'i "keni banison shashanci, Idan

zaki dafamin ki dafamin, idan kuma bazaki dafaba ni in tashi in dafa da kai.........

Be ida rufe bakiba, Laraba tashigo gidan da sallama, mal Lawal naganinta jikinsa yafara kyarma, yace "la......la....la...raba miya kawoki nan? Ba yanzu kikaje gona kik

a sameni,

Cike da ladabi Laraba ta dur'kusa har 'kasa tace "wallahi baffa banje gonarkaba, ni yanzuma daga gida nake, dan Allah baffa ka taimakamin da abinci yunwa nakeji,

Cike da tsoro baffa Lawal yace "bamu dafa ba, ki koma idan mun dafa zan kawo

maki har gida, jiki ba 'kwari Laraba tanufi hanyar fita daga gidan, matar baffa Lawal ce taji wani irin tausayinta yakamata, ta kirata taje d'akinta ta d'auko mata wata tsantsamar fura tace anshi kisha ko wannan ce kafin ayi abincin akawo maki, jiki na 'ky

arma Laraba ta kar6a ta kafa kai ta shanye sannan ta ajiye

kwaryar tace "nagode, sannan tabar gidan zuciyarta cunkushe da ba'kin ciki da takaici.

Laraba kuwa daga gidan baffa lawal maimakin tayi hanyar gida saita yanki hanya tayita tafiya cikin daji, s

aida tayi nisa da Gari, wani wawakeken rami ta iske gabanta, nan ta tsaya tana kallon fad'in ramin da zurfinsa, take wasu zafafan hawaye suka wankemata fuska, a fili ta furta "'kara in mutu da rayuwar ba'kin cikin danake ciki, lokacin kuma taji kanta ya sa

ra,idanunta sun rufe, bata ganin kome, nan ta fad'i war-was gata gab da ramin, dan motsi kad"an zatayi ta ida afkawa ciki.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Tafiya yake cikin had'ad'd'iyar motarshi 'kirar Camry mai ruwan sumunti, tu'ki yake ciki

n kwanciyar hankali, cikin motar kuwa ba abunda ke tashi sai sanyin a,c daya had'e da kamshin freshener, sai kuma 'kirar'ar sheik Abdurrahama sudais dake tashi,

Tafiya yake amma zuciyarshi na raya mashi abubuwa da dama, game da 'kauyen kwata-kwata babu

titi ko d'aya sai dai mutum yayita bi cikin jar 'kasa da burji,

Kamar ance yakai dubansa gurin, lnnalillahi yafad'a yayin da ya hango mutum kwance 'kasa, gab da wani wawakeken rami, da sauri yayi fakin din motarshi yafito, addu'a yafarayi kafin yakai

hannunshi gareta, saida ya tabbatar da sauran numfashi jikinta sannan ya kinkimeta ya sata bayan motar shi,

Juya akalar motar yayi yakama hanyar komawa cikin gari, tafiyar awa ukku ta dadashi da garinshi, asibiti ya wuce kai tsaye, da sauri aka amshi L

araba aka shiga wani d'aki da ita domin duba lafiyarta.

Awon farko aka gano yunwace ke neman halaka ta, nan aka d'aura mata drip, sannan akayimata Allaurai, bata farka ba amma likitan ya tabbatar mashi da lafiya lau babu wata matsala zata iya tashi koda

wane lokaci, saboda haka asamo mata abinda zataci, dan tana tattare da yunwa kuma tana bu'katar abinci mai kyau.

🖊

Zee Elkaseem

Mmn khady

💋

[10/16, 8:11 PM]



😭

*_ALHINI_*

😭

🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇

®```NWA```

_written by_

*_Zee Mmn khady_*

😘

2

⃣

7

⃣

to2

⃣

8

⃣

🖊

Motarshi yanufa a zuciyarshi yana tausayama halin da yarinyar take ciki, mintina da basu wuce sha ukku ba suka sadashi da gidan iyayenshi, wani 'katon gid

a ne had'adden gaske, bakin get yayi horn me gadi ya bud'e mashi get yashiga da motarshi, gurin ajiye motoci ya ajiye motarshi, motocine gurin kusan guda shidda, sai lokacin nagane ashe wacce naganshi ciki batada kyau, dan manya- manyan moticine masu tsada

r gaake ajiye gurin, wannan yafita da itane dan yasan yanayin garin da zaya.

Hanyar da zata sadashi da ainafin cikin gidan yanufa, kai tsaye falon hajiyarsa yanufa.

Wata dattijuwar mata ce zaune cikin falon, cikin shiga ta Alfarma, idonta sanye cikin

wani siririn farin glass, wanda da alama medical ne, hannunta ru'ke da Al Qur'anic, tana nazari, gefe kuma wata 'kya'kyawar yarinyace wacce bata wuce shekara sha biyarba, ita kuma ta maida hankalinta gun kallon TV, tashar sunnah tv take kallo.

Sallamar

yayan nata yasa tayi saurin kai dubanta gareshi tare da amsa sallamar, tace "lah Yaya Mukhtar, ya akayi ka dawo yanzu, ko baka kai da tafiya bane, yace "naje mana, amma ban kai ga isaba wata 'yar matsala ta maidoni, tace matsala kuma Yaya, Tame?

"To t

ambai, wannan tamaboyoyi haka, kamar wata 'yar jarida, tace "hm Yaya Mukhtar ai ko banzama 'yar jaridaba kasan abinda nake burin zama,

Yasan kullum burinta be wuce na tazama lawyer ba, murmushi yayi yace "Allah taimaka, inaso ki shiga kitchen keda Uwani

me aiki ku dafamin abinci, jallouf d'in wake da shinkafa zakiyi, ayi amfani da hanta gurin girkin, dan bani bu'katar wani kalan nama, sannan a dafamin ruwan zafi ahad'a kayan tea,

zatayi magana yayi saurin tarbarata "banison tambaya kiyi sauri ina jira

nki yanzu, haka Jidda tanufi kitchen a zuciyarta tana tinanin me Yaya zayayi da abinci yanzu kuma harda kayan tea.

Sai da yagama da Jidda sannan yanufi inda mahaifiyarsa take, wacce duk abinda suke shida Jidda tana jinsu, itama zuciyarta cike take da ta

mbayoyi da dama gareshi.

Cike da ladabi ya isa gurin hajiyar tashi, yasamu guri ya zaune kusa da 'kafafunta, yace "Hajiya barka da hutawa, cike da fara'a ta kalleshi tare da rufe Qur'anic dake hannunta tace "yauwa, kafin tayi wata magana yace "nasan zak

iyi mamakin ganina yanzu, wata yar matsalace ta maidoni, nan ya kwashe yanda ya tsinci

Laraba ya gaya mata, take tausayin yarinyar yakamata, kuma tayi alwashin taimakamata.

Saida sukayi sallar magrib sannan suka nufi asibiti, Mukhtar ne ke driving, sai

Jidda dake zaune gefensa duk ta isheshi da surutu, sai Uwani me aike dake bayan motar,

Jidda ta kalli yayan nata tace, wallahi yaya har na 'kagara inga yarinyar nan, wallahi ta matu'kar bani tausayi, ko ina iyayenta suka barta, har yunwa na neman halak

ata, kai wallahi mutanen 'kauye basuda hankali, wai sai mutum yayi zaune da yunwa har sai tayi mashi lahani,

Mukhtar dai jinta kawai yake tanata zuba, be cemata uffan ba har suka iso asibitin,

Parking d'in motarsa yayi inda aka tanada dan ajiye motoc

i sannan suka nufi cikin asibitin uwani na d'auke da kwandon da aka jero kayan abincin ciki.

Sun shiga d'akin da Laraba take, zaune suka isketa, tayi zuru da alama tafad'a kogin tinani, saida sukayi mata sallama sannan ta dawo hayyacinta, binsu kawai ta

yi da kallo dan su duka ba wanda tasani, jidda ce tafara magana, tace "Yaya wannan itace yarinyar daka tsinta d'in, kai Amma ky'k'kyawa da ita, amma gaskiya mutanen 'kauye basuda wayo da har sukayi sakaci da wannan 'kya'k'kyawar yarinyar... Wata uwar harar

a yayan nata ya daka mata, hakan yasa tayi saurin jan bakinta tayi shuru,

Sannan ya maida kallonshi ga uwani yace "Uwani gatanan ki bata abincin, Uwani da tunda suka shigo take kallon Laraba, tana yaba irin kyawun da Allah ya zuba mata, tace "to amma y

akamata ta d'an watsa ruwa taji dad'i kafin taci wani abu, sai dai kuma babu kayan da zata canja idan tayi wanakan, jidda tayi saurin cewa "yaya muje gida in d'auko mata cikin kayana, Mukhtar ya gyad'a kai yace barshi kawai bari inje in siyo mata, ya kalli

uwani yace a taimaka mata tayi wankan kafin indawo, sannan yafice daga d'akin.

Bayan fitarshi uwani tahad'ama Laraba ruwan d'umi ta kaita kewaye, ta gwada mata yanda zatayi, dayake Laraba yarinyace mai nutsuwa batayi wani karanbani ba, yanda aka gwada

mata haka tayi, ta dade tana wanke jikinta da sabulu mai 'kamshi, wanda rabon datayi wanka da ruwa ma har ta manta, sai da ta tabbatar da tayi fess sannan tafito daga kewayen.

Bata dade da fitowaba mukhatar yashigo da wata 'katuwar Leda a hannunsa, ya m

i'kama Uwani, sannan yafita daga d'akin yabasu guri dan suji dad'in aiwatar da kome.

Jidda ce tayi saurin zazzage kayan tana dubawa, kayane kusan kala takwas duk na kanti, wasu riga da siket wasu kuma dogayen riguna,

Wata doguwar riga jidda ta d'auko,

kalar sararin samaniya daga gaban rigar anyi mata kwalliya da duwatsu dark blue tace wannan zaki sanya, Laraba dai binsu kawai take da ido, dan ita har yanzu batasan a ina take ba, ba musu ta 'kar6i rigar ta sanya sannan jidda ta d'aura mata d'an kwalin r

igar, wani irin kyau tayi duk da ba wata kwalliya bace a fuskarta, jidda kasa yin shiru tayi tace "kinga

yanda kikayi kyau, wai miye ma sunanki, sai lokacin karaba ta iya bud'a Bak tace "sunana Laraba, jidda tayi murmushi tace wallahi na d'auka larabci zan

ji kinyi, dan kwata-kwata kinfi kama da jinsin larabawa, to amma miye asalin sunanki dan Laraba ba suna bane...

Mukhatar ne yashigo da sallama, yakai dubansa ga Laraba, wani dum

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login