Showing 15001 words to 18000 words out of 31402 words
San Matsala ta bazasu kuma zama daniba_.
Hajiyace ta maidota daga dogon tinanin datake, tace "Laraba, laraba ta d'ago fuskarta ta kalli Hajiya, sannan t sadda
kanta 'kasa tana kallon kafet d'in dake malale tsakiyar falon.
Hajiya tacigaba da magana "kamar yanda kika Sani mun taimakeki kuma Alhmdulillahi kin samu lafiya kin warware, kuma nasan bazaki rasa sanin inda 'yan,uwanki da iyayenki sukeba, saboda haka
inaso ki sanar damu ke wacece? Kuma miye ya jefaki cikin mawuyacin halin da shi mukhtar ya tsinceki a ciki?
Saboda munaso mu maidake gurin iyayenki.
Shiru Laraba tayi takasa ko motsi dan jin tambayoyin da hajiyar ta jero mata lokaci guda, wasu zafaf
an hawaye suka zubo daga idanunta, batada niyyar d'ago fuskarta, saida Hajiya tayi mata magana karo na biyu tace "laraba ke muke sauraro.
Laraba ta d'ago da fuskarta wacce tayi sharkaf da hawaye, ganin haka yasa hankulansu tashi su duka, cike da damuwa
jidda ke rarrashin Laraba tasa hannu tana goge mata hawaye "kiyi ha'kuri 'kawata ki gayama Hajiya abinda ta tambayeki, ni nasan hajiyata mai tausayice zata taimaka maki a kan abinda kike Neman taimako, inshaAllahu.
Haka jidda tayita rarrashinta da kalam
ai masu taushi, hartayi shuru sannan ta goge hawayenta tafara basu Labarinta, kamar haka:
_*Sunana Fatima amma amfi kirana da laraba kamar yanda kuka Sani, mahaifiyata yar Asalin 'kasar camaron ce, sun h'ad'u da babana ne lokacin yana zuwa fatauci
can 'kasar.*_
_*Mahaifina kuma d'an nan cikin garin karsina ne a wani 'kauye dake 'karamar hukumar malumfashi me suna 'kurungafa' Allah yayima mahaifina rasuwa tin ina 'yar shekara ukku a duniya, kamar yanda naji mahaifiyata tana fad'a,*_
_*Haka yasa
muka taso cikin wahala nida mahaifiyata, kasancewar batada kowa a nan 'kasar shikuma babana su biyu ne gurin iyayensu daga shi sai 'kaninsa baffa Lawal, baffa Lawal mutum ne wanda bashida taisayi ko kad'an hakan yasa baya taimaka mamu da koda ruwan sha,*_
_*Haka mukacigaba da rayuwa nida mahaifiyata, yau da dad'i gobe babu har nakai shekara shidda lokacin kuma mahaifiyata tasakani makarantar bokon dake 'kauyenmu, bayan na kammala aji shidda ne samarin 'kauyen sukayo ca Kowa nason Neman aurena, lokacin i
nada shekaru sha ukku a duniya*_
_*An tsaida wani saurayi matsayin wanda baffa lawal ya amince dashi, dan baffa Lawal Isa da ta'kama ba wanda bayayi mamu amma kuma idan neman taimakone sai ya nuna be sanmu ba, ana gab da bikinane Allah yayima mahaifiyat
a rasuwa, Al'amarin daya sakani cikin mayuwacin hali, dan bayan rasuwarta da sati biyu saurayin dazan aura ya aiko a maida mashi duk wani abu daya kawo gidanmu yafasa aurena, nan fa tashin hankalina ya 'karu.*_
_*Baffa Lawal da kanshi yazo har gida yaci
mani mutunci, yana cewa ai nasan abinda nayimashi yace yafasa aurena, saboda haka tsinke baze barmin ba cikin kayan da yaron ya kawo, inaji ina gani ya tattare kome yasa kai yabar gidan, haka na zauna na had'e kai da gwiwa ina kuka ni 'kad'ai cikin gida ba
bu me rarrashina, dan dama tunda mahaifiyata ta mutu yazamana ni d'aya ke kwana gidan, tun ina jin tsoro har zuciyata ta saba*_
*_Ban fuskanci babbar matsalaba sai da na wayi gari banida abinda zanci, yunwa tayimani mugun kamu wanda har wani matsanancin
ciwon ciki ya kamani, hakan yasa na lalla6a naje gidan baffa Lawal ko ze taimakamin amma sai yayimin korar kare, lokacinne na 'kudiri niyyar kashe kaina ta hanyar fad'awa wani 'katon rami dake nesa kad'an da 'kauyenmu, dan lokacin na 'kwammace mutuwa da h
alin da nike ciki, ga ba'kin cikin rayuwa ga ALHININ rabo da iyayena....._*
Wannna shine labarina, laraba ta fad'a tana goge hawaye,
Jidda ma kuka take saboda tusayin larabar, "Lallai laraba kinsha gwagwarmaya, Allah Sarki, ta fad'a tana sharar kwal
la.
3
โฃ
7
โฃ
to3
โฃ
8
โฃ
very
๐๐๐ป
๐
Zee Elkaseem
Mmn khady
๐
[10/16, 8:11 PM]
๐ญ
*_ALHINI_*
๐ญ
๐๐๐๐๐๐๐๐๐
ยฎ```NWA```
_written by_
*_Zee Mmn khady_*
๐
3
โฃ
7
โฃ
to3
โฃ
8
โฃ
๐
Haka jidda takama hannun Laraba suka wuce d'aki, tashiga rarrashinta "kiyi ha'kuri Laraba ki d'auki rayuwar da kikayi a baya amtsayin jarabawa, kuma kiri'ka yima iyayenki Addu'a Allah kai haske kabarinsu, kuma ina me tabbatar maki ba
zamu gujekiba, zaki zauna damu har 'karshen rayuwarki inshaAllah, Laraba tasa hannu ta goge hawayen dasuka zubo a kumatunta tace "ko yanzu nabar gidannan nasan kunyi min hallacin da 'kanin mahaifina yakasa yimin wanda shi kad'ai yarage a dangina, nagode Al
lah saka maku da Alkhairi.
Jidda tace ba kome laraba ki d'aukeni a matsayin 'yar'uwarki Hajiya kuma a matsayin mahaifiyarki Yaya mukhtar kuma a matsayin yayanki, inshaAllah bazaki 'kara fuskantar Matsala a rayuwarki ba.
Haka jidda tayita rarrashin La
raba har zuciyarta tayi sanyi, ta goge hawayenta,
Nan jidda tacigaba da bata labarai kala-kala tun tana jinta kawai harta biye mata ta saki jiki tana dariya kamar ba itaba.
A falo kuwa Hajiya ta kalli mukhtar jiki a sanyaye tace "kaji abinda yarinyar
nan tafad'a ya ka gani, Mukhtar Wanda shima duk illahirin jikinsa yayi sanyi dan jin labarin Laraba, yace Hajiya kawai abinda ya kamata shine mu ri'keta ta zauna gurinmu muga abinda Allah zeyi.
Hajiya tace hakane, zatacigaba da zama gurinmu kuma zaka s
amo mata form a islamiyyar su jidda suri'ka zuwa tare.
Sannan idan su jidda zasuyi Exam ayi 'ko'kari asakata ciki, tafara daga s.s.1 tunda kaga yanzu takai kimanin shekaru sha hud'u baze yiyu asata j.s one ba tayi girma, sai asamo Wanda zeri'ka mata les
son a gida kafin sufara karatun.
Cike da jin dad'i mukhtar ya amsa ma Hajiya, zuciyarshi cike da farin ciki, dan ko kad'an dama bayaso ayi maganar maida Laraba garinsu.
Jidda Kuwa dataji hukuncin da Hajiya ta yanke na zaman Laraba gidansu murna tash
igayi hada tsalle.
Laraba kuwa cikin ranta tana tsoron ranar da zasu gane gaskiyar labarinta data 6oye masu, dan tasan muddin suka gane to zasuyimata korar kare.
_```BAYAN SHEKARA UKKU```_
Wasu kyawawan yan mata na hango su biyu tsaye bakin titi
kusa da school d'insu sanye suke cikin uniform d'insu rigar chek pink, sai wando brown, sai 'yar karamar abayar da bata ko rufe hannuwansu ba, kafafunsu sanye cikin brown sandals sai farar safa computer, sunyi kyau sosai kamar 'ya'yan larabawa.
Wata ba
'kar mota 'kirar 4matic tayi parking gabansu, sannan matashin dake cikin motar ya sauke glass d'in motar yakai dubansa ga 'yan matan, da gudu 'yan matan wad'anda basu wuce shekara sha bakwai ba suka nufi motar suka shige, kowace baki ya'ki rufewa saboda fa
rin ciki.
Sun fara tafiya a motar jidda dake gaba, kusa da yayan nata ta juyo ta kalli Laraba ta kashe mata ido, murmushi kawai Laraba tayi mata dan tasan jidda da surutun tsiya, yanzu haka akwai abida takeson fad'a...
Bata gama tunanin datakeba, ta
tsinkayi muryar jidda tana cewa "Yaya bakayi mana congratution ba yau munyi graduated, ya juyo ya kalleta yace tun nan a mota zanmiki congrat d'in, to ke bari inyimaki amma Fatimana sai munje gida zan mata, yafad'a yana kallon Laraba yakashe mata ido, ita
ko wata irin kunya ke kamata idan yakirata fatimarsa, jidda kuwa cewa tayi eh na yarda ayimin anan, ya juyo ya kalleta yace "lna tayaki murna 'kanwata, yanzu saura musha biki keda Usman, cike da jin kunya jidda tarufe idonta, daga lokacin bata 'kara magana
ba, dan wata irin kunyace takamata, Usman shine saurayin datake masifar so kuma shine Wanda zata aura, dan maganar harta kai ga iyaye, dama makaranta kawai ake jira ta kammala.
Laraba kuwa na kula da ita, saboda haka tari'ka kallonta ta madubin motar t
ana mata dariya
๐
itakuma girgiza kai tayi, Alamar zasu had'e........
Haka suka Isa gida cike da farin ciki, bakin get sukayi horn megadi yabud'e masu get suka shige, sukayi parking, da gudu suka nufi cikin gida suna kiran Hajiya,
Hajiya na bedroo
m tajiyo haniyarsu da sauri tafito tana masu sannu da zuwa, nan suka zauna anata labarin makaranta, Hajiya tayimasu congrat, sukaji dad'i har cikin ransu.
Sai lokacin mukhtar yashigo fuskarshi d'auke da fara'a yasamu guri ya zauna, lokacin kuma Hajiya t
akoma d'akinta dan cigaba da aikin datake,
Tasowa yayi yazo gaban laraba, ya du'ko inda take zaune har numfashinsu na gauraya dana juna, hannu yasa aljihu yaciro wata had'ad'iyar waya mai kyan gaske, kirar tecno Hยณ yami'ka mata, tare da cewa *"Congrat
ulation on your graduation Fatima na* cike da jin kunya ta amsa tace *Thank you very much, My Brother*.
Duk abinnan jidda na zaune tana kallonsu, a zuciyarta tagama yarda yayanta son laraba yakeyi.
juyawa yayi yanufi hanyar barin falon, da sauri jid
da dake zaune tana jiran ami'ko mata tata wayar tayi saurin kamo hannunshi, cikin shagwa6a tace "Yaya nifa, cike da zaulaya yace "kikace iyimaki murna tun a mota, kuma nayi maki.
Cikin shagwa6a tace ay ba cewa nayi kada kabani phone ba, dariya yayi sann
an ya fiddo wayar itama ya mi'ka mata iri d'aya data Laraba.
Da gudu tanufi inda laraba take tana tsalle,......
3
โฃ
9
โฃ
to4
โฃ
0
โฃ
Very
๐
๐๐ป
๐
Zee Elkaseem
Mmn khady
๐
[10/16, 8:11 PM]
๐ญ
*_ALHINI_*
๐ญ
๐๐๐๐๐๐๐๐๐
ยฎ```NWA```
_written by_
*_Zee Mmn khady_*
๐
3
โฃ
9
โฃ
to4
โฃ
0
โฃ
๐
maganar Auren jidda da Usman d'inta ta kankama, dan har ansa ranar biki wata hud'u, jidda kuwa dad'i har cikin zuciyarta, amma
takaicinta d'aya yanda Laraba bata kula maza ko kad'an, dan akwai wani abokin Usman daya nuna yana sonta kamar zeyi zauci amma ta bad'e ido toka ta nuna ita bata soyayya, tome hakan ke nufi? Amma ko badad'e ay dole tayi aure tunda tsarin gidansu ne mace b
ata wucewa gaba da karatu daga secondry, barantana tace karatun tasa gaba.
_```Bayan kwana biyu```_
Yaune Hajiya ta tara 'ya'yan nata tana masu magana, kamar haka "Alhmdlh ke jidda banda ke cikin wannan fad'an da zanyi, ta maida kallonta ga Laraba ta
ce "Fatima saboda me bakison ki fidda miji kiyi aure? Bata jira abinda laraba zata fad'aba tacigaba da magana "ita mace duk yanda take jin dad'i gidan iyayenta to gidan mijinta yafishi, kome duk Kyan mace da dukiyarta ko mulkinta darajarta shine d'akin mij
inta.
Haka Hajiya taketayi masu nasiha, suduka sunyi kasa'ke suna sauraronta, shikuwa mukhtar tsoro yake acikin zuciyarshi kada Fatimarsa tafad'i wani namiji tace shine wanda ta tsaida a matsayin miji, bayan shekarun daya d'auka yana fama da dakon soyar
yyarta a zuciyarsa.
Hajiya tayi gyaran murya tacigaba da cewa "kodayake ga yayanku nan shima tun yaushe nake fama dashi akan ya fiddo mata yayi aure amma yayi biris da maganar, amma 'kila so yake insamo wata koda 'yar Almajirace in had'ashi da ita, jidd
a ta kyalkyale da dariya, tace "kai Hajiya Yaya yafi 'karfin Almajira, itama hajiyar dariya take tace to kada ya fiddo matar kusha mamaki daga ke har shi,
Sai lokacin mukhatar ya d'ago da idonshi wanda suka kad'a zuwa ja, ya kalli hajiyarshi cike da ji
n kunya yace "Hajiya ayni na dad'e da samun matar da zan aura, sai kuma ya sadda kanshi 'kasa yana shafa kanshi da Alamar kunya tattare dashi, Hajiya tace "uhum ina saurarenka wace mai sa'ar ce wannan, shiru yayi yakasa furta kome.
Jidda tace Allah Haji
ya nasan ko wacece, Hajiya ta harareta "ke banison shirme ina sauraronka, "dama...hm..dama ba wata bace sai Fatima, cike da jin kunya yake maganar.
Jidda tace dama nasan wlh Hajiya Yaya ya dad'e yana son Laraba, Hajiya tace "to uwar surutu wai waya sany
o bakinki cikin maganar nan, tayi saurin sa hannu tarufe bakinta
๐
.
Cike da farin ciki fuskarta kuma d'auke da fara'a tace kai amma naji dad'in wannan abu, ta kalli laraba wacce tunda mukhatar ya furta Kalmar so gareta duk illahirin jikinta kyarma yake
.
Haka Hajiya tagama dasu ta sallamesu, tawuce d'akinta, Shima Mukhtar d'akinsa ya wuce zuciyarshi cike da farin ciki.
6angaren laraba kuwa tun lokacin da Mukhtar ya furta Kalmar so gareta tayi sukuku, kamar marar lafiya, jidda na kula da halin da
take ciki takan tambayeta ko lafiya, sai ta 'ka'karo murmushin 'karfin hali tace mata ba kome, itakuma jidda sai tacigaba da tsokanarta tana cewa amaryar yayanmu, Laraba sai dai tayimata murmushi amma ita kad'ai tasan abinda takeji a zuciyarta, dama ranar
data dad'e tana gudun zuwanta kenan, dan dama ta dad'e da lura da take-taken mukhtar na sonta, amma ba kome dole ta samarma kanta mafita, bawai son mukhtar ne batayiba, dan ko itace ta d'aurema butulci gindi a duniya bekamata tace bata son mukhtar ba, mats
alarta d'aya shine abinda yabarota daga 'kauyensu, mutum nawa suka mutu dalilin aurenta, tabbas tasan idan mukhtar yadage akan aurenta shima 'karshen rayuwarsa yazo, wasu irin hawaye masu rad'd'i suka zubo daga idonta tasa hannu ta goge, duk abinnan bata y
arda ta nuna damuwarta fili dan kada mutanen gidan su gane.
_```Bayan wata d'aya```_
Soyayya me 'karfi ta 'kulle tsakanin mukhatar da Laraba, wacce a yanzu ta canja suna takoma sunanta na Asali wato *Fatima*
Ranar ne kuma Hajiya takira Laraba tac
e mata, yakamata ki bada address d'in baffa Lawal saboda za'a tura magabatan mukhatar suje neman aure.
Laraba cike da damuwa da far gaba tace "Hajiya kibari da safe zan bada yanzu kaina yana min ciwo, Hajiya ta tausaya mata tace "eyyah Allah sauwa'ke to
kisha magani kafin ki kwanta kinji, tace "to, sannan tanufi d'akinsu zuciyarta cike da tunani kala-kala, *gaskiya bekamata ta sakama mutanen nan da sharri ba, yanda suka d'auketa amatsayin 'ya suka ri'keta suka nema mata gata wanda ko a mafarki batayi tun
anin samun irinsaba, gaskiya dole tasamoma kanta mafita*
Haka ta isa d'akin ta iske jidda tana chat da Usman d'inta tana dariya ita kad'ai kamar mahaukaciya, laraba ta kalleta batayimata magana ba ta haye gadon tayi kwanciyarta.
Jidda ta kaimata duka
, "ke yau baki chat da yayana, nasan yana online yana jiran zuwanki, Fatima tayi wani d'an guntun tsaki ta 'kara gyara kwanciyarta tace "kaina ne yakemin ciwo nasha magani bacci zanyi, cike da tausayawa jidda ta dafa kanta tace "Allah sauwa'ke, itama sai t
aji chat d'in yafita ranta haka sukayi sallama da Usman yanata magiyar kada ta tafi ta barshi, tace "kayi ha'kuri sister d'inace ba lafiya bazanji dad'in yin chat d'ina, yace "Allah sauwake sukayi sallama.
Itama jidda kwanciya tayi bayan tayi addu'a tas
hafe jikinta, sannan tayima Fatima addu'ar dan ta lura da lokacin data kwanta batayi addu'ar ba.
Duk abinnan Laraba na jinta dan ba bacci tayiba, tunanine kala-kala cikin zuciyarta.
Jidda bata dad'e da kwanciyaba bacci yayi awon gaba da ita, haka lar
aba tayita juyi kan gado bacci ya gagari idanunta, wayarta ta d'auko ta duba 'karfe 1:58 am na dare, a zuciyarta tace yanzu ne yakamata in samoma kaina mafita, dan muddin nasan idan nabari mutanen nan sukaje 'kauyenmu sunan dana 6oye masu nawa na *mayya* z
ai bayyana.
Saboda haka ahnakali ta tashi cikin sand'a ta d'auko site bag d'inta ta bud'e wadrope ta d'auki kaya kala 2 sannan ta cire rigar baccin jikinta ta Sanya wata doguwar riga ta atamfa sannan tasa wando legis daga ciki, sannan ta Sanya wata 'yar
'karamar hijab, ta d'au takalminta a hannu, ta lalla6a tayi sa'ar barin gidan batare da Kowa ya gantaba kokuma yaji motsinta.
Bakin titi ta tsaya ta 'karema unguwar kallo bakajin kome sai kukan maguna da karnuka, da tsintsaye, haka ta yanki hanya tacig
aba ta tafiya, zuciyarta cike da tsoro.......
4
โฃ
1
โฃ
to4
โฃ
2
โฃ
Very
๐๐๐ป
๐
Zee Elkaseem
Mmn khady
๐
[10/16, 8:11 PM]
๐ญ
*_ALHINI_*
๐ญ
๐๐๐๐๐๐๐๐๐
ยฎ```NWA```
_written by_
*_Zee Mmn khady_*
๐
4
โฃ
1
โฃ
to4
โฃ
2
โฃ
๐
Tafiya take batare da tasan inda zata dosa ba, ta d'anyi nisa kad'an da gidan zuciyarta cike da tsoro, sai tajiyo Alamar tafiyar mutane bayanta suna tafiya suna magan-ganu wanda bata iya jiyo
abinda suke cewa, saboda suna d'an nesa kad'an da ita, hakan yasa zuciyarta kara tsorata, tayi maza ta 'kara sauri cikin sa'a tayi karo da wani gida da aka fara ginawa amma ba'a karasaba, aiko tayi saurin shigewa ciki dan ta 6uya, da sauri ta shige wani gu
ri a cikin gidan wanda da Alama d'aki ne amma ba'a karasaba dan ko rufi ba'ayiba, gidan dai kamar kango ne dan duk illahirin gidan ba 'kofar da aka sanyama 'kyaure, sai uwayen karikitai da Shara a cikinsa.
Tana cikin kangon gidan data 6uya 'kirjinta na
dukan taraยฒ, sai ji tayi wad'annan mutanen data 6uya dominsu sun iso gurin, jitayi sun tsaya bakin 'kofar kangon gidan data 6uya suna magana, muryar guda taji yace "gaskiya nifa na gaji da abinda mutuminnan yake samu muna aykatawa, kawai hakanan yasa muri'
ka kawo mashi 'ya'yan mutane yana 6ata Masu rayuwa.
Gudan yayi dariya, cikin wata muguwar murya marar dad'in sauraro yace "nikam bazan ta6a barin wannan sana'ar danikeba, dan in baccin ita ina zamu ri'ka samun 'kudin da muma zamuji dad'in rayuwarmu, hab
a baba, kazo muje kawai mucigaba da neman abinda ya fiddo mu, gudan yace to yanzu ina zamu nufa? Kasan dai yanzu duk wata d'iya mace indai tanada mutunci to tana gidan iyayenta, gudan ya gagga6e da wata irin dariya yace "yo dama duk wacce muka kama yanzu a
y bata mutunci bace, dama mu irin 'yan iskan nan muke nema masu yawon dare, idan sunsha sun bugu mukuma sai muyi awon gaba dasu, suduka sukasa dariya marar dad'in sauraoro.
Duk abinda suke Fatima na La6e cikin wannan gidan tana jinsu in banda kyarma ba
abinda take, lokaci guda ta had'a wani uban gumi, dan tariga ta