Showing 24001 words to 27000 words out of 31402 words
neman mutunci to anemi aurenta gun dangin mahaifinta, shiyasa kikaga na matsa akan aje
gun baffa Lawal d'in....
Fatima ta fashe da wani sabon kuka tace "dan Allah Hajiya ki taimaka min ki barni kada inje 'kauyenmu, wallahi banison zuwa, ba yanzu bane lokacin dana yanke zanje 'kauyenmu, nayimaki Al'kawarin idan muna raye inshaAllah ba sai
kinyimin maganar ba da kaina zan gayamaki zanje....
Jidda tayi karaf cikin fuskar tausayi tace "dan Allah Hajiya ki barta, idan lokacin yayi zataje da kanta.
Cike da tausayi Mukhtar yace "Hajiya dan Allah kiyimata Alfarma ki barta duk lokacin data bu
'kata sai taje....
Hajiya tayi murmushi tace "tayaro kyau take bata 'karko, idan kunce inbar fatima kada taje 'kauyensu waye ze zama wakilinta ranar Aurenta?
Jidda tayi sauri tace "Hajiya ga 'yan'uwankinan, dan Allah su zama wakilanta.
Fatima ta
taso jiki sanyaye ta dur'kusa gaban Hajiya ta d'ora hannunta kan 'kafafunta tace "Hajiya kece uwata, kece ubana, kece dangina, nasan Hajiya zaki iya tsayamin akan kome, dan Allah kiyimin kome ba sainaje 'kauyeba, idan lokaci yayi zanje...
Cike da taus
ayi Hajiya tace "to shikenan Allah shige mana gaba, suduka suka amsa da Ameen, jidda hada yin wani gajeren murmushi dan jin Hajiya ta Amince da bu'katar Fatima, dan ita a duniya tana masifar son abinda Fatima keso.
*_BAYAN SATI BIYU_*
Ansaka ran
ar Auren Laraba da mukhtar, lokaci d'aya aka sanya dana jidda, hakan yayi dai-dai da saura wata d'aya da sati daya ayi bikin.
Wai kada kaga farin ciki tsakanin masoyan, jidda kuwa tafi kowa murna, dan tana masifar son kasancewar fatima amatsayin matar y
ayanta.
Tun daga ranar da'aka saka biki hankali ya kwanta hidima ta kankama,
Bayan sati biyu mukhtar yasa akayo ma amaren odar kayan d'aki kome da kome yasa sukayi Mashi list,
Ankawo kaya abin gwanin ban burgewa, mukhtar kuwa angama 'kera mashi g
idanshi a unguwar dutsin safe malali quaters, gidane nagani na fad'a dan ba 'karamin 'kerashi akayiba.
Ana saura sati biyu biki aka kawo lefen jidda daga gidansu sahibinta Usman, akwati shidda nar'ke da kaya nagani na fad'a.
Washe gari kuma mukhtar y
a dam'kama Fatima nata lefen akwatina takwas, nar'ke da kayan arzi'ki, ranar saida Fatima ta zubar da hawaye na abu biyu, wani 6angaren farin ciki wani 6angaen kuma tana _*ALHININ*_ rashin mahaifiyarta lokacin dazatayi aure, tasan datana raye datafi kowa f
arin cikin kasancewar zuwan ranar.
A 6angaren Hajiya kuwa hidima takeyi sosai dan duk wani Abu daya dace uwa tayima 'yarta lokacin aurenta Hajiya tayima jidda da Fatima, babu wani banbanci take had'e kome tanayimasu tare.
Maman Ummi itace 'Kanwar Haj
iya wacce sukafi sha'kuwa, saboda haka ita Hajiya tabarma 'kwangilar kome na gyaran amare.
Ana saura sati d'aya bikin Maman Ummi tazo har gida tatafi da amare dan gyaresu.
Gyara kuwa sosai amare sukasha, cikin kwana biyar, idan kagansu dole ka 'kara
kallonsu dan wani masifaffen 'kyau dasukayi, jikinnan nasu har wani she'ki
yakeyi, dan dilkar da Maman Ummi kemasu irin wacce ake yiwa larabawace daga 'kasar saudiyya, tataho da ita musamman saboda gyaran amaren,
Dan Maman Ummi saudiyya take zaune sab
oda bikin kawai tazo, dan sune *Amara 'Kirjin biki*_{Littafin badi'at lbrahim}_ dan batada biki kamar na jidda *Autar Hajiya*_{Littafina daya gabata}_
Aiko sunsha gyara gurin Maman Ummi dan wani abun idan tashafe masu jikinsu dashi jin fatarsu suke kamar
ta jarirai saboda laushi, 'kamshi kuwa ajikinsu kamar anyi 6arin turare.
Gurin 6angaren kayan tsumi kuwa, ba'a magana, dan suma Maman Ummi tazo dasu daga 'kasar saudi, _*(Hmm ni su Maman Ummi mutanen saudia, kome na larabawa)*_
๐
๐
Zee E
lkaseem
Mmn khady
๐
[10/16, 8:12 PM]
๐ญ
_*ALHINI*_
๐ญ
๐๐๐๐๐๐๐๐๐
ยฎ```NWA```
_Written by_
_*Zee Mmn khady*_
๐
5
โฃ
7
โฃ
to5
โฃ
8
โฃ
*_RANA BATA 'KARYA SAI DAI UWAR
'DIYA TAJI KUNYA_*
๐
Ni zee da inada dogon hanci dana rangad'a guda, amma ko yanzuma bata 6aciba dole ince
๐๐ป
Ayuuririri........
๐๐ป
Yau nahango dandazon dubban jama'a 'kofar gidan su jidda da mukhtar wad'anda suka halacci d'aurin auren Mukhtar d
a amaryarsa fatima (laraba) sai jidda da angonta Usman, kowanensu akan sadaki dubu sittin-sittin.
Wai kada kaso kaga farin ciki gurin masoya aranar, mukhtar na hango ansha shadda hada uwar babbar riga, ga hula an d'ora, takalminnan nasa designer
massara
ci abin dai yabadada kala, kallo d'aya zakayima angwayen kagane suna cikin farin ciki, dan kowannensu bakin ya'ki rufuwa.
Amare kuwa acikin gida Mmn Ummi tagama shiryasu cikin wani rantsatstsen material, kalar purple sai takalmin 'kafafunsu fari kowace
da Jakarta fara, sai manyan mayafinsu fari da aka yafa musu, sunyi wani masifaffen 'kyau kamar yayan sarakuna, kome iri d'aya akayimasu musamman Hajiya tayi masu kaya kala shidda-shidda domin yin hidimar biki, dan suduka ba wacce tayi amfani da kayan lefen
ta.
Da misalin 'karfe biyar na yamma Hajiya ta tara amaren a bedroom d'inta tana yimasu nasiha, ba abinda sukeyi sai kuka, jidda na kukan rabuwa da hajiyarta da kuma farin cikin kasancewa da masoyinta, yayinda Fatima kukanta ya kasu kashi ukku, wani 6an
garen farin ciki wani 6angaren kukan rabuwa da Hajiya matar data zama tamkar uwa uba dangi agareta, sannan babban jigon yin kukanta shine *_ALHININ_* rabuwa da innarta, taso ace inna na raye a dai-dai wannan likacin itama taga Auren 'yarta tayi farin ciki
, amma ina ba haka Allah ya 'kaddaraba...
Ana cikin haka motar Alh mansir tayi parking a harabar gidansu jidda, Alh Mansir 'kani ne ga mahifinsu Mukhtar kuma shine ke shige masu gaba akan kome idan bu'katar hakan ta taso.
Ganin shigowarsa yasa Ameeno
saurin tashi daga zaman datayi kusa da Maman Ummi wacce keta bata labarin saudiyya, dama Ameenoo da Mmn Ummi 'kawayene, tun kafin Maman ummin tayi aure sukoma saudiyya itada me gidanta, Ameeno kuwa a gombe take aure amma duk da haka suna waya da Maman umm
in.
'Dakin Hajiya tanufa ta iske ta tasa maren gaba tanayimasu nasiha, guri tasamu ta zauna itama ta d'ora da nata nasihar, dama Amino badai nasihaba, dan kan nan nata cike yake da wa'azi da nasihohi.
Ahaka mutanen dake falon suka fara magana afito d
a amaren, jidda najin haka tafad'a jikin hajiyarta tana kuka, da 'kyar aka 6am6areta jikin Hajiya aka fita dasu kowace na sharar hawaye.
Alh Mansir da kanshi yakai kowace gidanta, sauran mutane kuwa sai dai sukabi daga baya dan ganin gidajen amaren.
Alhmdulillahi jidda ma gidanta ya had'u a unguwar layout aka kaita, fatima kuwa malali quaters mukhtar ya 'kyan'kyara masu 'kerarren gidansu.
Bayan mutane sunje anga gidajen amaren anyimasu duk abinda yadace bayan sallar isha'i kowace takama gabanta,
anbar amare su kad'ai a gidajensu.
Fatima zaune tsakiyar gadonta ta had'e kai da gwiwa tana sharar hawaye wanda ita kanta ta kasa tantance na minene, farin ciki ko *_ALHINI_* A haka angon nata ya risketa, tanajin shigowarshi amma bata d'ago ta kallesh
iba.
Hawowa yayi kan gadon ya zauna gab da ita har jikinsu na gugar na juna, hannu yasa ya yaye lullu6in dake kanta, yasa hannu ya d'ago da 'kya'kyawar fuskarta wacce duk ta 6aci da hawaye, yace fatimana miye yasaki kuka, Baku far in ciki da kasancewa m
allakina ne,? Shiru tayi mashi tacigaba da zubar da hawayenta wani na bin wani.
Farin handkerchief ya fiddo daga Aljihunsa yasa yana goge mata hawayen dake zuba daga idonta, wani daddad'an 'kamshi dake jikin handkerchief ya doki hancinta batasan lokacin
data saki wata ajiyar zuciyaba,
"Plz fatimana ki dainamin asarar hawayenki, baniso, idan kuma kinaso nima kiga nawa hawayen to kicigaba da zubar danaki, kinriga kinsan damuwarki damuwatace, farin cikinki shine nawa, ki taimakeni ki daina kukannan.
Hak
a yayita rarrashinta harya samu tayi shiru, sannan ya tashi ya nufi kitchen da kansa ya d'auko plate da duk wani abu dayasan zasu bu'kata.
Dan'karaยฒ kajine guda 2 ya baje musu da kanshi yari'ka yaga yana samata abaki, da tana d'an nonno'kewa tanajin kun
ya har dai tasaki jikinta taci, shima yaci sosai sannan yazuba musu lemu cikin glass cup suka sha sannan sukabi da ruwan roba, bayan sun kammala ne ya kalleta yace "kinyi sallah isha'i kuwa kai kawai ta iya d'aga mashi alamar eh dan duk illahirin jikinta '
kyarma yake sakamakon wani mayen kallo dataga mukhtar namata, yace "to sai ki tashi mu d'auro Alwala mu gabatar da sallar nafila domin nuna godiyarmu ga Allah daya cika mana burinmu,
Nan fa ta daburce tarasa wacce amsa zata bashi dan tasan tana fashin sa
llah ne kuma bazata iya fad'a mashi ba.
Tashi tayi tafad'a toilet tashe'ka wanka ta gyara jikinta, sannan tafito shima wankan yashiga, kafin yafito ta shafe jikinta da mayukan masu dad'in 'kamshi tare dayima jikinta 6arin turarruka masu 'kamshin gaske,
sannan tanufi wadrope ta d'auko rigar baccinta tasaka tabi lafiyar gado.
Mukhtar kuwa daya gama wanka sai ya d'auro alwala, yana fitowa yaganta kwance, beyimata magana ba saida ya d'auko wata jallabiya milk me gajeren hannu ya Sanya sannan yace "ki taso
muyi sallar, shiru tayimashi tare da lumshe idanunta kamar bata jinsa, ganin tayimashi shiru yasa ya hawo kan gadon ya tallafo ta yace my fati kitashi muyi sallah, ahankali ta baud'e idonta tace nayifa sallah yace "eh kinfad'amin sallah nafila nake nufi,
cike da jin kunya tace "uhm ina fashi ne, wani irin fad'uwar gaba yaji dan jin tace tana fashin sallah dan yau yayi niyyar suci amarcinsu, amma ba hali, haka ya kwantar da ita yaje ya kabbara sallah nafila raka'a biyu yayi sanan yayi addu'a yashafa, kafin
yagama bacci me dad'i yayi awon gaba da ita.
Yana kan prayer mat yajuyo ya kalleta baccinta take cikin kwanciyar hankali, ya 'kurama 'kya'k'kyawar fuskarta ido yayi wani 'kyawataccen murmushi, addu'a yayi ya shafe jikinsa sannan itama yayi addu'ar yasha
fe mata jiki, sannan ya kashe fitilar d'akin ya kunna masu ta gefen gado, sannan ya haye gadon ya rungumota jikinshi zuciyarshi cike da farinciki, a haka har bacci me nauyi yayi awon gaba dashi.
A 6angaren jidda kuwa a ranar Usman ya more kud'in sadakin
sa dan be d'aga mata 'kafaba, ba 'karamar hawala tasha ba, haka ya rin'ka raraahinta yana shimata Albarka, wani irin sonta ya'karaji cikin zuciyarshi dan yanda yasameta yaji dad'i sosai.
๐
Zee Elkaseem
Mmn Khady
๐
[10/16, 8:12 PM]
๐ญ
_*ALHINI*_
๐ญ
๐๐๐๐๐๐๐๐๐
ยฎ```NWA```
_Written by_
_*Zee Mmn khady*_
๐
5
โฃ
9
โฃ
to6
โฃ
0
โฃ
*_BAYAN SATI BIYU_*
๐
da misalin 'karfe biyu na rana fatima na hango kitch
en tanata ha'kilon had'ama me gidanta abinci.
Cikin awar da bata wuce d'aya da rabi ba tagama shirya kome kan dining, sannan tanufi d'akinta bayan tagyara kitchen d'in tsaf ta goge ko'ina kamar ba yanzu tagama girki ciki ba.
Kai tsaye toilet tafad'a
ta she'ka wanka, sannan ta d'auro Al'wala tafito ta kabbara sallar azahar, bayan ta kammala sallar gaban dressing mirror ta zauna tafara d'and'asa kwalliya, bayan tagama wadrope tanufa ta d'auko wasu riga da siket na atamfa ta Sanya, kayan kuwa sun zauna d
a6as jikinta kamar a jikin nata aka d'inkasu, sannan takashe d'aurin d'an kwali, turarruka ta feshe jikinta take 'kamshin jikinta ya gauraye da 'kamshin preshner dake d'akin da 'kamshin girkin datayi, yabada wani kalar 'kamshi me dad'in sha'ka.
'Karar t
sayuwar motar angonta taji, da sauri tafito ta zauna falo tana jiran shigowarshi, dan yahanta zuwa tarboshi harabar gidan saboda me gadi na kallonta shikuma yana masifar kishinta.
Da sallama yashigo falon, da sauri ta tashi ta tako zuwa gurinshi tana wa
ni yanga tana karairaiya kamar wacce batasan taka 'kasa, rungumeshi tayi tare dayimashi 'kya'k'kyawan Sumba a kumatu tace "welcome my husband, yace welcome fatimana, nasameki lafiya, cikin zazza'kar muryarta tace "lafiya lao, kadawo lafiya yace "lafiya.
Tace kafin kome muje ka watsa ruwa tukun, ba musu yabita zuwa toilet dinshi tahad'a mashi ruwan wanka sannan yashiga itakuma ta jawo mashi 'kyauren toilet d'in, sannan tazauna bakin gado tana jiran fitowarsa.
Bayan ya fito ya sanya kaya marar nauyi sa
nnan tayimashi jagora suka nufi dinning.
Cike da jin dad'i da farin ciki suke cin abincin, har suka kammala, sukayima Allah godiya,
Mukhtar ne yafara tashi daga dinning d'in yakoma kan kujera three seater ya kwanta, itakuma fatima tsayawa tayi tana ta
ttare kayan dasukaci abinci.
Bayan takai kuloli kitchen tadawo zata d'auki jug da cup's, sai taga wani had'ad'en zobe kan table d'in, dariya tayi sannan ta d'auki zoben tace nayi tsintuwa, mukhtar najin haka yatuno da zobenshi daya ajiye kan table din,
da sauri yataso yace kibani ring dina,
๐
nasan dai shine kika gani, cike da tsokana tace bazan bayar ba, saika fad'amin wacece tabaka, cike da tsokana yace budurwata tabanishi kuma zoben Al'kawarine, bekamata ta ganni babu shi a hanuna ba, fatima ta yamu
tsa fuska tace "idan taganka babu shi ta tambayeka kace mata wacce tafita power a gurinka tarabaka dashi, matsowa yayi gab da table d'in yace "kibani abuna tun muna wasa da juna, cike da nishad'i ta 'kyal'kyale da dariya tace "bazan bayarba, yana kallo ta
zirashi a yatsanta, aiko da sauri yanufota yana dariya yace "kkkkk kada ki Sanya........
Kafin yazo harta Sanya aiko ya nufota ze kar6a da gudu ta ruga tana dariya yabita haka suka rin'ka zagayen falon amma besamu ya dam'keta ba, bedroom tanufa dagudu
yabita tana 'ko'karin turo 'kofar yayi saurin turawa yashiga, dariya takamayi tafad'a kan gado tana maida numfashi, shima kan gadon yafad'a kusa da ita yana maida numfashi, rungumota yayi jikinsa yace "waye nakama, dariya tayi tace baka kama kowaba, dariy
a yayimata yace zakiyi bayani zaki san ban kama kowaba,
Nan fa wasa ya canja salo, a lokacin saida suka samu ladar aure,
Saida sukaji amfara kiran sallar la'asar sannan suka dawo hayyacinsu, toilet suka nufa suka she'ka wanka sannan suka d'auro alw
ala, mukhtar yawuce masallaci, itakuma fatima Bakin gado ta zauna zuciyarta cike da farin cikin yanda mukhtar d'inta ke nuna mata tsantsar so da 'kauna.
Wayarta ta lalubo ta 'kira jidda, ringing biyu ta d'auka "hellow sister ya kike, "lafiya lao sister
ya amarci, to Alhmdlh zamuce, haka sukasha firarsu, kusan kullum dama sai sunyi waya akalla sau hud'u ko sau shidda.
Bayan sunyi sallamane fatima ta tashi domin gabatar da sallar la'asar.
Rayuwa me dad'i da so da 'kauna tsakanin masoyan abin gwanin
birgewa,
6angaren jidda ma tana samun kulawa sosai daga gurin Usman d'inta.
Fatima da jidda sukam sunyi dacen mazaje saidai suyima 'yan baya fatan samun mazaje kamar nasu.
Sai dai lokaci zuwa lokaci fatima na kukan *_ALHININ_* Innarta, kuma tana
son zuwa 'kauyensu amma lokacin data tsarama kanta na zuwa 'kauyen beyiba.
๐
Zee Elkaseem
Mmn khady
๐
[10/16, 8:12 PM]
๐ญ
_*ALHINI*_
๐ญ
๐๐๐๐๐๐๐๐๐
ยฎ
```NWA```
_Written by_
_*Zee Mmn khady*_
๐
6
โฃ
1
โฃ
to6
โฃ
2
โฃ
*_BAYAN SHEKARA 'DAYA_*
๐
Fatimana......Fatimana.....tun daga falo yake kwalamata kira, amma yaji shiru, cike da mamaki ya nufi d'akinta dan yasan muddin tana lafiya to dataji ts
ayuwar motarshi take zowa bakin 'kofar falo tajira shigowarshi ta tarbeshi, amma yau sai yaga akasin haka, cike da fargaba yanufi d'akinta dan yimata Albishir Wanda yasan idan tajishi har 'kyauta sai tayimasa, dan kuwa so yake ya gayamata haihuwar jidda, d
an kullum batada magana saita haihuwar jiddar, duk da itama tana fama da tsohon cikinta haihuwa ko yau ko gobe koma yanzu.
Ringing d'in wayarta yajiyo bedroom d'inta hakan ya tabbatar mashi da tana ciki, dan haka da sauri yanufi d'akin.
Innalillahiwa
'inna'ilaihirraji'un ya furta tare da saurin 'karasawa ya tallafota ya had'ata da jikinshi yana fad'in "lafiya fatimana meya sameki, meya faru, cikin tsananin azabar rad'ad'in ciwon dake addabarta ta nuna mashi mararta, sannan ta dafe bayanta tana wash....
Can ciwon ya'kara tsinkulota tafara salati cikin wata wahalalliyar murya "wayyo yayana zan mutu ka taimakamin bayana ze 6alle 'kuguna, tana fad'i tana 'kara shigewa jikinsa tana kuka, cikin tsananin rud'ewa Mukhtar ke rarrashinta ga kuma wayarta gefe tan
ata ringing amma bebi kantaba, lalla6ata yayi ya kwantar da ita tare da fita domin yakira wata makwabciyarsu malamar asibiti, da sauri yashiga gidan sister safiyya ya sheda mata halin da Fatima take ciki, ba'afi minti gomaba suka shigo gidan tare,tana zowa
tasa safa ta dubata taga ta kusa haihuwa, nan ta rubutama Mukhtar duk abubuwan da ake bu'kata.
Da sauri yaje chemist d'in kusa dasu ya siyo, yana dawowa yabata kayan ba'afi mintuna 5 da dawowarsaba laraba tayi wani 'kwa'k'kwaran nishi me 'karfi tare da
santalo sankad'ed'en yaronta.
Sister safiyya tayi hamdala sannan ta gyara yaro tayima Fatima duk abinda ya dace, mukhtar kuwa dan tsananin murna bakinshi ya'ki rufewa nan ya fiddo yawa yakira Hajiya ya sanar da ita haihuwar Fatima, sannan yacigaba da '
kiran 'yan'uwa da abokan arzi'ki yana sanar dasu.
Bayan sister safiyya ta taimakama Fatima tayi wanka ta gyarata itada baby.
Fatima ta fito shar da ita kamar ba itabace wacce ta haihu sai buga uaban 'kamshi take itada baby, sister safiyya da kanta
ta shiga kitchen tahad'oma Fatima tea me kauri Wanda yaji milo sosai takawomata tana zaune bakin gado, saida ta tabbatar data shanye duka sannan tabata magungunanta tasha sannan tafito da niyyar tafiya gida.
A harabar gidan tagamu da mukhtar yana niyya
r fitowa daga mota, da Alama wani wuri yaje amma bame nisaba saboda be dad'e da fitaba, ganinta yasashi saurin ida fitowa daga motar yace "ah sister har kin fito?
Cikin fara'a da sakin fuska tace "harna fito Baban baby, zanje gidane kafin in 'kara zagayow
a inga lafiyar baby da momynsa.
Cike da jin dad'i mukhatar yayimata