Showing 3001 words to 6000 words out of 31402 words
sun tafi,
Wata irin kunya takamata tasa
hannu tarufe fuskarta, tace "kace munkusa zama miji da mata, Hashim yayi dariya yace "Allah dai yacika mana burinmu, wlh Laraba dan bakisan yanda nake sonkiba, ina maki 'kaunar da duk cikin masoyanki babu wanda yata6a yimaki makamanciyarta,
Wani lok
aci nakan zauna inta tainani, inga kamar baffanki baze bani keba, sai inji gabana yayi wani mummunan fad'i.
Laraba ta kalleshi cike da tausayawa, dan ko ita tagama yadda da son da Hashim yake mata bana wasa bane tace "ka kwantar da hankalinka masoyina i
ndai muna raye inshaAllahu bakada wata mata bayan ni.
Cike da jin dad'in kalamanta Hashim yace "Allah sa tace "Ameen.
Haka ta Ebi ruwan Hashim d'in ya d'aukar mata suka kama hanyar gida suna tafiya suna tad'i cike dajin dad'i.
Saida suka kawo gab
da gidansu Laraba sannan yami'ka mata tukunyar ya tsaya nan saida yaga shigarta sannan ya wuce.
Da sllama tashiga gidan, inna tayi saurin 'kar6ar ruwan dake kanta, tace "Laraba kindawo,
Kallo d'aya tayima innar tata tasan tana cikin 6acin rai, tasan
arina _(wai ansaci zanin mahaukaciya)_ muddin ldan baffa Lawal yazo gidan to dole sai inna ta zubar da hawaye.
Bata ko tambayi inna dalilin 6acin ranta ba, tashiga rarraahinta tana bata ha'kuri.
Inna ta kalleta cike da tausayawa tace "Laraba 'kanin m
ahaifinki yazo, ko ban fad'aba kin riga kinsan halinsa, yace ya sanya bikinki da Hashim nan da sati ukku, ina ro'konki da dan Allah kada ki d'aga hankalinki ki zamo me biyayya sai kiga an zauna lafiya.
Laraba bataji komeba dangane da abinda mahaifiyarta
ta fad'a mata sai cewa tayi "inna kitayani Addu'a Allah za6a min abinda yafi zama Alkhairi a rayuwata, inna ta share wasu guntayen hawaye tace, tashi kiyi wanka ga abincinki can gindin bushiya, cikin langa, ba musu ta ebi ruwa cikin bokiti tafad'a kewaye,
inna kuma tacigaba da matsar kwallar tausayin yarta.
🖊
Zee Elkaseem
Mmn khady
💋
[10/16, 8:10 PM]
😭
*_ALHINI_*
😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
®```NWA```
_written b
y_
*_Zee Mmn khady_*
😘
9
⃣
to
🔟
```Page```
🖊
Ranaku suna wucewa lokaci na tafiya, yau saura kwana hud'u d'aurin Auren Laraba da masoyinta Hashim
Hidima sosai 6angarorin guda biyu sukeyi, lnnar Laraba kuwa bata wani damu ba game da abubuwan d
a ake bu'kata gurin biki, saboda dama tanada kome ta tanada, sai d'an abinda ba'a rasaba,
6angaren Laraba kuwa yau sun fita gayya itada 'kawarta indo, sun gayyato 'kawayensu da dama wad'anda mafi yawansu sunada aure, marassa auren basuda yawa, wasu ma
harda 'ya'yansu.
A gajiye suka dawo, gidansu indo suka sauka, lnnar indo tayi masu sannu,
Sannnan suka wuce d'aki suka cire mayafansu suka fito suka d'aura alwala suka gabatar da sallar la'asar sannan lndo ta d'auko masu abinci suka fara ci, dambun ma
sara ne yaji zogale, sai 'kamshin man gyad'a ke tashi,
Sun kammala indo ta d'ebo masu ruwa me sanyi a tulu suka sha, sannan suka cigaba da tattauna yanda shirin bikin ze kasance, sun shirya taron 'kawayen amarya ana gobe d'aurin Aure.
Sai gab da magrib
suka fito indo zatayima Laraba rakiya ta tafi gida, suka gamu da ilu saurayin lndo,
Laraba ce tafara gaidashi, ya amsa cike da fara'a,
Sannan lndo ta gaidashi cike da jin kunyarsa, ya amsa sannan ya maida dubansa ga Laraba cikin tsokana yake magana "
Amarya baki laifi,.... Laraba tayi saurin tarbarsa "kada dai ka ida wannan magana dan ba yanda za'ayi mutum yakashe d'an masu gida ace beyi laifi ba, kai ko kazar masu gida marya takashe sai tayi laifi barantana d'a.
Suduka sukasa dariya, ilu yace yanzu
fa nan da kwana hud'u kinzama marya, tayi dariya tace kai kuma nan da wata d'aya kazama ango, yace "inshaAllah ga kuma amaryata, ya nuna indo ya wani kashe mata ido, cike da jin kunya indo taja hannun Laraba tace zomuje dan Allah yamma na'karayi, haka suka
wuce suka barshi cike daso da 'kaunar indon sa.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Yau Yakama Alhamis, kuma daren d'aurin auren indo,
Yau ne kuma suke taro da 'kawayenta, sun taru gidan wata mata nan makwabciyarsu, anata shewa, Kowa kagani cikin f
arin ciki, abin Alhamdulillah.
Indo ce tafito cikin shigar sabuwar atamfa riga da zani d'inkin yayimata kyau, duk da simple ne d'inkin amma ya'kara fito da kyawunta,
Kafarta tasha 'kunshin Jan lalli, tayi kyau tafito amarya sak _(amma a 'kauyensu)_
😜
Sun zauna Kowa na yaba kyawu irinna Laraba, wata daga cikin 'kawayensu me suna hansai tace "gaskiya Laraba kinada kyau, inama ace yayana ne ze aureki ki ri'ka haifo masa kyawawan 'ya'ya masu Kama dake.
Murmushi kawai Laraba tayi mata dan tasaba jin
haka 'kawayenta da dama sunaso ta auri yayyensu.
Hansai ta matso kusa da Laraba ta rad'a mata a kunne, wallahi yaya habu ya d'ad'e yana sonki, abinda yasa be furta maki ba dan yaga lokacin bashida 'kud'i, tun bayan rasuwar masoyinki na farko, yanzu kuma
yadawo daga birni yayi kud'i, amma sai yadawo da rashin sa'a ya iske saura sati d'aurin aurenki.
Wani mummunan fad'uwar gaba Laraba taji lokacin da hansai ta tuna mata da rasuwar saurayinta, sai lokacin ta tuna da samari biyu nefa aka saka masu rana s
ai ana gab da d'aura masu aure suka mutu.
Wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonta tasa gefen mayafinta ta goge, cikin ranta tace _(Ya Allah kada ka kashe Hashim Allah sa muna da rabon kasancewa inuwa d'aya nida shi)_
Ganin Laraba na hawaye yasa han
sai tayi shiru da maganar datake tace "dan Allah kiyi ha'kuri idan maganata ta 6ata maki rai, bata jira jin abinda Laraba zatace ba ta tashi ta koma cikin 'kawaye aka cigaba da labari, amma tana yawan satar kallon Laraba dan ganin yanda lokaci d'aya hankal
inta ya tashi.
Indo tafito da biskit da cingam wanda suka kulla cikin ba'kar leda tashiga rarrabawa, saida ta tabbatar da Kowa ya samu sannan takoma kusa da Laraba ta zauna, tin tana cikin rabon kaya ta lura da 'yanda 'kawar tata take cikin wani irin ya
nayi.
Sai gab da magrib 'kawayen amarya Kowa ya watse, lokacin lndo da Laraba suka wuce gidan su Laraba.
Gidan cike yake da 'yan'uwa da abokan arzi'ki, anata hidima, nan suka gaisheda mutanen dake tsakar gidan sannan, suka wuce d'aki.
Suna shiga L
araba ta cire mayafinta ta zauna da6as kan tabarmar dake shimfid'e tsakar d'akin jikinta ba 'karfi ko kad'an,
Indo ta kalleta tace "Laraba na lura dake tun d'azu baki cikin nutsuwarki, wai me ke damunki?
Wasu zafafan hawaye suka zubo daga idanunta tace
, "lndo jikina duk ya mutu, hankalina yakai 'kololuwa gurin tashi, gani nake Hashim mutuwa zeyi kamar yanda, lro da sabi'u suka mutu... ta fashe da wani irin kuka me ban tausayi.
Indo tace ki daina wannan tinanin acikin ranki, dan Allah ki daina kuka in
shaAllah Hashim baze mutuba, ay mutum baya mutuwa sai kwananshi sun 'kare, suma da suka mutu dama Allah ya 'kaddaro hakan ne garesu.
Nan lndo tarin'ka rarrashinta, sai bayan isha'i sannan tabar gidan cike da tausayin halin da 'kawarta take ciki.
°°°°
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Rana bata 'karya sai dai uwar d'iya taji kunya```
'Daruruwan mutane sun taru 'kofar gidansu Laraba domin halartar d'aurin Aurenta.
Yayinda itakuma a ranar ta tashi sukuku, jikinta ba 'karfi ko kad'an, matar 'kan
in babanta ce mal Lawal ta matsa mata tayi wanka ta shirya cikin wata koriyar atamfa, riga da zani sannan tayi mayafi da kalar zanin atamfar,
A 'kofar gida kuma yan'daurin aure sungama taruwa dangin ango kawai ake jira a d'aura aure, amma shuru basu ba
labarinsu,
Mal Lawal yagama 'kulewa shiru kawai yayi, jira yake dangin angon suzo sai ya sauke masu ta cikinsa snnan a d'aura auren.
Bayan kamar minti talatin mal Lawal yanata cika yana batsewa, sai ya hango ml bala tare da wasu mutane guda biyu su
na tinkaro su.
Cike da bala'i mal Lawal ya mi'ke dan ya saukema mal bala ta cikinsa, sai mal bala yafad'a mashi wata magana wacce ni kaina bansan meya fad'a ba, sai ji nayi ya rafka uban salati, nan mutane suka taso suna tambayarsa "meya faru?.
Cikin
gida kuwa mata sunata tsegumin an'ki d'aura aure an shanyasu, jira suke a d'aura atafi da amarya gidan mal Lawal daga can za'a d'auketa akaita gidan miji.
Baba salame ce wata makwabciyarsu tashigo gidan hankali tashe, bako sallama, da sauri mutane suka
yo kanta ana tambayarta "meya faru? Sai ta fashe da wani irin kuka, wata magana tafad'a masu bansan me tafad'aba saboda cikin muryar kuka tayi maganar sai jinayi suduka sun d'auki salati.
*To fah
🤔
nifa ansani aduhu
😱
miye ake fad'a wanda yake tada
hankalin mutane
😭🙆🏻
*
_ku biyo zee mmn khady dan jin cigaban labari_
_08166169254_
🖊
Zee Elkaseem
Mmn khady
💋
[10/16, 8:10 PM]
😭
*_ALHINI_*
😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
®```NWA```
_written by_
*_Zee Mmn khady_*
😘
1
⃣
1
⃣
to1
⃣
2
⃣
🖊
zaune take d'aki tasha lulli6in zanin atamfa, wani mummunan fad'uwar gaba taji, kawai sai jitayi hawaye suna gangarowa daga idonta, suna diga bisa jikinta.
Hayaniya tajiyo
a tsakar gidan, a tunaninta an d'aura auren ne amma koda ta 'kara saurarawa sai taji sa6anin haka *_Dukkan me rai mamacine, Allah ji'kan hashim_*
Wata uwar 'kara ta saki tare da fashewa da wani irin kuka, wanda yajawo hankalin mutane zuwa gareta,
Lokaci guda tanemi numfashinta ta rasa, ta fad'i 'kasa sumammiya, nan fa aka shiga tsananin tashin hankali, inna tayi saurin tallafota tana kuka, tana kiran sunanta, da sauri aka d'ebo ruwa aka yayyafa mata sannan numfashinta ya dawo, amma duk da haka bata
san inda kanta yakeba.
A ranar dai anga tashin hankali, mutanen dasuka taru d'aurin Auren Hashim sune sukayi jana'izarsa,
Bayan an kaishi makwancinsa aka dawo aka cigaba da zaman makoki, mutane kowa na Al'ajabin yanda mutuwar Hashim ta kasance, dan k
uwa ranar saida abokaninsa duka suka taru, yashiga wanka bayan yafito ya shirya cikin farar shaddarsa, har sun fito zasu tafi, yace masu kanshi na ciwo zeje chemist ya siyo magani.
Har wani cikin abokanin yace bari yaje ya siyo mashi, amma sai yace ya b
arshi kawai zeje da kanshi, haka yatafi yabar abokaninsa suna jiran dawowarsa su wuce gurin d'aurin auren,
Sun kai kimanin minti arba'in suna jiransa amma shiru,saboda haka suka Yanke shaawarar binsa.
Innalillahi'wa,inna,ilaihirraji'un suka furta, l
okacin da suka hango Hashim kwace cikin ciyayi, ga jini duk ya 6ata farar shaddar dake jikinsa, amma ba Alamar rauni jikin sa.
"To ta ina ya samu wannna jinin? Tambayar dasuka rika yima Kansu kenan wacce basuda amsarta.
Nan suka d'aukeshi suka nufi g
ida hankali tashe,
Kafin kace miye labari yagama baje gari, abunka da 'karamin gari duk inda kanufa maganar akeyi, dan wasu har sun fara yima abun wata mummunar fassara,
*_°Bayan sati biyu_*°
6angaren Laraba kuwa tun rasuwar Hashim batasan inda ka
nta yakeba sai yau tadawo hayyacinta, abin mamaki batayi maganr mutuwar Hashim ba, kawai tacigaba da hidimominta,
Wanka tayi ta shirya cikin, sabuwar atamfarta d'aya daga cikin wacce aka kawomata na lefen aurenta, da aka maida gidansu Hashim suka 'ki k
ar6a,
Kwalliya tayi sosai, tayi gwanin kyau abunka ga 'kya'kyawa duk yanda tayi kwalliya yimata kyau take, duk da tana tashin 'kauye, gyale ta dauko ta rataya kafad'arta tazo gaban inna tace inna zanje gidansu lndo, inna ta d'ago idanunta ta kalleta ci
ke da damuwa, da mamakin yanda halayyar Laraba ta canja bayan rasuwar Hashim, tace "haka zaki fita Laraba yakamata ki sanya hijab d'inki, ta turo baki tace ni gaskiya inna bazansa hijab ba kamar wata me takaba, lnna ta girgiza kai cike da takaici da kuma m
amakin abinda ke damun 'yarta wanda har zatayimata magana tace ba hakaba, wanda da ba halinta bane.
Koda taga Inna batada niyyar mata magana kawai sai tasa kai tafice, tace "saina dawo, cike da takaici inna ta matse kwallan dasuka taru idonta tace "Alla
h maidoki lafiya.
Tafiya take hankalinta kwance abinta, ga gyalenta rataye a kafad'a gashi ta wani kashe d'aurin d'an kwali,
Kan hanya kuwa duk wanda yagamu da ita cikin wannan yanayin sai yayi mamaki, kafin kice me mutane sun fara tsorata da Al'amari
nta.
A zaure ta iske indo da saurayita ilu suna zance, Wanda yau yarage saura sati d'aya bikinsu, dama suna cikin tattaunawa ne akan maganar Larabar ne, inda ilu ke garagad'in indo a kan ta rabu da laraba indai har tanason su shirya, sai gata tashigo, t
a kalli ilu cikin sakin fuska tace ango kasha 'kamshi,...
Wani irin fad'uwar gaba ilu yaji lokacin daya jad'a ido da Laraba , saboda haka jiki na kyarma yayima lndo sallama yabar gidan.
Cike da mamaki lndo ta kalli Laraba, tace "kawata yau kece da wa
nnan shigar abinda ban ta6a gani kinyi ba,
Laraba tayi dariya tace "lndo kenan yo kuma kullum haka zanta yawo da hijabi kamar me takaba, ay nan gaba ma ko gyalen barin sawa zanyi.
Cike da mamaki indo tace "to Allah ya 'kyauta, sannan suka wuce cikin g
idan.
Innar indo na zaune tana shan iska taji shihowarsu,
Laraba ta gaisheta, wani mummunan fad'uwar gaba taji da ganin Laraba, dan taji rad'e-rad'in da akeyi agari, *aiko dole tasan yanda zatayi taraba 'yarta da Laraba tun kafin suma ta kashesu.
Indo ce ta lura da yanda mahaifiyarta tashiga dogon tunani tace "inna Laraba na gaisheki ko bakijiba ne? Firgigit tadawo daga dogon tinanin datake ta washe baki tana ya'ke tace lafiya lao.
🖊
Zee Elkaseem
Mmn khady
💋
[10/16, 8:10 PM]
😭
*_ALHINI_*
😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
®```NWA```
_written by_
*_Zee Mmn khady_*
😘
1
⃣
3
⃣
to1
⃣
4
⃣
```Bayan kwana sha ukku```
Yau ake taron 'kawaye na lndo, gobe kuma d'a
urin aurenta, 'kawayenta ne cike ma'kil da gida anata shewa, Kowa kagani cikin farin ciki, hansai ta kalli lndo tace "waini indo ina Laraba naga tunda nazo ban gantaba, lndo tayi murmushi tace "tun d'azu muna tare ta koma gidane ta shirya, amma nasan tana
gab da dawowa, hansai tace Allah sarki, sai ta tashi ta goya d'anta tace "to amarya ni zan wuce sai kuma gobe idan Allah ya kaimu, lndo tace "kai hansai tun yanzu bazaki bari Laraba ta dawo tabaki biskit d'in ba? Hansai tayi dariya tace a'a ba kome wlh ay
zan dawo gobe, kafin tarufe Baki suka jiyo sallamar Laraba, aiko ko kallon inda take Hansai batayiba tasa kai tafice daga gidan,
Can sai wasu gun-gun 'kawayensu suka taso suma sun kai su goma suka ce "muma dai mun wuce, cike da mamaki lndo ta kallesu "tu
n yanzu baku bari ajima, tare suka had'a baki suka ce "a'a akwai inda zamu ne, suka sa kai suka fice,
in takaita maku labari shigowar Laraba gidan saida yasa duk mutanen dake gidan suka tafi.
Indo tasan dalilin tafiyarsu, har ga Allah bataji dad'iba a
mma ba yanda zatayi, ta dad'e da sanin mummunan zaton da mutanen 'kauyen keyima Laraba, wasu guntayen hawaye suka zubo daga idonta tasa hannu ta goge batare da Laraba ta kula da halin datake ciki ba.
Ranar dai haka suka gama yinin, abin ba dad'i.
Larab
a kanta ta fahimci yanda mutanen garin ke gudunta, a zuciyarta tace
_"me nayima mutane suke guduna_ *_Innalillahiwainnailaihirraji'un_*
Tafad'a tare da goge wasu zafafan hawaye.
Washe gari aka d'aura auren lndo da ilu, da dare aka kai amarya,
R
anar Laraba taga tashin hankali, dan 'kiri-'kiri mutane suke nuna tsana da tsangwama da 'kyama gami da tsoro agareta.
Hakan yasata barin gidan bikin batare da ta shirya ba, lndo ta tausayama 'kawarta, cike da tausayi take mata addu'a Allah ka yayemata a
binda ke faruwa da ita.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Kiyi ha'kuri kinji Laraba, inshaAllah kome ze wuce, kiri'ka addu'a kinji Allah yaye maki matsalar dake tattare dake, wasu zafafan hawaye suka zubo daga idanunta tasa hannu ta goge "yanzu shi
kenan inna babu ni babu maganar Aure duk namijin dayace ze aureni da lokaci ya gabato sai a wayi gari ya mutu, gashi nazama abin tsoro cikin mutane duk inda naje sai afara barin gurin, ta'kara fashewa da wani sabon kuka.
Inna har cikin ranata take tausa
yama d'iyarta, itama hawayen take, tace "kiyi ha'kuri Laraba ki d'auki wannan matsayin kaddara, inshaAllah wata rana kome ze zama labari.
Nan lnna tayita rarrashinta tana kwantar mata da hankali,
Harta samu tayi shiru tace "tashi ki d'au tukunya ki d'e
bo ruwa kiyi wanka, ba musu ta tashi ta dauki 'yar 'karamar tukunya tanufi rafi, bako gyale jikinta barantana hijab wanda har ta manta yanda ake sanyashi, inna tayi fad'an harta gaji ta 'kyaleta
Haruna ta hango zaune cikin gonarshi shida wani abokinshi
suna cin gyad'a me 6awo, suna fira, abokin nashi ne yafara hangota ta doso inda suke, cikin dabara ya tashi yacema Haruna "ina zuwa bari in d'an zagaya can wlh jiya naci wata tafasa tad'an 6atamin ciki.
Haruna yace "Allah sauwa'ke, ya mi'ka mashi ruwa,
ya amsa yawuce, yayi nesa kad'an ya hango Laraba ta iso inda Haruna yake zaune tanayimashi magana, a fili yace "Allah nagodema da Laraba bata riskeni gurin can ba, da sauri ya 'kara gaba yayi cikin gari yana tinanin yanda abokinshi ze rabu da Laraba *Mayya
* la'kanin da mutanen 'kauyen suka fara kiranta dashi kenan dan su acewarsu mayya ce shiyasa duk wanda yace yana sonta take cinye kurwarshi ya mutu.
Da fara'a take magana "Haruna dama ina nemanka, cike da tsoro ya kalleta, duk illahirin jikinsa kyarma y
ake amma bakinsa yakasa furta kome,
Bata kula da halin dayake cikiba tacigaba da magana,