Showing 6001 words to 9000 words out of 31402 words

Chapter 3 - ALHINI complete.

"waini Haruna ya maganar soyayyarmu, tunda Allah besa anyi da Hashim ba mizai hana ka dawo a d'aura mana aure.

Sai lokacin yasamu yayi magana cike da tsoro bakinsa

na 'kyarma yace "Laraba dan Allah kiyi ha'kuri ni wallahi tuni nafasa yin Aure, bazanyi Aureba kwata-kwata.....

Cike da mamaki Laraba ta 'kara matsowa inda yake tace bazakayi aureba fa kace Haruna, nice fa Laraba ka manta irin soyayyar da kace kanayi

mani, a da,

Yace "a da ba amma yanzu na daina soyayya kiyi ha'kuri, Laraba ta'kara matsowa kusa dashi yana matsawa "Haruna nice Laraba baka ganeni ba ne?

Cike da tsoro yace "na...na..ganeki mana, haba sai lokacin yasamu ya ranta a na kare

🏃🏻

Mamak

ine tare da takaici da ba'kin ciki suka rufe Laraba ta dur'kusa nan tana kuka.

_Allah sarki laraba na tausaya maki_

🖊

Zee Elkaseem

Mmn khady

💋

[10/16, 8:10 PM]



😭

*_ALHINI_*

😭

🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇

®```NWA```

_written by_

*_Zee Mmn khady_*

😘

1

⃣

5

⃣

to1

⃣

6

⃣

🖊

Zaune suke sun buga uban tagumi, Laraba na zubar da hawaye itama lnna hawayen take zubarwa dan taji yanda ake maganar Laraba a 'kauyen

mutane suna kiranta *mayya* tasa hannu ta goge hawayen dake idonta, abinda yafaru da ita jiyane yashiga dawo mata a kwalwa,

shikenan yanzu abin Laraba har inna yake shafa, dan jiya akayi bikin wani d'an Aminiyarta, wacce a da matar taso ace d'anta Lara

ba ya aura amma Allah be nufaba, lnnar Laraba batada aminiya wacce ta wuceta, amma har aka fara biki ba'a gayyacetaba, saboda haka tace bari taje tayi mata Allah sanya Alkhairi,

Haka ta shirya ta nufi gidan, tana isa zauren gida, magan-ganun dataji anay

i gidanne yasa hantar cikinta juyawa,

Muryar mata taji daban-daban suna magana "wah ay Laraba ta fiddo maitar ta fili, yanzu fa mutum ukku ta kashe 'kauyennan kinsan kuwa maitarta takai inda takai, can wata mata ta kar6e zancen "ay ance gado tayi gurin

mahaifiyarta, dan ance ita ta kashe mahaifin Larabar, muryar wata matar taji tana cewa "to mudai uwar biki Allah sa baki gayyato mamu suba, dan nasan bakida Aminiya kamarta, can sai tajiyo muryar amiyar tata tana cewa "a da ba, amma banda yanzu dan ban ga

ji da rayuwaba inaso inga auren auta ta har inga jikokina, suduka sukasa shewa "heyyyyyy, wata tsagerar mata takama hanci ta rangad'a guda "ayyuririiii,.........

Innar Laraba najin haka wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonta, zuciyarta tayimata nauyi

, kanta yayi wata irin Sarawa, take ciwon kai me tsanani ya saukar mata jitake kamar kanta ze rabe, haka ta dafe kanta tanufi gida cike da takaici da ba'kin cikin magan-ganun data ji, dan gidan bikin da bata shiga ba kenan,

Kan hanya ma duk wanda tayima

magana sai taga ya matsa da Alamar tsoro tattare dashi baze ko amsa maganar ba,

Wasu kau dasun hangota suke rugawa, abin ya matu'kar d'aure mata kai.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Yanzu kai habu larabar kake so, kana ganin yanda mutane ke g

udunta, amma kai karasa wacce zaka za6a sai ita, kuma kariga ka gama sanin *mayya* ce,

habu ya kalli abokinsa cike da takicin kalmar mayya daya furta ga Laraba yace "eh ni ina sonta koda zata ri'ka yankan naman jikina tana ci d'anye 'karewar maita zan au

reta, abokin nashi yace to "Allah raka taki gona, nidai kaga tafiyata, kuma muddin kasani idan kana tare da Laraba to abotarmu ta 'Kare, habu yayi wani guntun murmushi mai d'auke da takaici yace, Allah had'a kowa da rabonsa, rabuwar habu kenan da abokinsa

.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Zaune suke sunyi tagumi duniya tayi masu zafi itada innarta, dan fitama wahala take masu kullum suna gida basuda aiki sai tinani sai kuka,

Rabon kau da wani mutum yashigo gidansu har sun manta,

Itako Laraba d

a gidan lndo kad'ai take zuwa taji d'an dad'i-dad'i shima yanzu yaushe rabon dataje, tun ranar dataje ilu yayimata wula'kanci yace kada ta 'kara zuwar mashi gida idan kuma bata dainaba hukuma zata rabashi da ita,

Suna cikin wannan yanayin sukaji an bank

ad'o kyauren gidan kad'an yarage a karyashi, mal Lawal ne yafara magana cikin bala'i da masifa, watau kin koyama d'iya maita tana kashe mutanen gari, to wallahi ba maitaba ko uban maita ke gareki dole Laraba ta fito da miji inyimata aure, dan bazan yarda

tana yawo agari ana zagina a matsayin mahaifinta na gaza aurar da itaba.

Tunda yafara magana basu cemashi 'kala ba, saida yagama bala'i sannan ya kalli Laraba yace "waye kuma yanzu kike so wanda tsautsayi ke shirin afka mawa,

Cikin kuka da bakin cik

i tace "dama Haruna ne tin kafin rasuwar Hashim yake sona, mal Lawal yace "to bari yanzu inje in samu Haruna idan da gaske yake ya

turo iyayenshi dan bazaki 'kara sati biyu a gidannan ba, sadaki kawai ze kawo a d'aura aure, haka yafita gidan yanata bal-bal

in bala'i, inna dai bata cemashi ci kanka ba illah kuka datakeyi.

Haruna Zaune shida abokinsa suna fira, mal Lawal ya iso gurinsu, suka gaidashi ya amsa, sannan yace Haruna gurinka nazo kan maganar Laraba, wani irin fad'uwar gaba Haruna yaji,

jin an a

mbaci sunan Laraba, mal Lawal be jira abinda Haruna ze fad'aba yaci gaba da magana, "tace kaine wanda ta tsaida shine nace ka turo magabatanka bamu bukatar kome daga gareka sadaki kawai zaka kawo nan da sati d'aya a d'aura maku aure.

Haruna Wanda tinda

mal Lawal yafara maganar jikinsa ke rawa kamar mazari yace "a'a ni maganar soyayayya bata ta6a had'ani da Laraba ba, kuma bani sonta, inaji ba dai ni harunan take nufiba

A fusace mal Lawal yabar gurin da niyyar yaje gida yaci mutuncin Laraba da mahaif

iyarta.

Tinda mal Lawal yabar gurin jikin Haruna ke 'kyarma, ya kalli abokinshi yace kanafa jin wannan mutumin, abokin nashi yayi dariya yace "watako yarinyar nan tasaka a zuciyarta tagama kwad'aituwa da kai walh saika tashi tsaye,

Kazo muje gidan kak

ata 'yar me ganye tana bada maganin mayu, Malam abaka kasha kayi wanka.

Ba musu Haruna yace mutafi,

Sun isa gidan 'yar me ganye anba Haruna maganin daze ri'ka ji'kawa yana wanka dashi sannan aka bashi tazargade yari'ka haya'ki, matar tace indai yana a

mfani da wannan badai maye ba, ko sarkin mayu sai dai yaganshi ya 'kyale.

🖊

Zee Elkaseem

Mmn khady

💋

[10/16, 8:10 PM]



😭

*_ALHINI_*

😭

🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇

®```NWA``

`

_written by_

*_Zee Mmn khady_*

😘

1

⃣

7

⃣

to1

⃣

8

⃣

🖊

"lna 'yar iskar yarinyar nan take, dan ubanki kinsan babu soyayya tsakaninki da Haruna kika turani gurinshi, naje naji kunya, to bari kiji in gaya maki tunda dai kinzamar ma mutane bala'i k

in zamar masu 'karfen 'kafa to zan aurar dake ga duk wanda naga dama,sannan ya juya gurin inna wacce tunda yafara fad'anshi ta kauda kanta gefe tana zubar da hawayen takaici, shin wai dame zasuji da tsana da tsangwama da tsoro da 'kazafin da 'yan garin kem

asu koda masifa da bala'in mal Lawal.

Yaci gaba da magana, cikin d'aga murya "Kara Ku yanke shawara tun kafin nan da kwana biyu idan kuma ba hakaba zan yanke duk hukuncin da naga dama, yasa kai yafice yanata kumfar baki.

Yana Fita Laraba ta taso tafa

d'a jikin innarta ta fashe da wani irin kuka me ban tausayi, itama lnnar kuka take amma duk da haka rarrashin 'yar tata takeyi.

*```Bayan kwana Hud'u```*

Inna ce ke rarrashin 'yarta wacce duk yinin yau kuka take, ko ruwa takasa sama cikinta saboda ts

ananin damuwa, tariga tagama sanin sunan da ake kiranta dashi a 'kauyen na *Mayya*

"Kiyi ha'kuri Laraba duk tsanani yana tare da sau'ki, in Allah ya yarda duk masu gudunki sai sun dawo suna binki, kedai kiri'ka addu'a Allah yayi maki maganin matsaka

rki.

Suna cikin wannan ne sukaji an bankad'o 'kyauren gidan, suduka suka maida hankalinsu ga 'kofar ganin 'kyauren sukayi 'kasa ya karye, kasancewar dama na langa-langa ne bayada wani 'kwari.

Mal Lawal ne yabi ta kan 'kyauren yashigo gidan a sukwane,



Laraba na jikin inna ta 'kan-'kameta duk tsoro yakamata gani take yau baffa Lawal dukan ta zeyi.

Kudi ya watso jikinta yace "ga sadaki nan na d'aura aurenki da habu, yayan hansai, idan kin cika ke mayyace yau kada ya kwana da rai, tinda sauran kafin

a d'aura kike kashesu, to wannan karan an d'aura kuma 'kurwarsa kur kuci kanku, *Mayu*.

Wani irin kuka Laraba ta 'kara fashewa dashi, ta 'kara shigewa jikin innarta Wanda shi kad'aine yanzu take ra6a taji sanyi tace.

"Shikenan inna bamuda Kowa bamuda

Wanda zamu ra6a muji dad'i, abin takaici da ba'kin ciki wai hada baffa Lawal ake kirana *Mayya* to waye ma baze kirani da *mayya* ba tinda 'kanin mahaifina ma yakirani haka.

Bayan magrib mal Lawal da kansa yazo ya tafi da Laraba tana kuka tana kome ya

kaita gidan miji, basu iske kowa gidan ba amma duk wani Abu na Al'ada na tarbar amarya an kawo an aje masu,

Haka baffa lawal ya ajeta yabar gidan, tunda Allah ya halicceta bata ta6a ganin irin wannan auren da akayimata ba, gashi dai ankawota gidan miji

amma ba kowa sai ita kad'ai cikin gida kamar *Mayya* _(sunan da mutanen 'kauyen ke kiranta dashi)_

Ta fad'a kan soson katifar da aka kawota dashi wanda ko zanin kirki bayadashi, ta fashe da wani irin kuka, baiwar Allah Laraba tana cikin tashin hankali,

duk tabi ta rame, ta kod'e idanun nan nata sunyi zuru-zuru, hancin ya 'kara tsawo sai wani uban 'kashin wuya daya fito yayi mata 'kwaro-'kwaro.

A 6angaren habu kuwa yariga yasan an kawo amarya, yaje gun 'yan uwanshi yaro'kesu akan suje gidan ayi d'an s

hagalin bikin da akeyi bayan an kawo Amarya amma sukace "ina ay basu gaji da rayuwaba tukun, waye ze kai kanshi ga halaka.

Indo kuwa taso zuwa bikin 'kawarta kuma aminiyarta, amma ilu ya bad'e ido toka yace bazataba, 'karshe data isheshi da magiya sai c

ewa yayi idan ta'kara maganar zuwa bikin Laraba to bakin aurenta, hakan yasa ta ha'kura badan ranta yaso ba.

Bayan habu yagama fama da 'yan uwanshi akan suje gidanshi sun'ki sai yatafi gidan 'kanwarsa hansai, da sallama yashiga gidan, ta amsa sannan ta

gaisheshi ya amsa, nan yake tambayarta

"Hansai ya ban ganki gurin bikin ba, lafiya kuwa? Hansai ta yamutsa fuska tace lafiya lau, kaina ne yake d'an yimani ciwo, cike da tausayi yace eyyah Allah sauwa'ke tace Ameen.

Yace Amma naga kamar kin d'anji s

auki, kozaki daure ki le'ka gidan kai amaryar,

Cikin firgici Hansai ta kalli yayanta tace "wah ni Yaya habu, idan ka ganni lahira kaini akayi, wallahi bazani gidan *mayya* ba.

Cikin 6acin rai habu ya d'auke hansai da mari yace "idan bazakiba ki zauna,

amma kada ki kuma kiran matata da *Mayya* yasa kai yafice ranshi a 6ace.

Me zai faru yana fita daga gidan Laraba yagani tanayimashi murmushi, ta 'karso gurinshi tace masoyina nagaji da jira ne gida ni 'kad'ai shine na biyoka...

cike Da mamaki yace "y

a akayi kikasan ina nan, murmushi kawai tayi Mashi ta kama hannunshi suka nufi gida.

🖊

Zee Elkaseem

Mmn Khady

💋

[10/16, 8:10 PM]



😭

*_ALHINI_*

😭

🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇

®``

`NWA```

_written by_

*_Zee Mmn khady_*

😘

1

⃣

9

⃣

to2

⃣

0

⃣

🖊

Tafiya suke Laraba na ri'ke da hannun angonta Habu, sai da sukayi nisa da gari sun shiga gonaki, baka ganin kome sai duhun daji da kukan tsuntsaye,

kasancewar akwai 'yar tazar

a tsakanin gidan Hansai da gidan Laraba, sun shiga cikin duhun ciyayi, Habu ya waigo ya kalli Laraba yace "Amma Laraba nayi mamakin yanda kika san ina gidan Hansai, kodai wani ya gaya maki ina nan?

Shuru yaji tayi batada niyyar amsa mashi tambayar da ya

yi mata, hakan yasa ya juyo ya kalleta, suna had'a ido da ita gabanshi yayi mummunan fad'uwa dan ganin ta yayi ta d'ad'd'aure fuska yanda kasan tunda Allah ya halicceta bata ta6a dariya ba, ga fuskar tata tayi duhu, ba alamar haske tattare da ita, kamar ba

larabar da yasaniba, kya'kyawar yarinya fara tas fatar ta kamar ka ta6a jini yafito, amma lokaci guda ta sauya takoma ba'ka, ga fuskar ba Alamun fara'a tattare da ita.

Lokaci guda jikinsa yafara 'kyarma kamar mazari, yakasa matsawa daga inda yake, sai

da 'kyar yasamu ya iya daga baki yace La....la....Lara...ba, miya sa kika biyoni, miyasa zaki tsoratar dani......

Kafin ya rufe bakinsa yaji ta gagga6e da wata irin mahaukaciyar dariya tace,

"Tambaya kake yanda akayi nasan inda kake, to ayni ba sai

na tambaya ba, tunvdaga ranar daka furta kalmar so gareni nake biye dakai, kuma kasani sai nazama ajalinka..... Hhhhhhhhhhhhhhhhh, ta 'kara gagga6ewa da wata nahaukaciyar dariya karo na biyu.

Habu kuwa banda 'kyarma ba abinda yake, yariga yagama sad'auk

ar da rayuwarsa, dan yasan 'karshen rayuwarsa ne yazo, kwata-kwata kasa yin wata addu'a yayi dan tsananin tsoro, sun kai kimanin minti ashirin tsaye gurin Laraba, tana tsoratar da Habu.

Sai zuwa can Allah yabashi ikon furta kalmar *lnnalillahiwa,inna'il

aihirraji'un* sannan yasamu 'kafar guduwa daga gurin,

Gudu yake iyakar 'karfinsa, domin yau ya tabbatar ma kanshi maganar da mutane ke fad'a suna cewa Laraba *mayya* ce, a zuciyarshi yana cewa koma miye Nina jawoma kaina, dama ance _(Wanda beji bari ba

yaji hoho)_.

😱

Lokaci guda yahad'a wani uban gumi, ga tsabar tsoro ga kuma uban gudun dayasha, da kyar yashiga gida ya maida 'kyaure yarufe, yana maida numfashi.

'Daki yanufa yana nishi yana goge uwar zufar data rufeshi kamar wanda aka watsama r

uwa,

Mutuwar tsaye yayi dan wani babban tashin hankalin daya tarar a gidan, yasan dai yabaro Laraba a daji, amma kuma yanzu gata ya tarar da ita kwance kan 'yar katifarta tana kuka.

Jin alamun shigowar mutum yasa Laraba tashi daga kwancen datake, ta

d'ago da manyan idanunta wanda suka kad'a sukayi jawur saboda tsabar kukan data sha.

Cike da mamaki Habu ke kallonta, a zuciyarshi yace "to wai miye ke shirin faruwa dani ne, kodai ba Laraba bace wacce nabaro a daji.

Ganin bashida niyyar ida 'karaso

wa cikin d'akin yasa Laraba tayi magana "Sannu da zuwa, tafad'a cikin zazza'kar muryarta mai sanyin sauraro.

"Yauwa yafad'a zuciyarsa na dukan ukku-ukku, "bari inje in dawo nayi mantuwa a gida, cike da tsoro Laraba tace "miye kuma ka manta, nifa wallahi

tsoro nakeji ni d'aya gida, a zuciyarsa yace _"Ai kece abin tsoron laraba, ke yakamata aji tsoro bake zakiji tsoron wani abu ba_

"Tinanin me kakeyine, ta tambayeshi dan ganin ya tsaya a gun bayada niyyar tafiya,

Yayi saurin dai-daita nutsuwarsa ya

ce "a'a zanje bari intafi bazan dad'eba zan dawo, sannan yasa kai yafice, cike da tsoro yafita daga gidan, zuciyarshi cike da tunani kala-kala.

Tafiya yake bekoyi nisa da gidan ba amma wani mugun abun tsoro daya gani shine yakusa sanya numfashinshi ya d

'auke, dan Laraba yagani gabanshi, ta kashe d'an kwali ta ri'ke 'kugu tana jijjiga jiki, suna had'a ido ta gagga6e da wata mahaukaciyar dariya, sannan kuma ta d'aure fuska kamar bata ta6a dariyaba.

Tace "Habu kana gan-ganci da rayuwarka, inaso kafin nan

da safiya ka gaggauta yankema kanka hukuncin daze fitar dakai.

🏃🏻

Da gudu yayi baya yakama hanyar gidanshi, tashin hankali wanda ba'a samashi rana

😳

Laraba ya iske a tsakar gida tafito daga kewaye hannuta ri'ke da buta.

Wata irin gigitattar 'kara

yasaki nan take yafad'i 'kasa kanshi yabugu da wani dutsi dake tsakar gidan, aiko kan yafashe jini yafara zuba.

_Innalillahiwa'inna,ilaihirraji'un_ Laraba tashiga furtawa, tanufi inda Habu yake kwance tana jijjigashi tana kiran sunanshi amma ba alamar

numfashi tattare dashi.

🖊

Zee Elkaseem

Mmn khady

💋

[10/16, 8:10 PM]



😭

*_ALHINI_*

😭

🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇

®```NWA```

_written by_

*_Zee Mmn khady_*

😘

2

⃣

1

⃣

to2

⃣

2

⃣

🖊

"wayyo nashiga ukku dan Allah habu katashi kada ka mutu, idan kamutu nasan bazan 'kara shan ruwa garinnan ba, dan Allah ka taimakeni, Laraba ce ke fad'in haka cikin muryar kuka,

Yayinda habu yake kwance har yanzu besan inda kanshi y

akeba, ga kuma inda kanshi yabugu har yanzu zubar da jini yake,

"Ya salam laraba tafad'a "Lallai rayuwata tana cikin had'ari ya Allah ka fitar dani, wasu sabbin hawaye suka gangaro kan kumatunta.

Lokaci guda jikinta ya mutu li'kis kamar wacce akayima

duka

Ta tashi da sauri tanufi d'aki ta dauko wani tsohon zani cikin zannuwanta ta yaga ta d'aurema Habu kanshi inda jini ke zuba, cikin ikon Allah kuwa sai jinin ya tsaya, amma har yanzu ba Alamar numfashi tattare dashi,

Sai lokacin dabarar ta yayyafa

mashi ruwa ya fad'o mata a arai, da sauri tanufi randa ta d'ebo ruwa me sanyi ta yayyafa mashi, a firgice ya tashi yana "cewa

"dan Allah kiyi ha'kuri Laraba kada ki kasheni, Laraba ni me 'kaunarki ne bekamata ki sakamin da sharri ba.

Wata irin 'kara Lar

aba tayi, cikin wata gur6atacciyar magana take cewa, Habu bazan ta6a raga makaba, babu ragi ba ragowa tsakanina dakai, nariga na gaya maka kafin gari ya waye ka nemama kanka mafita,

Cike da tsoro da firgici habu ya kalli Laraba, yaga fuskarnan tata ba A

lamar sassuci, tabbass idan yaci gaba da zama da ita ze iya rasa rayuwarsa, hakan yasa ya yanke shwarar rabuwa da ita.

"Laraba"yakira sunanta,

Jiki a sanyaye ta juyo ta kalleshi, yace "kije na sakeki *Saki ukku*

Daga yau babu ni babu ke,

"Hhhhhhhhh

hhhhh, wata irin mahaukaciyar dariya sukaji ta gauraye gidan, har tsawon minti biyar sannan dariyar ta lafa, wata irin murya sukaji wacce basu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login