Showing 12001 words to 15000 words out of 31402 words

Chapter 5 - ALHINI complete.

yaji gabansa ya fad'i dan bacin yasan uwani da jidda suna d'akin da sai yac

e wannan ba yarinyar daya tsinta bace, saboda wani masifaffen kyau datayi mashi.

Tambaya yayi taci abincin kuwa, Uwani tace "jira nake agama shirin sai in zuba mata abincin, wata harara yayima jidda dan yasan kicifin tane, mutumin da beda lafiya har wan

i shiri za'ayimashi.

Da kanshi ya had'a tea mai kauri Wanda yaji madara da Milo ya mi'ka mata.

Ba musu ta 'kar6a ta kafa kai ta shanye, dayake tanada bu'kata dama, sannan aka zuba mata jallouf d'in wake da shinkafa wanda yaji kayan lambu da hanta, nan

ma taci amma kad'an kasancewar tean data sha yacika mata ciki.

🖊

Zee Elkaseem

Mmn khady

💋

[10/16, 8:11 PM]



😭

*_ALHINI_*

😭

🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇

®```NWA```

_written

by_

*_Zee Mmn khady_*

😘

2

⃣

9

⃣

to3

⃣

0

⃣

🖊

sai bayan sallar isha'i sukayi niyyar barin asibitin bayan sun yanke cewa Uwani zata zauna gurin Laraba, aiko itama jidda kafewa tayi dole sai an barta ta kwana gurin Laraba, saida mukhtar yayimata fad'a

sannan suka tafi, ranta yayi matau'kar 6aci dan an hanata kwana gurin Laraba,

Haka suka tafi tanata zum6ura baki ita a dole fushi take, dan ko surutun data sabayima yayan nata yau batayiba tunda ya 6ata ranta,

Yana lura da ita yanda taketa cika tana b

atsewa, amma sai yayi kamar besan tanayiba,

A haka suka iso gida, bakin get sukayi horn me gadi ya bud'e masu get suka Shiga, gurin ajiye motoci yayi parking d'in motarsa, kafin ya gama gyara parking tafito daga mortar tanufi cikin gida da gudu, tana zuw

a falo bata taradda Hajiya ba, saboda haka bedroom d'inta ta wuce kai tsaye, zaune ta isketa kan abin sallah tana tasbihi, fad'awa tayi jikinta tana kuka,

Cike da mamaki Hajiya ke tambayarta "lafiya jidda meya faru, meya saki kuka ina yayan naki,? Kafi

n ta bata amsa sai gashi yashigo, cikin ladabi yake gaisheda hajiyarsa, sannan yace "Hajiya bafa wani abune yafaruba, kawai dan nace bazata kwana asibiti bane shine take fushi,

Murmushi Hajiya tayi tace "haba Jidda yaza'a barki ki kwana, asibiti ayba g

urin zaman yaro bane, kibari idan Allah ya kaimu gobe tunda ba school sai mu tafi tare nima zanje in gano yarinyar,

Haka Hajiya tayita rarrashinta har tasamu ta saki ranta, tayi murmushi tace "Hajiya bakiga yarinyar ba wlh kya'k'kyawa da ita, ni naji d

ad'i nasamu 'kawa, Hajiya tayi murnushi tace daga ganin sarkin fawa sai miya tayi za'ki, daga ganin yarinya sai kice kinyi 'kawa,

Mudai iyakarmu taimako, kuma data samu lafiya ta warware zamu maidata ga iyayenta, nasan yanzu duk inda iyayenta suke suna ca

n hankalinsu ba kwance ba,

Jidda tayi saurin tashi daga kwancen datake kan cinyar Hajiya tace "dan Allah Hajiya kada a maidata, inasonta inaso tazama 'kawata,

Hajiya bata cemata komeba sai murmushi kawai tayi, *(Yaro man kaza)* sai lokacin Mukhta

r yayi magana yace "kedai baki gajiya da shirme, ke yanzu kinaso arabaki da Hajiya wasu su ri'keki,

ta turo baki tace to ayni hajiyata na sona bazata barni da yunwa ba,har in kusa mutuwa wasu su tsinceni, harara yayi mata sannan yafita yabar d'akin.

'Dakinsa yanufa kai tsaye zuciyarshi cike da tausayin Laraba, shi kanshi yanda jidda tafad'a hakane bayason rabuwa da Laraba, dan tsakanin wannan d'an lokacin wani irin abu yakeji dangane da ita,

Da wannan tinanin yafad'a toilet ya she'ka wanka,

sannan yafito ya canja kaya, jallabiya yasa me gajeren hannu sannan yanufi babban falo, can ya iske Hajiya da jidda kan dining suna niyyar cin abinci, shima kujera d'aya yajawo ya zauna kusa da hajiyarsa, jidda ce ta zuba mashi tuwon shinkafa da miyar Alay

yahu, sai 'kamshin curry ke tashi,

Haka suka ci abincin kowanensu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, bayan sun 'karasa suka kora da kunun aya me sanyi, sannan suka ta6a fira

Sai gurin 'karfe goma sannan, sukayi bankwana, mukhtar ya wuce d'akinsa, ji

dda kuwa d'akin Hajiya tanufa, Hajiya ta kalleta tace "kika biyoni nan d'akin naki kuma fa? Cikin shagwa6a tace "Hajiya ki barni in kwana anan idan aka sallamo Laraba ta dawo nan gidan sai mu koma d'akin nida ita kinga nasamu abokiyar

fira, murmushi Hajiya

tayimata sannan ta canja kaya zuwa kayan bacci, itama jidda kayan baccin ta sanya sannan suka haye katafaren gadon wanda yasha wani lallausan bedsheed, sukayi addu'a suka shafe jikinsu.

Mukhtar kuwa koda ya koma d'aki tinanin Laraba ya zauna a kwa'kwal

warsa, cikin zuciyarshi yari'ka ro'kon Allah sa iyayenta su yarda ta zauna tare dasu, dan shima har ga Allah baya son rabuwa da ita, yarinya 'kya'k'kyawa amma dayake 'kauye ta taso sukayi sakaci da rayuwarta har tana neman halaka.

Da wannan tinanin bacc

i yayi awon gaba dashi bayan yayi addu'a Ayatul kursiyyu da qula'uzzai ya shafe jikinsa.

_```Waye Mukhtar```_?

Mukhtar Abass shine asalin sunanshi, haifaffen d'an garin katsina ne, a wata unguwa me suna 'yan,shuni.

Mahaifinshi Alh Abass, mutum ne

mai ilimin addini, kuma yana aiki dashi, dan duk wani abu daya shafi addini yana fidda dukiyarshi yayi hidima da ita, shiyasa kullum Allah ke 'kara bud'a mashi, kuma dama yana dukiya me yawa ga kuma taimakon na 'kasa dashi da miskinai, ga fidda zakka duk s

hekara kamar yanda Allah ya hukuta.

sunyi auren saurayi da budurwa da matarshi wato Hajiya Zainab, bayan aurensu da shekara ukku Allah yabasu haihuwa inda suka haifi namiji aka sanya mashi suna Aliyu, har Aliyu ya shekara bakwai Hajiya Zainab bata kuma

haihuwa ba, wata rana an taso su Aliyu makaranta yafito bakin titi yana jiran driver yazo d'aukarsu wata mota ta bankeshi, kafin akaishi asibiti rai yayi halinsa, Hajiya Zainab da Alh Abass sunyi kukan rashin d'ansu, 'karshe suka ha'kura suka fawwalama Al

lah lamuransu, kuma daga lokacin Hajiya Zainab bata kuma samun cikiba sai bayan shekara biyu tasamu cikin mukhtar, bayan an haifeshi ne da shekara bakwai aka haifi jidda, wanda daga ita hajiya Zainab bata kuma haihuwaba.

Jidda nada shekara ukku Allah ya

yima mahaifinsu Alh abass rasuwa bayan yayi fama da gajeruwar rashin lafiya,

Bayan rasuwar Alh Abass da shekara d'aya 'yan'uwan Hajiya zainab sunso takoma garesu amma sai tace sam bazata komaba zata zauna ta ri'ke yaranta dan bataso ta dorama wani nauy

insu.

Haka Hajiya Zainab tacigaba da kula da karatun yaranta da tarbiyarsu, amma haka be hana 'yan,uwan Alh Abass taimakonsuba, dayake mahaufinsu mutum ne mai taimakon 'yan,uwa.

lokacin da muke yanzu, mukhatar yazama cikakken d'an kasuwa, dan sana'a

r babansa kenan kafin ya rasu, hakan yasa mukhtar karantar business, ga kuma kiyo da suke a gidan gonarsu da mahaifinsu ya bar masu gado, lokcin da mukhatar ya tsinci laraba gidan gonar tasu yanufa, sai Allah ya had'ashi da ita.

Jidda kuwa yanzu take ju

nior secondary, j.s.s 3 bana zasu zana jarabawa.

*_WANNAN SHINE TAKAITACCEN TARIHIN MUKHTAR_*

🖊

Zee Elkaseem

Mmn khady

💋

[10/16, 8:11 PM]



😭

*_ALHINI_*

😭

🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇

🐇

®```NWA```

_written by_

*_Zee Mmn khady_*

😘

3

⃣

1

⃣

to3

⃣

2

⃣

🖊

Haka Uwani tacigaba da kula da Laraba, yayinda mukhatar kullum sai yayi zuwa yakai shidda asibitin, dan bayaso anemi wani abu baya nan, hajiyar Mukhtar kuwa sau ukku tana zuw

a ganin Laraba, jidda kuwa 'yar rigimar kullum nan take yini, kuma sai anyi daga da ita gun komawa gida, dan kullum kafewa take sai ta kwana,

Satin Laraba d'aya asibitin taji sauki sosai, ta'kara fari tayi wani fresh, dan har 'yar 'kiba tayi, tana samu

n kulawa sosai daga malaman asibitin zuwa ga mukhtar sai kuma Uwani me aiki itama tana bakin 'ko'karinta.

Yau Likitan dake dubata yazo round nan ya duba jikin uwani ya tabbatar da kome normal, sannan yarubuta masu sallama.

Mukhtar ne ya d'aukesu a mo

ta, jidda ce gaban mota kusa da yayanta, yau dai farin ciki fal a zuciyarta, dama kullum addu'a take a sallamo Laraba 'kawarta ta dawo gidansu da zama,

uwani da Laraba kuwa bayan motar suke sunata sauraren jidda da keta zuba uban surutu.

Dai-dai g

et d'in gidan sukayi horn me gadi ya bud'e masu get suka shiga,

Tunda sukazo Laraba kebin gidan da kallo, saboda tsananin 'kyawunsa, cikin zuciyarta tace _"Anya ba mafarki nake ba, dan bani tinanin akwai irin wad'annan gidajen nan duniyar da muke_

Nik

o nace *Hmm Laraba kenan sai ma kin shiga gidan zaki tabbatar da ba irin duniyar da kk sani bace, (wani hanin ga Allah baiwa ne)*

Jidda ce takama hannun Laraba sukayi cikin gida, wani irin tsoro yakama Laraba dan ganin 'kawatuwar falon, kai lallai dama

ashe akwai masu irin wannan jin dad'in a duniya, haka kawai take fad'a a zuciyarta.

Cike da murna da sakin fuska Hajiya ta tarbesu tanayimasu sannu da zuwa, jidda kuwa murna yau gurinta bakin har ya'ki rufewa, da kanta ta zaunar da Laraba kan kujera tac

e "Zauna 'kawata ki huta kafin anjima kiyi wanka,

Laraba dai kallon mutanen kawai take, duk abinda sukace shi take yi, tazama tamkar ra'kumi da akala,

Bayan sallar azahar suka zauna kan dining suna cin abinci, jidda ce ta matsama Laraba ta zauna suci

, amma ita duk d'arare take ba kamar idan da mukhtar gurinta dan wani irin kwarjini yake mata.

Bayan sun kammala ne jidda ta kama hannun Laraba tace 'kawata zo muje ciki kiyi wanka ki canja kaya, ba musu Laraba tabita zuwa d'akinta,

Toilet taje t

a had'a mata ruwan wanka, tare da zuba mata turarurrukan wanka masu 'kamshi gaske, sannan tazo ta kama hanunta ta kaita har toilet ta gwada mata yanda zatayi, sannan ta jawo mata 'kyauren tafito tana jiran ta.

Laraba ta dad'e tana dirje jikinta a kewaye

, kafin tafito d'aure da zanin atamafa jikinta, dan 'kin yarda tayi da d'aura tawul, dan bata ma san yanda zata d'aura shiba.

Jidda tace "harkin fito, ta kamo hannunta zo inyimaki kwalliya irinna larabawa, laraba tayi murmushi tace " Hmm jidda kenan'har

wata kwalliyar larabawa akeyi, jidda tayi dariya tace kedai bari kigani idan nayimaki ke kanki sai kin kasa gane kanki, murmushi kawai Laraba tayimata, dan abun jidda har mamaki yake bata yanda take nan-nan da ita, tun batayi mata magana har tad'an fara s

akin jiki tana maida mata amsa idan tayimata.

Haka jidda ta zaunar da Laraba gaban mirror tafara d'and'asa mata kwalliya, make-up tayi mata sosai, fuskar nan tafito ta larabawan sak yanda jidda ke fad'a, dan ba 'karamin kyau Laraba tayiba, dan koda ta k

alli fuskarta a madubi kasa sheda kanta tayi, in baccin ma jikinka jikinka ne da Laraba tace ba fuskarta bace a madubin.

Jidda kanta tsayawa tayi tana kallon kyawun da Allah yayima Laraba, kasa yin shuru tayi tace _"tsarki ya tabbata ga ubanjin daya ha

litta wannan 'kya'k'kyawar sura_, juwowa Laraba tayi dan ganin wace kya'k'kyawar sura ce jidda ke fad'i amma bataga kowaba sai jiddar hakan yasa ta tabbatar da ita jidda take.

Murmushi tayi tace, kai jidda wallahi baki gajiya da zaualaya, yanzu nice kik

ema wannan zuzutawar, bayan nasan kin fini kyau nesa ba kusa b....... Jidda tayi

saurin sa hannu ta rufe bakin Laraba tace, bari kada kiyi sa6o, inani ina had'a kaina dake,

Wadrope d'inta tanufa ta d'auko ma Laraba wasu riga da zani na less cikin kayant

a, tace "amshi ki saka wannan nasan zeyi maki 'kyau.

Laraba ta gyad'a kai tace "jidda da kinbar kayanki na sanya cikin wanda Yaya Mukhtar ya siyomin, tunda akwai ma wanda ban sanyaba har yanzu,

Jidda ta harareta cikin wasa tace banison haka, ay nice

nace ki sanya idan kuma bazaki sanyaba to ki gayamin, bata jira me Laraba zata fad'aba tashige toilet domin itama ta watsa ruwa.

Haka laraba ta rin'ka juya less d'in a hannunta tana yaba kyawunsa, dan ko a mafarki bata ta6a tunanin zata sa irin wannan

kayanba, Allah mai yi yanda yaso da bawanshi, wasu siraran hawaye suka zubo daga idonta dan tunowa datayi da Innarta, tasa hannu tayi saurin gogewa dan kada jidda tafito taga tana kuka ta isheta da tambaya, dan tagama karantar halin jidda ahegen surutu gar

eta, ga kuma tambayar tsiya kamar tamabai......

🖊

Zee Elkaseem

Mmn khady

💋

[10/16, 8:11 PM]



😭

*_ALHINI_*

😭

🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇

®```NWA```

_written by_

*_Zee Mmn

khady_*

😘

3

⃣

3

⃣

to3

⃣

4

⃣

🖊

Bayan sun kammala shirinsu tsaf, Laraba ta sanya less d'in da jidda tabata ta Sanya, aiko less d'in yayi masifar yimata kyau ya zauna d'as ajikinta, itama jidda less ta sanya tayi kyau sosai, ta kalli Laraba tace kin san wa

ni abu,? Laraba ta gyad'a kai Alamar a'a, Jidda tace wannan kwalliyar gurin Yaya kawai yakamata muje yaga yanda kikayi kyau, 'kilama idan ya ganki baze ganekiba,

Laraba tayi murmushi tace, "sai dai idan wata fuska na canja, to sannan na yarda baze ganeni

ba, amma fuskar da yayi kusan sati biyu yana tare da ita yaushe dan yau d'aya kinyi min kwlliya kice baze ganeniba.

Jidda ta kyal'kyale da dariya tace "lnda ba 'kasa nan ake gardamar kokowa, inaji ai yayan yana gidan ba inda yaje saboda haka muje araba

gardama,

Laraba ta zaro ido tayi dariya tace "kefa dad'ina dake jidda baki gajiya da shirme, to idan munje muce masa me?

Jidda tayi dariya tace kedai kibar komi a hannuna, yau zaki tabbatar ma kanki tsananin kyawun da kikayi idan ni baki yarda da mag

anata ba,

bata jira me laraba zata fad'a ba ta kama hannunta tace "zo muje, laraba ba yanda zatayi da jidda haka yasa tabita kawai, cike da mamakin shirme irinna jidda..

A falo suka iske Hajiya tana hutawa, suduka suka iso gareta suka rissana sukace

"barka da hutawa, ta kai dubanta garesu, wani irin fad'uwar gaba Hajiya taji dan ganin wani irin kyau da Laraba tayi mata, cikin zuciyarta tace *Allah sarkin halitta lallai Allah ya ajiye kyau tattare da Laraba ga nutsuwa da sanin ya kamata*

Cikin fara

'a Hajiya ta amsa "yauwa 'yan matana, wannan kwalliya haka, kamar 'ya'yan saraki, murmushi laraba tayi cike da jin kunya, Jidda kuwa dariya tayi tace "Allah Hajiya laraba tafi 'ya'yan sarki kyau, murmushi kawai Hajiya tayi masu,

Jidda takama hannun Lar

aba, suka nufi hanyar fita daga falon, Hajiya tace "ina zaku haka,? Jidda tace zamu gurin Yaya ne, Hajiya tace to 'yan gidan Yaya, idan kunje kuce ina nemansa yanzu, kutaho tare, tare suka had'a baki suka amsa da "to.



A lambun gidan suka tarar dashi,

yana zaune kan wasu fararen kujeru, gabanshi kuma wani 'karamin table ne d'auke da laptop d'insa yana danne-danne, gefe kuma fresh milk ne da cup d'in glass, besan isowarsu ba saboda haka jidda tace ma Laraba "kawata ki tsaya bayan wannan flower so nike in

ba Yaya mamaki, laraba tace "wane irin mamaki zaki bashi kuma? Jidda tayi saurin rufe mata baki tare da jan hannunta ta turata bayan wata flower, sannan ta isa ga yayanta wanda hankalinshi na kan computer shi, bema san sun zo gurin ba.

Sallama jidda ta

yi mashi, d'ago kanshi yayi yakai dubanshi gareta sannan ya amsa sallamar, murmushi yaga tanayi, saboda haka yasan akwai magana tattare da ita, hakan yasa ya tambayeta "ya dai 'kanwata? Ta 'kara fad'ad'a murmushin dake fuskarta tace Hajiya ce ta aikoni gur

inka, amma kafin in gaya maka sa'kon inaso in baka *surprise* yayi murmushi yace mamakin me za'a bani kuma? Tace kaidai ko miye zakagani amma ka rufe idonka tukun.



Yasaba da shirmen 'kanwarsa saboda haka beyi musuba yasa hannu ya rufe idonsa, yana jira

n yaga yau kuma da wane shirman tazo mashi.

Tana ganin yarufe idonshi tayi saurin zuwa inda ta 6oye Laraba ta kamo hannunta suka nufi inda Mukhtar yake zaune.

Laraba nagani haka tarin'ka bin jidda kamar ra'kumi da akala, saida sukaje gaban mukhtar sa

nnan tace "Yaya bude idonka,

Ahankali ya sauke hannuwanshi daga idonshi ya saukesu kan laraba, kallonta yacigaba dayi, cikin zuciyarshi yace *tsarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci wannan 'kya'k'kyawar yarinya, lallai Allah ya ajiye kyau a nan* .

Laraba ta kula da yanda mukhtar ya tsareta da ido hakan yasa taji duk ta tsargu, takama hannun jidda tana janta Alamar tazo su tafi, dariya jidda tayi, wacce ta dawo da mukhtar daga dogon tinanin dayake, tace "Yaya dama hajiyace tace kazo yanzu tana nem

anka.

Basu jiran amsarshiba suka wuce cikin gida, Jidda na dariyar yanda yayanta ya tsare Laraba da ido, Ita kuwa Laraba bata ji da'din hakan ba amma bata nuna ma jidda taji haushi ba ko kadan.

_*Kuyi ha'kuri da wannan

👆🏻

yau ina busy be*_

3

⃣

5

⃣

to3

⃣

6

⃣

very

🔜

🖊

Zee Elkaseem

Mmn Khady

💋

[10/16, 8:11 PM]



😭

*_ALHINI_*

😭

🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇

®```NWA```

_written by_

*_Zee Mmn khady_*

😘

3

⃣

5

⃣

to3

⃣

6

⃣

🖊



Laraba na ri'ke da hannun jidda suka shigo falon, suka samu guri suka zauna, basufi minti biyar da zama ba sai ga yayan su yashigo, cike da ladabi ya zauna kan kujerar dake facing d'in Laraba ya zuba mata idanunshi masu tsananin

kwarjini yana kallonta, ita

ko ta lura da yanda yake kallonta hakan yasa duk ta daburce.

Hajiyace tayi gyaran murya tare da 'kara gyara zamanta tace "am mukhtar abinda yasa nace akira mani kai shine kan maganar Laraba,

Wata irin fad'uwar gaba laraba taji dan jin maganar da Hajiy

a tayi, a zuciyarta tace _"shikenan nasan lokacin barina gidannan yayi, dan nasan muddin suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login