Showing 27001 words to 30000 words out of 32230 words

Chapter 10 - MUMMUNAN ZATO BOOK1 COMPLETE

ta ce, gaskiya kam, amma dai ka raba mana kwana saboda ko bata gyara maka shinfi

ɗ

ar ba, saboda ƴan matsalolin ta kaga sai ka rinƙa ji,ya ce haka ne.

Bayan sun gama

jawabansu, tana dai jin su,ta ƙosa ta koma

ɗ

aki don jinta take tamkar kan ƙaya,ba don komai ba sai don Jummai,don haka ta soma hamma,ya ce je ki ƙwanta ai kafin ya rufe baki har ta miƙe ta nufi

ɗ

akinta.

Jummai ta dube shi, Alhaji ni ko nawa ganin ba yi ba

ne kace zaka ƙyale ta,ka san yaran yanzun da wayonsu sarai,mu da muke son yara ka tsaya renonta? Ya yi shiru, sannan ya ce ni abubuwan ne sun min yawa dubi fa yarinyar zan cutar da ita,ƙirjin ma babu komai sannan sai in dinga ganin tamkar in na ƙwanta da s

u ne suke mutuwa,shi yasa nake tsoro.

Jummai ta zaro idanu "kada fa asirinta ya tonu,ta ce mishi haba dai to da haka ne dani yanzun sai dai labarina ka daina wannan tunanin." Shiru ya yi yana nazarin maganarta,sai dai shi kam nashi ra'ayin ba zai ta

ɓ

a

ɗ

an

ɗ

ana nauyin juna ba yanzun a tsakaninsu,yana ganin in ya

ɓ

ullo da haka

ɗ

an sakin jikin da take mishi zata daina, amma sai ya bar wannan a ranshi don sirrinshi ne. Ya dubi Jummai ya ce haka ne,shi kenan sai ku riñƙa yin ƙwana bibbiyu in na gama ƙwanakina ci

ke da jin da

ɗ

i ta ce Allah ya taimake mu ya bamu Sa'a, ya ce amin.

Abinda ya soma

ɗ

aga hankalin Jummai shi ne,yau satin amarya biyu, kullum tana jiran ta ji Alhaji Saddiƙ ya ce jama'a ku zo, har yau shiru. In ta kira Karima ta mata magana sai ta ce bata d

a haƙuri ne sun ta

ɓ

a yin wannan abin ya yi musu gaddama? Ta ce ko dai har yanzun bai ƙwanta da ita bane? Jummai ta ce oho amma yau zan bugi cikinta. Matsiyaciyar yarinya kina ganinta haka na kula zata yi salo don yanzun kin san kullum daga Ofis sai ya aiko

an kar

ɓ

ar mishi wani zo

ɓ

o da take mishi?" Kari ta ce daina bani labari, zan dai zo gidan gobe.

A'isha kam yanzun tafi ƙosawa da karatunta,don haka sai ta

ɗ

ebo littattafan ta na makaranta tana ta karantawa, Uncle ya shigo ta ajiye ta miƙe tare da yi mishi

sannu da zuwa,da sha'awa ya dubi takardun me ki ke karantawa ne Beby ? Ta ce ina

ɗ

an duba books

ɗ

ina ne na school,ya ce kin tuna min,an kusa a koma hutu ko? Ta ce ni da jiya ma zan koma Sunday. Ya zauna kina son makarantarki ne ko in samar miki wata? Ta y

i shiru sannan ta ce duk yanda kace bani da za

ɓ

i Uncle,da

ɗ

i ya ji sannan ya ce to shikenan,nan da ƴan ƙwanaki zaki ƙara zama student ko Bebyna? Ta yi dariya har kumatunta suka lo

ɓ

a. Abinda yake burge shi sosai.

A'isha tana ta gyaran

ɗ

akinta domin tunda ta

ke sau

ɗ

aya ƴar aikinta ta ta

ɓ

a zuwa ta gyara mata daga nan bata dawo ba,don haka sai ta ci gaba da aikinta,dama ba ta

ɗ

auke shi aiki ba,ta gama ta jona na'urar da ake saka turaren wuta,ta zuba nan fa ƙamshi ya soma tashi. Hajiya Jummai da Hajiya Kari suka

yi sallama,ta amsa nan take gabanta ya shiga fa

ɗ

uwa ta soma karanta Allahumma kafihim bima shi'ita,domin yanzun addu'ar da ta koma karantawa Jummai kenan.

Suka shigo ta zauna ƙasa ta sunkuyar da kai,su kuma suka zauna bakin gado. Ta gaishe su kanta yana

ƙ

asa suka amsa cikin fara'a, sai kurum suka ji an bugo ƙofa a tsorace A'isha ta

ɗ

ago kai. Suwaiba ce cikin rashin kunya ta ce Hajiya ki zo kinyi baƙi,me kike yi ne

ɗ

akin wannan ƴar ƙauyen? Jummai ta miƙe tana cewa ubanki nake yi kin ji ko? Ta bita suka fit

a. Hajiya Kari ta girgiza kai tare da cewa, Allah wadaran irin wannan tarbiyya da Jummai ta koyawa yaran nan, ta dubi A'isha ƴar nan sai fa haƙuri kin dai ga abinda nake gaya miki nan,ta sake matsowa gaya min yanda kuka yi da Alhajin naki,baki dai gudun sh

i ko?" A'isha ta

ɗ

aga kai amma zuciyarta cike da tsanar matar, ta ce yauwa ƴar nan,to ya ya kukeyi

ɗ

akinshi ki ke zuwa? Ran A'isha ya

ɓ

aci ta yi mata banza tana ta tambayarta A'isha tayi shiru, da ta matsa mata sai ma ta saka kuka.

Hajiya Karima ta ce yau

na shiga uku daga tambaya? To yi haƙuri,wayar A'isha ta soma ringing ta share hawayenta ta

ɗ

aga Uncle ne ya ce na turo direba, ya amshi zo

ɓ

on nan na ji shi shiru, ta ce bai zo ba ko ƙila yazo bai samu wanda zaya aiko ba, ya ce to bari na kira Uche ya amsa

ya bashi,ta ce to sai ka dawo, ya ce ba wata matsala ko? Ta ce a'a babu komai ta ajiye wayar bayan ta kashe ta kalli in da Karima take, tana nan zaune ba ta koma ta kanta ba, sai kawai ta shiga ha

ɗ

awa Uncle

ɗ

inta zo

ɓ

on da ta riga ta ha

ɗ

a cikin wani

ɗ

an ƙy

akƙyawan ƙwando,yau har da cin-cin da diblan ta ha

ɗ

a irin na bikinta ta zuba cikin wani

ɗ

an ƙwanon tangaran saiti ne da jug

ɗ

in ta zuba kofunan jug

ɗ

in Uche ya ƙwanƙwasa ƙofar ta bu

ɗ

e mishi sannan ta bashi tana juyowa taga Hajiya Kari ta miƙe ta ce, to sai

anjima tunda kin ƙi mu yi hira A'isha can ƙasan maƙoshi A'isha ta ce to ta shige toilet.

########

[12/6, 16:20] Ummi Tandama

😇

: *

📗

Page 15*

Cike da al'ajabi Kari ta isa

ɗ

akin Hajiya Jummai da sauri, Jummai ta miƙe ta ce ta sanar dake komai? Karima

ta ce, ina fa, wannan yarinyar tana da shegen wayo, na lura muna mata kallon biri ne ita kuma tana mana kallon ayaba.

Jummai ta dafe ƙirji ya ya ku kayi ne? Karima ta zauna,yarinyar da na matsa mata sai kurum ta saka min kuka,can kuma in gaya miki sai Alh

ajin ya kira ta,zo kiga kashe murya don sanabe Uncle ma take ce mishi an ha

ɗ

a su so

ɓ

o da cincin an kai mishi.

Jummai ta ce,ni yanzu zama bai ganni ba,Kari shirya kawai mu nufi maguzawa in ko Boka na kan Dutse ya yi kuskuran aikin nan ne to ya cuceni,Kari

ta ce daina wannan zancan kema kin san ba zaya ƙi yin aikin nan ba sai dai in tanan ne aka samu mishkila, amma yanzun ki bari sai gobe mu je muji dalili. Jummai ta ce bana bacci fa Karime, kullum sauraron ganin gawar yarinyar nake yi. Kari ta ce ki dai haƙ

uran ma goben.

Washegari tun safe ta fice ta riga maigidan fita, gidansu Kari ta nufa, shi dama ba'a

ɗ

akin ta ya ƙwana ba, amma ga tsarin shi ko ba kece da shi ba zai shigo har

ɗ

aki ku gaisa. To ya shigo

ɗ

inne su Suwaiba suka ce mishi ta fita. Ya kalli ag

ogon hannunshi,baƙwai da ƙwata ya dube su ina taje? Suka ce ba su sani ba,ya yi tsaki sannan ya fita. Ya samu A'isha tana gyaran gadonta, ya ce a'a Beby ina mai aikin naki ne? Ta ce Uncle ni na ce ta barshi bana son zama bana aikin komai shi ne dalilin,ya

ce good,ta rusuna ta gaishe shi, ya ce zai fita,yau dai ta daure ta ce to Uncle kace ma Uche in aiki ya yi mishi yawa ni zan dinga taya shi, domin bai dace kana fita baka karya ba, kallonta ya dinga yi some times tana

ɗ

aure mishi kai in tayi wata maganar d

omin sai ya ji tafi Jummai wadda ta haifeta hankali. Ya ce Beby kina son in dinga karyawa a gida ne? Ta

ɗ

aga kai alamar eh,ya ajiye jakarshi ta Ofis ya zauna kan kujera je kitchen ki ha

ɗ

o min ko menene zan ci,ta ce to amma kana ganin Anty Jummai ba zata ga

kamar na canza mata tsari ba? Nan ma kallonta yake yi,ya girgiza kai sai ta saka takalmi to bara na zo ta fita ya bita da kallo zuciyarshi tana ta kai kawo an ya kuwa in ya ce zai bar A'isha sai zuwa wani lokaci ba zai ƙwaru ba? Shi yana mata kallon yarin

ya amma komai nata irin na masu hankali. Koda yake haka Allah yake ikonshi, sai ka ga yaro da hankalin manya.

Ita ko tana shiga kitchen ta samu Uche yana ta aiki suka gaisa nan ta tsaya tana kallon na'urorin girkin da yake amfani da su. Ta ce,ya

ɗ

ora mata

ruwan zafi, sannan ta

ɗ

ebi dankali zata fere da wuƙa nan ya amsa yasa na'urar fere-fere nan da nan sai ga shi cikin lokaci ƙanƙani ya gama nan dai ya dinga taimaka mata ta shirya mishi abin kari mai sauƙi tunda sauri yake yi ta cika tire.

Ta zauna gabans

hi tana cewa Uncle yi haƙuri na tsaida kai, ya ce Beby kenan,nan ta ha

ɗ

a mishi tea tare da baje mishi dankali da ƙwai, duk da yana cewa tea bai dame shi ba,ya sha sosai, har ma ya gano ba wai baya son tea

ɗ

in ba ne,ba a iya ha

ɗ

awa bane. Ya dubi A'isha ya c

e Beby kin san da can ina shan tea lokacin ina gidan Hajiya, daga baya sai na ji ban son shi,ta ce la ban sani ba shine kasha da ka gaya min me ka fi so da nayi maka shi. Ya ce a'a wannan ya yi min da

ɗ

i ina son irin shi, amma yaushe za ki min irin kunun gy

a

ɗ

annan da Ummanki take yi? Ta ce gobe in ka fita ka ce Uche ya zo zan rubuta abubuwan da zana yi amfani da su sai ya siyo zan maka gobe,ya ce na gode.

Sun isa maguzawa kai tsaye suka zarce gidan bokan dutse,sun samu wasu halakakkun ƴan'uwansu a gurin,

sai da suka jira suka fito sannan su kuma suka shiga. Yana kallon su ya soma sheƙa dariya tare da cewa, kowane shege ya ci tuwo damu miyar ma ba zai sha ba, Hajiya Jummai ta kalleshi,na kan dutse me ka ke nufi? Kari tayi saurin cewa ba dai ka

ɓ

ata mana aik

i ba? Ya kuma ƙwashewa da dariya,na san dole ku dawo domin na san ba zaku ga da ƙyau ba. Jummai ta zaro idanu ya ce ke ƴar tselan uwar menene na zare idanu,kin maida ni kidahumi tunda ina daji ban san komai ba,kin kawo tsohuwar mota buga-buga an kawo min,t

o nima shi yasa na ce zaki gani, zufa ta shiga ketoma Hajiya Jummai, ta ce kash, to yanzu ya ya za'ayi ne? Ya ce ki zube ku

ɗ

i in miki aiki, ta ce haba na kan dutse, wannan aikin ai na biya ka na motar ne kurum aka sami akasi, ya ce ban san akasi ba,ta ce t

o naji yanzu nawa zan ba da? Ya ce sai kin zube min dubu

ɗ

ari biyu,shiru tayi abin duniya ya ishe ta,ta dubi Karima,to yanzu ya ya kenan? Kari ta ce kawai ki nemo ku

ɗ

i kin san na dutse bai san Allah ba bare a roƙe shi," ta ce to shikenan zamu dawo ta miƙe

cikin damuwa,Karima ma ta miƙe suka fita. Cikin mota Hajiya Jummai sai mita take yi har da kukanta don baƙin ciki Karima ta ce

ɗ

an iska ko yaushe ma ya san mota da har yasan an yi mata ƙwasƙwarima ne? Jummai ta ce bar matsiyaci ni yanzu ma ku

ɗ

in cikin acco

unt

ɗ

ina da ƙyar in ya kai dubu

ɗ

ari, Karima ta ce ki ƙwaƙula jikin shi mana. Hajiya Jummai taja tsaki tare da cewa, kada ki ban haushi Hajiya Kari kina yi kamar baki san halin shi ba? Kin san fa dole sai ya san me zan yi da ku

ɗ

i kafin ya bani,ta ce ke ja

can, inji Kari wani sa'in sai ki ringa yin abu tamkar wawuya,ba za ki iya ce mishi biki ko sunan ƙawa ba? Ta ce, to zan dai ƙwatanta in bai bani ba sai na saida abin hannuna (warwaro) in yaso shima sai nasa a min aikin da na tambayi ku

ɗ

i zai bani,Kari ta c

e kin yi tunani haka za'ayin ma kawai. Cikin satin zuwan Hajiya Jummai maguzawa uku, kuma ta kai duk abinda boka na kan dutse ya buƙata ta koma tana sauraron abinda zai biyo baya.

A'isha tana zaune tsakar

ɗ

akinta kallon Cartoons take yi a tashar mbc 3 amm

a zuciyarta tana can ga tunanin Uncle

ɗ

inta Wanda ya tafi Angeles ta ƙasar Amerika,don kasuwancinsu tafiyar ta ƙwana uku ce yau zai dawo gashi har yanzun bai iso ba, kuma tun safe ya ce sun taso,baya da abokin hira hasali ma tunda Uncle baya nan ba ta fita

, domin su Suwaibar nan dariya suke mata tare da yi mata ba a wai ƴar ƙauye, ita ko Hajiya bata zama ma bare ta ƙwa

ɓ

a musu,don haka sai ta daina ma fita tunda tana da komai kuma Uche in ya gama abinci zaya kawo. Kasa

ɗ

aurewa ta yi ta jawo wayarta ta shiga

neman layin shi na can, cewa akayi ba zai je ba ta ajiye wayar ta saka kanta cikin guiwa. Sam bata ji turo ƙofa ba,bare taku sai dai taji an dafata a bayan ta. Firgigit ta waigo cike da tsoro, tare kuma da fa

ɗ

in innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un. Ganin U

ncle sai taji wani shegen da

ɗ

i cikin fara'a take cewa har ka dawo? Sannu da zuwa ya ce yauwa sarkin tsoro, ta

ɗ

an rufe fuskarta sannan ta ce zauna,ta nufi

ɗ

an fridge

ɗ

in dake

ɗ

aki ta ciro mishi ruwan swan tare da kofi.

Ta tsiyaya mishi ya amsa ba tare day

a zauna ba, har zai kai ruwan bakin shi yana cewa yauwa Beby. Ta ce Uncle ka zauna mana, Manzon Allah (S.A.W) ya ce kada

ɗ

ayanku ya sha yana daga tsaye. Uncle ya zauna yana cewa,na gode Beby, kin tunasar da ni,ya sha ya aje kofin bari nayi wanka ko? Kai ta



ɗ

aga shi kuma ya fita dama yau gurin Jummai yake.

A'isha kam baki tasa ki tana kallon tsarabar da Uncle ya kawo mata,shin an ya ma Uncle yana sane ya kawo mata kayan nan kodai yayi mantuwa ne? Ba wai da yawan kayan ko tsadar su ba, a'a illa ganin ƴan bul

awus ne na yara tare da takalma sawu ciki, sai rigunan jeans da wandunansu, wani abin dariya har da Tedi,ta tasa kayan tana kallo tana juyawa,ƙofarta aka bu

ɗ

o tare da sallama,ta amsa, Nafisa ce ta miƙe da sauri tana cewa "Anty Nafisa sai yau? Ta zauna tana

cewa yauma nazo in yi muku sallama ne, A'isha ta dube ta haba? Ina za ki? Zan koma ma makaranta mana, A'isha ta cika da mamaki, ta ce dama ba ki gama ba Anty Nafisa? Nafisa ta ce sauran wata shida in kuma na tafi ba zan dawo ba, sai na gama. A'isha ta ce,

Allah sarki,za ki bar Hajiyarmu ita

ɗ

aya dama Uncle ya maida ni can kafin ki dawo, yanda A'isha ta karya murya,ta yi maganar ya yi matuƙar bawa Nafisa dariya, ta ce ban da shirme irin naki yaushe ki ka ga matar aure ta bar

ɗ

akinta,ta koma wani gida? Ta ce

can ma fa gida ne don Allah ki gaya ma Uncle dama fa ban ta

ɓ

a zuwa ba tun lokacin da su innata suka kai ni.

Nafisa dariya take yi tare da ƙara yarda,lallai A'isha ƙaramar yarinya ce, Uncle ya shigo da sallama. A'isha zumbur ta miƙe tsaye tana mishi sannu

da zuwa. Ya amsa yana duban ta yauwa sannu Beby,ya zauna bakin gado yana kallon Nafisa,auta kin zo ne? Tana dariya ta ce eh jiya Hajiyarmu ta ce kazo bana nan gidan Anty Fatima na ƙwana ya kuma sai ga tsaraba, A'isha ta isa fridge ta

ɗ

ibo goran ruwa da na

jus ta tsiyaya ta miƙa mishi ya ce yauwa Beby shi yasa ko'ina na shiga da naji ƙishin ruwa sai kawai na tuno ki. Nafisa ta ce a'a da yake kai Uncle

ɗ

inta ne amma ni ai bata bani ba. Cikin tsokana Nafisa tayi maganar, A'isha ta dube ta tare da cewa,ayya An

ty Nafisa ba haka ba ne,ko fa gaisawa ba mu gama ba fa don Allah,ta

ɗ

auko wani kofin tana zuba mata. Nafisa ta ce,ba wani shima Uncle

ɗ

in naki ai tun kafin ma ya gama zama ki ka bashi. Ta miƙa mata ruwa to gashi yi haƙuri shi dai Uncle dariya ya ringa musu

, A'isha ta ce sha to,ki gani nima ga tsarabata.

Nafisa tana

ɗ

aga kayan ta shiga gumtse dariya don kada Brother ya ci ƙaniyarta, amma wannan kayan da bai wuce su Maama su saka shi ba yaran Anty Sadiya.

A'isha ta ce kuma zai min dai dai Anty Nafisa? Uncle

ya katse ta da cewa,baki gwada ba ne Beby? Nawa kema ki ke za suyi miki mana.

Nafisa ta kasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login