Showing 21001 words to 24000 words out of 32230 words
kamar tana neman ƙarin bayani, domin A'isha yarinya ce sannan ba wai suna zama da ƙawayanta suna hirar samari ko ta aure ba ne,haka nan bata da wata ƙawa wadda ta yi aure ballantana ma taji labarin zaman auran, kazalika ita ba
ma'abociyar karance-karance ba ce, ita ana ta zaton in an mata aure zata na girki tana kai ma mijin ruwan wanka tasa mishi na buta kamar yanda ta gani Ummanta tana yi, sai ko gyaran
ɗ
akin Abbanta da Umman bata bari wani ya yi sai ita.
Abba ya katse mata t
unani da cewa, ma'ana in ya neme ki kada ki guje shi, Umma ta ce,nima na miki duk nasihar da ta dace,na sani ke dama mai biyayya ce,ki girmama ƴan'uwansa,ki
ɗ
auki mahaifiyarsa tamkar taki, haka mahaifinshi, matarsa ki yi mata biyayya."
Hawaye suna zuba da
ga idanunta, ta ce insha Allah zan yi Abba da Umma, suka sa mata albarka tare da yafe mata,ta miƙe ta fita suka bita da kallo cikin tausayin ta yayin da ita kuma ta wuce cikin tsananin damuwa.
Ƴ
an
ɗ
aurin aure sun hallara in da aka
ɗ
aura aure. Maroƙiya ta
shigo tana ranga
ɗ
a gu
ɗ
a, A'isha dai-dai lokacin tana wanka wanda Umma Rabi ta matsa mata ta yi umma Rabi ƙawar Ummanta ce,tun suna dutse tana fitowa ta ji gidan ya kaure da gu
ɗ
a, duk sai taji wata fargaba a cikin zuciyarta. Inna Uwani Ƙanwar Umma, ita ta c
iro mata wani leshi baƙi mai ado, ruwan lemon zaki tasa ka,sun bata siket da bes da kuma pant duk baƙaƙe.
Aunty Hasiya mata ƙanin Abba ta ce ni ban ga ma rigar nono ba cikin kayan? Umma ta ce ba a saka ba, Umma Rabi ta ce to me za'a sakama ƙirjin ba komai
, ita dai A'isha tana jin su, Ummanta ta ce kin ji saka kayanki ki tafi nan duk iyayan banza ne suka taru. Ta gama shirinta ta fita, bayan an
ɗ
an natsa da gama
ɗ
aurin aure sai kuma aka shiga shirin tafiya Katsina,kai amarya. Duk wanda ya cancanta ya yi wa
amarya nasiha ya yi mata,dangin Uwa da na Uba. Idanu ta zuba ma Ummanta a zuciyarta tana raya cewa, ta yi wa mahaifiyarta kallon ƙarshe. Haka nan aka fita da ita tana ta rusa kuka.
Abbanta da sauran mutane suna waje gurin mota suna ta ce wa
ɗ
anda zasu je K
atsinan,don kowa yana son zuwa, kuma tafiya ta gari ba kusa ba,don haka suka ce dole ne wasu su haƙura ba kowa da kowane zasu je ba, an fito da ita tana cin kuka ganin Abbanta sai kuma ta ƙwace ta nufi gurinshi.
Ya riƙe mata hannu yana cewa haba menene ha
ka kuma? Ganin yanda take rusa kuka har ma wasu daga cikin dangi suma sun soma taya ta, sai Abban ya kama hannunta ya ce,zo muje,
ɗ
akinshi suka je ya zaunar da ita ya shiga lallashinta da cewa menene na damuwa bayan ta yi musu biyayya sannan ya san Friend
ɗ
in shi zai kula da ita, zatayi karatun ta duka biyun, kuma suma da an ƙwana biyu za su zo shi da Ummanta. Ya miƙe ya
ɗ
auko alƙur'ani izifi sittin da fiƙihu da Tauhidi ya ce ki riƙe wannan kin ji A'isha?" Ta share hawayenta tasa hannu biyu ta amsa tare da
cewa , to Abba da gaske za kuzo? Ya ce in Allah ya so, tashi muje ga mutane can sun shiga mota ke dama ake jira. Allah ya yi miki albarka zan kira ki in kun isa,ta ce to. Abba da kanshi ya kai ta har mota inda ta zauna tsakiyar Inna Uwani da kuma Aunty Rab
i matar ƙanin Abba. Suka nufi Katsina bayan ta yiwa gidan su kallon ƙarshe, tare da duban Abbanta da Yaya Abdulrahman Munnir da kuma Jafar.
Alhamdulillah ƙarfe free Pages kenan idan baki siya ba kiyi ƙoƙari ki mallaki naki akan farashin masu son DOCUMENT
book 1&2&3 Complete ₦600,masu son PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number
👇🏻
*
```1632036584
Sa'adatu Balarabe
Access Bank,a turo shaidar biya ta 09068032427 wancan account
ɗ
in namu ya samu matsala ne, idan mun gyara zamu d
awo dashi```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*
[12/4, 20:23] Ummi Tandama
😇
: *
📗
Page 12*
Can katsina kuwa, gidan Alhaji Saddiƙ yana cike da danginshi, na gefen Hajiya Jum
mai da kuma ƙawayanta. Amma shaƙiƙan ƴan'uwanshi irin su Fatima, gidansu Hajiyarmu suke yin bikin su. Kuma a nan suka yi girkin saukar amarya domin suna isowa direbobin zasu kira su a waya kamar yanda suka shedawa direbobin.
Gefen Hajiya Jummai kuwa tana
ɗ
aki tsakiyar aminanta suna ta tofin Ala tsine ga Alhaji Saddiƙ
ɗ
in da ƴan'uwanshi da kuma amarya da danginta. Tuni suka sa ma amaryar suni mai ƙararran ƙwana.
Yamma ta yi sanda motar amarya ta iso, tunda suka shigo Katsina direbobin suka yi waya suka san
ar da su Hajiyarmu. Nan take su Fatima Anty Sadiya su Nafisa da sauran dangi suka ciko mota da kuloli
ɗ
auke da nau'ikan abinci kalolin abin sha, suka nufo gidan Brother
ɗ
insu. Suna shigowa kallo ya koma kan su nan dai aka je aka tsegun tama Hajiya Jummai i
ta da ƙawayenta suka fito falon suka shiga yada habaici, domin tsarin gidan ƙaton mahaukacin falo ne mai
ɗ
auke da
ɗ
akuna hu
ɗ
u, falon ya shiryu da kalolin kujeru na alfarma gefe-gefe.
Kusan seti uku ban da (dinning),
ɗ
akin Hajiya Jummai sai na su Suby sai
ko na A'isha, yanzun
ɗ
ayan na baƙi ne, sai hanyar da zaka bi don zuwa gefen shi yanda ya shirya kujerun falon yana nufin kamar kowace mace da nata, domin kalar kujerunki kalar labulanki kuma suna daf da
ɗ
akinki kayan kallonki kuma suna nan a gurin, domin t
sakanin kowane
ɗ
aki zuwa wani
ɗ
aki da
ɗ
an tazara. Akan kujerun A'isha suka zauna babu jimawa sai ga motocin amaryar sun iso,suka fito suka tari amarya,in da Nafisa taje ta rungumo A'isha tana cewa amaryarmu sannu da zuwa. Ta laluba kunnan A'isha tana cewa
kada ki manta ki shiga gidanki da ƙafar dama tare da addu'o'i,kai A'isha ta
ɗ
aga. Dama tun kafin su shigo gidan take zabga addu'o'i,suna shigowa sai wata cikin matan ta soma ranga
ɗ
a gu
ɗ
a.
Hajiya Jummai ta miƙe zumbur tana haki,su Hajiya Karima suka riƙe
ta tare da cewa,haba-haba Hajiya Jummai ai an wuce nan,me yasa ki ke tada hankalinki? Kada idanunki su rufe ki manta matsayinki, ta sauke huci, da zuwa zan yi in
ɗ
auke matar da ta zabgo min wannan gu
ɗ
ar a cikin gidana da mari suka ce a'a Hajiya Karima ta j
ata cikin toilet me zai sa ki nuna kanki? Kada ki manta da zaran ya sadu da ita ta zama gawa kamar yanda yake faruwa da sauran matan,nuna musu faran-faran yanda za'a tafi ana yabonki,me yasa wannan karan duk ki ka kasa control
ɗ
in kan ki ne?.
Ta dubi Haji
ya Karima nima ba zan ce ga dalili ba, sai dai ina samun kaina da matsanancin Kishin yarinyar. Na tsane ta fiye da sauran kuma naga Alhaji ya fi nuna
ɗ
okin aurenta fiye da sauran na baya. Hajiya Karima ta ce don Allah manta da kishin nan gawa ce fa, yanzu
dai zo muje mu taryesu ki canza kayanki kiyi sabuwar shiga,mu rufa miki baya ki gaishe su kada ki nuna mata kishi don Allah, ta ce shikenan suka fito. Nan ko take ta zabga wani uban sun less mai shegiyar tsada, suka rufa mata baya zuwa
ɗ
akin amarya.
Lokac
in wasu suna sallah yayin da wasu ke cin abinci, A'isha dai lokacin tana zaune bakin gado. Nafisa tana kusa da ita tana waya, tamkar mutuniyar ƙwarai ta durƙusa tana gaishe su ƙawayanta ma suka gaishe su,ta ce ina ƙanwar tawa? Umma Rabi ta ce gata nan ta ƙ
udundune kai, Hajiya Jummai ta ce zamu ganki ne har mu gaji suka ce ƙwarai kuwa, Nafisa dai ko kallon ta batayi ba, amma don makirci har da cewa Hajiya Nafisa waton yau ana gurin amarya kenan ko?.
Nafisa ta gama waya amma sai ta cigaba da magana tamkar ba
ta gama ba, don kada ma suyi magana da Hajiya Jummai. Suna fita kuwa su Umma Rabi suka soma yabonta kan cewa gaskiya wannan mata tana da kirki, Allah ya ha
ɗ
a kansu. Nafisa dai bata ce komai ba,don ba wai suna zarginta da kisan matanshi ba ne, a'a shirine
kawai basayi da ita,su kuwa suna komawa
ɗ
aki Hajiya Karima ta ce,ni ban ga mutum ba a nan? Jummai ta ce,ai shine duk da tana rufe amma yarinya kamar ƴar kalan hanji? Wata da suke kira Hajjaju ta ce don rashin tausayin namiji sai fa ya ce zai neme ta ko? A,
sosai ma, inji Hajiya Jummai, duk matan haka yake auro su amma ba ya
ɗ
aga musu ƙafa, wannan ma ba zai kalleta ba,bugu da ƙari ma ni nafi son ya take ta. Hajiya Karima ta yi saurin ƙwabarta da cewa to ke dai ya isa zancan haka,mu dai Allah ya bada zaman ha
ƙ
uri ki dai kauda kanki kawai,ta yi haka ne saboda wannan kashe-kashen sirrinsu ne sauran ƙawayan ba su sani ba. Nan take Jummai ta gano kuskuran da ta so tayi don haka sai suka shiga wani zancan.
A'isha tana zaune kan sallaya ta idar da sallar isha'i, Na
fisa ta durƙusa ta ce sai da safe tunda kin ƙi cin komai sai dai zan fa
ɗ
a ki da Uncle
ɗ
in naki cewa tunda ki ka zo kin ƙi shan ko da ruwa ne.
A'isha ta dube ta,haba don Allah kar ki gaya masa. Umma Rabi ta ce ai gara dai ki sanar da shi
ɗ
in. Nafisa ta fit
a tana cewa to sai da safenku, suka ce to ki gaida Hajiyarmu mun gode sosai,ta fita Inna Uwani ta ce yanzun A'isha haka za ki ƙwana da yinwa? Ta dube ta Allah Inna ni bana jin yunwa fa.
Hajiya Jummai ta shigo da sallama, fuskarta
ɗ
auke da fara'a ta ce,san
nunku, sannunku fa suka ce yauwa ta ce duk kun yi sallah kenan? Suka ce mun yi Hajiya. Ta ce,to bari a kawo muku abinci, suka ce wallahi duk mun ƙoshi,kin gan shi can ma wani ne ko bu
ɗ
a shi bamu yi ba,ta ce to shikenan ku zo muje in kai ku masaukin baƙi,in
ya so sai amaryar da ƙawayanta su ƙwana a nan. Suka ce to, suka miƙe suka bi ta sai sa'anninta uku aka bari.
Ita dai tana zaune kan sallaya,
ɗ
akin baƙin yana da girma ga ƙaton gado sannan ga wasu manyan katifu guda biyu an baje duk sun sha shinfi
ɗ
a. T.V n
a bango ne a
ɗ
akin kamar dai na falon sai dai shi ƙarami ne,ga (AC) ga kuma bayi. Ta bu
ɗ
e wordrobe ta ciro musu manyan barguna kasancewar lokaci ne na sanyi, sannan ta ciro parnpas ta ce, masu yara gashi nan suyi musu nafkin,ta kunna musu T.V tashar da ake
yin wasan Hausa,wato fim
ɗ
in Hausa. Ta ce,in zaku yi bacci sai ku cire soket
ɗ
in, kada ku manta da yiwa yara addu'a kun ji ko? Ku karanta musu ƙulhuwallahu,falaƙi da Nasi ƙafa uku-uku, da kuma ayatul kursiyu duk ku shafe jikinku da shi dana ƴaƴanku, suka
ce to mungode fa Hajiya, Allah ya saka miki da alkhairi,ta ce haba ba komai sai da safenku,ku huta gajiya suka ce to Allah ya bamu alkhairi,ta fita ta ja musu ƙofa,su kuwa suna ta yabonta da cewa Allah ya saka mata tana da kirki,lallai A'isha ta yi dacen d
angin miji da kishiya,ita kuwa fita ta yi tana cewa ƴan iska ba zaku gane ba ne sai kun zo zaman makoki.
Ita ko A'isha tana nan zaune kan sallaya ta zuba tagumi, yayin da su Naja suka yi
ɗ
ai-
ɗ
ai kan gado har sun soma bacci saboda gajiya zuciyarta ta nata
neman dalilin da yasa
ɗ
azun da Hajiya Jummai ta zo musu sannu da zuwa gabanta ya yi mugun fa
ɗ
uwa, yanzun ma haka. Tana sallama ta ji gabanta ya fa
ɗ
i,in ko haka zata ci gaba da ji lallai zata bani tunda guri
ɗ
aya suke. Ta soma tambayar kanta da cewa menene
ma na jin tsoron ta ko fa
ɗ
uwar gaba dan ta ganta? Mace mai karamci da mutunci.
Ƙ
wanƙwasa ƙofar tare da bu
ɗ
ewa ne ya katse ta,a hankali ya yi sallama tamkar yana ciwon baki,ko kuma baya son ya tashi ƙaramin yaro. Kanta na ƙasa ta amsa, amma bata
ɗ
ago kai b
a,ya tako har gabanta ya tsugunna,sam bata ma san ya iso ba, sai dai ta ji yace Beby (a hankali) ta
ɗ
ago idanu ta zuba mishi. Yana sanye da wandon jeans baƙi da rigar sanyi tafkekiya ta saƙar baƙin zare da fari, sai ta ganshi tamkar
ɗ
an matashin saurayi,ko
kusa ba ya kama shekarunsa,ƙyawun fuskarshi ya sake fitowa saboda ƴar rama da ya yi,ta sauke idanunta ƙasa, hancinta yana ci gaba da shaƙar ƙamshinsa,ya yi
ɗ
an murmushi yanda Bebyn tasa ke dubansa, cikin yanayin damuwa ya ce Beby baki ci abinci ba, saboda
me? Ta gyara zama bana jin yunwa ne Uncle, ya ce Nafisa ta ce min kina cikin damuwa ko ruwa ba ki sha ba,why Beby? Kina fargaba ko? Ta ce ba haka ba ne Uncle, ya ce to gaya min ya ya ne? Ta rasa me zata ce, ya ce ok,kina tunanin cewa in kinci wani abu na
gidan nan shi ne zaki mutu ko? Da sauri ta dube shi, Uncle ba na nufin haka, ya ce to in ba ƙya nufin haka ki ci wani abu in gani, ta ce to,ya ce me ranki yake so a kawo miki shi yanzun? Ta ce komai ma zan ci ba sai na daban ba, maimakon tsugunnon da yake
sai ya zame ya zauna sannan ya kira wayar Uche. Ya ce ka kawo min kaza mai zafi in kuna dashi a kitchen da maltina ko fresh milk ya kashe wayar ya dubi gefe,su Naja ƙawayan naki sun yi bacci da sun taya ki ci ko? Itama ta dube su,sun gaji ne, ya ce dole su
gaji don da nisa. Uche ya ƙwanƙwasa ƙofa, ya miƙe yaje ya amso tiren ya dire a gabanta sannan ya zauna, "ci in gani" nauyinshi take ji don haka sai ya kauda kanshi gefe ya ciro wayar shi ya soma neman wani layi, aka
ɗ
auka suka ci gaba da hirar kasuwancins
u.ita ko nan ta soma cin kazar nan wadda ta ji ha
ɗ
i ta kuma gasu, ta ci sosai ta sha maltina ka
ɗ
an sai ruwa. Ya dube ta har kin ƙoshi? Ta ce,eh ya ce yauwa to tashi kije ki ƙwanta zuwa ƙarfe uku in gajiyar mota ta barki sai ki tashi kiyi alwala ki yi nafil
a ki tsananta roƙon Allah ya albarkaci aurenmu, ta ce to, kanta na ƙasa ta tashi ta hau gado ta kwanta tsakiyar su Naja ya ce sai da safe,kizo ki rufe muku ƙofa kiyi addu'a fa,ta ce to. Bayan ta karanta ƙulhuwallahu,falaƙi da Nasi,ta tofa cikin tafukan ha
nnayanta sannan ta shafa tun daga kanta da fuskarta har da sauran ga
ɓ
obin jikinta,ta yi haka har sai uku ta karanta Ayatul kursiyu.....
######
[12/5, 20:22] Ummi Tandama
😇
: *
📗
Page 13*
Amanar rasulu, sannan ta karanta da sunanka ya Ubangijina na ƙwanta
kuma da izininka ne nake tashi in ka riƙe raina da (mutuwa) to ka ji ƙanta in ka sake ta ya Allah ka kiyayeta da abinda ka ke kiyaye bayinka salihai da shi, sannan ta ce:--
Allahumma innaka kalaƙta nafsi wa'anta tawaffaha naka mamatuha,wama hayaha in ahy
etaha,fahfadha wa'in amattaha,fagfirlaha. Allahumma inna as'alukal afiya,tana koyi da Manzon Allah (S.A.W) in tazo ƙwanciya sai tasa hannunta na dama ƙarƙashin kuncinta ta ce:--
Allahumma ƙiyni,azabaka yauma tab'asu ibadaka. Sau uku, sannan ta ce bismikal
lahumma a mutu wa'ahaya. Lokacin ta soma hamma sosai don haka sai ta tsaya nan gurin ta kuma ƙwanta.
Shigar Alhaji Saddiƙ
ɗ
akin da fitarshi kai har zuwan Uche duk a kan idanunta ne. Hajiya Jummai ta yi ƙwafa sannan ta ce lallai ban da yarinyar nan mutuwa
zata yi ƙila da na ƙunshi takaici gidannan,dubi yanda mutumin nan ke ta faman sintiri a
ɗ
akin yarinyar nan tun baƙi na nan,ta ciji yatsa tare da cewa kash, da na sani da har ƙawayan nata na ce su je can shi ko nasan da nan zai ƙwana ba kuma zai bar ta ba,i
n ya so tana mutuwa suyi zaman makokinsu gaba
ɗ
aya an huta,su koma Jigawa su dawo, amma tunda an riga an yi haka shi kenan,sun dawo
ɗ
in tunda ya kama su ne.
Washegari tuni tasa Uche a dama koko ga ƙosai. Rahina mai aiki tana ta suya. Sai ga ƴan aikin Haji
yarmu tare da Nafisa
ɗ
auke da ruwan zafi gwangwanayan madara milo suga da kuma ƙatuwar kula mai
ɗ
auke da soyayyan dankali da kuma ƙwai. Sanda su Sofy da Suby suka shigo
ɗ
akin babu ko sallama suka aje bokitin koko sun same su suna ta wadaƙarsu da shayi sor
oro suka tsaya sannan suka