Showing 12001 words to 15000 words out of 32230 words
*Ɗandano page 7*
Abdulrahman yana biye da ita da kaya, cikin wani
tsararren kitchen ta hangi Umma, Umma tana juyowa ta yi arba da ƴarta, da sauri ta fito tana cewa ga ƴan makaranta ga ƴan makaranta." A'isha ta fa
ɗ
a jikin Umma tana kuka.
Ramarta ta tsorata Umma, ta ce, "A'isha kin yi ciwo ne?" Dai-dai nan Abba da Abdulr
ahman suka shigo, Abba ya ce, "ƙawallin taki ta bani tsoro, Ummansu kin ga yanda ta ƙare?" Umma ta ce "Shine ai,wane ciwo ki kayi haka?" Cikin kuka A'isha ta ce, "Nima ban san ciwon ba,ni dai duk jikina ne bana jin da
ɗ
in shi. Suka shiga falo kan kujera ta
ƙ
wanta tana ƙara kallon yanda aka tsara falon da ku
ɗ
in jini, duk sai ta samu kanta da ƙyanƙyamin komai na gidan. Umma ta zubo mata abinci ta tasa shi ta kasa ci, har dare Umma ta yi tayi A'isha, amma ta ƙi cin komai. Hankalin Iyayen ya tashi, cikin dare za
zza
ɓ
i ya rufe ta saboda tsananin damuwa da kuka, dole da safe suka nufi asibiti, duk binciken likitan bai gano komai ba, sai damuwa. Don haka yasa mata ruwa tare da allurai don ta samu bacci.
Ƙ
wananta biyu aka sallame ta, tunda ta dawo ko yaushe jugum ba
ta magana. Umma ta matsa mata da tambayar abinda ke damunta,don likitan ya ce tabbas akwai abinda ke damunta. A'isha tana son sanar da Umma amma tana tsoron kar ta gaya wa Abba, shi kuma ya yi fa
ɗ
a. Ko ma ya yi fushi da ita,don haka ta yi shiru.
Abba yana
zaune yana cin abinci, ya tasa ta gaba wai itama sai ta ci nata. Umma ma ta shigo
ɗ
akin na A'isha, wanda ya ji uwar katifa sai (T.V) ance ba za'a cika
ɗ
aki da kaya bane tunda cikin hutun nan ne za'ayi bikinta, Umma ta zauna tana cewa,ka ce kana nan na fit
o ban ganka ba,ya ce "eh, ina nan gurin A'isha so nake ta ci abincin a gabana in gani," Umma ta ce "to nima dama na zo ne in tsare ta, yarinya duk tasa kanta a uku" ta dubi A'isha wadda take ta ƙoƙarin ganin ta ci abincin,ko don hankalin iyayenta ya ƙwanta
, ta ce, "To ko saboda aurenki da Alhaji Saddiƙ ne?" Da sauri ta kalli Abba, wanda ya tsura mata ido, sannan ta girgiza kai, "Ba haka ba ne Abba" ya ce "ai bani ne na tambaye ki ba, Ummanki za ki bawa amsa, tunda ni dai ai mun gama magana,jiya ma nake sana
r da shi dawowarki, sai dai ban sanar dashi ciwon ki ba, saboda zai ce zai bar aikinshi ya zo,ya ce dai zai zo kafin su kawo kaya."
Umma ta ce "bari na saka mata wayarta ma a caji, saboda ƙila zai neme ta. A'isha ta yi ajiyar zuciya,lallai ya kamata ta sa
nar da Umma, domin dai ba su san komai kan Uncle ba. Sai da Abba ya fita sannan A'isha ta dubi Umma, ta ce "Umma zan gaya miki abinda ke damuna, amma sai kin yi min alƙawarin ba zaki sanar da Abbanmu ba" cikin fargaba Umma ta ce, "Sanar dani,ba zan gaya mi
shi ba." Ta soma hawaye, "Umma ashe Uncle
ɗ
an yankan kai ne? Ashe duk ku
ɗ
in shi na jini ne?" Umma ta daburce tare da cewa "Wane Uncle
ɗ
in?" A'isha ta ce, "na Katsina, kinsan ƙawata ƴar Katsina ce nan dai ta koro ma Ummanta labarin da ta ji game da Uncle
ɗ
i
n nata, Umma ta shiga damuwa,zufa ta shiga keto mata duk da cewar da takeyi anya kuwa A'isha zancan nan gaskiya ne? Duk suka yi shiru kowa yana tunaninshi, can dai Umma ta yi ƙarfin hali ta ce "A'isha wannan zancan ba na shiru ba ne, dole Abbanki ya ji, do
min dai duniya yanzu babu gaskiya, ku
ɗ
i suna kai mutane cikin halaka, sannan kai ka yarda da mutum shi ko yana da nashi burin a kanka".
A'isha ta soma kuka tana fa
ɗ
in, "Don Allah Ummata kada ki sanar da Abba,ba zai ta
ɓ
a yarda ba saboda ya yarda da Uncle
ni dai na haƙura zan auri Uncle
ɗ
in tunda dai dama na san ƙarshena mutuwa zan yi."
Abba da ke ƙoƙarin shigowa
ɗ
akin tun
ɗ
azun,ya ji A'isha tana sanar da Ummanta A ranshi ya ce, "shikenan sun ji zancan da ya ke
ɓ
oye musu,ya zama dole ya shiga ya sanar da s
u gaskiyar lamarin domin ya yarda Alhaji Saddiƙ ba zai mishi ƙarya ba,ba zai cuce shi ba,ba zai ci amanar shi ba, kuma ba zai kasance
ɗ
aya daga cikin masu shan jini ba.
Da sallama ya shiga duk da baya da kuzari amma ya yi ƙarfin halin cewa "kuna hira ne?
Umma cikin damuwa ta ce "wane hira Abbansu zauna ka ji". Ya zauna tare da fa
ɗ
in "lafiya dai ko? Umma ta ce "da sauƙi dai,dama Abbansu dama ashe irin sana'ar da yake yi kenan?" Abba ya ce "wa?" Ta ce "Alhaji Saddiƙ mana ta shiga jero mishi bayani yanda A'is
ha ta sanar da ita. A'isha dake ƙwance jikin Ummanta tana kuka,ta ce "Abba ka min afuwa na sani ranka ba zai so ba, amma duk da haka zan aure shi.
Abba ya ce "ku kwantar da hankalinku ni kaina na san wannan labarin kuma shi da kansa ya yi min bayanin zarg
in da jama'a suke masa. Tabbas tun daga kan Hajiya Jummai duk Mata da ya aura mutuwa take yi, gaske ne ya yi aure kusan tara ko goma ne? Duk sun rasu," A'isha ta zaro ido, Abba ya ci gaba da cewa, "ina so ku sani cewa, dukkan mai rai mamaci ne, haka nan ma
tansa da suka riga mu gidan gaskiya,ku yarda wa'adinsu ne ya zo, batun yana yankan kai babu gaskiya cikin zargin da mutanan unguwar suke mishi."
Umma cikin matsananciyar damuwa ta ce, "to yanzun Abbansu matan nasa suna mutuwa haka za'a bashi A'ishan?.
Ya
ce, "Haba Fatima,ya ya ki ke dawo da hannun agogo baya? Na gaya miki na sake gaya miki aure babu fashi, mutum baya mutuwa face ƙwananshi ya ƙare. Ya fita yana cewa "ki zo."
Ɗ
akinta ya shiga, Umma ta biyo shi jikinta babu ƙwari. Ya dube ta yace, "Haba Fat
ima,me zai sa kiyi min haka? Ke kin san son da nake ma A'isha,kin sani ba zan cutar da ita ba, aure bautar ubangiji ne, zan yi murna a ce ta mutu tana ibada,don haka ki natsu kuma ki ƙwantar da hankalin ki,ki bani goyon baya. Ki yaƙi shai
ɗ
an mu tattaushe t
a,nima wallahi ƙarfin hali nake yi,in tana ganinmu cikin damuwa zata kasa ƙwantar da hankalinta kullum zata zama cikin fargaba."
Umma ta ce, "Shikenan, zan yi yanda ka ce," ya ce "yauwa, addu'a kurum ita ce magani,ki tsaya tsayin daka da addu'a,ba dare ba
bu rana. Itama A'ishan ki tsaya kanta ta dage da yin azkar safe da yamma. Cikin fargaba ta ce "To."
Sanda Umma ta shigo
ɗ
akin A'isha, ta samu A'ishar tana zaune gabanta wayar ta ce tana ta ruri tsabar tsoro ya hana A'ishar
ɗ
aga wayar Umma ta kalli fuskar
wayar Uncle
ɗ
ina haka taga an rubuta nan take ta gane,ta cewa A'isha an sa shi mana? Ki natsu ki ƙwantar da hankalinki,ki mishi magana cikin natsuwa,kada ki
ɗ
aga mishi hankali,kin ji?" Ta ce "Ina jin tsoron shi ne Umma" Umma ta ce "Daina tsoron shi, shi ba
mugu bane sharri ne mutane suke masa,
ɗ
auki wayar." Ta kai hannu zata
ɗ
auki wayar, ta katse a karo na biyu.
Ya sake kira a karo na uku, Umma ta
ɗ
auki wayar ta miƙa mata, hannunta yana rawa ta amsa ta danna green ta sa a kunne. Cikin muryar nan tashi mai
natsuwa da hikima yace, "amincin Allah ya tabbata a gareki Humaira Beby". A'isha ta dubi Umma,harara Umma ta zabgo mata, sannan ta fita can gefen. Ya ce "kina jina ƴar Abba?" Ta daure, sannan ta ce, "Ina yini Uncle?" Ya ce, "lafiya lau,kin dawo lafiya?" Ta
ce, lafiya lau, ya ce "Masha Allah" a zuciyarta kuma fa
ɗ
i take, Allahumma kafihim bima shi'ita,tana maimaitawa tana sake fa
ɗ
a,ya
ɗ
an yi gyaran murya,ya ce "A'isha ina labari?" Ta yi shiru,ya ƙara sanyaya murya,ya ce "A'isha kina ji na?" Ta ce, "Umh" ya ce
, "zan zo week end,tun Friday kin ji? Kamar ta ce A'a, sai kuma ta ce Umh, ya yi ƴar dariya sannan ya ce "to Bebyna,me da me zan kawo miki?" Ta ce,babu komai.ya ce Shikenan, sai na zo, tace, "To ka gaida Nafisa" cikin jin da
ɗ
i ya ce "ita ka
ɗ
ai ban da Haji
yarmu?" Da sauri ta ce "har da su." Ta ƙosa ƙwarai ya gama maganganunshi, kamar ko ya sani, ya ce "to bari na ƙyale ki sai kin ganni ko?" Ta ce Uhum, ta riga shi kashewa,ana shi gefen bai damu ba zaton shi kunya ce.
Daran juma'a,sam A'isha bata runtsa ba,
tama rasa tunanin da zata yi, duk da lallashin da Umma take mata, bayan sun karya, Umma ta matsa mata suka shiga kitchen don girka abin tarbar baƙo.
Sun gama sha biyu da rabi nan Umma ta bar ta ta ha
ɗ
a mishi zo
ɓ
o da sauran kayan sha. Ta shigo falo ta ƙwa
nta kan kujera, Umma ta fito don zuwa kitchen ta ce har kin gama?" A'isha ta ce,eh, Umma ta miƙa mata waya ga shi yana ta kira ni ina wanka." A'isha ta amsa Umma ta koma ciki.
Wayar ta soma ringing. Ta tsurawa wayar ido, ita dai kullum ƙara tsoron shi ma
take yi, amma ba ta da yanda zata yi dole ta
ɗ
aga wayar tare da addu'a a can ƙasan zuciyarta. Sannan ta ce, "Salamu alaikum" ya ce "wa'alaikumus Salam, Beby ina ki ka shiga ne? Ina ta kiran wayarki?" Ta soma magana cikin in'ina, "ina....am......wannan ne a
kitchen ne," ya yi ƴar dariya, "ni kike yiwa girki kenan?" Ta yi shiru, ya ce "ok,shiru yana nufin eh ne,to na gode. Yanzu haka na shigo Jigawa, masauki kawai zamu je, sai na iso kenan" ta ce,to, Ya kashe wayar.
Ta tsaya tana kallon wayar,dadda
ɗ
ar muryar
shi har yanzun tana yi mata gizo, murya mai cike da kamala kamar yarda fuskarshi take nunawa ta tuno suffarshi a fili ta ce lallai Uncle bashi da makusa in ban da na mugun halinshi koda dai su Umma suna ƙaryatawa.
Ta fito wanka tayo alwalla tana idar da s
allar azahar mai ta shafa sama-sama saboda zafin garin ta zazzago farar hoda a hannunta,ta
ɗ
an murza a fuskarta ko madubi ba ta duba ba,dama ita bata ƙwalliya. Don haka ba ta ma duba madubi,kai ita fa ko kaya bata da za
ɓ
i duk wanda Abbanta ya sai mata sun
yi,don tana saka kaya ne don suturta jiki ba wai don gayu ba, ta
ɗ
aga aƙwatinta ta ciro kayan da ke sama. Wata atamfa ce ta mutanan Ghana, fara ce ta saka taje ta
ɗ
auko abincinta,ta zauna tana
ɗ
an cakula tana dai cin abincin ne amma hankalinta duk yana kan
Uncle ganinta ƙila ma tun yau zai gama da ita. Jafar da Munnir suka shigo,suna cewa Umma ga Uncle
ɗ
in mu ya zo yana waje yana waya. Umma ta ce, "tare da Abbanku su ke?" Suka ce "a'a shi ka
ɗ
ai ne, amma Yaya Abdulrahman yana gurinshi, ta ce "Abbanku yau ina
ga aiki ya mishi yawa ne,ko gida bai dawo ba, ina ganin daga Office
ɗ
in ya wuce Masallacin juma'a.
Jafar ya fita waje,jim ka
ɗ
an ya dawo. "Umma Yaya Abdulrahman,ya ce ki bada makullin
ɗ
akin baƙi" taje ta
ɗ
auko, A'isha kam tana zaune kamar gunki tana jin s
u. Yaya Abdulrahman ya shigo, "Umma Uncle yana
ɗ
akin baƙi ya ce yabi ta Ofis
ɗ
in Abba,sun tafi masallaci, shima yaje ya yi sallah ya koma Ofis
ɗ
in basu dawo ba shi ne ya zo nan gida". Umma ta ce, "bai kira wayarshi ba?" Yana ta kira bai samu ba sai yanzun.
Umma ta ce, "To ai shi kenan, tunda ma ya sameshi. Ta leƙo falo "A'isha tashi ki je ki shirya mishi abinci,ki kai mishi." Jiki babu ƙwari ta tashi ta fita.
____________________________
*
📗
MUMMUNAN ZATO
📗
*
*NA*
*HALIMA ABDULLA
HI K/MASHI*
*Ɗandano page 8*
*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number
👇🏻
*
```ACT}:--1632036584
Sa'adatu Balarabe
Access Bank,a
turo shaidar biya ta 09068032427 wancan account
ɗ
in namu ya samu matsala ne, idan mun gyara zamu dawo dashi```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu haj
ar su suyi magana ta wannan number 09068032427*
```
Babban tire ne ta shaƙe shi da kuloli masu
ɗ
auke da kalolin abinci. Sai plate da cokali, da sallama ta shiga,ƙasan zuciyarta kuma tana maimaita addu'ar Allahumma kafihim bima shi'ita.
Ya yi matuƙar ƙyau
cikin shadda mai tsada kalar ja mai duhu,hular da takalman duk kalar jan ne,ƙamshin dadda
ɗ
an turarenshi ya cika falon. Duk da tsoronshin da take ji bai hana zuciyarta yaba ƙyanshi ba. Ta dire tire kan tebur
ɗ
in, gabanshi ta jawo teburin sannan ta sunkuyar
da kanta ƙasa ta ce sannu da zuwa Uncle, ya ce "yauwa ƴar Bebyn Uncle,I hope kina lafiya?" Ta ce "lafiya lau,ya ya su Nafisa da su Hajiya?" "Duk suna gaishe ki, cikin jin da
ɗ
i yake bata amsa, domin yarinyar ta shiga ranshi har yana mamakin yanda wasu loku
tan ya kan shagala da tunaninta,ya kan ji kewar ƴar siririyar muryarta, da Beby face
ɗ
in ta, abinda bai ta
ɓ
a yi kenan a kan mace ba, duk matan da ya aura baita jinsu kamar yanda yake jin A'isha ba,a ranshi. Ta cika kofi da ruwan zo
ɓ
o mai sanyi ta miƙa mish
i cike da ladabi, ta koma gefe ta zauna, ya ce "No, come on hau kujera ki zauna,ta ce nan ya yi Uncle, ya ce to nima bari na sakko ƙasan, ta yi sauri ta hau kan kujerar ta
ɗ
an
ɗ
ofanu yana ƴar dariya shima ya gyara zaman shi.
Sannan ya soma shan zo
ɓ
on ta g
efen idanunta ta ke kallonshi. A ranta ta ce "Oh,ga mutum har mutum, amma cikin zuciyarshi gara kura da shi. Ya katse shirun da cewa "Beby in Allah ya gwada mana ki ka koma gidana, ina son kina min wannan zo
ɓ
on kin ji?" Ta
ɗ
aga kai alamar ta ji ya ce "to a
bincin fa zo ki zuba min," ta ce to, tana bu
ɗ
e kular farko yaga saƙwara fara ƙar-ƙar, ya ce "ai shikenan Beby yau kuwa har in tafi ita zan ta ci.
Nan ta zuba mishi da miyar agushi, ga nama manya-manya,ya cika cikinsa dam,ko magana ba ya iya yi, sai da ya
gama sannan ya dube ta yana goge fuska da fari ƙar
ɗ
in handkachief ya ce, Beby kin ganni babu ba ka sai kunne ko? Ta sunkuyar da kai.
Ya ce,"Beby sai naga kamar kin rame min a ido hakane?" Ta ce na
ɗ
an yi mura bayan haka kuma ga makaranta," ya ce "kin man
ta
ɗ
ayar ga kuma maganar aure". Ta rufe fuska, ya yi ƴar dariya sannan ya ce zan sa su kawo kaya da zarar na koma gida nan da sati biyu zuwa uku,kin zama ƴar mutanen K.T? ko?" zancan ya daki zuciyarta, nan take ta raya ma ranta haka yana nuna nan da sati h
u
ɗ
u zuwa biyar zata baƙunci kabarinta, tunda an ce matan nashi ba sa wuce sati biyu zuwa uku suke mutuwa.
Ya katse ta. "Ko ya yi nisa a rage?" Da sauri ta girgiza kai,ya ce "a barshi haka?" Ta
ɗ
aga kai alamar Eh. Nan ya ciro mata tsarabar ta, abubuwan ci
ne tare da turaruka har da wata ƴar Tedi ta wasan yara. Ya miƙa mata ledojin ya ce "to duk da kin ce baki son tsaraba gashi nan ki basu Jafar ke kuma ga naki" ya miƙa mata Tedi.
Baki ta saki tana kallonshi, shima ita yake kallo tamkar masu kallon soyayya,
sannan cikin sanyin murya ta ce "Uncle me zan yi da wannan?" Ya ce "wasa mana" ta ce, "am not a small girl," ya ce haba? Ta sunkuyar da kai tace,da gaske,ya ce shikenan to ki ajiye min in kin haifa mana Small boy sai ki na bashi yana wasa," ga mamakin shi
sai ya ji tace "in kuma na mutu fa?"
Da sauri ya dube ta,a ranshi ya soma zargin ko taji cewa matanshi suna mutuwa ne? Amma a fili sai ya ce,"nima ina yawan tuna haka, sai dai duk sanda na tuna cewa zan iya mutuwa ko ke ki mutu ban ga
ɗ
an kaina ba, ina s
higa wani mawuyacin hali, zuciyata tana sonki da yawa." Ta sunkuyar da kanta ƙasa,ko dai mummunan zato ne a ke mishi? Ko dai zargi