Showing 9001 words to 12000 words out of 32230 words
/>
ɗ
auka, tare da fa
ɗ
in "lafiya Hajiya Jummai?" Ta ja tsaki "to kasa sarkin ba
cci in ce dai kin wartsake? Magana zamu yi."
"Ina jin ki" inji Kari, "kin ji na da wannan sarkin
ɗ
aukakkiyar" "Wa fa?" Inji Kari, "Alhaji mana, aure ya kuma ƙirƙirowa, duk abinda ya faru baya bai ishe shi saduda ba." Kari ta ce, "ke ki bari, aure kuma ya
ƙ
ara lakatowa?" Jummai ta ce, "ke dai bari, sai ma kin ji yanda ya wani canza murya yana magana da ita a waya, ina zaton da farko ma bai yi niyyar sanar dani ba, kawai na kama shi suna waya."
Hajiya Kari ta ce, "To ya ya kikayi?" Ta ce, "bu
ɗ
e wuta mana, y
anzun nan in gaya miki kaca-kaca mukayi da shi". Hajiya Kari ta ce, "Kash! Ai ke kin ji matsalar ki,ke da zakiyi kwanto kamar yanda muka saba,me ma kika sani game da yariyar?" Hajiya Jummai ta ce, "Me kuwa? Abinda na sani kawai ya ce min ƴar abokinsa ce,ki
shi ya rufe ni na hau masifa." Hajiya Kari ta ce, "lallai kin so ki kwafsa,ko sunanta ba muji ba, saboda haka da safe ko kuma yanzu ki je ki bashi haƙuri ki ce masa zafin kishi ne, daga nan sai ki bugi cikin shi muji komai."
Hajiya Jummai ta ce, "sai dai
goben, amma yanzun kamar ba zai saurareni ba,na san shi sarai ina ganin wannan karon ko boka na dutse ba zai iya aiki kan Alhaji ba, zan nemi wani tunda har yau bana juya shi yanda nake so,sai yanda ya ce, dole haka za'ayi."
Hajiya Kari ta ce, "kada ki da
mu, zan zo gobe sai mu yi magana a tsanake, amma don Allah ki kwantar da hankalinki" ta ce "zan yi ƙoƙari."
Yana saka kaya ta shigo da sallama. Ta ci gayu cikin shadda mai kalar ja, ƙyan shaddar da tsarin
ɗ
inkin shine ya toni asirin tsadar kayan,ƙamshinta
ya cika
ɗ
akin,cike da salo ta iso gurinshi ta amshi (Nect tie)
ɗ
in tana gyara mishi tare da fa
ɗ
in, "ka ganka kuwa Alhajina? Kai ka yi ƙyau." Bai ce mata komai ba, haka nan bai saki fuska ba, kuma bai katse ta da gyara mishi (Nect tie)
ɗ
in ba, sai da ta ga
ma yana kallonta,ta
ɗ
auko turarenshi Matador ta fesa mishi ka
ɗ
an, sannan ta ce sauran ka (break) ya ce na ƙoshi,ta dube shi da sauri ban gane ka ƙoshi ba? Kana nufin ba zaka ci ba zaka fita?"
Ya soma tafiya,tasha gabanshi cikin yanayin tausayi,ta ce "Haba
Alhajina, kayi haƙuri na san ban ƙyauta ba laifin kishi ne, sonka ne ya sani na yi maka haka." Ya tsaya yana dubanta, sannan ya ce "Don kina kishina sai ki min rashin kunya? Har kina gaya min cewa ni macuci ne?" Ta zube ƙasa guiwa biyu.
"Kai min afuwa,ba
zan sake ba." Ta soma hawaye, mai tausayi ne musamman ga mata,don haka ya ce "naji tashi shi kenan, amma kada ki sake,batun Break kuwa na yi latti,in na dawo zan ci na dare" cikin shagwa
ɓ
a ta ce,"ka kula min da kanka." Ta rakashi zuwa ƙofar falo,yana fita
ta ce,zaka sani ne, tunda ka ce mata kasa gaba.
Hajiya Kari ta dubi Hajiya Jummai.
"Ina jin ki."
"Wai kin san da ya ya ma ya fa
ɗ
a min sunanta?" Ta
ɗ
an dakata,kafin ta cigaba "sai da siyasa,na ce haba Alhaji ko baka huce ba ne? Kana ji ina tambayarka su
nan ƙanwar tawa amma ka min banza."
"To me zan ce miki" haka fa ya ce min sai daga baya yake ce min "A'isha." Yaƙi gaya min ma lokacin bikin."
Hajiya Kari ta ce, "ki bar shi,ai dai in lokacin ya matso dole muji, tunda mun samu sunanta shi ne kawai abin b
uƙata, yanzu kuma mun ji."
Yanzun sai mu sa ranar tafiya maguzawan, "To yaushe ne zuwan? Inji Hajiya Jummai,ta cigaba "Kuma sai dai mu je da direbanki, kamar kowane lokaci" "Eh,ai ina sane ba zamu bar wata kafa ko ya ya take wadda zata tona mana asiri ba,
ke dai ki shaƙi ku
ɗ
i don bokan dutse yanzun idanunshi sun bu
ɗ
e da son ku
ɗ
i,da, ko akan dubu biyar ma sai ya yi kisan rai." Jummai ta ce,"A sosai ma kuwa,
ɗ
an iska ni har yau ma ban sai mashi motar da yake naci ba". Hajiya Kari ta ce "ke dai bar
ɗ
an iska ko
ina ruwan wanda ke cikin daji da mota?" Jummai ta ce,"nima shine na gani, shiyasa na share shi,rabo na da zuwa gun shi tun aikin ƙarshe da ya yi mana,na matar ƙarshe da Alhaji ya aura." Hajiya Kari ta ce, "ƙyale shi wannan karon sai ki sai masa ko ƴar sta
rlet" Hajiya Jummai ta ce "hakan za mu yi" nan dai suka ci gaba da shirya ranar da zasu tafi.
Da gudu suka rungume juna suna murna.
*A'isha Mustapha kin
ɗ
an rame." Inji Suwaiba Ringim.
"Nayi rashin lafiya ne, Zainab K.T bata iso ba?"
Sam, A'isha ba t
ayi niyyar sanar da Aminan nata batun auren nata ba, saboda kunya take ji, duk cika bakin da takeyi na cewa ita karatu zatayi kamar ba gobe,don Doctor zata zama yanzun ma har Doctor Aisha suke ce mata,in ko suka ji ta san zata sha tsokana, sai dai su shafa
su ji bata dawo ba, Zainab ma ta iso kuma sun duƙufa karatu babu wasa.
Alhaji Saddiƙ ya yaba da yanda Abba ya tsaya tsayin daka, aikin kamfanin ya kammalu. Guri ya yi ƙyau duk mutane sun yaba,don haka shima bai yi wasa ba wurin kawo duk wani abu da kam
fanin ke buƙata don fara aiki.
Alhamdulillah,tuni kamfani ya soma aiki, Abba kuwa ya samu kujerar manaja, yanzu sunturi yake yi tsakanin Dutse da Jigawa, Alhaji Saddiƙ ya ce mishi ya nemi gida nan Jigawa sai a siya, sannan ya saya mishi ƴar mota,ba a jima
ba suka samu gidan suka dawo Jigawa.
[12/1, 19:47] Ummi Tandama
😇
: ____________________________
*
📗
MUMMUNAN ZATO
📗
*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Ɗandano page 6*
Aisha tana makaranta ba ta san ana yi ba.
Gu
rin Abba Alhaji Saddiƙ ya ji cewa satin da zamu shiga ne visiting day
ɗ
in su mutuniyar shi,ya ce "To Friend ka bari ni zan je mu da Nafisa" Abba ya ce,"shiyasa na sanar da kai don tasan cewa magana tana nan.
Waya ya yiwa Nafisa cewa,ta shirya zasu je visi
ting tana jin haka ta soma murna. Sun
ɗ
au hanya in da Yahaya direban shi yake jan su. Aikin shi yake yi a bayan mota cikin laptop, harkokin business
ɗ
in shi yake ta yi. Nafisa ko sai dai kallon ƙauyuka take yi, sai da suka isa garin Kano sannan suka tsaya
bakin Sahad Store ya yi mata tsaraba mai ban mamaki, sannan suka
ɗ
auki hanyar Munjibir.
Da tambaya suka isa makarantar,Henesy baƙa wul tana ta sheƙi,ta
ɗ
auki hankalin da yawan ƴan makarantar,gilashinta masu duhu ne,don haka suke ganin mutane. Ya dubi dire
banshi ya ce "Yahaya fita ka samo mana ofis
ɗ
in (PC)
ɗ
in makarantar."
"To ranka ya da
ɗ
e" inji Yahaya.
Jim ka
ɗ
an ya dawo.
"Ranka ya da
ɗ
e ga ofis
ɗ
in can, har ma na yi mishi bayanin cewa maigidana yana son ganinshi,kuma ya ce mu shigo" "To ai shi kenan."
Inji Alhaji Saddiƙ, tare da Nafisa suka fito. Ƙwarjinin Alhajin ya sa ya zama abin kallo gurin
ɗ
aliban tare da masu ziyara. Kai tsaye ofis
ɗ
in (PC)
ɗ
in suka nufa,suna shiga shima (PC) din ya miƙe tare da ba Alhaji Saddiƙ hannu,don daga ganin shi ya jiƙe da
Naira. Sun gaisa, sannan suka zauna kan wasu kujeru da ke gefe,ya nuna ma Nafisa wata kujera ya ce, "Bismilla Malama" shi ko Yahaya cewa ya yi,bari ya koma gurin mota.
Alhaji Saddiƙ ya ce,"mun zo ziyarar yarinya ne."
"Ya ya sunanta?" Inji P.C.
"A'isha
Mustapha, daga Gumel ta jihar Jigawa."
P.C ya ce,(S.S) take ko JS?"
"S.S one." Inji Alhaji Saddiƙ.
"Ok" ya miƙe yana fita ya kira shugabar
ɗ
alibai ya aike ta neman A'isha,ya dawo ya ce bari a kira ta.
Alhaji Saddiƙ ya ce,"Ba komai" ya zauna tare da cew
a, "Ranka shi da
ɗ
e ƴar ka ce?" Alhaji Saddiƙ ya amsa da cewa "Eh,ƴar abokina ce", wayarshi ta shiga ruri,ya
ɗ
auka yana magana.
Shugabar ta gano A'isha ne tare da ƙawayanta Zainab da Suwaiba,in da Yayan Zainab ya kawo mata ziyara daga Katsina, ta ce kece A
'isha Mustapha ko?" Ta amsa da "eh,ni ce."
"To ki zo inji P.C"
A tsorace ta ce,"lafiya?"
Nima ban sani ba" ta ce "Ina jiran ku" ta nufi ofis
ɗ
in shugabar ce ta shiga,ga ta nan Sir,ya ce ta shigo, nagode miki ta fita sannan ta ce A'isha ta shiga, ita kum
a ta tafi. Tana shiga ta ji hancinta ya shaƙi dadda
ɗ
an ƙamshin turaren Uncle,gabanta ya fa
ɗ
i amma ta daure ta shiga,sanye take da wando da riga ha
ɗ
e da gyalen su, kayan mutanen Pakistan masu kalar sararin samaniya, kai tsaye teburin P.C
ɗ
in ta nufa, inda t
a gaishe shi cikin harshen Turanci, sannan ta ce gata,ya nuna mata Alhaji Saddiƙ da ke waya.
"Ga masu visiting na ki." Ya miƙe "Bari na barku, ku gaisa ko?" Ya fita.
Duk sai taji kunya ta rufe ta, har ma ta ja gyalenta ta rufe gefen fuskarta. Ta dubi Naf
isa,ga zatonta matarshi ce. Cike da dariya Nafisa ta ce, "zo mu gaisa A'isha." Ta isa gurinta ta zauna, sannan ta ce "Ina yini? Ya ya hanya?" Nafisa ta ce "lafiya lau,hope kema kina lafiya?" A'isha kanta a ƙasa ta ce "lafiya ƙalau." Nafisa ta ce "Hajiyarmu
da Alhajinmu sun ce mu gaishe ki" A'isha ta ce, "ina amsawa, na gode."
Dai-dai sannan Alhaji Saddiƙ ya gama waya ta
ɗ
an saci kallonshi da gefen ido. Wata jiƙaƙƙiyar shadda ya saka kalar ƙasa,ya yi ƙyau sosai ta zamo daga kan kujera don ta gaishe shi.
"I
na yini Uncle?"
"Bana cin miƙe A'isha, daga nan za ki gaishe ni?".
Ta saka gyale ta rufe fuskarta, sannan ta miƙe taje gefenshi ta tsugunna,muryarta ƙasa-ƙasa ta sake gaishe shi. Ya amsa yana dariya.
Nafisa ma dariya take yi, sannan kunyar A'isha ta bur
ge ta, A'ishan ta mata ƙyau,sai dai yarinya ce ƙwarai, ya ce "Nafisa yau dai ga ki ga A'isha" Ya dubi A'isha ya ce, "Ga ƙanwata Nafisa." Ta kuma duban Nafisan.
"Sannu da hanya"
"Yauwa," Nafisa ta amsa da fara'a.
A'isha ta miƙe tana kallon Nafisa, "Bari
na kira ƙawayena." Har za ta fita, ya ce "Zo" Ta dawo ta tsugunna.
"Wa zaki ce musu ya zo?"
Ta rufe fuska,tana
ɗ
an murmushi. Ya ce, "Umh,wa zaki ce musu? Ko har kin basu labarina ne?" Ta girgiza kai, sannan ta ce, "Ce musu zan yi Uncle
ɗ
ina ne." Ta miƙe
ta fita da sauri. Dariya Nafisa ke musu, ta ce "Yaya Saddiƙ duk da A'isha yarinya ce kun matuƙar dacewa, Allah dai ya yi mana jagora tare kuma da shige mana kan matsalarmu." Ya ce "Amin sister."
Ta je gurin su Suwaiba ta kira su, ce musu ta yi Uncle
ɗ
inta
ne daga Katsina, suka shigo suka gaishe shi,ya tambayi sunayen su suka gaya mishi,ya ce "Har da ƴar garinmu? To sannuku,ku dage da karatu ko?" Suka ce, "To mungode" ya ce "nima na gode." Suka fita suna mamakin dama A'isha tana da Uncle a katsina, Amma ba
ta ta
ɓ
a gaya musu ba? Zainab kam so take ta tuna inda ta san shi.
Nafisa ta miƙe, "A'isha bari na bi ƙawayenki na
ɗ
an miƙe ƙafa," A'isha ma ta miƙe ta fito, kira ta ƙwalawa su Zainab.
"Ga baƙuwa ko zaku je school shop."
Suka ce, "To" ta dawo ofis
ɗ
in t
a zauna, ya dube ta "Ya ya bayan rabuwa?" Ta ce "Da godiya, shi Abbana ba zai zo ba?" Ya ce,in gaishe ki ba zai samu zuwa ba, saboda aikin shi ya koma Jigawa. Kuma yanzun Jigawan ku ke" ta dube shi, "Mun tashi daga Dutse?" Ya ce "Haka ne,to yanzu yaushe ne
zakuyi hutu?" Ta ce, "Nan da sati biyar zuwa shida." Ya ce, "To so nake a shirya komai kafin kuyi hutu, cikin hutunku za'a
ɗ
aura aure tare da bikin." Gyale taja ta rufe fuskarta. Ya ce, "Me kika ce?" Ta ce, "Duk yadda ku ka yi,ni dai karatuna na fi ji" Ya
ce, "wannan babu komai, sai makarantar da ki ke so ita zan kai ki" ta ce "Bari na samo maka wani abu." Ya ce, "No,bar shi am ok." Ya dubi agogo bari muyi sallah mu zo mu tafi." Ta ce, "To."
Bayan sun yi Sallah,ya dawo ya yi ma P.C alkhairi mai yawa,P.C y
a rako shi har gun motarsa. A'isha taje ta kira su Zainab su yi sallama,har ma ta ce ma Sani Yayan Zainab,ya zo ya bi su Uncle
ɗ
in ta mana tunda suma Katsina za su je.
Sanda suka iso gurin motar Yahaya,yana ta aikin jibge ƙwalaye a ƙasa daga boat
ɗ
in mota
r,Sani yaja baya ya tsaya yana mamakin ganin Alhaji Saddiƙ K.T. mutumin da ya yi ku
ɗ
i da jinin mutane, yanzu kuma dabarar da ya sake kenan? Ta shigowa makarantu yana son shan jinin ƴan makaranta? Sun gama sauke kayan suka shiga mota.
Alhaji Saddiƙ ya miƙa
ma Nafisa bandir
ɗ
in ku
ɗ
i yace ba ƙawayan nata. A'isha ta leƙo tana cewa, "Nafisa ku sauka lafiya,ku gaida ƴan garin." Ya ce, "Ni fa ko Nafisa ka
ɗ
ai ki ka sani?" Nafisa ta ce, "yauwa ga Yayan Zainab shima Katsina zai je". Alhaji Saddiƙ ya ce, "To ya shiga
mu je." Ta zo gurin su, ina Sanin?" Yana daga bayansu ya ce,"A'a su tafi ni dama sai gobe ina da aboki nan cikin Munjibir,ta je tace su tafi su Zainab ma suka je sukayi godiya.
Suna tafiya sai ya zo gurin su ya nuna A'isha, "wannan mutumin ne Uncle
ɗ
in k
i?
Zainab ta ce, "Ka san shi ne? Nima ina ta mishi kallon sani."
"Sani ya ce, "kin san shi mana, Alhaji Saddiƙ Usman K.T
ɗ
in ne baki sani ba."
Zainab ta dafa ƙirji da ƙarfi.
"Kana nufin me ku
ɗ
in jini?" Ya ce "shi ne mana."
A'isha ta zaro ido,me ku
ɗ
in
jini kuma?" Sani ya ce, "tab
ɗ
i,ke da baki san halin Uncle
ɗ
in na ki ba? Koda yake ai basa cin na gida sai bare."
Jikin A'isha ya soma rawa, cikin matsanancin tsoro ta ce, "Don Allah ku gaya min gaske ne?" Zainab ta ce, "kada ki damu zan baki labari,ku zo
mu ƙwashe kayan nan." Ta ce, "ai ni bazan
ɗ
auki wani abu ba har sai naji labarin Uncle." Suwaiba da Zainab har ma da Sani suka shiga ƙwashe kayan. Zama tayi bakin gado tana tunanin baƙon al'amarin, har suka raka Sani suka dawo.
Zainab ta zauna kusa da ita
, A'isha dama baki sani ba,shan jini suke yi,An ce aure-aure ya ke yi, duk wadda ya aura ba ta sati biyu take mutuwa,aurenshi goma, uwargidan ce ka
ɗ
ai bai cinye ba, ke yanzu fa ba a bin layin gidan shi,don ance kana cikin tafiya a layin wani abu zai ja ka
zuuu sai dai ka ganka a cikin wani
ɗ
aki a gidan,ke kina ganin gidan kin san ana cin mutane a cikinshi, ko ba ki san gidan ba?"
A'isha cikin tsananin tsoro ta ce "ban ta
ɓ
a zuwa ba".
Suwaiba ta ce, "Tab! Amma ya yi ƙyan banza." Zainab ta ce "kinga gidan ne
wani mahaukacin gida ga bishiyoyi."
A'isha sai kuka,lallai Allah ya so ta tana zuwa gida zata sanar da Abbanta. Duk kayan da ya kawo ta ce bata so,ta ma fita hayyacinta cikin ƙwana uku ta ƙwanta ciwo,ƙwananta biyu ta
ɗ
an samu sauƙi. Amma duk ta rame su Z
ainab sun yi ta matsa mata da son jin gaskiyar lamarin ta da Alhaji Saddiƙ don sun ga yanda ta
ɗ
auki abin da zafi ƙwarai. Ta gaji ta gaya musu cewa Babanta ya riga ya bashi ita,sun jajanta mata tare da kuma bata shawarar ta tashi tsaye da addu'a, Allah ya
shiga tsakaninta da sharrinshi. Sun ce suma za su taya ta.
A daddafe dai suka yi jarabawa, Abba da Abdulrahman ne suka zo
ɗ
aukanta, Abba ya dube ta, "A'isha ciwo ki ka yi haka? Na ganki ne babu ko ƙyan gani?" Hawaye ya soma zubo mata, cikin sanyi murya ta
ce "Abba nayi ciwo ne sosai."
Sun isa Jigawa misalin ƙarfe biyar na yamma,suna tsayawa A'isha ta fito tana kallon sabon gidansu,ga dai gida mai kyau amma ta kasa jin farin ciki, kuma ta yarda cewa iyayenta suna cin ku
ɗ
in ƴarsu ne. Nan take hawaye ya soma
zubo mata,ta shiga ciki.
#######
[12/2, 08:00] Ummi Tandama
😇
: ____________________________
*
📗
MUMMUNAN ZATO
📗
*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*