Showing 27001 words to 30000 words out of 96827 words
kamar zata d'auki wani abu" ta mintsinesa daga tsakkiyar k'afarsa me cike da gargasan gashi"bata janye hannunta ba saida ya janye k'afar tasa"ta d'ebo spoon guda ta nufi bakinsa dashi tana
dariyar yadda kamal ke santi"Ahankali tace" ga snacks nan sai sa'ada takai muku mota ko?da sauran dambun"gaskiya kin kyauta sosai muna godiya Amaryar mu"dama da my leemart nazo Amma ranar dinner
zaki ganta" to shikenan Allah yakaimu lafiya...dinner? Abdal
lah ya maimaita kalmar Azuciyarsa yana tauna dambun naman"saidai d'and'a nonsa ba k'aramin dad'i yamasa ba"Amma A bad'ini saiya yamutsa fuska" kamal yatashi tsaye yana fad'in tashi muje mu jirashi Amota ko baby?"yafad'a yana k'ok'arin d'aukar warmer guda"
sa'ada da dama ta gama ta tashi ta d'auki warmer guda ta kalli ummul khairy tace"Anty ai zaki rako yaya idan zai tafi ko?"Eh"to shikenan sai muyi sallama dg nan idan kin fito"dato ummu ta Amsa tana jin tsoron subarta dg ita sai A
bdallah a parlourn"bata gam
a wannan tunanin ba suka fita....
✍
️
wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251
Idan kika karanta mun b
ook baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
❤
🔥
❤
🔥
*AUREN YARJEJENIYA*
❤
🔥
❤
🔥
*21&22*
....... Da sauri ummu ta matsa nesa dashi tana wasa da yatsun hannunta"Abdallah kuwa tab'e baki yayi yana danna wa
ya"Ahankali tace"ina wuni?...."bana son ita gaisuwar taki"yafad'a kamar daman jiran ta gaidashin yakeyi"shikenan insha Allah bazan koma gaisheka ba"kikace mene?"yafad'a yana tsareta da ido"tak'i kallonsa kuma tak'i mgn"yaja tsaki yana fad'in saura 8days Ai
?"mekake nufi?"bansaniba"last warning d'ina dake na k'arshe"duk lokacin dakika koma sawa naci Abinda yafito dg k'azamin hannunki saina baki mamaki"ban mance motar da kika saka na bud'e miki ba"ga yanzun kin koma sawa naci Abinda banyi niyaba"to sonake ki c
ika na ukkun dan Allah kiga yadda zamu kwashe dake"ni sai yanzun nake tausayawa wanda kikeso sbd ba k'aramin k'ok'ari yayiba"yafad'a yana jan tsaki ya mik'e tsaye yanufi bakin k'ofa"har zai fita sai kuma ya tsaya saida yagama shan k'amshin sa kafin yace"na
ji zancen dinner"bansan da itaba kuma bbu Abinda zanyi Akai"keda wanda kukayi gulmar buga invitation d'in sai kusan yadda zakuyi Amma ni baranjeba"ke wai nan Amarya ce ko?"yafad'a yana juyowa yana murmushi yana kallonta"zaki san ke Amarya ce kuwa very soon
....duk irin bak'ak'en maganganun dayake gaya mata tanaji Amma ta lashi takobin bazata kulashiba"yaso ta tankasa Amma saita share"ya bud'e k'ofar yafita ya bugata da k'arfi"ta mik'e tsaye ta biyo bayansa sbd suyi sallama da sa'ada"saida ta had'a da sauri
sannan harta taddosa suka jero suna tafiya bbu me mgn Acikinsu"sosai maganganun sa sukayiwa ummu zafi Azuciya"hakan yasa suna fitowa kallo d'aya kamal yamata yasan tanada damuwa"sosai yaji tausayinta"ya diro dg samqn motar yana fad'in ranki yadad'e sai yan
zun aka barsa yafito?"murmushin yak'e tayi batace komaiba"sa'ada ta fito dg cikin motar tana kallonta tace"Anty sai ranar dinner d'in ko?"kanta ummu kawai ta gyad'a mata kafin tace"ki gaishemun da Ammi Allah ya tsare"dg haka ta juya ta koma ciki da sauri
sbd kukan dake k'ok'arin k'wace mata"kamal ya harari big man yabud'e mota ya shiga"suka saka sa'ada A tsakkiya"kamal nason yamasa mgn Amma bbu dama"sa'ada kuwa sai surutu takema kamal yana janta da fira"wacce duk
firan kan ummu ne"big man dayaji surutunsu
yayi yawa ya bigema sa'ada baki"yana fad'in yaushe na zama Abokin wasanki??"kai kuma meye Abin kabiye mata kuna fira irin haka??"yafad'a yana kallon kamal"shikuwa tab'e baki yayi yace"bazan fasa fira da ita ba"kai kuma sai kayita yin shirun da bakinka"okay
toko saukeni zakuyi ne? duk yadda ka zab'a haka za'ayi"cewar kamal ak'ule sbd yafara bashi haushi"banza big man yamasa k'asan zuciyarsa yana jin dad'in yadda yaga damuwa Atare da ummu yanzun"da wannan tunanin suka iso gida"kamal ya kalli sa'ada yace"ki kw
ashe kayan ki kai ciki"gobe zanzo na maida mata warmers d'in"tamkar big man yayi mgn sai kuma yafasa sbd ya lura haushinsa kamal keji"fitowa dg cikin motar yayi hakan yayi daidai da kiran Ammi ya shigo wayarsa"Amsar key d'in motar wajen driver yayi batare
da yabi takan kamal ko sa'ada ba ya wuce yana bin kiran Ammin......
Ummu na komawa ciki ta samu waje ta lab'e tasha kukanta"saida taji zuciyarta tayi sanyi sannan ta koma parlourn ta d'akko ruwa swan ta wanke fuskarta"saidai ta fauwalawa Allah l
amarinta"sbd tasan jinkirin Aurenta da wanda kuma zata Aura d'in da irin Auren da zasuyi! duk k'addarartace tazo mata A hakan"kawai zata dage da Addu'ar Allah ya azata samqn wannan me girman kan"da wannan tunanin ta wuce babban parlourn gidan"umma da goggo
murja da Anty Aysha da lawisa suna zaune tsakkiyar parlourn suna kallon kayan lefen"kowanansu bakinsa washe da fara'a"ummu na shigowa lawisa tayi Ihu ta taso ta rungumeta tana fad'in masha Allah k'awata! kinyi goshi wlh"harda gwalagwalai da key d'in mota
"super kala 50"laces kala....dan Allah ya isa lausy nidai basai kin fad'amun ba kizo muje ki rakani gida"ah ah bbu inda zakije kizo ki duba kayan a fidda kala 12 Akai wajen d'inki"tunda kinga wuri ya k'ure"cewar goggo murja"ummu batayi mgn ba ta zauna k'as
a kan carpet tana kallon kayan bata tab'a ba"komai classic ne Aciki"bbu lace d'in 40k daga na 50k sai Abinda yayi sama"kaya kala 100 ne sai English wears da dubai Abayas da kayan k'asar turkish kala 50"takalmi da jaka dozin biyune gyalema haka"saidai bbu h
ijab sai inner wears da kayan bacci dana shafa dana kwalliya"sai sark'oki da y'an hannu da zobba da Agoguna"gwala gwalan kuwa fiddasu akayi daban"itadai ummu tana kallo lawisa nata d'agawa"bayan sun gama gani lawisa ta fidda mata kala 12 da zata kai d'inki
"wanda ummu bata soba"sbd Aganinta ta Amshi lefensa bayan ba Auren dindin bane"kuma bbu Abinda zai shiga tsakaninsu idan Anyi Auren"idan yace ta biyashi fa?"ta tambayi kanta lokacin da goggo murja ke cewa nan za'a barshi kowa gobe yazo yagani"dangi da Abok
an Arzik'i kowa sai yazo yagani"bazamu kai kayan can ba Aje Asace sbd nasan wacece kakarta da kishiyar mamanta"umma tace"to shikenan sai Ayi hakan"ummu batace komaiba ta tashi suka koma d'akin lawisa"ita ta kwanta gefen bed tana tunani sbd ba sallah take
ba"ita kuwa sallar magrib tayi"bayan ta ida ta kalleta tace"ki kira telan naki yazo da dare ya Amsa ko?"wai lawisa manta kalar Auren da zamuyi kikayi?"taya zqn tab'a masa lefe bayan kinsan AUREN YARJEJENIYA ne?"idan naje gidansa yace na biyashifa?"kinsan d
ai banida halin biyansa Abinda na tab'a ko?"d'an murmushi lawisa tayi ta mik'e tsaye ta dawo gefen bed d'in ta zauna tana fad'in"dama na lura kinada damuwa"to bari kiji wata mgn"muddin kikayi saken da wannan Auren yarabu kin tabbata wawiya ummu"ko bakiso b
ig man sbd dukiyar saba zakiso sbd kyawunsa da kasancewar na daban Acikin maza"musammun daya kasance be kula mata"wanda da wuya kisamu namiji da irin wannan halin awannan zamanin....kin sanfa halinsa lausy wace irin mgn ce kikeyi haka?"bazan iya rayuwa da
wanda baya sona ba yana kuma wulak'antani"hmm! ki kasance me d'aukar shawara k'awata"Ahankali Ahankali wlh zaki janye hankalin Abdallah bbu boka bbu mlm"kiyi hak'uri
ki shanye komai saiya kamu sannan kijashi k'asa ki nuna masa cewa mata suna suka tara"kuma
kowace da irin baiwarta da darajarta"ina fatan kin fahimta?"ba wai ina nuna miki k'i shige masa ba"ah ah shi yak'i d'an siyasane sannu a hankali zaku saba"inaso Ace idan kunyi Auren harma girki kece zaki masa"banaso idan kin shiga gidan ki masa rashin kun
ya ko masa musu"no bishi da yadda yakeso ki kuma yi k'ok'arin kyautata masa shida mahaifiyarsa da k'anwar sa"dan yanzun haka umma sunyi bincike mamansa ta fita dg gidansu"matar babansa itace sila kuma big man baya shiri da ita"Abinda yaka mata kiyi kijawo
sa'ada Ajiki ki kuma nisanci matar babansa"musammun tunda Ance gidansu zaku fara zama"kiyi hak'uri kiyi Addu'a insha Allah sai kinyi farin ciki da wannan Auren wata rana k'awata"ina jin hakan sosai Ajikina"saidai karki sake ki nuna fara'a garesa ko shishsh
ige masa ko cusa kai"ah ah kema ki nuna da ajinki"ina zaune zanji labarin yasoke AUREN YARJEJENIYA insha Allah"su mabashshir sai kuma Akama wani sarkin"ta k'are maganar tana dariya"ummu tasaki Ajiyar zuciya domin ta gamsu da shawarwarin Aminiyar tata"bbu b
'ata lokaci takira telanta Anan ma gidansu lawisan yazo yasameta ya Amshi kayan...."saidai Abin mamaki hjy yaya da goggo luba da Asiya kasa hak'urin gari yawaye suzo ganin kayan sukayi"Acikin daren sukazo suka gani"hjy yaya ta nuna kayama gidanta za'a kais
u sai bayan bikin Akaima ummu"saidai baba yatake mata burki"goggo luba kuwa A daren ranar batayi bacci ba sbd bak'in ciki da hassadar ganin dukiyar da'aka mallakawa ummu....
Ayau friday take dinner"tun wajen k'arfe 4 Aka gama wankema Amarya lalle ja
da bak'i da yayi wani irin fitinan nan kyau"kowa yaba tsaruwar lallen yakeyi"tana gama wanka suka tafi wajen make up"sai 6 pm suka dawo gida"wanda dama da kayanta ta tafi ta shirya Acan"duk wanda bema ummu farin sani ba da wuya yaganeta"sbd yanda tayi wan
i irin mugun kyau"make up yayi kuma an nad'a mata d'aurin d'an kwalin yadda ya kamata"material ne me k'yalk'yali white me zanen silver tasaka"d'inkin fited gownt"takalmi da post da net d'in data yafa dg baya duk silver ne"haka y'an kunne da sark'a da Agogo
ful silver ne"ga wani irin fitinan nan k'amshi me dad'i dake tashi Ajikinta"itama lawisa ta shirya cikin sabon material maroon colour tasha make up"itada nura ne da zata Aura a front sit sbd shine yakaisu wajen make up d'in kuma yakoma ya d'akko su"da k'y
ar sukayi parking dg farko farkon shigowa layin" sbd duk wajen yacika da maka makan motoci na Alfarma"lawisa ta juyo ta kalli ummu dake danna waya tace"k'awata ba 7 pm kamal d'in yace za'a tafiba?"Amma naga tun 6 waje yacika da motoci"Eh nima nayi mamaki"
okay Amma muje ciki muga friends d'in mu sun fara taruwa ne"dato ummu ta Amsa ta bud'e k'ofar Ahankali ta fito"duk ga maza nan Abokan big man da y'an ganin k'wam"tj da junuid suka kafe ummu da ido suna ganin Abdallah yadace da samun kyakykyawar mace"ita ku
wa batama lura dasuba"lawisa na rik'e da hannunta suka tura get d'in gidan su lawisa d'in suka shiga"wanda hakan yayi daidai da motar sadeeq tayi parking Awajen"ya d'akko k'anwarsa leemart da sa'ada"sbd leemart tace"sun had'u da kamal Acan"dan tasan shida
Ango zasu tafi"tasan kuma big man bbu wasa... sa'ada tasha gayunta cikin farin leshi iri d'aya itada leemart"ga make up An musu suka fito rik'e da hannun juna itada leemart"sadeeq na rik'e da hand bag d'in sa'ada yasaka mata kud'in lik'i a ciki sannan ya m
ik'a mata"ta Amsa batare datasan meya saka ciki ba"itada leemart suka shige gidansu lawisa"sadeeq kuwa ya zauna samqn motar sa yana danna waya"tj dake kallon komai yatab'o junuid yana tab'e baki yace"ina gafa wancan yaron kamar kamun sa'ada yakeyi"ta yaya
ka gane?"irin yadda yake shige mata da irin kallon dayake mata"kuma wlh ni sonta nakeyi"nan gaba kad'an idan ta k'ara girma nakeso na nuna"kasan na Auri k'anwar big man Aina warke"kallon bakada hankali junuid yajefasa dashi yana fad'in ka manta waye Abdall
ah wlh?"ko nayi rantsuwa bazanyi kaffaraba bazai tab'a bari ka Auretaba"kasan ikon Allah?"shiru junuid yayi yana kallon wasu y'an mata da zasu wuce yace"Ango dai shiru be isoba har yanzun"k'ilan yana hanya ko?may be.....
Ango kuwa suna can suna rigima
da kamal Akan yakafe bazai zoba"ko Inda za'a yi dinner d'in da Abinda za'a ci duk kamal ne ya d'auki nauyi"kamal kuwa ransa yab'aci matuk'a yasanar masa kuma muddin bejeba bbu shi bbu shi har Abada tunda be isa dashi ba"yayi tafiyarsa yabarsa part nasa"ba
dan yasoba yafara shiri"bayan yagama yaturama kamal text yazo ya d'aukesa ya shirya"shima text ya turo masa yasamesa dg wajen get d'in gidansu"dan dama bayan yabar part d'in Abdallah be tafiba ya zauna cikin mota"dan yatabbatar da cewa da gaske Abdallah d'
in bazai jeba"cikin izzah had'e da shan k'amshi yafito wajen"bayan ya disga body guards nasa Akan karsu biyosa"sanye yake da suit farare k'al sabbi"kuma manyan ne da ak'allah kud'insu zasuyi 500k "Agogo da takalmi na fata duk farare yasaka sai zabban Azurf
a guda 2 dake sanye Agudan yatsun hannunsa"sumar kansa tsabar gyaran datake sha har walk'iya takeyi"ya had'e rai bbu Alamar Annuri samqn choko face nasa"saidai yyi kyau har yagaji"kamal dai yatab'e baki ya zuro hannunsa yabud'e masa back sit tunda Anan umm
u itama zata zauna idan sunje d'aukarta yanzun"kasancewar Abdallah cikin haushi yake bema tsaya tambayar ma'anar shigarsa back sit ba kawai sai ya shiga ya zauna"bbu me mgn Acikinsu suna dai tafiya"kamar Ammasa tilas yace"ina zamuje?"gidansu Amarya"kana nu
fin sai munje d'akko wannan kucakar?"girgiza kansa kamal yayi yace"kana bani mamaki Abdallah"be halattaba cin fuskar musulmi da wulak'antashi da bashi tsoro batare da hakk'in shariah ba"karka manta itama bata sonka da wanda takeso Allah ne yawanzo wannan k
addarar tsakaninku"meyasa ka kasa ka manta sab'anin daya faru tsakaninku da ummu ?"wanda kai hukuncin daka d'auka yafi nata"ita marinka tayi"kai kuwa jini ka fidda mata"kasaka tayi jinya bayan ta zubar da hawaye"idan har kasan zaka wulak'antata meyasa zaka
nunawa duniya kana sonta kana son Auren??"to bari kaji Akwai friends namu da kuma Abokan kasuwancinka da sukazo har dg kasashen waje sbd suje gun dinner Akuma d'aura aure dasu"yanzun haka duk na kaisu masauki"idan kasaki wata b'araka kaine zakaji kunya"ka
kuma san jajayen fata suna matuk'ar bama soyayya daraja da mahinmanci Arayuwarsu"suna kuma girmama matansu"idan kaji shawarata fine idan bakajina ma fine"nidai Abinda nasani ina tare dakai tsakanina da Allah tun muna yara"sau tari idan yakama nayi badaida
i har hjy (mahaifiyarsa) tana kiranka ta sanar maka"ka kuma bani shawara koka tursasani nayi Abinda banaso sbd ka isa"Amma ni ka nunamun ban isaba"kafison kabi shawaran su junuid da badan Allah suke tare dakai ba"dg k'arshe kaji tsoron Allah karka cutar da
yarinyar mutane ku zauna lafiya har kurabu lafiya....shikenan! iya Abinda Abdallah yafad'a kenan sbd yaga Abinda yayiwa kamal be kyautaba"kamal kuwa parking yayi dg bayan wasu motoci Alayin gidansu lawisa"y'an mata nata fitowa anata jidarsu cikin motoci"w
ayarsa yazaro yakira leemart"bugu 3 ta d'auka"sweet heart kuna kusa da Amarya?"dg d'ayan b'angaren leemart ta Amsa da Eh"okay kice nace ta fito mu wuce lokaci na tafiya"kema ku fito Atare"dato ta Amsa ya yanke wayar"yajuyo suka had'a ido da Abdallah"harara
Abdallah yasakar masa"yayi murmushi yana fad'in baka tab'a yin kyau kamar na yau ba"lallai Aure rahama ne"be kulasaba ya bud'e k'ofar motar yafito"duk wasu sauran matan da mazan kallon big man dake tsaye gefen motar yana Amsa waya
sukeyi"Anata cewa ga Ang
on can"Adaidai lokacin kuma security mota guda suka iso sbd suyiwa couples d'in rakkiya.....lawisa ce Agaba tana rik'e da hannun ummu"sai sa'ada data rik'e gefen rigar ummu dake jan k'asa"sai leemart ne gefensu"da sauran friends nasu na biye dasu"masha All
ah!! masha Allah!!! Abinda kamal yafad'a kenan yana satar kallon Abdallah yaga yaya zaiyi idan yaga wannan kyakykyawar Amarya tasa?"danshi inba daya gansu sun fito da itaba bazai gane taba Inda ita kad'ai yaganta"mutumin gata nan fa Anfito da ita"yafad'a y
ana kallon big man"tab'e baki yayi yad'ago kansa"cikin second 10 yak'arema ummu kallo"Aransa yace"she is beautiful!"d'an sakin fuska yayi tun kafin su k'araso yanufesu cikin tafiyarsa ta kasaita"su tj da wasu samari suka saki Ihu"wasu y'an matan na bud'a"u
mmu kuwa gabanta ne keta fad'uwa"tunda ta hango big man"gashi yamata wani irin shegen kyau Ayau...wani irin harbawa zuciyarta tayi dataji mayataccen k'amshin turarensa"da sauri ta d'ago kanta"befi tak'i biyu ba ya iso gefen ta"sa'ada tayi murmushi tana fad
'in sweet heart baka jiran mu rakota?"Amamakin ummu sai taji Abdallah yace"No baby gara dai nazo na Amshi kayata nagaji da jira"yak'are maganar yana tsayawa gaban ummu"duk y'an matan nata kallonsa kamar tv" suna matuk'ar mamakin wanda ummu zata Aura"lawisa
na murmushi ta cika hannunta ta matsa gefe"Aikuwa yakama hannun nata guda ya d'an duk'o saitin kunnanta na gefen dama murya can k'asa yace"bakiyi kyau ba....rintse ido ummu tayi tana saka hannunta guda da nufin ta ture masa fuska yarik'e hannun yana sakin
murmushin mugunta" da hanzari Aka fara d'aukarsu pics"wanda kowa d'aukar masoya masu matuk'ar son junansu ake musu"shidai kamal nata smiling yana musu photo da wayarsa iphone"Abdallah kuwa cikin mugunta yayi k'asa da hannun nata yana murd'e mata shi"gashi
yayi tsaye gabanta jikinsu na gugar juna...yaya muje kushiga mota mana"cewar sa'ada"big man beyi mgn ba ya rik'e hannun ummu suka fara tafiya"ana biye dasu bbu me mgn Acikinsu"kamal yayi hanzarin bud'e musu back sit yana fad'in ranki yadad'e barka da isow
a"batayi mgn ba ta daiyi murmushi"itace tafara shiga sannan Abdallah yashiga"leemart ta zauna gefen kamal sannan yatashi motar"yayinda sa'ada na cikin motar sadeeq....tunda suka shiga motar ummu ta takure jikinta Awaje guda ta matsa can nesa"shima bebi tak
antaba sbd ganin basu kad'ai bane Acikin motar"bbu me mgn sai kamal dakema leemart surutu"tsoron ganin Abdallah yasaka ta kasa Amsawa"yayinda Abdallah keta Amsa wayoyin jama'a dake jiran isowarsu wajen dinner d'in"ba k'aramin mamakin ganin wajen cike da mu
tane Abdallah yayi ba"motoci gasu nan basu k"irguwa....ku zama on ready danayi muku knocking saiku fito"cewar kamal yana fita dg cikin motar shida leemart"sai sannan Abdallah yasaci kallonta yace"sannu Amarya kinji?"ya mutsa fuska tayi tace"niba Amarya bac
e sbd kafi kowa sanin irin Auren da zanyi"nan gaba kad'an dai zan zama Amaryar"dan Allah?"shiru tayi tak'i mgn"yaja tsaki yana fad'in duk ki Adana wannan tsiwar taki gaba kad'an zata miki Amfani"Akwai friends nawa da sukazo har daga k'asashen waje dole ida
n Angama dinner ku gaisa ki musu godiyar Attending d'in bikin ki da sukayi"saidai da harshen turanci zakiyi musu mgn"idan kinsan baki iyaba garama ki sanar mun karki bani kunya gaban mutane.....ummu na k'ok'arin mgn kamal yamusu knocking"hakan yasa batace
komaiba ta bud'e k'ofar dake side d'in datake zaune