Showing 15001 words to 18000 words out of 35352 words
maganin da ya bani ya kashe min dukkan jijiyoyin jiki sai kaina da ke faman juyi tamkar an jefa ƙwarya a ruwa.
Wata kwalba ya
ɗ
ora daidai wurin y
a soma tatsar jinina har ƙarar fitarsa kake ji,kamar minti biyu kafin ya cire kwalbar ya ajiye ta kan teburi.Wani magani ya shafa min a daidai ciwon mai bala'in zafi,har sai da raina ya kusa fita kafin da sauri ya cika bakinsa da wasu ruwa ya zo ya fara sh
ayar da ni su.Duk
ɗ
igo
ɗ
aya na ruwan da zan sha to tamkar ana warware azabar da yake jikina ne , wannan yasa nake shan maganin cike da zalamar da ta haifar min da soma shan yawunsa da kuma la
ɓ
ansa.
Jikin Uncle Salem ne ya
ɗ
auki wata irin rawa jin Naf
ɗ
insa na sumbatarsa kamar za ta cinye le
ɓ
ensa,duk wani tsohon feeling nasa da yake faman yin ƙasa da shi a kowacce safiya ya soma taso masa.A daidai ga
ɓ
ar da ya soma mayar mata da martani kuma tuni bacci ya
ɗ
auke ta,idonsa na fitar da wasu irin hawayen jar
aba ya soma sunsunar wuyanta yana jin tamkar ya mayar da ita cikakkiyar mace ko zai samu salamar ruhi.
Dakyar ya rareashi kansa ya janye daga jikinta,da
ɓ
as ya zauna yana duban yadda take baccin wahala . Ƙonannen jinin mai tattare da guba yayi baƙi ƙir
in a cikin kwalba,sai ya
ɗ
auke shi ya je ya zubar toilet ya wanke kwalbar.
Sai da ya je ya sake wata alwala sannan ya nufi masjid,a can ya samu Daddy bayan sun yi sallar sun fito ne Uncle Salem ya dubi abokin nasa ya ce “ Abdul Hameed ban san me yasa ka
za
ɓ
i ka
ɓ
oye min rufaffen sirrin Nafisa ba,amma hakan bai da wani amfani don kusan na fahimci matsalar junun da ke jikinta ya samo asali ne daga can tushe ba wai gamo ta yi da su ba”
Cak Daddy ya tsaya yana kallonsa, Uncle Salem ya jinjina masa kai ya
ce “ tabbas ko yau sun ziyarce ta,saboda sakacin addu'ar da ba ta yi ba”
Daddy ya ce “ mu je can gida zan yi ma bayani” haka suka wuce suka isa,a ke
ɓ
a
ɓ
en falon Daddy duk suka zauna tare da yin shuru Uncle Salem ya matsu ya ji labarin yayin da shi kuma D
addy ya rasa ta ina zai soma.Can ya nisa tare da furzar da huci kafin ya ce “ to da farko dai kamar yadda na fa
ɗ
a ma ni
ɗ
ana ga sarauniya Ayodele Ayush,kafin zuwan Musulunci a Victoria Falls suna bautar ababen bauta iri-iri ,yin tsafi kuma sai ya zama adon
garin.Sai dai sannu a hankali duk komai ya canza saboda yadda mahaifina sarki Ameer ya taka muhimmiyar rawa ganin ya kawar da duk wani fasadi sai dai kash zuwana duniya kuma aka tsiro da wasu sabbin canfi wai alamomi sun nuna za a sake yin maimaici wato d
aga cikin tsatsona za a samu wacce za ta jagoranci mulkin ƙasar.Amma tabbas ni ba magajin sarki ba ne,sosai na ji tsoro da jin haka don tamkar karatu haka ake biya min maganar nan har na mallaki hankalin kaina”
Uncle Salem yayi saurin katse shi da cewa
“ haba aboki ta ya za ka yarda da wani canfi?”
Daddy yayi murmushi wanda ya fi kuka ciwo kafin ya ce “ dole na yarda mana,duba da tun ina
ɗ
an shekara ashirin a duniya na ajiye iyali saboda yadda kullum nake kasa bacci ina harin neman abokiyar rayuwa wac
ce zan jefar wa da ƙwan haihuwar shugabar gobe ko zan samu sukuni ”
Uncle Salem ya ce “ kana nufin wai Naf?”
Daddy ya jinjina kai ya ce “aboki tun lokacin da na yi aure zan ce ma wannan larurar da ka san ni da ita ta mugun feeling ta kau,shi ma tun a
daren farkonmu.Sannan kana dai ganin yadda lamarin aurena ya kasance a sirrance sai daga baya iyayena suka sani,har bisa yanzu sarki fushi yake da ni saboda na ƙi yarda na zauna a can Victoria Falls ni kuma ina gujewa Nafisa ƙalubalen da za ta fuskanta ne
in ta zama shugaba”
“To amma mene yake baka tabbacin cewa hakan za ta kasance?” Uncle Salem ya tambaya .
Daddy ya ce “ saboda kama take da wata goggon Mamana ita ce mace ta biyu da ta mulki Victoria,to yadda ka ga Nafisa ita ma haka take kai kace tsa
ga kara ne aka yi.Hakan kuma babbar matsala ce domin zai iya kasancewa ita ta dawo duniyar nan a gangar jikin Nafisa ”
“ Wai ko sarauniya Deborat?” Uncle Salem ya tambaya,don kuwa ita
ɗ
in ba
ɓ
oyayya ba ce a duniyar nan duk kusan labarinta ya kara
ɗ
e ƙasa
shen duniya saboda shahararta wurin iya yin tsafi,sai dai ko kafin Daddy ya ce wani abu tuni tv
ɗ
in da ke manne jikin bango ta soma yin wata tsaga “ƙiiiii!” kafin kuma ta fa
ɗ
o ga ƙasa ,sai iska kuma mai ƙarfi wacce ta haifar da fashewa ƙwan lantarki ji kak
e
ɗ
uuu haskensa ya
ɗ
auke sai labulaye suka soma tashi sama suna wulwulwul....
[28/02 10:12] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*
☠
️
```LoVe aNd HoRrOr story```
👽
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI
💫
✍
️
}
*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman mak
aranta.
*FCWA*
☀
️
________________________
04
A cikin duhun
ɗ
akin ne Daddy da Uncle Salem suka hango wata mace sanye da fararen kaya wanda ko tantama babu likafani ne.A tsaye take jikin window sam ƙafafunta ba su ta
ɓ
a ƙasa ba sai wani lilo
suke kamar wacce aka rataye,farin gashin kanta kuwa sai yin sama yake iska na na
ɗ
a shi.
Cikin muryarta wacce kana ji ka san ba ta
ɗ
an adam ba ce ta soma yin magana,“ ko kai ko abokinka babu wanda ya isa ya dakatar da ni daga yunƙurin da nake,Yarima Abd
ul Hameed ban sani ba ko ka san cewa sunan Deborat ya haramta ga duk wanda yayi hijira ya bar gidansu domin guje abubuwan da allolinmu za su zartar,ka sani cewa Nafisa jaruma ce ba mu za
ɓ
e ta ba sai da sanin za ta iya.Sannan ka godewa Allah da ya kasance a
ikin alkhairi ne za ta gudanar ba wai na cutar da al'umma ba,sannan kai kuma da kake ta ƙoƙarin dakatar da mu ziyartar ta ka sani akwai lokacin da maganinka ba zai yi aiki a jikinta ba don haka gara ka baiwa kanka lafiya ka bar matarka ta yi aikinta yadda
ya kamata.A tunaninka hatta auren naku ba mu sani ba? Mun sani sarai saboda kai ne za ka yi jinyarta a lokacin da ta kammala aikinta na farautar azzalumai ” tana gama fa
ɗ
a kawai ta bi ta window ta fita yayin da kuma komai ya dawo normal hatta hasken ƙwan l
antarki rasss ya koma yana yi .
Daddy da Uncle Salem sai suka fara ƴar kallon-kallon ba tare da sun cewa juna komai ba.
Can Daddy ya kasa yin shuru ya ce “ aboki ka yarda da fatalwa?”
“ Na yarda mana saboda ni ma ita ce ta raine ni” Uncle Salem ya b
asa amsa .
“ Ban gane ba”
“ Eh kamar yadda na fa
ɗ
a ma ni kaina ban san iyayena ba domin a titi aka tsince ni to Inna Delu ta raine ni ta bani dukkan tarbiyya da kuma kulawa ta uwa,sai bayan na mallaki hankalin kaina ne ta sanar da ni ita wace ce sabo
da za ta koma makwancinta“
Daddy ya ce “ wai kana nufin dama Inna fatalwa ce?”
“ Eh sosai ! Bari na je na duba na ga ko Naf ta tashi” ya fa
ɗ
a tare da miƙewa ya fita ,hankalinsa da tunaninsa na kan fatalwar Deborat wacce kusan duk dare Inna Delu na yi
masa gatanarta.
Ko da ya shiga
ɗ
aki ya tarar Nafisa na ta yin baccin gajiya ,ya dubi agogo ya ga lokaci sai tafiya yake ga shi kuma ba ta yi sallah ba.Sam bai son ya tashe ta amma sanin sallar asar ma nada ƙurarren lokaci yasa ya soma shafar fuskarta da
tafin hannunsa mai taushi da sanyi.
Cikin bacci na soma jin sanyi na ratsa min kumatu,ga taushi kamar auduga.A hankali na ware idona na sauke su kan kyakkyawar fuskarsa,ban ida warkatsewa ba ya ce “ lokacin sallah Naf”
Jin ya ambaci sallah na y
i saurin tashi hankali tashe don na tsani na makara,ya
ɗ
an ja da baya yana mai ci gaba da kallona kafin kuma ya fita.Ni ma fitowa na yi na wuce can sashenmu sai da na fara gabatar da sallar sannan na yi wanka na saka riga doguwa marar hannu na
ɗ
aura kallab
inta sannan na fita.
Yunwa nake ji hakan yasa direct kitchen na shiga,Ammy ce da A'i mai aiki ke ta faman yin girki da dukkan alamu yau sarautar ta Daddy ta motsa shi yasa Ammy ke aikin da kanta.
“Yunwa nake ji” na fa
ɗ
a kamar zan yi kuka,A'i ta yi dari
ya ta ce “ oh shagwa
ɓ
arki Nafisa ko auta albarka ”
Ammy ta ce “ bar ni da ita dai ta ci gaba da sakalcin in ta je can ƙauyen ai na ga wacce za ta yi wa”
Kamar wacce suka yi wa allurar zaburar wa kuwa haka na wani kwanto jikin A'i mai aiki wacce nake ki
ra da Inna na ce “ ai tare da Innarmu zan tafi ita za ta dinga kula da ni,kafin na dawo ta yi min girki mai da
ɗ
i” A'i ta washe baki don sosai take jin da
ɗ
in yadda Nafisa ta
ɗ
auke ta tamkar Kakarta sam ba ta nuna cewa ita ke ƙasa gare ta,haka kuma ita ce ta
raine ta tun tana cikin tsumman goyo ko aiki za ta yi haka take goye ta in kuma ka ga sun rabu to Uncle Salem ne ke gidan.
“ Ki ma cire wannan a ranki don Inna A'i ba za ta bi ki ba” cewar Ammy tana mai zuba min kunun gya
ɗ
a a kofi.
Na ce “ wai Innar
mu ba za ki je ba?”
A'i ta ce “ ke wasa take yi miki fa,tuni ai na ha
ɗ
a komatsaina na ƙulle a buhu” cike da jin da
ɗ
i na
ɗ
auki kofin kunun gya
ɗ
ana na fito falo na zauna,tv na kunna na saka horror film ina kallo ina sha sam ban jin tsoron abubuwan da ake nu
nawa wani sa'in ma ji nake tamkar ƴan uwana ne.
Ƙ
amshin turarensa ne ya fara yi min maraba kafin shi ya shigo,na
ɗ
aga kai ina kallonsa .Sanye yake cikin kakin soja sun yi bala'in yi masa kyau sai dai ya aske gemunsa da sajensa,da sauri na ajiye kofin
hannuna ina turo baki ina kallonsa tuni kuwa ya fahimci dalili don tun ina yarinya nake fa
ɗ
a masa ina son saje,sannan Inna A'i ta ta
ɓ
a fa
ɗ
a min ranar farko da na fara ganin Uncle Salem ya cire sage da gemu haka na yi ta kuka ina
ɓ
ata fuska sannan kuma na ƙ
i yarda da shi .
Da sauri na miƙe zan bar wurin yayi saurin kamo tsintsiyar hannuna yana mai cewa “ oyaaa Naf
ɗ
in Uncle kar ki yi fushi zo ki shanyen kununki ki zo mu je na yi miki shopping ” jin ya ambaci shopping yasa na juyo don na san duk cikin shir
ye-shiryen tafiyata ne.
Na sake turo baki a karo na biyu kafin na ce “amma shine ka aske ...” yayi wani murmushi mai sauti yana cewa “ zai fito ai,kin ga kar ki yi fushi da Uncle
ɗ
inki” sai ya zaunar da ni tare da
ɗ
aukar kofin ya ci gaba da bani kunun h
ar na shanye kafin ya ce “ je ki canza kaya ki zo mu wuce”
Da murna na koma
ɗ
akina,sai dai ban canza kayan ba kawai dai na zumbulo dogon hijabi har ƙasa.Ina fitowa Uncle Salem ya matso kusa da ni kafin ya ce “ ki canza kaya Naf ” da mamaki na dube shi,
ko ta ya aka yi ya gane ban canza ba.
Na marairaice fuska na ce “ Please mu tafi kar dare yayi” ya
ɓ
ata rai yana kallon ƙirjina,sai na turo baki na koma
ɗ
aki na je gaban madubi na yi tsaye ashe rabon a yi ne ya kai ni don kuwa ina tsaka da tantance yadda
saka hijabin bai
ɓ
oye ainihin shap
ɗ
in jikina ba sai na hango wata farar mata tana saka min abubuwa a jaka,ta yi zaune daram kan gadona.Na waiga da sauri sai na ga wayam,ina maida dubana kan madubi daidai nan ta bi ta window ta fice.Da mugun sauri na je ba
kin windown sai na gan ta a bu
ɗ
e alhalin kullum a rufe take ban barinta a bu
ɗ
e .
“ Naf wai har yanzu ba ki shirya ba?” na ji muryar Uncle Salem a bayana,na juyo da sauri ina cewa “ yanzu zan shirya“ sai kuma na ga yana bu
ɗ
e ƙofofin hancinsa ya ce “ wa
nnan wai ƙamshin mene ne kamar na Gawa?”
Da ido na tsure shi ina kallo jin ya ambaci gawa,a zuci na ce ‘ kenan dai da gaske ne abin da idona ya gane min? Ko
ɗ
aya daga cikin fatalen da ake cewa sun shigo duniyarmu ne?’
“ Ki yi sauri ina jiran ki a mot
a” ya fa
ɗ
a tare da fita.Kayan atamfa na saka kafin na
ɗ
ora hijabi sama,sai da na je na shaidawa Ammy kafin na fita can tsakar gida inda yake jirana.Bayan motar na shiga na zauna kusa da shi,waya na tarar yana yi sai da ya bai wa direba umarni sannan ya som
a tuƙa mu.
Sai da muka hau titi sosai kafin ya kashe wayar wacce duk rabinta turanci ne da kuma sunayen makaman yaƙi.Na
ɗ
aga kai na dube shi daidai shi ma ya
dubo ni,sai muka ha
ɗ
a ido hannuna ya kamo yana murmushi ban san dalilin da yasa ni ya hana ni n
a dinga riƙe hannunsa amma shi in ya yi niyya haka yake kamo ni.
“ Fa
ɗ
a min me da me kike son saya?” ya tambaye ni yana
ɗ
an matsa hannuna,ko ka
ɗ
an ban jin wani abu na daban saboda a matsayin uba na
ɗ
auke shi.Na langwa
ɓ
ar da kai na ce “ Chocolat da kum
a teddy babba,sai turare da kuma ƙumbar kanti,da lipstick,da uhmm yawwa da sabuwar waya Uncle Please ” na ƙarashe tare da ciro ƙafafuna na yo sama da su tare da
ɗ
ora su kan nasa,ina jin lokacin da ya ja wani numfashi kafin ya ce “zobe fa?” ya tambaye ni sa
boda yadda ya san ina son zobe sai dai duk in ya siya min ban san ya ake yana
ɓ
ata ba.Na saki
ɗ
an murmushi kafin na ce “ na hannunka nake so” sai na soma ƙoƙarin zare wani zobensa mai shegen kyawu da sauri ya dakatar da ni yana mai cewa “ zan saya miki wan
i dai”
Na turo baki na ce “ Uncle wannan zoben dai kamar a tare aka haife ku ko kuma wani
ɗ
anka sam ba ka son rabuwa da shi,ina ga ma ka fi sonsa fiye da Niii!” na
ɗ
an ja ƙarshen ban shirya ba saboda yadda ya kafe ne da rikatatun idonsa masu matuƙar kaifi
.
“ Shi zoben?” ya tambaye ni cikin wata irin murya,ban iya cewa komai ba sai kai da na
ɗ
aga masa alamar eh.A gabana ya cire zoben daga babban yatsansa na tsakiya sai ya kamo hannuna na hagu ya zura min shi a yatsana na biyu,a hankali yayi ta shafar zo
ben yana kallon tsakiyar idona har ya gama daidaita shi,sam tunanin ta ya aka yi zoben da shi kansa a babban yatsa kawai ya tsaya masa amma ni kuma a yatsa na biyu? Wannan tunanin sam bai shigo kwanyata ba sai na shiga yin murna har da wani rungume shi, Un
cle Salem ya ƙara jan ajiyar zuciya a karo na biyu.
Muna isa Mall
ɗ
in ya ja ni izuwa ciki,ana ganinsa da kakin soja duk a soma basa girmansa,
ɗ
aya daga cikin ma'aikatan wurin aka ha
ɗ
a ni da ita muka je tana nuna min kaya masu kyau sam ban san Uncle yayi ta
fiyarsa ba sai da muka sauko ƙasa ina ta baza ido amma ban gansa ba.Idona ya ciko da hawaye har zan tambayar mai kula da shiga da fita sai ga shi ya shigo ,ya sakar min murmushi kafin ya ce “ zo ki za
ɓ
i wayar kafin a kira sallah” ya wani kama hannuna zuwa
inda aka jera wayoyin manyan masu tsada Iphone na
ɗ
auka sai muka zo nan ya biya ku
ɗ
i muka wuce mota yayin da kuma aka kawo min kayana har mota.
Tun a hanya aka soma kiran sallah ga shi wurin da
ɗ
an nisa, Uncle ya ce “ Jabeeru
ɗ
an tsaya mu yi sallah kar
jam'i ya wuce mu,dama da alwala ta” wuri direba ya samu ya parker suka fita suka bar ni nan,ina duba sabuwar wayata na ji an ƙwanƙwasa gilashin mota.Da sauri na dubi wurin sai na ga wata tsohuwa mai ƙusumbi a tsaye tana