Showing 3001 words to 6000 words out of 29631 words

Chapter 2 - THE TWO LIGHTS COMPLETE

yan uku duka maza, tabbas a wannan ranar ƙasar Egypt da Kano ta

girgiza ta Kuma dauki bayani, al'ummar wa'yannan kasa biyun sun girgiza musamman mahassada da azzalumai dake

ɗ

an kare a ko wani kusurwa ta kasashen gida da waje, sun kasa zaune sun kasa tsaye abun duniya duk ya ishe su, ta bangaren Sultan AbdulMalik ko ji

yake tamkar akansu ya fara samun jikanu kasancewar Muhd Kahter shine dansa na fari namiji sauran manyan duka mata ne, hakan yasa yake jinshi tamkar an mishi albishir da gidan aljanna.

Anyi biki da shagulgula masu ƙayatarwa wanda ya tsole idon makiya wan

da a gaskiya ba ƙaramin saka jama'a dayawa yayi ba cikin tsananin tashin hankali da zallan damuwa, ganin tun farko basu kai ko ina ba har Sultan AbdulMalik ya fara dan ƙa masu wasu daga cikin kadarorin sa da suka fi kowanne daraja, tabbas hakan ya tada tar

zoma musamman tsakanin ƴaƴan Sultan Abdul Malik wanda suke ganin tamkar be musu adalci ba wanda daga

ɓ

angaren shi yana sane da ƙananan maganganun da suke yi da tsare tsare da suke ta faman yi hadi da sihiri wanda kai tsaye be dogara da kowa ba se Allah hak

a kazalika da ayoyin Alqur'ani masu daraja yake amfani dasu wajen samarwar kansa kariya shi da jikokin sa.

Haka Lokaci yayi ta tafiya yayin da yake barin zuciyoyi da dama

ɗ

auke da wasu sirrika na tsakanin bawa da Ubangiji sa, yakan iya kasance wa na a

lkairi ne haka kazalika ya kasance na sharri ne, har ilah yau Allah be azirta Sarki Othman Zunnurain da samun ƙaruwa ba wanda a yanzu ya bar wa Allah komai ya kuma meda hankalinsa kan jikansa Muhd Kahter wanda Allah ya jarrabesa da son kasancewa da kakan n

asa wato Sarki Othman Zunnurain a kasar Kano, shi ko kadan rayuwar ƙasar Egypt bata masa yafi son rayuwa a kasar Kano tare da kakanninsa, hakan yasa rabi da kwatan rayuwarsa yazama anan ƙasar wanda a yanzu yake da shekara 35 a duniya, yayin da Sarki Othman

Zunnurain tsufa ya kama shi sannan har ilah yau bashi da Magaji, sede wani tunani da lissafi ya fado masa wanda yake ganin baze iya rikewa ba se ya fitar da shi kuma ba'a kowa ba se Sultan Abdul Malik, ba wani bata lokaci yayi kyakkyawar shiri ya kuma san

ar da Sultan Abdul Malik cewar yana hanya yana kuma so ne ya zayyana masa wani al'amari da yake fatan ze samu kar

ɓ

uwa.

Cikin ikon Allah Sarki Othman Zunnurain ya isa ƙasar Egypt lafiya ya kuma samu kyakkyawar tarba daga ahalin Sultan Abdul Malik, ba ƙar

amin da

ɗ

i yaji ba ya kuma samu wani kwanciyar hankali da tunanin cewa buƙatarsa zata samu guri, hankalinsa be kara kwanciya ba be kuma ƙara yabawa ahalin Sultan Abdul Malik ba se da yaga tilon yarsa yadda ta zama, abun ya matukar bashi nishadi yaji da

ɗ

i ya

kuma yaba da ƙoƙarin su da rikon alƙawarin su.

An samar wa Sarki Othman Zunnurain masauki na alfarma me cike da kayan alatu da more rayuwa, aka kuma cika shi da abinci kala kala, wanka yayi ya kuma huta gajiyarsa kafin yaci abincin wanda yana kaiwa l

oman farko ya jijjiga kai saboda kai tsaye yasan wannan girkin bana kowa bane se na tilon yarsa me sonsa da gaskiya, ya yaba mata ya kuma sa mata albarka, yaci sosai ya koshi ya kuma samu kwanciyar hankali, ta fannin Sultan Abdul Malik kuwa sanda ya tabba

tar da cewa Sarki Othman Zunnurain ya huta kafin ya samu iso gurin sa don su tattauna maganar su wanda shima kai tsaye bakinsa cike yake da zance, bayan dogon musabaha da sukayi ne suka shiga tattaunawa cikin nustuwa da karama irin Nasu na manya ha

ɗ

i da da

ttaku, cikin nutsuwa Sarki Othman Zunnurain yake zayyano abinda ke ransa cikin wani yanayi na son buƙatarsa ta samu kar

ɓ

uwa wanda alokacin da Sultan Abdul Malik ya gama sauraronsa cikin wani yanayi na fara'a da gamsuwa da zancen nashi wanda shima kai tsaye

abinda ke ransa kenan, Murmushin yayi ya ce "Mashallah yabo da godiya sun tabbata ga Allahu Subhanahu wata'ala, haƙiƙa Sarki Othman kazo da babbar magana wanda Ni kaina abinda ke raina kenan, don har bincike Sheik Imam yayi kuma Alhamdulillah akwai alkair

i acikin yin hakan,"

Sujudi Shukhri Sarki Othman Zunnurain yayi ya godewa Allah Subhanahu wata'ala me kowa me komai ya ha

ɗ

i da kirari ga Ubangiji yana kuma gode masa ya dau akalla minti uku kafin ya dago idonshi yayi ja, dafa kafadan shi da Sultan Abd

ul Malik yayi ya ce " Innallah maa sabirin, lalle Allah yana tare da me hakuri, kayi hakuri kayi addu'a a zaune a kwance a tsaye hatta akan tafiya nasan kayi addu'ar Allah ya baka Magaji sede shi Allah yasan abinda ya tsara kuma duk abinda Allah ya tsara

wa bawansa to tabbas hakan alkairi ne agaresa, abu me sauki ne kaso abu se kuma ya kasance sharri ne agareka, yayin da wanda kaƙi kuma se ya zama maka alkairi dawwamamme, tabbas Allah shi ya tsara Wannan lamari mul

ɗ

in namu aiwatar wa ne kawai, inshallah go

be ba jibi ba za'a na

ɗ

a Muhammad Kahter matsayin shugaban ƙabilar Fulani dake ƙasar Kano da yardar Allah,"

Lumshe idonshi kawai Sarki Othman Zunnurain yayi yana jin wani nishadi ha

ɗ

i da kwanciyar hankali ga kuma wani farin ciki daya mamaye ko wani ƙusu

rwa na jikinshi, hamadala yayi ga Ubangijin sa ya kuma gode masa.

Kamar yadda Sultan Abdul Malik ya fada hakan kuwa akayi washegari ba

ɓ

ata lokaci suka nufi ƙasar Kano yayin da akayi ƙakkaurar sanarwar akan za'a na

ɗ

a sabon Sarki, ba ƙaramin tashin han

kali mutane da yawa suka shiga ba baya Wazirin Sarki yafi kowa ru

ɗ

ewa yana tafiya har tuntube yake yi, an hallara a fadar Sarki Othman Zunnurain an kuma yi tsit kowa da abinda yake saƙawa a zuciyarsa, ana hakan aka fara sanarwar cewa za'a na

ɗ

a Muhammad Kah

ter matsayin Sarki wanda tunda aka sanar dashi ya rasa nutsuwarsa shi ko kadan baya kaunar shugabanci shi yasa ma baya son zama a nasu Masarautar yake tafowa nan gurin kakaninsa.

Cikin wani yanayi na rashin amincewa Wazirin Sarki yake magana ya ce "b

a'a san

ɗ

an mace da gadon sarauta ba mu anan ƙasar Hausa ya haramta gazawa ce sannan faduwa ne, hakan na nuni da alamun rashin nasara da jarumta,"

Ba tare da wani shakka ba ko duba da girma da Waziri keda shi na matsayi da kuma shekaru ba Sarkin dogarai

ya zuba mishi dorina cikin

ɓ

aci rai ya ce "hattara

ɗ

an mastiyata ka tsaftace kalmomin ka, bakin rijiya ba gurin wasan yaro bane kamar yadda duk zilamar ƙura da jarumtarsa daya ga zaki yake arcewa, kuma duk girman Giwa aƙasan Zaki yake saboda haka ka kiya

ye harshen ka, "

Waziri be ƙara cewa komai ba se gumi dake keto mishi tako ina ga wani azaba da ke ratsa sassan jikin sa ji yake kamar ƙasusuwansa sunyi daga daga yayin da kanshi yake ƙasa, fuskar shi tayi ja abinka da bafulatani farin fata, ji yake kam

ar yayi ta kwara ihu atakaice so yake wani ko uffan yace dashi ya fashe da kuka, sede ba wanda ya kula da har kansa haka kazalika kowa yasha jinin jikinsa ganin yadda aka bulale Waziri batare da Sarki yace ƙala ba hakan yasa duk suka meda sukan su.

Ciki

n wani yanayi na

ɓ

aci rai Sarkin dogarai wanda yake ji shi a shirye yake ya bada ransa a sarki wato ya sadaukar da rayuwar sa sarki da iyalinsa saboda irin halaccin da taimakon da yayi mishi a rayuwa. Ya ce " akwai wani Ƙaramin alhakin da yake da ja akan a

binda Sarki Allah ƙarawa tsawon rai yafa

ɗ

a ," shiru kake ji tamkar Mala'ikan

ɗ

aukan rai ya kawo wa wannan fadar ziyara, ba tare da

ɓ

ata lokaci ba aka soma gudanar da abinda ya hallara su a wannan wajen yayin da Muhammad Kahter ya kullaci maganar da Waziri

yayi ya

ɓ

ata masa rai ya kuma yi alƙawarin se ya bada kunya zeyi mulki irin wanda ba'a taba yin irin sa ba a tarihin ƙasar Kano gaba-daya, ze shinfida gaskiya ya zama ƙasar ta kawar kowa kuma ze sa ƙafan wando

ɗ

aya da dukkan azzaluman dake cikin Masarauta

r, dama ya sansu daya bayan daya sede shi baya sa kansa a irin wannan lamarin amma yanzu zasu kwashi kashin su a hannunsu.

Anyi na

ɗ

a lafiya yayin da aka ha

ɗ

a da

ɗ

aurin auren Sabon Sarki wanda dama har ansa rana lokaci kawai ake jira yanzu kuwa an daur

a, ya auri Ƴar Sarkin Gombe Gimbiya Fatima , taro yayi taro Abu yayi armashi sede kowa da abinda yake ransa kowa da tuggu na mugunta da yake shirya wa, baya Waziri wanda shima nashi ya ƙare don a gurin aka tsige shi aka kuma na

ɗ

a Sarkin dogarai a matsayin

sa wato Wazirin Sarki, abun ya mugun baƙanta mishi rai ya kuma yi alwashin ganin bayansu gaba daya, kasancewar sa gagarumin matsafi wanda ba kowa bane yasan hakan ya dau alwashin hana Ahalin Sarki Othman Zunnurain zaman lafiya yayi alƙawarin raba kansu na

har abada, ya bada kanshi ga dodon tsafinsu kasancewar wani kungiya yake ciki wanda shi ba ƙaramin maƙami bane dashi saboda jajircewarsa wajen iya aiki yasa suke ji dashi, hakan yasa suka karbi bukatansa na bada kanshi da yayi wato yayi sacrifising kanshi

dan biyan

ɓ

uƙatan shi, acikin ƴaƴan shi ko jikannunsa kai hatta tattaba kunnuwansa za'a samu wanda zai hallaka wannan ahalin a sirrance, haka abun kuwa yake tafiya yayi jinya sosai har rai yayi halinsa yayin da ahalinsa dake cikin masarautar suka ƙullaci S

arki Othman Zunnurain da nashi ahalin da niyan ganin bayansu kota wani hali.

AlhAmdulillah wai duk Zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana sho se yayi, tabbas wai rana bata karya sede uwar

ɗ

iya taji kunya haka kazalika sannu sannu baya hana

isa, Masarautar Sarki Muhd Kahter wanda

aka fi sani da SUHATAJ ya matukar kafuwa sosai irin kafuwar da babu tsaransa din nan, ya sanu, duniya sun shaida wannan masarautar wajen abubuwa da yawa musamman tarihin ta dayake jan hankalin mutane da dama suke so

n kuma kulla alaka da ita, ta fannin arziki ba'a magana haka kazalika fannin Ilimi na Addini da boko wannan ma ba magana saboda komai a tsare yake se hamdala, gaskiya da adalci shi yayi tasiri ko nace yafi komai tasiri a wannan masarautar ha

ɗ

i da rikon add

ini, ko kadan Suhataj baya wasa da addininsa da kuma nemawa kansa da ahalinsa kariya da ayoyi na alƙurani da kuma wasu magani na gargajiya wanda addini be haramta amfani dasu ba sauƙar Alqur'ani, da sauran wasu abubuwan sosai ake yi ba kakkautawa, ya fahim

ci mutane da yawa ba Allah aransu sun

ɗ

auki shirka abunyinsu shi yasa ya dage da nemawa kansa da

ɗ

an Yarima Abdallah Ibn Muhd Kahter kariyar Ubangiji, wanda shi kuma yaron sam be damu da irin wa'yannan abun ba shi a cewar sa tsafi ƙarya ne shi be damu da i

rin abubuwan nan ba ya dauke su Fairy tales, sosai Mahaifin nashi ke ƙoƙarin jawo hankalinsa amma shi sede kawai ya bishi da to.

Tafiya yakai tafiya anyi nisa shekaru sun ja Suhataj Muhd Kahter ya tsufa yana buƙatar yin murabus daga fannin ƴan uwa shi

kuwa Muhd habibullah wanda rai yayi halinsa Allah ya ƙarbi abunsa shi ya gaji mahaifinsu wanda shima yanzu babu shi, Sultan Muhd habibullah ya bar yaya biyu mace da namiji SULTAN da SUBAIHAT, se matarshi Maryama Binta Idriss Imam, a wannan lokaci Sultan

be kai ya gaji sarauta ba hakan yasa dan uwan mahaifin nasa ya gaji sarautar wato Muhd Mubaraq, wanda shima Allah ya azirtasa da mata da kuma yara guda biyu mata NUBIA da NASHWA se matarshi Madina Binta Abdulaziz, wanda a yanzu shimaze yi murabus za'a na

ɗ

a

Sultan a matsayin MALIK na ƙasar Egypt, yayin da yake auren yar baffan nashi wato Nubia Binta Muhd Mubaraq, yayin da Yarima Abdallah ya auri NASHWA yar uwar Nubia.

AlhAmdulillah wannan ahali guda biyu masu banbancin al'ada da ƙabila se ƙara wanzuwa suk

e yi ana ƙara sanin su a fadin duniya saboda ba ƙaramin contribution suke bayarwa ba wajen ci gaban al'umma, Suhataj Abdallah ya ƙara aure ya auri Saudat Fuad Hashim wata yar president ne a wannan lokacin yayin da Nashwa kuwa ta haifi jarumai yan ukunta ma

su daukan hankali masu kuma dauke da tarin baiwa wanda ke tsole idon maƙiya tun basu kai ko ina ina ba.

Sun ci gaba da tafiyar da rayuwar su da da

ɗ

i ba da

ɗ

i yayin da bayan rasuwar tsohon Suhataj komai ya canja musamman game da kafi na masautar, kamar

yadda kuka sani Suhataj Abdallah ko kadan shi be yadda da tsafi ba, be kuma yadda ana yinta ba, hakan ya haifar da matsaloli da dama, kasancewar bata gari sun soma kai hari a masarautar, sede hakan be canja wassu abubuwan ba kamar tarihi da yanayi na ƙarfi

n iko na sabuwar masarautar, haka suka cigaba da rayuwa har yara suka girma suka kai munzalin aure, kamar yadda kuka sani Suhataj Abdallah yana auren Nashwa Binta Muhd Mubaraq, yayin da Allah ya azirtasu da yara maza uku wato yan uku, inda suka ci suna Oth

man Zunnurain, Muhd habibullah, Muhammad Kahter, se kuma Saudat Fuad Hashim wanda Allah ya azirtasu da samun

ɗ

iya mace sunanta Sareena, Masha'allah shine abin fa

ɗ

i yara duk sun taso sun kuma samu kyakkyawar tarbiyya daga iyayensu mata zan iya ce muku kowa

da irin tarbiyyar da tasa mahaifiyar sa basa.



Yaran Gimbiya Nashwa wanda muka fi sani Da FULANI a yanzu, ta matukar yin ƙoƙari wajen tarbiyantar da yaranta da kuma daura su bisa tafarki na Musulunci, bugu da ƙari ko kadan batayi kuskuren barin su giy

an Sarauta ya bugar dasu ba bare har su kai ga yin sa'insa da juna, suna mutunta juna da kuma girmama juna ga kuma girmama na gaba dasu, duk da kowa da irin nasa halin da kuma salon rayuwa, Yarima Othman Zunnurain wanda shi ya kasance babba wato Hassan ya

kasance mutum ne shi da baya

ɓ

oye abinda ke zuciyar sa mutum ne shi wanda inze yi to zeyi in baze yiba to baze yiba, shi baya Abu dan ya burge mutane se dan ya burge kansa kawai, shi mutum da maganar mutane be dame sa ba muddin zaka yi abayansa ba'a gabans

a ba to da kai da banza duk daya ne a gurinsa ko ince babu, inko wani ya kawo mishi gulma tofa ze sa a kira masa me maganar se ka maimaita abinda ka fada a gabansa, baya ga haka yana da adalci sosai sannan bashi da son kai ko kadan don a shirye yake daya s

adaukar da kansa ga ahalinsa, sannan ya kasance mutum ne biyayya ga iyayensa sede kome zeyi se yayi nazari da bincike, ma'ana inhar abinda suka saka shi be sabawa addinin musulunci ba ko ya kasance me cutarwa a gareshi shi dasu ba to tabbas ze aikata abind

a suka umarce shi da yayi.

Se Yarima Muhd habibullah wanda ake masa take da damo Sarkin hakuri, mutum ne shi ne tsananin hakuri da kawaici,kunya hadi da fulaku, bugu da ƙari mutum ne shi me tsananin biyayya ga iyayen shi ga tausayin na ƙasa dashi .

Na ƙarshe shine Yarima Muhd Kahter, wato

ɗ

an ƙaramin su babban su shalelen Suhataj da Fulani zan iya cewa ko Sareena da take yar auta Suhataj baya ji da ita kamar yadda yake ji da shi sede kusan duk

ɗ

an da aka fi so tofa yafi iya shegantaka, atakaice

shi mutum ne da baya son reni ki kadan akan yiwa wassu ƙirarai da da kudin ka naka murmushin ka na kowa, tofa shi nashi kirarin yasha banban da wannan doon shi kudin shi na kowa ne murmushin shi kuwa se me Sa'a ko wanda ya wanke idonshi da ruwan zinare, se

de duk da haka besa ya wulaƙanta na ƙasa dashi ba se kyautata musu da yake yi, sede ko kadan shi baya hada hanya da marassa gaskiya dan ƙo kafi bishiyar dabino tsayi da shekaru baze hana shi

ɗ

aukan mataki akan ka ba.

Se kuma Sarauniya Sareena wanda ta

samu bahagon tarbiyya daga gurin nata mahaifiyar, ataƙaice ita ita ko kadan bata ganin darajan na ƙasa da ita ta dauki duniyar ta da zafi ta kuma

ɗ

an kwara ranta akan sarautar da ba samu zata yi ba, sede ta ku

ɗ

iri aniyar ko zata yi yawo daga se fatari a

ƙ

asar Kano tofa se ta juya wannan masarautar.

END OF PAGE 2

Story and writing by

Queen Mahirah (Word smith)

Account number 9168962485

Shaidar biya ta wanan layin 09168962485

500 ne kacal ba yawa

🥰

Ki biya se ki cigaba da karatun ki cik

in salama

THE TWO LIGHT

RIKICIN GIDAN SARAUTA(THE GAME OF THRONE

🤴👸🔥

)

BOOK 2

Story and writing by

Queen Mahirah (Word smith)

.

PAID BOOK



3

Ɓ

angaren Malik Sultan kuwa

Allah ya azirtasa da yara uku na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login