Showing 6001 words to 9000 words out of 233169 words

Chapter 3 - DAN MACE COMPLETED

/>
ku ne kad'ai duniyata kuma dangina,bayan ku ban san kowa ba,,ciki har da mahaifina,ban san wane ne shi ba,yaya yake.? A ina yake.? Duk ban sani ba,ban san komai game da shi ba,even his name ban sani ba,and u know ina son sanin abubuwa da dama game da rayu

wata,but ban san mene ne dalilin da yasa kuka kasa sanar dani ba,,shin ina mahaifina yake ne..?? Ina son sanin wane ne shi.? Mene ne ya faru dake bayan samuwata.? Jikina ya jima yana sanar dani akwai damuwa a cikin rayuwarmu,,ina son sanin komai.."

Sh

iru ya d'anyi yana sakin numfashi,jikinsa duk ya sake yin sanyi,a hankali ya kai hannunsa ya goge hawayen da suka gangaro masa yaci gaba "All i wish a rayuwata shi ne na ganki kinyi rayuwa kamar kowa ne bil'adam mai y'anci,, sai dai ban san yaya zanyi ba k

o ta yaya ne hakan zai kasance.. Duk irin sonyayyar da nake miki a matsayin mahaifiyata,na san ban isa na cire miki wannan larurar ba,,ina tsananin sonki,soyayya irin wacce baki bazai iya fad'a ba,ina miki so irin na tsakanin d'a da mahaifiya,ina sonki da

dukkan zuciyata,,ana ahabbuk Mamah.. Ahabbuk.! Ahabbuk-thtiir.!"

Kansa ya sauke a hankali zuwa saman jikinta yana ci gaba da sauke hawayen damuwa da ajiyar zuciya masu nauyi,Annie dake tsaye bakin k'ofa tun d'azun ta gama jin kalaman da yake furtawa

ita kanta bata san yaushe hawaye suka fara gangaro mata ba da sauri ta juya ta bar wajen tana ci gaba da hawaye masu d'umi da k'una,kitchen ta shige ta kulle kanta a nan tayi kuka har ta godewa Allah,bayan wucewar wasu mintuna still tana zaune ta buga tagu

mi take tunanin anya ta yiwa Nuraz d'in adalci da taja baki tayi shiru har tsayin wannan lokacin.? Shin tsayin wane lokaci ne zasu d'auka tana b'oye masa asalinsa.? A yanzun shekarunsa da hankalinsa ya kai ace yasan wane ne shi.? To amma ta ina zata fara s

anar masa.? Shiru tayi tana sake zurfafa tunani har zuwa tsayin wani lokaci kafin ta yanke shawarar abunda take ganin shi ne yafi mata dai².

Yana kwance a jikinta bayan tafiyar Annie Dr Waseem ya shigo d'akin da sallama bcos lokacin daya kamata ya

dubata yayi,har ya k'araso kusa da shi bai san ya shigo ba sai da ya tab'a shi

"Hello handsome..!"

A d'an tsorace Nuraz ya d'ago duk da ya fahimci muryar waye,cikin dabara ya goge idonsa sannan ya waiwayo ya mik'awa Dr Waseem hannu bayan y

a k'irk'iro murmushi

"Welcome Dr."

Suka yi musabaha Dr Waseem yana sake tambayarsa

"How are u,,nd how was the patient.?"



"Alhamdulillah." Yace yana sake kallonta



"Allah ya k'ara mata lafiya" Dr Waseem ya fad'a

yana maida hankalinsa kanta,Nuraz ya amsa da "Ameen" d'akin yayi shiru,Dr Waseem ya wuce kusa da ita ya fara shirin duba jikin nata,,Annie ta sake dawowa a karo na biyu bayan sun gaisa da Dr Waseem,ba tare da ta kalli Nuraz dake mak'ale da hannun mahaifiya

rsa ba tace

"Habibiiy! Zo maza ina son ganinka yanzun ka kyale Dr yayi aikinsa.!"

Tana fad'a bata jira ba ta juya ta bar wajen,kamar bazai tashi ba ya fara binta da kallo har ta fita kafin ya mik'e ya bita yana jin zuciyarsa duk babu dad'i,a pa

rlor ya tarar da ita zaune ta dafe chin d'inta da duka hannayenta biyu,tana ganin fitowarsa da sauri ta nuna masa kusa sa ita tace

"Sit" babu musu ya nemi guri ya zauna yana d'an kallonta but k'irjinsa yana ji kamar ana kwala masa abu ta ciki,nan da na

n ya fara ji yayi masa wani irin nauyi,idanunsa ya runtse yana d'ora hannunsa a dai² saitin zuciyarsa slowly ya shiga karanta

"Allaahumma inniiy a'uzhu bika minal-hammi walhazan,wal'ajazi walkasal,walbukhli waljubni,wa'dhala'id-dayni wa'ghalabatir-rija

al."

A hankali² yana ta maimaitawa har ya fara jin k'irjinsa yana sanyi,damuwar da yake tare da ita ta fara yayewa,ci gaba yayi da maimaitawa har tsayin lokacin da yaji ya dawowa nutsuwarsa tamkar dama can wani abu bai faru da shi ba sannan ya dakata y

ana sake fuskantar Annie da itama shi d'in take kallo tun d'azun ganin yayi shiru da idanunsa a rufe.....





#Posting wannan karon yana wattpad da yardar Allah,but idan na ga babu voting zan ajiye na koma whatsapp & facebook kamar last novel.





#Vote,

#Comment &

#Share pls.

#Real Smasher.



💠💠💠💠💠

*©®2020.*

*'DAN MACE..*

(T

ʜ

ᴇ



ᴘ

ꜱ

ʏ

ᴄ

ʜɪ

ᴀᴛ

ʀɪ

ꜱ

ᴛ

)..

💥



*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*

https://my.w.tt/29u2S26SG2

Alkhai

rin Allah ya kai miki uwa ta gari *Hajiya Maryam Alhassan (Oum Feedy & I)* ina mik'o gaisuwa,da addu'ar fatan alkhairi gare ki,Ubangiji ya raya zuri'ah,ya albarkaci rayuwarsu.

P

ᴀ

ɢ

ᴇ

3.

#T

ʜ

ᴇ

B

ᴇ

ɢɪɴɴɪɴɢ

Duk abunda yake idanunta na kansa,duk da

niyyarta da farko data kira shi,ta shirya yi masa nasiha ne akan damuwar da yake sawa kansa cikin kwanakin,but ganin da tayi masa a yanzun da maganganun da yake yi lokacin data shiga

d'akin,yasa taji duk guiwoyinta sunyi sanyin da har tana ji a ranta baza

ta iya sake b'oye masa komai dan gane da rayuwarsa ba,,sun d'auki lokaci zaune shiru babu wanda yayi magana tun zamansu ko wannensu da tunanin da yake zuciyarsa,fitowar Dr Waseem yana tambayar Annie abincin da aka dafa mata ya taimaka wajen dawo dasu ciki

n hankulansu,jikin Annie a sanyaye ta kira maidservant d'insu Bareerah dake taimakonta ta b'angaren kulawa da gidan ta kawo masa ya karb'a ya wuce,hannun Nuraz ta rik'o cikin nata a hankali bayan sun kasance su biyun tana sauke nauyayyun ajiyar zuciya tace



"Samahniiy ya ibniiy..!"

A d'an dake ya kalleta yace "Annie what's going wrong kike neman yafiya ta.?? Ni mene ne kika yi min,a iya sani na tun dana taso ni baki tab'a min komai ba.. Daya wuce kyautatawa."

Hannunta tayi saurin d'orawa

saman lips d'insa tana girgiza masa kai tace

"Skutiiy habibiiy.. Kada kace komai.!"



"Annie.! Stop this drama,ni na san baki yimin komai bafa."



"A'a habibiiy kada kace haka,,tabbas a gareka na kasance mai laifi,kai ne dai d

a baka san na aikata hakan ba kake k'ok'arin nuna min bani da laifi a gurinka,,but idan har baka yafe min ba tabbas ban san yaya zanji a rayuwata ba,ban san ina zan kai girman hak'k'in ka akaina ba."

Ajiyar zuciya yayi ya sake damk'e hannunta a nasa

fuskarsa bayyane da damuwa yace

"Annie.! Dan Allah ki bari,nifa babu abunda kika yimin,,idan ma akwai ni ina so ki k'addara a ranki tun kafin kiyi na yafe miki,bcos baki cancanta da zama a sahun wad'anda za'a ga laifinsu ba idan sunyi KUSKURE..I kn

ew KUSKURE ne ba don kina sane ba.."

Sai da tayi murmushin samun sukuni ta shafo gefen fuskarsa sannan tace

"Shukhraan'kthiir habibiiy,,sai dai sam fa ba yadda kake tunani bane.."



"Uhn!" Yace yana sake zuba idanunsa akanta,kallon

sa itama ta sake yi tace

"Je kayi breakfast tukun kazo,akwai maganganun da nake son muyi da kai a yau idan rabb ya nufa."



"Really Annie.!?" Tace "Haka nake tunani idan rabb ya ara mana lokaci!" A hankali ya jirkita kansa gefe sannan yace

"Okay" ya tashi ya nufi dining,Annie nata kallonsa har ya fara bud'e warmers dake gurin,shi yayi serving kansa,bayan ya zauna ci kawai yake amma sam baza ka tab'a gane yanayin dake kan fuskarsa ba,kad'an yaci ya ture plate d'in da mug daya had'a tea,ya ta

so ya dawo kusa da ita yana fad'in

"Annie na gama.."



"Uhn!" Tace,,haka nan tunda ta amsa ya tsinci kansa da sake nutsuwa idanunsa a k'asa yana ta addu'ar Allah yasa ko mene ne zata fad'a masa a dai² lokacin yazo masa da sauk'i kuma ya

kasance alkhairi,muryar Annie ta katse masa tunani data kirashi

"Habibiiy.!" A sanyaye da irin muryar data kira shi yace "Na'am Annie",jim tayi kafin tace

"I want to tell u something,,though i know it's extremely ugly.. But ina fatan baza ka k'a

rawa kanka damuwa ba bayan kaji abunda zan fad'a."

Gabansa yaji ya fad'i da sauri ya d'ago ya kalleta yana marairaicewa "Annie.! Please idan dai zai tada mana hankali kawai ki barshi ba sai kin fad'a ba,ni banga amfanin ace a yanayin da muke kuma mu

na sake sharing wani damuwar ba,kawai a hak'ura ba sai kin fad'a ba,dama haka Allah ya nufa.."



"Ya zama dole ka sani habibiiy,,wajibi na ne na fad'a maka,ko dama ace na b'oye maka a yanzun,dole ne wata rana nan gaba kad'an kai da kanka ka sake

tambaya,wannan dalilin yasa tun kafin zuwan lokacin na yanke shawaran sanar da kai,ni na huta da dako kaima ka huta tunani da damun rayuwarka akan son binciko gaskiya."



"Amma Annie.!"



"Kayi shiru ka saurari abunda zan fad'a,idan

na gama kaji koma mene ne daga nan sai ka yanke hukunci,, amma kada kace na bari,a yau na riga nayi niyyar sanar da kai ne bisa umarnin zuciyata ba tare da ka tambayeni ba."

Ajiyar zuciya yayi yace "Shi kenan Annie,tunda har kin yanke hukunci,Allah y

asa hakan ya zama mafi alkhairi a gare mu."

Shiru gurin ya d'auka for a while kafin Annie ta sauke dogon ajiyar zuciya tace

"HABIBIIY.! Nasan ka jima kana bibiyata da son sanin wane ne asalin mahaifinka.. A ina yake.? Wanene shi.?"

Kai ya

gyad'a yace "Ehh! Annie but u already told me he was pass away"

Kai ta fara gyad'awa a hankali cikin wani yanayin damuwa muryarta tana rawa tace

"Tabbas na fad'a maka haka a bayan saboda wani dalili nawa,duk da na san this is not true habibiiy

.."

Da mugun mamaki yace "But Annie kefa kika ce haka.?" Kai ta gyad'a tace "I knew a baya na fad'a maka cewa ya mutu ba don komai ba sai don ina son ka nutsu ka cire shi a cikin rayuwarka kamar yadda ya yanke ka daga jikinsa,,but a yanzun kuma ina sak

e shaida maka he's alive.."

Wani gagarumin gumi ne ya fara yanko masa,yana ci gaba da kallon Annie da mugun mamaki yace

"Annie! Kin san abunda kika fad'a.?"

Kai ta gyad'a tace "yeah! I knew,kuma ina cikin nutsuwa ta ne nake sanar da kai m

ahaifinka da kake damuwa da son sanin wane ne shi yana raye..!"



Kamar bai yarda da abunda kunnensa yake jiyo masa ba yace "Annie.! Yana raye fa..!?" Tace "K'warai yana raye bai mutu ba,abunda nace kenan..!"

Zuba mata idanu yayi ko k'iftawa

ya kasa yi,mamaki kwance akan fuskarsa na abunda yaji,haka nan duk sai ya kasa motsawa but ya tsinci kansa dai da cewa

"Annie.! Idan har yana raye kamar yadda kika fad'a a ina yake..?? Kuma wane ne shi.!?"



"Zan sanar da kai yanzun da i

zinin Allah.. Saboda haka ka saurare ni kawai.."

Nutsuwarsa gaba d'aya ya sake tattarawa ya mik'a ta gurinta duk da yana cikin rud'ani,a hankali ta kalleshi sannan ta fara da cewa

"Mahaifinka ya kasance wani hamshak'i,wanda zan iya ce maka duniy

a gaba d'aya ta san da zamansa,shahararsa matsayi da yake da su kad'ai yasa shi mallakar lasisin shiga duk k'asar da yaso a lokacin da ya so.. Duk da na tabbatar ba lallai ne duk wanda zan fad'awa ya yarda da abunda zan fad'a ba kai tsaye,but wannan itace

gaskiyar kuma ita nake shirin zan bayyana,,,mutum ne shi shahararre da duniya ta aminta da shi,haka nan shahararsa ba iya nahiyarmu kad'ai ta tsaya ba,sai da ta had'a da zagaye duniya,al'ummah ta sanshi ta yarda da ingancinsa,duka wannan maganar da nake yi

ina yinta ne akan mutum d'aya tilo,bak'ar fata jinsinmu da ya fito daga Africa,,,ba kowa nake nufi ba face mahaifin da yayi silar zuwanka duniya wato *SUPERIOR."*

A mamakance a kuma razane ya d'ago yake kallonta bayan mik'ewa tsaye zubur da yayi,,b

akinsa da duk wata gab'ar dake jikinsa tana aiki banda kyarma babu abunda yake sakamakon abunda yaji ta ambata yace

"Annie is he my Dad..!? Shi ya haifeni kike son cewa..??"

Tace "K'warai wannan mutumin shi ne asalin mahaifinka."

Wani murmushi

ya saki mai ciwo yana kad'a kai alamun abunda yaji bazai tab'a faruwa ba yace

"Impossible! Annie ace kamar wannan mutumin shi ne Daddy na,,kin san wane ne shi da kike dangatashi da ni..?? Abeg.! Annie stop this drama,mutumin fa da kike magana baya zam

a k'asar nan,shi da ahalinsa sun jima basa nan,idan ya shigo ma within k'ananun hours yake barinta,me zai had'a mu da shi.? And how zai zama mahaifina.? Annie! Ba sai kinyi haka ne zan fahimci asalina ba,yau idan kika ce min bani da mahaifi wollahi Annie i

will accept my fate a duk yadda yazo,zanyi hak'uri cos haka ubangijina yaso na kasance,Annie even a bite wollahi ban tab'a tsammanin irin wannan furucin daga gare ki ba,but for the sake of Allah nake rok'on ki,ki rufa mana asiri dan girman Allah Annie mu

zauna a matsayinmu please..! Na amince na yarda da k'addara,please and please ki bar maganar nan ma kawai ya wuce.. Na hak'ura da sanin ko ma waye mahaifin nawa.."

Hannayensa ya had'e cikin rashin sanin abunda zai sake fad'a ya runtse idanunsa,Annie da

ke ta kallonsa da tausayi ganin bai yarda ba tace

"Habibiiy..! Did i tell u such things a baya can..??"

Yayi saurin girgiza kai alamun A'a,tace "why yanzun kake neman k'aryata ni..?"

Idanu ya zaro yasa hannunsa d'aya ya dafe bakinsa d'ayan kuma y

a d'ora shi akansa yace "Annie! Ta ina na isa nace kinyi k'arya.?"

Had'e rai tayi tace "gashi yanzun mun fara."

Da sauri ya rik'e ta yana marairaicewa yace "I'm really sorry Annie idan har abunda nayi yasa kinyi tunanin na k'aryata maganar

ki,ki gafarce ni wollahi bazan sake ba.."

Duk sai ya koma abun tausayi cikin k'ank'anin lokaci jikinsa ya d'auki wani lalataccen rawar tsoro,a hankali tana d'auke kanta gefe tace "It's okay!"

Kallonta yayi yana langab'ar da kai yace "kin hak'ur

a.?"

Ta gyad'a masa kai kawai,shi dai Allah ya sani tun da yaji sunan mutumin da tunaninsa yake kawo masa ko a mafarki hanya bata isa ta had'o su ba bare a gaske ace suna da wata alak'a ya shiga tashin hankali,d'agowa yayi da kansa dake sunkuye a karo

na sau babu adadi yana jinjina kalmar mahaifinsa ya kalleta fuskarsa har lokacin da alamun rashin yarda da abunda yaji,tambaya yake shirin watso mata kafin ya kai ga yin hakan tayi saurin tarar numfashinsa

"Ina so ka saurare ni a yanzun,,cos na riga

na san abunda kake shirin tambaya ta,tun kafin muzo wannan gab'ar na shirya domin sanar da kai wannan muhimmin sirrin,,dan haka idan kaji wani abu daya shige maka duhu bayan na gama kana iya tambayata,ni kuma zan sanar da kai asalin yadda aka yi hakan ya

faru da yardar Allah.."

Ajiyar zuciya yayi ba tare da yace komai ba yana ta kallonta,idanunsa,zuciya da jikinsa duk jinsu yake kamar sun daina motsawa sosai ga wani irin tsoron da yake jin yana taso masa a rai,Annie da ta kula da halin firgicin da ya

shiga ta dafa kafad'arsa tana fad'in

"Kada ka damu habibiiy,ko mai zai zama dai² da yardar Allah,,sannan ni a yanzun abu d'aya kawai nake da buk'ata daga gare ka,shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login