Showing 9001 words to 12000 words out of 233169 words

Chapter 4 - DAN MACE COMPLETED

ne ina so kayi min *ALK'AWARI* bayan kaji labarinka daga gare ni,ina so ya zama ba

zaka tab'a sawa ranka damuwa akan abunda ya riga ya wuce ba.."

Kai ya girgiza mata a hankali sai dai bai ce mata komai ba,kamar mai tunani itama Annie tana kallonsa ta ci gaba da fad'in...

"Abunda ya faru..!"

*FLASHBACK...*

*(The be

ginning of the story).*

*"RAFEEK ZAKAR LABBO* shi ne cikakke kuma asalin sunan mahaifinka,wato *CHIEF ECONOMIST* kamar yadda kaji na ambata

a farko ne,sai dai kamar yadda na sani ne kuma kaima ka sani a yanzun al'ummah gaba d'aya tafi kiransa da

*SUPERIOR* kuma shima wannan sunan yake amsawa,wannan suna ne da zan iya ce maka ya samo shi ne tun bayan da d'aukakar sa ta bayyanar da shi a duniyar shahararru,,asalin iyayen Rafeek ba y'an garin Kano bane,zama da yanayin canjin gurin aiki irin na ma'ai

katan force ya kawo iyayensa garin Kano,Allah ya had'a mu mak'otaka da su,tun kafin su haifeshi har zuwa bayan haihuwarsa muke zaune tare da su cikin unguwa d'aya,asalisu sun kasance Fulani ne su da suka fito daga jihar *YOLA*,,Mahaifin Rafeek Alhaji Zakar

Allah yayi masa rufin asiri da dukiya dai² shi wanda duk wani bawa da yake neman rufin asiri a gurin ubangiji ya samu kamar wannan a iya cewa ya more,kasancewar iyayen Rafeek tun a wancan lokacin suna da arzik'in su dai² su,mahaifinsa Alhaji Zakar ya kasa

nce mutumin k'warai daya rik'e muk'amai da dama a cikin hukumar su ta *CUSTOMS* kafin Allah ya kaishi matsayin *ASSISTANT COMPTROLLER* a b'angaren d'amarar tasu,daga nan ne kuma bai sake yin gaba ba saboda ajiye aiki da yayi (ma'ana yayi retire).

Duk

wanda ya san su yasan mutane ne su na gari masu mutunci da ake zaune da su lafiya,tun farkon zuwansu kafin a samu mahaifinka,babu wanda zai zo yau yace sun tab'a yin ko da musayar yawu,haka ko bayan haihuwar Rafeek zuwa tasowarsa babu abunda ya canja,,a d'

abi'u irin na yarinta ko wane yaro zaka ga da irin abunda tunaninsa da ra'ayinsa yafi karkata akai,ko nace muradinsa da idan ya girma zai so ya zama,,a wancan zamanin lokacin da shekarun Rafeek suka yi dai² da wannan stage bayan tasowarsa cikin hukuncin ub

angiji,ya kasance gwani wanda yake da burin ganin ya nemi na kansa a k'ok'arinsa na ya wadata kansa ta inda ko ya girma ba zaiyi kukan rashi ba,,sab'anin sauran yara sa'anninsa da zaka tarar dole sai sunje gida suna y'ar murya suke samun biyan buk'atunsu,,

sau da yawa a wannan lokacin tun bashi da shi,da y'an kud'in makarantarsa da yake ragewa yake siyo y'an k'ananun kaya da basu fi karfin aljihunsa ba a shaguna yana siyarwa a k'ofar gidansu,yau da gobe aka ce a gurin ubangiji tafi k'arfin wasa,akan wannan h

ali da mahaifinka ya d'auka mutane suka fara yi masa kallon shirmen yarinta yasa shi yin hakan,yayin da shi a gare shi bil'hak'k'i ya d'auki al'amarinsa,lokaci² idan ya samu yan kud'ad'ensa ba tare da yayi shawara da kowa ba zai je ya siya yan abubuwan da

suke da rangwamen kud'i,kama daga kan sweet,chewing gum,biscuit da sauransu,ba don komai ba sai dan ya tallafi kansa ta hanyar neman halal d'insa and ba tare kuma da ya jira anyi masa a gida ba,and ba dan ya rasa gata ko idan yace ayi masa a gida za'a gaga

ra yi masa ba,sai dan yana so ne ace wata rana shima ya dogara da kansa,,,tun a farkon lokacin daya fara wannan sana'a a lokacin da jama'a suke kan yi masa dariya,sam bai d'auki hakan wani abu ba,ya maida hankali sosai wajen ci gaba da siya yana siyarwa,ha

d'e da nunawa mutanen dake masa dariya,dariyarsu bai dame shi ba,duk da wasu a ciki sukan yi masa izgili ta hanyar tsallake shagunan unguwa zuwa gurinsa,to idan sun zo d'in ma dai mai makon su jira ya

basu,su da kansu suke d'auka suna masa wasa da kayan sa

na'a,idan yayi magana suci gaba da dariya suna tsokanarsa da fad'in maganganu marasa dad'i,abun ya fara damunsa a rai ya fara tunanin daina sana'ar tunda ita take kawo masa wulak'anci,sai kuma yayi tunanin shin idan ya bari d'in gurin waye zai dunga samun

kud'in b'atarwa da biyawa kansa k'ananun buk'atu na yau da kullum.?? Wannan tunani yayi masa jagoranci wajen yin watsi da al'amuran mutane yaci gaba da bin shawarar zuciyarsa,and ya d'ora daga inda ya tsaya,,a lokaci guda yana sana'arsa kuma yana ci gaba d

a karatunsa,kullum cikin ranakun markaranta da safe zaije makaranta,da yamma kuma zai zauna gurin sana'ar sa,duk da tun farkon fara wannan d'abi'a tasa mahaifansa sunyi iya yinsu akan ya bari tunda komai na rayuwa akwai a gida amma sai yace shifa sam su ky

ale shi yayi,to ganin ba dainawar zai yi ba yasa suma kansu suka hak'ura suka zuba masa idanu tare da binsa da fatan alkhairi,,,bayan wani lokaci da fara sana'ar tasa Allah ya sake bud'a masa,lokacin da Alhaji zakar ya fahimci da gaske yake son yin sana'ar

ya bud'e masa shop a nan jikin gidan,raba d'aya nasara ta kwankwaso masa k'ofa daga zube kaya saman tabarma ya koma babban container,yayi farin ciki sosai lokacin da yayi gamo da canjin da ya samu daga ubangiji,,akan haka rayuwarsa ta fara kullum cikin sa

mun bud'i daga ubangiji akan harkar kasuwancin sa."

Dan kallon Nuraz Annie tayi da yake ta kallonta tace "wannan duka ina tsakuro maka labarin abunda ya riga ya faru ne a tak'aice,kafin mu gangara kan asalin alak'ar data had'a mahaifanka. "

A hank

ali gyad'a mata kai alamun ya gane,Annie taci gaba

"Asalin alak'ar mu da juna,,,mun kasance tsakaninmu da mahaifinka neighbours ne mu kamar yadda na fad'a tun farko,mun taso cikin unguwa d'aya a cikin line guda,gidajen mu basu da wani nisa tsakani,ha

salima sun kasance suna kallon juna,but mun samu bambancin tsagi,ina nufin mu muna wannan gefen suma gidan su mahaifinka suna d'ayan hannun,kasancewar mu a haka na tsayin shekaru yasa babu yadda za'ayi ace bamu san juna ba,duk wanda yake cikin line mu ko d

a jiya ya zo mun san juna mu da shi,mun kasance mu da kowane gida kamar y'an uwan juna.

Gidan mu a gaba d'aya line ya kasance shi ne gidana farko da yafi kowanne tara mutane,bisa wannan dalilin yasa a kullum ba'a rabo da yin fad'a da y'an gidanmu,saboda y

awanmu da jaye²n fad'a irin namu yasa muka yi fice a unguwar,dalili yawanmu kuwa shi ne babanmu yayi aure²,wannan yasa adadin y'ay'ansa muka kai ashirin maza da mata,to kuma dai da yake ba'a samu macen data zauna ba a cikin matan daya aura sai mahaifiyarmu

,wacce ta zauna tare da shi tsayin lokacin har Allah ya karb'i rayuwar ta tana gidan,bayan mutuwarta sai wata bazawara daya sake aura,idan aka cire wad'annan matan biyu a tarihin gidan mu da aure²n babanmu sune kad'ai matan da suka zauna sama da shekara gu

da,duk wacce ta zo bata wuce haka,,sannan a yadda muke rayuwa gidan mu ya kasance yana da matsaloli,amma abu na farko daya nakasa gidanmu shi ne rashin had'in kai sai rashin wadataccen muhalli,wannan sune suka

bawa gidan tallafin da kullum a kowace safiya

yake kamar gidan haya,da zaran gari ya waye za'a fara hayaniya da fad'ace-fad'ace wannan ya tsokani wancan,kullum haka ake yini abu guda,idan har kaji baki ya huta tofa sai dai idan dare ne ya zagayo kowa ya kwanta hak'ark'arinsa,a nan d'inma gurin kwanciy

ar bawai ina nufin za'a yi shi lafiya bane,dole sai an yada hali kafin baccin,wani lokaci idan ta d'auro cikin baccin ma sai an daki juna,,rayuwar gidanmu ta kasance rayuwa ce ake yinta kowa yana ganin hanjin kowa,zaman lafiya yayi mana k'aranci,kowa tak'a

marsa shi kad'ai Babarsa ta haifa,kasancewar duk matan da suka shigo daga haihuwa d'aya ne zaman yake k'in dad'i wata ma bata haihuwar sai kaga an tafi,tafiyar da babu biko bare kome,,kowa shi kad'ai ne bashi da d'an uwa duka a cikin gidan,idan aka cire mu

ni da mahaifiyarka da muka kasance ciki d'aya kuma baba d'aya,komai namu mun kasance tare muke yinsa tun tasowar mu duk da tsakani na da ita akwai nisan shekaru biyar (5),bata tab'a raina ni ba,tana bani girma na a matsayin yayarta,yadda ta d'auke ni take

girmama ni a matsayina na y'ar uwarta da muka fito ciki d'aya,yana b'atawa sauran y'an uwanmu rai,a ganinsu ta yaya zamu kasance masu had'in kai al'halin duka gidan kawuna suna a rarrabe.? And duk wanda zai neme mu da fad'a bama kulawa daga ni har Hauwa,w

annan hali ne wanda mahaifiyarmu ta d'ora mu akai,duk abunda zasu ce idan zasu kwana suna magana bama tanka musu,,kafin Allah ya yiwa mahaifiyarmu rasuwa tayi iya kokarin da zata iya na ganin ta had'a kawunanmu gaba d'aya,ganin lamarin ya gagareta ta hak'u

ra ta zubawa sarautar Allah ido,Innar mu mace ce mai hak'uri da kauda kai,ta rasu lokacin Hauwa tana da shekaru uku a duniya,,to da yake a gidanmu bamu samu wadataccen muhalli ba,kasancewar duka d'akuna guda hud'u ne,babanmu d'akinsa daban,matar babanmu ma

haka,sai ya zama mu mata gaba d'aya muna d'aki guda,sauran d'akin kuma na y'an uwanmu ne maza,,a duka tashinmu halin babanmu guda biyu yake burgeni kuma nake matuk'ar so,duk da nasan da yawa mutane sukan yi mamaki da wannan halin nasa,amma agare mu ba abu

n mamaki bane,duk da kasancewar muna da yawa a gidanmu hakan ko kad'an baisa ya gagara ciyar damu ba,a kullum rana yadda ake d'ora tukunya a sauke sau uku a ko wane gida da suke jin suna da rufin asiri,muma haka nan ake yinsa a gidanmu,safe,rana da dare du

k lokacin da mutum ya b'ukaci abinci zai same shi,,amma batun girmamawa ga juna ko soyayya irin ta y'an uwantaka wannan ne babu shi,haka ko a b'angaren karatu ma dai² gwargwado baba yana iyakar k'ok'arin sa wajen ganin mun wadata da ilimi,sai dai mu d'in a

wannan fannin ba kowa ne hankalinsa ke kan karatun ba,duk wanda aka ce yau mahaifiyarsa bata cikin gidan mahaifinsa dole ne rayuwarsa ta samu nakasa dole ne kuma kaga bambanci da ratuwar wanda yake tare da tasa mahaifiyar,mahaifiya ita ce tushen tarbiyya

ga ko wane d'a,shin mu da bamu da iyaye wane ne zai ce muyi ko mu bari.? Duk wacce baba zai auro wani lokaci sharrin yau da gobe ke sawa ya rabu da ita,dan har ga Allah babanmu mutum ne da yake da saurin yarda da magana,sannan duk duniya idan har kana son

ganin b'acin ransa ka tab'a masa y'ay'a,a wannan

lokacin na tabbatar duk yadda kuke da shi lallai za kuyi hannun riga,,ganin abunda muke so shi muke yi yasa itama matar gidan da aka auro take zaune da mu bata tab'a hana mu,idan ana hayaniya bata tab'a cewa

mu bari,hasalima sai dai ta kad'e zaninta tayi wucewarta d'aki ta barmu nan,idan muna iyawa mu kashe juna ko mu hak'ura wannan duka ruwanmu ne,wad'annan dalilan yasa gaba d'aya kowa abunda ransa ya so yake yi,makaranta zuwanta sai wanda yaga dama ko yasa

kansa,duk safiya baba zai sa mu shirya mu fita saboda yana ganin hakan shine babban gatan da zai mana a rayuwa,zuwa kuma ya rage na mai niyya,iidan ka ji baka iyawa kana fita daga gida zaka iya wucewa gararinka,idan ka daidaici lokacin tashi ka biyo ayari

a dawo tare,,ruwanka ne kuma rayuwarka ce.

Lokacin da baba ya fara harkar bin y'an siyasa,sai ya zama babu ruwansa da wani binciken muna zuwa ko bama zuwa duk da a bayama ba damuwarsa kenan ba,shi dai yasan duk k'arshen term zai biya school fees

na gaba d'ayan mu,wad'anda suke zuwa da wad'anda basa zuwa,damuwarsa shi ne a tattara masa shaidar biya na gaba d'ayan mu a bashi,shin mutumin da aka bawa shaida kamar haka ta yaya ne ma zai san wanda bai je ba.?

Life goes on,,bayan tsayin shekaru da m

uka shafe still rayuwar gidanmu yana a yadda yake babu wani sauyi,kullum abu biyu ke yawo a tsakani dad'i/kishiyarsa da rashin watar zaman lafiya,,cikin hukuncin ubangiji a dai² lokacin dana kammala secondary school Allah ya kawo min mijin aure daga cikin

y'ay'an abokan Baba,,tunda aka tsayar da ranar aurena nake cikin damuwar barin gida,a zahiri kuma ba wai ina damuwa bane saboda zan tafi,sai dan a wannan lokacin duka damuwata ita ce Hauwa,tunani na a kullum yadda zan tafi na barta,saboda ban san yaya rayu

warta zata kasance ba bayan bana gida,na san matar babanmu bata kula da kowa a baya ba da yake cikin gidan bare yanzun nayi tunanin za'a fara,tak'amarta kuma shi ne bata haifa ba,babu wanda zata raina sannan baba ya nuna fifikon soyayyar mu akanta,shi yasa

tunda ta shigo gidan bata tab'a cewa muyi wannan mai kyau ne,ko mu bar wannan bashi da kyau,tunda aka tsaida ranar aurena hankalina ya kasa kwanciya,,but a wannan lokacin Hauwa tayi abunda ni ya kamata ace nayi,kasancewarta mai k'ananun shekaru a kaina,ka

mata yayi ace ni zan kwantar mata da hankali,amma abun mamakin shi ne ita da ake ganin bata da cikakken hankali ita take kwantarmin da hankalina,a duk lokacin da zata ganni cikin damuwa takanyi k'ok'arin taga ta sanya murmushi akan fuskata,har Allah ya kaw

o lokacin aurena,aka yi biki lafiya aka kai ni d'akina,a daren daya zama daren farko na rabuwarmu da Hauwa,ya kasance ni ina kukan rabuwa da ita a karon farko tun bayan tasowar mu,itama tana kukan shiga sabuwar rayuwar da babu ni a cikinta,a hakan ina kall

o y'an gidanmu suka wuce suka barni,naji babu dad'i sosai duk da ba zaman lafiya muke yi ba,amma ganinsu kad'ai a tare da ni nasan zai bani kwanciyar hankali,,tsakanin gidan mu da gidan da nake aure babu nisa,but mu a gare mu a wannan lokaci gani muke kama

r an

gama nisanta mu da juna,bayan y'an rakiyar amarya sun watse ango ya shigo d'akin amarya.."

Shiru Annie tayi tana sauke numfashi da kallon Nuraz sannan taci gaba

"A bisa tsarin addini komai angona yayi min,na tabbata mijina na sona haka nima

ina sonsa,kasancewar mutum ne shi daya dace da burin kowace y'a mace,,bayan komai ya lafa,duk wata hidima an k'are,aurenmu ya samu wasu kwanaki haka nan sai nayi nufin tuntub'ar babanmu akan maganar ko zai bari Hauwa ta dawo gurina dan a yadda na kula da i

ta cikin lokacin tana cikin damuwa da takurawar y'an gidanmu,amma kuma idan na tambaye ta duk lokacin da ta zo gurina bata iya sanar dani sai dai tace min komai lafiya,ni dai haka nan duk lokacin da zata fad'amin haka nakan ji ban gamsu ba,shi yasa lokaci

guda nayi nufin samun babanmu da batun,mijina ya bani goyon bayan na karb'o ta ta dawo hannuna,cike da wannan k'arfin guiwa da sa hannunsa muka je tare har gaban Baba da maganar,duk da a d'ar² muke bcos bamu sani ba zai amince ya bamu ita ko bazai amince m

ana ba mu dai gamu nan a probability....











#Share.

#Real Smasher.

💠💠💠💠💠

*©®2020.*



*'DAN MACE..*

(T

ʜ

ᴇ



ᴘ

ꜱ

ʏ

ᴄ

ʜɪ

ᴀᴛ

ʀɪ

ꜱ

ᴛ

)..

💥





*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*

http

s://my.w.tt/29u2S26SG2

P

ᴀ

ɢ

ᴇ

4.

#S

ᴏᴜ

ʀ

ᴄᴇ





Mun samu Baba a gida,bayan mun shiga mun gaisa da y'an gidanmu,muka samu Baba da batun,lokacin da muka gabatar da buk'atar mu ta son tafiya da Hauwa amma sai da amincewarsa,bai nuna mana koma

i ba yace muje zai yi tunani,idan zai iya bamu ita to,,ni dai tunda naji ya ce haka jikina yayi sanyi,dan Baba mutum ne shi kaifi d'aya,idan zai yanke hukunci da k'arfin guiwarsa yake zartarwa a take,haka ma idan bazai yi ba a take yake yankewa,but matuk'a

r kaga

yana abu kamar baya so,tabbas there's something behind,idan anyi sa'a kana da saurin fahimta ka gano dalilinsa na k'in amsa maka kai tsaye yace bazai yi ba ko akasin haka,jiki babu k'wari muka yi sallama da Baba muka tafi,,kwana biyu tsakani muka ji

shiru and there's nothing in return akan maganar,mijina ya sake tuntub'ata ko zan sake tunawa Baba maganar irin ace ko mantawa yayi.? Gudun kada nace wani abu shima ya ga laifi na,tunda ni dai na fahimci Baba bazai bamu ita ba,na amsa da "Toh" amma a zahi

rin gaskiya nasan Baba bai amince zai bari Hauwa ta bar gida ba,,lokacin da na je gida mun gaisa da Baba kafin nayi masa maganar ya haumin fad'an akan wane dalili zan d'auko masa mijina nace muna so ya bamu Hauwa.? Tunaninmu bazai iya kula da ita bane ko y

aya muke tsammani.? Ni dai nayi shiru na kasa cewa komai,k'arshe bayan ya gama fad'an yace "kuma kinji na fad'a miki ko da wasa bana son a sake min irin wannan titsiyen,ni ba lusarin uba bane da zan d'auki y'ata na bada ita zuwa wani gida al'halin nasan ba

aure nayi mata ba,duk hak'k'in dake kaina dai² gwargwado ina rok'on Allah ya bani ikon kamanta saukewa,daga yau bana son a k'ara min maganar za'a tafi da ita wani gida,ban amince da barinta gidan nan ba" ni dai tunda yake fad'an kaina ke k'asa kuma har ya

gama banyi ko tari ba,sai dana tabbatar ya gama na bashi hak'uri,nuna min yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login