Showing 21001 words to 24000 words out of 233169 words
sake gyad'a kai tace "Toh Hajiya,in sha Allah i won't"
Shiru parlor'n ya d'auka ts
ayin wani lokaci babu wanda ya sake magana,Rafeek sai bin iyayensa da Hauwa yake da kallo,so yake yayi magana amma ganin sun basar da shi a gurin ga tsoron hukuncin da zasu zartar sai ya hana shi tofa albarkacin bakinsan,bayan shafe tsayin lokaci ya fita y
a bar musu parlor'n,babu wanda ya tanka masa ko ya damu da shi har ya fice,a gefen Hauwa itama yadda ta bishi da kallo kad'ai ya isa sawa ayi saurin gane ma'anar kallonta,duk da ya ta'allak'a ne bisa yanayi mai wahalar fassara,siririn tsakin da yayi escapi
ng a bakinta tayi sauri ta rik'e shi bata bari kowa yaji sound d'in zuwansa ba,dukansu alhini suke da jimami,Hajiya mamakinta ya kasa b'oyewa dan har dare bata daina tunanin al'amarin ba.
A b'angaren Alhaji zakar da Maimunatu ma dai haka abun yake,kow
a tunanin dalilin da zaisa Rafeek ya musanta cikin a matsayin nasa yake,daren ranar gaba d'ayan ahalin gidan basu iya samun bacci cikin nutsuwa ba,washe gari da safe Rafeek ya shigo apartment d'in,a parlor ya iske su cikin shirin tafiya skul sun ci uban fa
raren kaya,kad'an ya kalleta ya d'auke ido soundly ya saki tsakin da yasa gaba d'aya suka kalleshi,not minded ya tsuguna yana sauke kai k'asa cike da ladabi
"Hajiya ina kwana.!?" Idan ta amsa ku k'addara parlor'n da item's dake cikinsa sun motsa ta s
hare shi a gurin dan kansa ya gaji ya zauna,har suka kammala breakfast suka yi niyyar tafiya skul babu wanda ya gaisheshi tsakanin Maimunatu da Hauwa,suna kammalawa suka yiwa Hajiya sallama sai sun dawo,ta bisu da addu'ar fatan alkhairi sannan suka fice su
ka barshi nan yana fama da latsa waya,,fitarsa babu jimawa ya mayar da wayarsa ya sake kallon Hajiya,so yake yayi magana amma duka ya rasa inda zai fara kamawa,fuskarta tamke kamar
kokon safe and not to look at his direction tace "Me ya kawo ka nan ne.!?"
In'ina ya fara yana sake sunkuyar da kansa k'asa,kallonsa tayi ta tab'e baki "Ka ga bana ciki da iskanci Rafeek,baka san tun jiyan da haushinka a zuciyata na kwanta ba ko.!?"
Bai d'ago ba yace "Ki yi hak'uri Hajiya"
Wani kallo ta mas
a tace "Nayi hak'uri.!?"
Ya gyad'a mata kai,gyara zama tayi tace "To ubana na yi,,yanzun yaya aka yi ne kazo min nan ka sani gaba.!?"
A sanyaye yace "Na zo na yi muku sallama ne ina son komawa.."
Wani kallo ta bishi da shi,kusan m
intuna uku tsakani kafin tace "Allah ya tsare to" daga haka ta yunk'ura zata tashi,saurin d'agowa yayi yace "Hajiya.!" Kallonsa tayi ya ji ya kasa maganar,data tambaya shi "yaya aka yi",still kasa magana yayi sai cewa yayi "babu komai ",tab'e baki tayi tac
e "toh tunda babu ka tashi ka wuce kada ka rasa flight ko..!?" Jikinsa a sanyaye amma idan ya tuno abunda ya faru jiyan sai yaji k'irjinsa ya cika fal da bak'in kishi,Hajiya da taga ya kasa tashi ya tafi wisely ta fara yi masa nasiha,yadda jikinsa ya nuna
ya karb'i nasiharta yasa ta bishi da addu'ar fatan alkhairi,sallama ya sake yi da ita sannan ya d'auki hanyar komawa inda ya fito,,duk abunda ya faru a ranar cikin nasihohin Hajiya da tayi masa akan cikin jikin Hauwa,bayan ta k'ara da fad'in ita dai ko da
ace wani abu bai shiga tsakaninsu da Hauwa ba to ta amince d'an da Hauwa zata haifa tana so ya tsaya a matsayin mahaifin cikin,duk maganganunta da nasiharta akan cikin da kula da Hauwa tayi masa shi,abunda ya janyo jikinsa ya mutu kuwa ba komai bane face n
asihar data masa akan marin Maimunatu da yayi da tunatar da shi lahira,but bayan tafiyarsa tun kafin ya isa k'asar Ghana al'amura duka suka warware bisa khud'ubar da shaid'an yayi masa akan lallai ya raba Hauwa da gidansu tun kafin ta raba shi da gidan.
Tunda ya koma yake tunanin yadda zaiyi ya raba ta da gidan amma ya kasa,daya tuna ai akwai waya ya kirata ya sanar da ita sak'on sa babu b'ata lokaci ya aika mata da sak'on kira,lokacin da Hauwa taga kiransa tayi tunanin kamar yadda Hajiya ta sanar mus
u ne bayan sun dawo daga skul,shi yasa ta d'auka da fara'a sosai a fuskarta tayi masa sallama,ta samu ya amsa sallamar amma gaisuwa sai ya basar da ita kamar bai jiba,daurewa tayi ta sake gaishe shi still yayi banza bai amsata ba,hakan yasa ta sha jikin ji
kinta akan lallai ba kiran lafiya yayi mata ba,abunda bai tab'a yi ba tunda suka
yi aure ranar shi yayi,ina nufin kiran sunanta kai tsaye,amsawa tayi babu damuwar komai a ranta dan ita kanta a lokacin ta gama shiryawa duk wulak'ancin da zai mata idan taji
baza ta iya ba tofa tabbas za tayi tafiyarta dan bazata tsaya auren wanda yake zarginta ba,maganarsa ta dawo da ita hayyacinta
"Hauwa! Shin gidan da kike zaune na wane ne.!?"
Kai tsaye Hauwa tace "gidan surukaina.." Girgiza kai yayi kamar tana ka
llonsa yace "ba wannan na tambayeki ba"
"Me ka tambaya ne.!?"
Yace "cewa nayi gidan da kike na wane ne.!?" Ta sake maimaitawa kamar farko,cije lips d'insa yayi na k'asa ya sake tambaya,gane abunda yake nufi a wannan karon yasa ta bashi
amsa da "gidan iyayen mijin da yake zargin naci amanarsa" duk da yaji amsar data bashi kamar yadda ya buk'ata hakan bai hana shi jin fad'uwar gaba ba,but ya dake yace "good.! Kenan ba gidan ku bane ko.!?"
Tace "Me zai hana ya zama gidanmu tunda in
a da iyaye a ciki da y'ar uwa.!?"
Murmushi yayi yace "amma ta dalilin waye kika same su.!?"
Tace "Ubangiji ya azurta ni da samunsu ba tare da wayo ko dabara ta ba.!"
Yace "Bayansu kina da iyaye ko A'a.!?"
Tace "ina da su,kuma kaima ka san ina da su" murmushi yayi mai kyau yace "good.!³" yana clapping hannunsa,jim tayi tana saurarensa gabanta sai tsananta fad'uwa yake ta daure tace "me kake nufi ne wai.!?"
Sai da yayi ajiyar zuciya a hankali
yace "abunda nake nufi kike son sani.!?"
Ta gyad'a kai tace "Uhn" k'wafa yayi sannan yayi shiru na wani lokaci continuously yace "tabbas nasan kina da iyaye,to amma mene ne dalilin da ya hanaki tafiya gidanku ki raini cikin ki a can!?"
"Kafi kowa sanin dalilin da yasa ban tafi ba ai tunda kai ka ajiye ni a nan,and u know ba zaman kaina nake ba."
"Okay! Zaman waye kike yi.!?"
Tace "Zamanka nake" yace "Really.!?" Tace "Sure" murmushi ya saki soundly followed by "Idan ha
r zamana kike zan iya cewa iska na wahalar da mai kayan kara.! Ke me ya kai ki jiran abunda bazai amfani rayuwarki ba.?"
Abunda yake bakinta ta had'iye da kyar tayi yak'e da fad'in "kamar yaya.!?" Yace "ina nufin.!"
Sai kuma ya yi shiru bai k
'arasa ba,sun d'an b'ata lokaci shiru kafin yaci gaba da magana cikin kaushin murya
"Ina son kiyi min wani abu guda d'aya,and not to seek favour in u" Ya fad'a da wani irin murya,cewa tayi "ina saurarenka fad'i kawai" yace "ina so ki bar gidan mu",gaba
nta na fad'uwa tace "ko mene ne dalilin ka na yin hakan.!?" Yace "saboda ke da kanki kin bawa kanki amsa nan inda kike gidanmu ne ba naku ba,so ina son ki tattara ba tare da kin fad'awa kowa ba ki bar gidan" murmushin k'arfin hali tayi tace "shi kenan zan
tafi in sha Allah kamar yadda ka buk'ata,amma da farko ka fara fad'amin" cikin hayaniya yace "me zan fad'a miki ne.!?" Tace "saurin mene ne kake yi haka.!? Ai zan fad'a maka"
Yace "Ina saurarenki"
"Da farko ina son jin bisa shawarar waye k
ake son na tafi.!?" Yace "bisa ra'ayin kaina", tace "Da kyau.! To amma ka sanar da su Hajiya ka ce na tafi.!?"
Kasak'e yayi yana saurarenta yace "kamar yaya.!?"
"Kamar dai yadda kaji na fad'a" yace "dole sai na fad'a musu za ki tafi.!?" Tace
"Sure sai sun sani,saboda kaika kawo ni gurinsu ka ga idan zan tafi ma bisa umarninka ne,kuma dole sai sun san zan tafi"
Yace "really.!?" Tace "sure" girgiza kansa yayi kad'an yace "but yanzun mene ne kike ganin zaisa ki tafi ba tare da sun sani
ba.!?" Bata yi tunanin wani abu ba tayi masa shiru,murmusawa ya sake yi cike da mugunta yace "kina ganin idan misali yanzun nace na yanke alak'a da ke,zaki sanar musu.!?" Danne tsoron daya cika mata zuciya tayi tace "sure",tsaki yayi saboda ba haka yaso ya
ji daga bakinta ba,yana shirin yin magana ko me ya tuna kuma ya fasa,can ya sake daurewa yace "Hauwa!" Ta amsa "Na'am" yace "Ni RAFEEK ZAKAR LABBO a yau ina son shaida miki na yanke alak'a ta dake" cikin tsananin tashin hankali tace "me kake nufi.!?" Yace
"abunda kika ji" tace "kana nufin ka rabu da ni.!?" Yace "sure",, "ka rabu da ni.!?" Ya sake maimaitawa "na sake ki nace"
Murmushin takaici tayi tace "Rafeek! Ya kamata kayi tunani kafin ka yanke hukunci,, idan ba ka tunanin baya akwai gaba fa,ka tsay
a ka yi nazari."
Tsaki yayi yace "kinga Malama ni ban tambayeki wannan ba,abunda kawai nace shi ne.. Na sake ki.! Idan kin samu wanda zai iya aurenki yayi k'ok'arin zama dake da halinki kina iya yin aure.."
Yana gama fad'a ya katse kiran,,wani ir
in nauyi taji k'irjinta yayi mata,ta toshe bakinta tana girgiza kai,har lokacin gani take maganar sakin da Rafeek yayi mata kamar mafarki take tana farkawa zata ga a bacci hakan ya faru,da yake a zaune take cikin d'akinsa data mayar nata tun zuwanta sai ta
mik'e tsaye ta fara zagaye d'akin cikin tsananin firgici da damuwa,lokaci guda maganarsa ta dawo mata
_"Na sake ki.! Idan kin samu wanda zai iya aurenki yayi k'ok'arin zama dake da halinki kina iya yin aure.."_
Zuciyarta ta harba lokaci guda ba
yan gano ma'anar abunda kalamansa suka k'unsa,a slow ta tsaya inda take tana dafe kanta da take jin kamar ana kwad'a mata guduma,cikin hayaniya take tambayar kanta kamar yana gurin
"Yanzun Rafeek na cancanci irin wannan hukuncin daga gareka.!? Me n
ayi maka da zaka min haka.!?,kana nufin ni karya ce bani da daraja.!?"
Shiru tayi kamar wata zararriya ta shiga girgiza kai
"A'a.! A'a.!! A'a.!!! Wollahi ba haka bane,ni ba karya bace,ina da mutunci na,kuma kaima ka sani,kai shaida ne akan mutunci
na..!"
Shiru ta sake yi tana kallon guri guda fuskarta d'auke da murmushin takaici tace
"Me yasa zaka min haka Rafeek.!? Me yasa zaka yi zargin bani da kamun kai al'halin kafi kowa sani idan ina da shi ko bani da shi.!? Me yasa zaka ce ka sak
e ni.!? Me yasa zaka ce cikina ba naka bane...!?"
Wani irin shiru ta sake yi jikinta yana kyarma ta k'urawa guri d'aya ido kamar mai tunani,haka tai ta juya words d'in a cikin kanta da zuciyarta da ta cika fal da tsoro,kamar sabon kamun hauka take ma
gana cikin hayaniya tana sake juya zancen,dai² ta kawo kan maganar cikin ta fizgo wayarta ta fara dialing number sa,rai a b'ace Rafeek ya d'auka yana daka mata tsawa yace....
#No comments,no voting,,,there's no posting till further notice.
.. Time to posting strike.
🚴🏻
♀
#Share.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*
*'DAN MACE..*
(T
ʜ
ᴇ
ᴘ
ꜱ
ʏ
ᴄ
ʜɪ
ᴀᴛ
ʀɪ
ꜱ
ᴛ
)..
💥
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2
P
ᴀ
ɢ
ᴇ
7.
#
B
ᴇᴄᴏᴍ
ɪɴɢ
ꜱ
ᴏ
ɴ
ᴏ
ғ
ᴀ
ᴡᴏᴍᴀ
ɴ
"Da Allah mene zaki kirani kuma.!? Ni yanzun mene ne zanyi miki.? Muna da wata alak'a ne kuma.!?"
Ta daure tace "Rafeek ina son muyi maganar cikin ka dake jikina."
A zafafe ya tari numfashinta "Hey! Hey.!! M
alama kada ki sake wannan KUSKUREN.!"
Tace "Rafeek wollahi ko ka yarda ko kada ka yarda ni banyi KUSKURE ba,kaine dai kake son yin KUSKURE ta hanyar nunawa duniya d'anka shege ne,,wollahi thumma billahi cikin nan ba shi da uban daya wuce ka kaf dun
iyar nan,ni na tabbatar cikin nan ubangiji ya nufemu da samun shi,amma kaine silar samar da shi,ina baka shawara kayi duk iya binciken da kake jin za ka iya yi,na tabbatar kai da kanka sai ka yarda bashi da uban daya wuce kai"
"Kada ki sake dan
ganta cikinki da ni."
A zafafe kamar yadda yayi tace "wollahi sai na fad'a naka ne"
Girgiza kai yayi kamar tana gabansa yace "ta yaya ya zama nawa.!? Daga yin abu sau d'aya shi ne sai ya zama nawa.!? Da Allah malama kada ki b'atawa kanki
lokaci,,ni Rafeek kike son lik'awa cikin wani ko.!? To wallahil'aziiym bazan karb'a ba,kuma har abadan duniya bana karb'arsa,can ki nema masa uban daya dace amma ni nafi k'arfin kiyi min sharri,,idan kina iyawa kici gaba da rainonsa har ranar zuwansa duni
ya,and ina fatan idan ya zo wata rana ko da zai tambaye ki maifinsa kiyi k'ok'arin sanar da shi gaskiya kada ki b'oye,cos duk ranar daya san gaskiya zai tsaneki a matsayinki na wacce ta kawo shi duniya,zaiji haushin kin b'oye masa gaskiya,bayan zunubin sam
ar da shi ta mummunar hanya,zai tsaneki bayan ya gano kina sane kika yi sanadin zuwansa ta k'azantacciyar hanya,,kafin duk wannan lokacin ya zo ina so kiyi tunani,sannan kiyi kokarin tara hujjojin da zaki fuskanci d'anki da su,ta hanyar bashi gamsassun ams
oshin da zasu wanke laifinki a gare shi,,kai tsaye ba sai kin yi masa k'arya ba a duk lokacin da ya b'ukaci jin asalinsa ina so kice masa shi shege ne bashi da baba..!"
"RAFEEK.!" Ta kirashi a zafafe,dariya yayi yace "mene ne.!? Wai kinji haus
hi.?''
"Kada ka sake sheganta d'anka,ka tuna kai kayi silar samuwarsa"
"Da Allah dakata Malama,ta ina na samar da shi ne.!?"
"Rafeek.! Kada ka yanke hukunci kan abunda baka da ilimi akansa,d'anka ne na sunnah."
"Ni ba d'ana bane,ki daina danganta ni da shi,,ke kanki kin san ba ni ne mahaifinsa ba.!"
"RAFEEK dank'a ne.!"
"Hauwa! Kada ki sake cewa nawa ne.!"
"Sai na fad'a dank'a.!"
Dariya yayi mai ciwo yace "Kina s
on lik'a min d'an da bashi da uba ko.!? Saboda kin maida ni mahaukaci na karb'i d'an da ban san *ASALINSA* ba.!?,k'arya ne wollahi bazan tab'a karb'a ba"
"Shi kenan Rafeek, idan har baka sonsa ni ina son abuna.."
"Dama dole ne ki s
o shi,tunda a yanzun ke kanki baki idan za'a tambaye ki ubansa baki san takaimaman wane ne zaki ce shi ne mahaifinsa ba,kinga kenan kece uwarsa kuma kece ubansa,dole ya zame miki ki so shi."
Sosai kalmar tayi mata muni da ciwo ta runtse idanunta jin
kirjinta yayi mata nauyi tace "shi kenan Rafeek na gode,,amma ina so ka san wani abu guda"
Yace "fad'i kafin lokaci ya k'ure miki"
Daurewa tayi duk da ciwon da take ji yana taso mata,a hankali ta dafe k'asan mararta muryarta da rauni tace "I
na so ko da zuwa gaba,a lokacin daka gane gaskiya,ka tabbatar kana da alak'a da d'ana,,ka yi min alk'awarin baza ka tab'a kusantar inda muke ba,sannan ba za ka kira Yarona naka ba.!"
Dariya yayi yace "wannan shi yafi komai sauk'i"
"Na gode
" tace muryarta a raunane tana fad'a ta katse wayar had'e