Showing 15001 words to 18000 words out of 233169 words

Chapter 6 - DAN MACE COMPLETED

ba tsayin lokaci yana nazarin maganarta,Hajiya ta sake yin amfani da wannan damar ta dunga kawo masa hujjoji da dalilan da take ganin idan har sun taimaki Hauwa zasu samu lada har gurin

Allah,,hankalin hajiya bai kwanta ba,sai data tabbatar Alhaj

i ya amince zai nemawa Rafeek auren Hauwa.. Wannan shi ne mafarin lamari,ina nufin mafarin matsalolin rayuwar Hauwa da mu kanmu.....

#Share.

#Real Smasher.

💠💠💠💠💠

*©®2020.*

*'DAN MACE..*



(T

ʜ

ᴇ



ᴘ

ꜱ

ʏ

ᴄ

ʜɪ

ᴀᴛ

ʀɪ

ꜱ

ᴛ

)..

💥



*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*

https://my.w.tt/29u2S26SG2

*The gift u gave me was more than perfect in each and every way..Thank u so much for it Cweet Mammah (Manab). I will always preserve and keep it with

me forever.*

P

ᴀ

ɢ

ᴇ

5.

#T

ᴜ

ʀ

ᴍᴏ

ɪʟ

Bayan Alhaji zakar ya gama yanke hukunci,shawaran samun Baba yayi a washe garin ranar da nufin ya sanar da shi ya amince da maganar,but da nufin nemawa Rafeek auren Hauwa zai je kamar yadda Babanmu ya buk'ata,ka

mar wancan lokacin suka had'u a k'ofar gida,Alhaji zakar ya rattabawa Baba buk'atarsa,a nan Baba ya fututtuke fuska gani yake kamar cin fuska ya kawo Alhaji zakar,bud'ar bakin Baba a take yace

"Haba Alhaji,,kada ka mai dani wani shawaragi mana,banda ka

i ko k'aramin yaro na koma ai kasan babu yadda za'ayi na yarda da cewa kamar kai zaka amince ka nemawa dank'a auren y'ar wajena.. Sai dai kuma ban sani ba ko ka zo ne ka zolaye ni kaji an samu wanda ya taya,amma ba kai da kanka kace ka zo nemawa dank'a aur

enta ba,,ina laifinma kace mai gadin ka ko y'an aiken gidanka..? Wannan kam ina iya yarda kuma na amincewa da kai."

Alhaji zakar yayi dariya da yake ya san iya gaskiyarsa ya fad'a yace "ko kad'an malam Baba ban zo da nufin na zolaye ka ba,,alal hak'ik'

a kamar yadda ka ji na fad'a maka babu batun

wasa a magana ta,wannan itace gaskiyar zuciyata kuma ita na fad'a maka,ko ka yarda ko kada ka yarda ni na san ban zo da nufin na yaudare ka ko na cutar da kai ba,kada ka manta tun farko kai ka bani dama kuma nag

a na yaba da tarbiyyar yarinyar ka,ina da buk'atar amfani da wannan damar daka bani,shi yasa na zo gare ka da batun,idan ka amince kamar yadda ka fad'a ranar jumu'ah idan Allah ya kaimu sai a d'aura auren,dama kace a cikin satin nan ka shirya aurar da ita

ko ba haka ba.??"

Baba yace "haka nace,,amma batun kana neman aurenta wa dank'a na fasa,ni da kaina zan nemo wanda ya dace da ita na aura masa."

Alhaji ya sake yin dariya yana kallon Baba daya fututtuke fuska yace "amma malam Baba kasan ba haka muk

a yi da kai ba tun farko ko.?"

Baba yace "to yaya muka yi..?? Ina ce nina baka dama tun farkon.. Yanzun kuma naga hakan bai minba na canja.!?"

Alhaji yace "haka ne kai ka bada dama,nima da naga ina buk'ata nazo da k'ok'on barata,kayi hak'u

ri ka yarda,kaga zumuncinmu ya sake k'arfi ko ba haka ba.?"

Baba dai yaga kamar Alhaji zakar na neman maida lamarin wasa duk da shi har zuciyarsa yake maganar,tsam ya tashi ya bar masa gurin ba tare da ya samu damar ce masa komai ba,Alhaji har lokacin

yana dariya saboda yadda Baba yayi fushi akan y'ar maganar shima ya tashi ya bar wajen,sai dai wannan karon ko daya tashi maimakon ya shiga gida,kai tsaye ya nufi gidan mai unguwa dan yafi son ace manyan unguwa su shiga cikin lamarin yarinyar ko da Baba ba

zai bawa Rafeek aurenta kamar yadda ya fad'a ba,yana so aja hankalinsa ya fasa aurar da ita a wannan lokacin,,anyi sa'a Alhaji ya samu mai unguwa a gida,suka yi magana ta fahimta,ba'a d'auki lokaci mai tsayi ba mai unguwa ya aika d'an sak'o ya kira masa B

aba,yaje aka sake maimaita zancen kamar yadda tun farko suka yi tsakaninsu shi da Alhaji zakar a gaban mai unguwa da y'an majalisar mai unguwa,jama'a suka shaida yadda akayi,mai unguwa ya bawa Baba hak'uri akan ya janye batun aurar da Hauwa a matsayinta na

karamar yarinya saboda matsalolin da ake fuskanta game da aurar da k'ananun yara,sai dai fa Baba ya kafe yace shi bai ga dalilin da zai sa ya canja ra'ayi ba,duk yadda za'ayi anyi akan ya sakko amma ya kafe kamar lalataccen k'arfe,bisa dole mai unguwa da

sauran yan majalisarsa suka hak'ura suka kyale shi bcos y'arsa ce kuma shi yake da iko da abarsa,yana da damar yayi duk abunda yaga yayi masa dai²,a nan ko da suka ga an ciza an busa bai amince ba Alhaji zakar ya sake gabato da buk'atarsa ta son amincewar

Baba da batun nemawa Rafeek auren Hauwa'r idan ya amince,Baba yaga da gaske Alhaji zakar yake babu batun wasa,nan take ya amince,mai unguwa suka shiga cikin maganar aka tsaida ranar jumu'ah ta zama ranar d'aurin auren Hauwa da Rafeek.

Anyi addu'o'i n

a neman sanyawar albarka kafin daga nan taron ya tashi,magulmata kuma suka samu na yi,aka tafi aka fara yad'a cewar Baba ya ga kud'i shi yasa ya amince ya bada

y'arsa ga d'an Alhaji zakar ba tare da tunanin abunda zai faru gaba ba,,cikin k'ank'anin lokaci

gari ya d'auka,duk inda ka zaga maganar auren ake,lungu da sak'o duk inda mutum baya tunani taje har ta wuce,,ranar jumu'ah bayan an sakko daga masallaci aka d'aura auren *Rafeek Zakar Labbo* da amaryarsa *Hauwa Baba Muhammad*,abisa mafi ingancin sadaki,d'

aurin auren daya samu halartar manyan mutane daga b'angaren Alhaji zakar da Baba cikin har da manyan y'an siyasa na k'asa daya shiga ya fita ya gayyato duk da yake bai jima da fad'awa harkar bin y'an siyasar ba (kuji fa baba da k'arfin hali,mutumin da bai

da wadataccen matsuguni shi ne ya fad'a siyasa).

A dai² lokacin da ake ta hidimar d'aurin aure,a b'angaren ango babu wanda ya sanar da shi badak'alar da ake a gidansu,bcos baya garin yana Zaria da yake a can yake karatu (A.B.U),kuma lokacin bai jima da

komawa ba,wannan dalilin yasa Alhaji yace kada a sanar masa shi da kansa zai masa bayanin komai idan an gama hidimar,da yake ma duka ba a lokacin zasu tare ba,yafi so sai Hauwa sun kammala secondary zuwa lokacin ta k'ara girma sai ayi biki,shima Rafeek zu

wa lokacin ya kammala degree d'insa na farko,akan haka Alhaji zakar ya bar batun but yace duk lokacin da Rafeek yazo hutu zai had'a su duka ya sanar da su matsayinsu ga juna,,bayan an yi d'aurin aure a ranar at that night Alhaji yasa aka d'auko Hauwa da y'

an kayanta daga gidanmu aka mayar da ita gidansa,a cewarsa wannan lokacin it was his greatest right to take care of her and all her other needs kasancewarta matar d'ansa,daga ita har d'an nasa kuma duka k'ark'ashinsa zasu ci gaba da zama zuwa sanda za su k

ammala karatunsu,matan daya aiko d'aukan amarya suka isar da sak'o,da aka sanar da Baba buk'atar Alhaji zakar yace a basu ita su tafi,bcos shima yana ganin tunda har Allah yasa ya aurar da ita all her right to nourish,watered,dress and lodge fall off his n

eck a yanzun komai nata ya koma wuyan mijinta,shi yasa ana fad'a masa sak'on Alhaji zakar babu musu ya sallamawa matan ita,at that day she cries as if her life depends on it saboda rashin mahaifiya ko wani da zaiyi d'awainiya da kai a irin wannan lokacin a

bune da yake tab'a zuciya,,duk wani nau'in gata da y'a take samu a yayin barinta gida babu abunda aka mata,daga gurin mahaifi har y'an uwa babu wanda yayi tunanin siya mata wani abun arziki da idan taje gidan aurenta zai amfane ta,a haka matan da suka zo t

afiya da ita suka tattarata suka nufi gidan alhaji zakar.

Zuwanta cikin gidan Alhaji zakar becomes such as the opening of a new page of life filled with light and peaceful,yadda Hajiya take kaffa² da kulawa da ita ta mayar da ita tsakaninta da Maim

unatu babu bambanci,haka kowa na gidan ya d'auke ta,ma'aikatan gidan suna girmamata kamar yadda suke yiwa asalin masu gidan,Alhaji ya d'auketa tamkar y'ar cikinsa abunda zai yiwa Maimunatu haka yake yi mata,nutsuwa da kwanciyar hankali suka sake bak'untar

ta,cikin lokaci kad'an tayi wani sauyawa na ban mamaki,kyaunta da nutsuwarta da suke b'oye suka sake bayyana.

Rafeek ya dawo hutu Alhaji ya had'a su yayi musu nasiha sannan ya gabatar da Hauwa a matsayin matar daya zab'a masa,cike da nuna biyayya

Rafeek ya nuna amincewarsa da zab'in da suka yi masa,cos dama shi bai cika shiga harkar mata ba,yayi godiya ga zab'in mahaifinsa tare da alk'awarin zai rik'e amanarsu kamar yadda suka shaida masa amanace gare shi,,tun daga lokacin da Rafeek ya san matsayin

Hauwa a gurinsa bisa ga umarnin mahaifiyarsa ya kasance yana kyautata mata da janta a jiki sama da yadda suke wasa da dariya da Maimunatu kanwarsa,duk da a bayan kafin zuwan wannan lokacin idan ta ganshi tana gaisheshi da bashi girma a matsayin yayan k'aw

arta,daya bayyanar mata a matsayin mijin aurenta hakan bai sa ta canja daga yadda take ba,sai k'arawa ma da tayi,cikin hukuncin ubangiji a hankali tun bata sake da shi ba,yanayin mu'amalarsa da barkwancinsa yasa ta fara sakewa da shi,kafin a d'auki lokaci

shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakaninsu,har ya kasance idan yana gari,ya zo hutu duk inda zata je shi yake mata rakiya,ya zame mata kamar wani bodyguard,mutanen unguwa kuma duk lokacin da suka gansu tare nan zaka ji yan gulamammaki suna ci gaba da yad'uwa,

but da yake Rafeek ba mutum ne shi mai yawan magana akan abunda babu ruwansa baya tab'a kulawa.

Alhaji ya maida Hauwa makaranta mai kyau tare da Maimunatu,aka ajiye su class d'aya,gurin zaman su da komai tare suke yinsa a gida ko a makaranta,thei

r closeness to each other continued to grow as they were blood relatives before.

Laying and rising is kinda loss of living,haka nan a wajen ubangiji shekara is like a day,su Hauwa sun gama secondary school bayan wucewar shekaru uku masu kyau,yayin

da Rafeek ya kammala degree d'insa har ya nemi wucewa masters but ba'a Nigeria ya nema ba,ya nema ne a k'asar Ghana,though har zuwa lokacin basu tura masa sun bashi admission ba,Alhaji zakar yayi deciding tunda Allah yasa duk suna zaune a gida,mai zai hana

ayi bikinsu,zuwa lokacin da can k'asar za su kirashi sai ya d'auki matarsa ko ya barta a nan gurinsu,da ace suna ta zaune basu san matsayin auren nasu ba,da ya sanar musu hukuncin daya zartar sun yi farin ciki sosai,bayan y'an kwanaki aka tashi hidima,Alh

aji zakar ya yiwa Hauwa akwatunan lefe guda bakwai kowanne cike taf da kaya na gani a yaba,aka tsaida ranar biki sati guda,,anyi hidima sosai a bikin auren su,yadda ya kashe dukiya babu wanda ba zai yi tunanin y'ar cikinsa yake aurar wa ba,tsayin kwanaki u

ku akayi biki bisa al'ada da tsari aka gama,aka kai amarya gidanta dake nan a cikin unguwar K'ofar Na'isan itama,tsakanin mu duka babu nisa sosai,tun da muka rakata muka dawo ake ta labarin gidanta,yadda aka kashe mata dukiya a d'akunanta,ko wata y'ar

gata

n ba zata nuna mata komai ba,a haka dai aka baro amarya a gidanta cikin rufin asirin Allah,,,a kowane dare kamar yadda ko wane ango da amarya suke kasancewa bayan sun kad'aita,a tarihin aure da ma'aurata suma gare su haka ce ta faru tsakanin su,lokacin da

komai ya lafa sun samu nutsuwa cike da k'aunar juna da nuna kulawarsu ga juna Rafeek ya lallab'ata tayi bacci,but a gurinsa shi kuma baccin ya k'i zuwa masa,saboda tsananin farin cikin daya tsinci kansa a ciki,a haka ya ga wayewar gari lafiya wacce ta kasa

nce musu mafari.

Kamar yadda na sanar da kai Rafeek ya nemi admission amma basu kirashi ba har time d'in,cikin hukuncin ubangiji duk kwanakin da aka d'iba a baya basu neme shi ba,sai ga shi kwatsam rana a sama,kimanin kwanaki uku da tarewarsu sun

aiko masa sak'on sun bashi gurbin karatu,duk lokacin daya shirya daga nan zuwa sati guda yana iya tuntub'ar su,,a lokacin da Rafeek ya samu sak'on sai da yaji kamar yace ya fasa tafiyar dan yana ganin kamar zai cutu idan ya bar Hauwa a 9ja,can k'asar da za

i je kuma shi ga shi ba sanin yaya take ya yi ba bare yace kai tsaye zai tafi da ita,wannan dalilin yasa yayi shawaran fara yin magana da iyayensa tukun kafin ya san abun yi,da yaje gida ya sanar da mahaifansa,suma dai basu bashi goyon bayan ya fara tafiya

da ita ba,sun k'arfafa masa guiwa akan tunda karatu ne kuma na shekara d'aya yana iya zuwa ya dawo,lokacin da yaso yana iya zuwa ya ganta,but batun tafiya da ita tunda su ba gida ne dasu a can ba bare wasu dangi,gwara ya barta a nan d'in yaje abunsa,,Rafe

ek dai ba haka ya so ba,though he respects the words of his parents dole ya sawa zuciyarsa hak'urin tafiya da ita.

Cikin satin ya kammala shirin tafiya,cike da kewar matarsa da yake tsananin so,bayan ya maida ita gidansu wajen mahaifiyarsa ya bar k'as

arsa ta haihuwa,,saukar sa a k'asar Ghana ya fad'a harkar makaranta ba da wasa ba,,kamar yadda a Nigeria suma su Hauwa Alhaji yasa aka nema musu gurbin karatu a School of nursing ita da Maimunatu a b'angaren *Midwifery* suka fara attending class,this time

too is like their secondary life d'insu ne komai tare suke yinsa,basu da wasu k'awaye sune abokan juna kuma aminin junan,sun fara karatu cikin nasara,,once again Hauwa becomes a star among her relatives,ta sake zama itace mace ta farko da aka samu a tarihi

n gidanmu ta tsallake matakin karatun secondary,,a kullum tunda Rafeek ya bar kasar idan ya fito daga skul ko ya samu intervals haka yake b'ata lokaci kiranta a waya,su shafe tsayin yini mak'ale da juna,shak'uwarsu yana sake k'aruwa,soyayyar su tana sake b

ayyana,tafiyarsa da y'an watanni Hauwa ta fara laulayi,lamarin daya zamewa ahalin gidan Alhaji Zakar babban abun farin ciki da suka jima basu gani ba,kowa ka kalli fuskarsa da yanayin kulawar da yake bata ya isa ya tabbar da tsantsar d'aukin da suke ga cik

in nata,but still a time d'inma babu wanda ya fad'awa Rafeek halin da ake ciki (this is the first mistake the family has made),kowa yaja bakinsa yayi shiru ba tare da tunanin za'a samu matsala ba,sai jiran zuwansa da kowa yakee yi daga

iyayen har maids kow

a jiran ganin lokacin dawowarsa suke,ko ita kanta Hauwa a lokacin the folly she did was bata sanar masa ba,a duk lokacin da zai kirata sai dai tayi k'ok'arin sake hidden,idan suna waya tana iya k'ok'arinta ta amsa shi kamar babu wani abu dake damunta,duk d

a yanayin cikin yazo mata da laulayi mai wahalarwa,ko yaya yaga canji a tare da ita yana tambayarta yace "tana lafiya.?" Takan ce masa "ehh! Tana lafiya" Idan ya tambaya babu matsala nanma takan ce masa babu,every day within 12 hours they spend countless h

ours suna aikin abu guda,yanzun zai kirata after a few minutes he will just make a call again badon komai ba sai dan ya tabbatar da lafiyarta,video call kuwa yadda suka maida shi kamar cin abinci yafi musu wuya,though duk kusan lokacin da suke wayan takan

yi covering jikinta da enamors hijab,shi yasa har zuwa lokacin da cikintan ya fara bayyana bai kula ba,sau da yawa sukan yi fad'a akan hijab d'in da take sawa,suyi fushin su shirya duka within few minutes,yakan ce mata "he don't know what's come over her t

ake wani rurrufe masa jikinta al'halin tasan halal d'insa ne idan ya gani",sometimes yakan ce yana so ta nuna masa some private parts of her,sai dai tayi dariya ko tace "u know fa babu kyau kallonsu,suna b'ata ido" mostly yana jin ta fad'i haka yasan bazat

a nuna masa ba,kuma duk wayon da zai mata,har ya nuna mata yayi kewarta ne shi yasa yake buk'atar ganinsun,bata yarda ta nuna masa,a haka ya shafe tsayin watanni biyar da tafiya,har a lokacin duk k'ok'arin da yayi na son zuwa ya ganta,but al'amura sun sha

kansa dole yake zaune cikin hak'uri tunda bai samu damar zuwan ba,watanni uku ya k'ara har da kwanaki wanda yayi dai² da watannin sa takwas da y'an kwanaki duk da a daddafe yayi su,yaga yayi hakur'in har ya koma takura rayuwarsa and ba komai yake fahimta b

a,wannan dalilin makes him decides to ya taho 9ja ko zai samu peace of mind daya rasa tsayin watanni,,ya iso Nigeria a ranar wata Sunday ba tare daya sanarma kowa yana zuwa ba bcos he wants to surprise them,yayin da suma a gurinsu sun b'oye batun cikinsa d

a Hauwa take d'auke da shi a k'ok'arin su na son su masa surprise,kowa burinsa shi ne yana son ganin yadda Rafeek zai yi idan ya ji labarin and ya gani da idanunsa,within few hours jirginsu ya sauka a Kano,daga nan ya nemi charter taxi da zai kai shi gida,

tafiya suke a hanya but Rafeek gani yake kamar ba yi suke ba,burinsa su isa ya damu ya ganshi kusa da matarsa,cikin hakan suka samu damar isowa dai² katafaren get d'in gidan su dake unguwar k'ofar Na'isa,ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login