Showing 12001 words to 15000 words out of 233169 words

Chapter 5 - DAN MACE COMPLETED

babu komai,daga nan ban samu damar shiga gida ba nayi masa sallama na wuce gidana,,da na dawo mijina ya ganni ni d'aya ya tambayi ina Hauwa? Na bashi hak'uri sannan na fad'a ma

sa Baba yace muyi hak'uri da karb'ar Hauwa,duk dai yadda muka yi da shi sai na gyara batun cikin sanyin kalamai na fad'a masa ta yadda ba zai zargi komai ba,duk da yaji rashin dad'i amma haka ya gwada min babu komai muyi hakur'in,,a b'angaren Hauwa kuma za

manta a gida gashi nan dai za'a ce,tun bayan barina gida rayuwa ta fara yi mata wahala,wani abun a lokacin da nake gida duk da ba shiga harkar y'an gidan muke ba,sukan raga mata ko don ganin idona,to amma da yake yanzun bana nan kuma an ganta yarinya ce k'

arama duk wanda ya deb'o cin mutuncinsa sai ya sauke kanta,haka nan dai take ta hak'uri da duk abunda za'ayi mata,har lamarin ya fara neman fin k'arfin shekarunta,bayan wani lokaci ta yanke shawaran sanar dani halin da take ciki,ta zo muka yi maganar da it

a ta fad'a min duk halin da take ciki,sai na ji ban ji dad'i ba,to amma yaya zanyi tunda Baba baya so nayi masa maganar ya bamu ita,shawaran da kawai na bata shi ne daga ranar idan ta dawo daga makaranta ko wani gurin zuwa,ta daina zama a gidan tunda ganin

ta a tare da su shi yake janyo mata shiga damuwa da wahala,na bata damar idanma bata da shi ta dunga zuwa gidana tana yini,a take tace min A'a Baba ya hana ta yanzunma bai san ta zo ba,ina jin haka dabara ta zo min,nace to me zai hana ta dunga shiga gidan

su k'awarta Maimunatu tana zama can idan ta dawo daga school,idan yaso sai tayi zamanta a nan har lokacin islamiyya yayi,which means ita da gida dai sai idan taji tana son yin bacci ta koma. Tace min "Ehh! To yaya wannan shawarar d'in dai ina ganin zaifi k

oh.?" Nace mata "haka nake tunani,kuma ina ganin ko Baba ma idan ya sani ba zaiyi fad'a ba" tace "haka nima nake gani,tunda dai ai ina kusa da gida,kuma duk

abunda za'a fad'a masa ma ba lallai ne ya yarda ba ko.?",tun bayan tafiyarta sai ya zama daga wanna

n ranar idan sun dawo daga boko sai tayi wucewarta gidan su Maimunatu duk da ba makaranta d'aya suke yi ba amma zaman unguwa d'aya da had'uwarsu a islamiyya aji guda yasa suke k'awance sosai duk dama Hauwa ta kasance tana yin baya² da shiga sabgogin mutane

,lokacin data fad'awa Maimunatu zata na zuwa gidansu,sosai Maimunatun tayi murna dan ita har ga Allah tana matuk'ar k'aunar Hauwa,itan ce dai da bata bada fuska ba yasa ko itama da kanta tayi baya² da ita tunda ta san ba'a k'awance dole,,cikin hukuncin uba

ngiji sanda Maimunatu ta fad'awa Hajiyar su hauwa zata dunga zuwa tana zama a nan,Hajiya ta amsa mata da k'arfin guiwarta bcos Maimunatu ita kad'ai ce y'arta mace,daga Yayanta sai ita su kad'ai suka mallaka,da taga tana murna itama tayi maraba da zancen,ci

kin tak'aitaccen lokaci rabin rayuwar Hauwa ya koma gidansu Maimunatu,idan ta fita tun safe ba ita zata koma gida ba sai dare lokacin kwanciyarta bacci,da safe ta sake shiryawa ta tafi makarantar boko,k'arfe 3:00pm sun tafi islamiyya,su da samun zama sai m

isalin 6:00pm idan sun taso daga islamiyyar yamma,rayuwarta ta koma gaba d'aya ta koma gidan su Maimunatu,,bayan b'illowar wannan al'amari na rashin zama tsakanin y'an uwanmu,idanunsu da hankulansu sai ya sake dawowa kanta,aka fara kai tsaiguminta gurin Ba

ba akan tana tafiya yawo ba'a ganin k'afarta sai dare,abincin gidanma bata ci,maganganu dai barkatai haka aka cakud'e su,wani abun ma k'irk'irarsa suka yi suka fad'a,tun Baba bai fara tanka musu ba,sharrin yau da gobe ya janyo har ya fara tuhumar inda take

zuwa tayi dare,a karon farko lokacin da ta sanar masa gidan Alhaji zakar labbo take zama,ta kawo masa dalilinta na yin hakan,ya gamsu kuma tun daga nan bai sake d'aga maganar ba,sai da aka sake soko mata sharrin k'arya tayi masa wancan lokacin,idan ta fit

a ba gidan Alhaji zakar d'in take zuwa ba,tana dai fakewa ne da can d'in a matsayin garkuwa,amma a zahiri yawon ta take tafiya,kwararo² babu inda ba'a santa ba yanzun saboda gantali,,ranar da aka kawowa Baba wannan maganar saboda zugashi da aka yi ya fusat

a sosai,maganar tayi masa zafi da yawa,ba tare da yayi bincike ya tabbatar da gaskiya ba yayi duka wa Hauwa,bayan nan ya yanka mata warnings masu tab'a zuciya akan ko da wasa ya sake ganin k'afarta a waje sai ya karairaya yasa an hura wuta da su,,a wannan

ranar Hauwa tayi kuka sau babu adadi har taji tamkar hawayen idanunta sun k'are,yanayin maraici,damuwa da kad'aici ya sake mamayeta,cos a wannan lokacin bata da wani da zata sanarwa taji sanyi,ni d'in da muke sharing damuwarmu ban jima da zuwa ba,ita kuma

Baba ya ce ko da wasa yaga k'afafunta waje sai ya sab'a mata,dan haka ta rasa mafita,a haka ta ci gaba da daurewa ta zauna cikin habaici da gori,makarantar da zata d'auke mata kewa itama ya hana zuwanta saboda a baya na fada maka Baba yana da halin yarda d

a abunda za'a fad'a masa,and baya damuwa da binciken gaskiya,kullum tana zaune gida ga damuwa ga kad'aici sai cin ranta suke,a gefe guda ga takurawar y'an gidanmu,,duka da yake ba shekaru gareta ba sai ta kasa yin wayon ko wani ne ta fad'awa yazo ya sanarm

in

halin da take ciki,,bayan kwana biyu da faruwar al'amarin Hajiyar su Maimunatu ta kula da rashin zuwanta tasa Maimunatun ta shiga ta duba ko lafiya bata ganinta cikin kwanakin.? Bayan zuwan tan suka d'an keb'e a d'aki duk dama an samu su ido,a hakan tay

i iya kar k'ok'arinta cikin bada sallahun azo a fad'a min halin da take ciki ko Allah zaisa na rok'i Baba ya kyaleta taci gaba da zuwa makarantar,ta kwashe duk abunda yake damunta ta zayyanawa Maimunatu,tana kuka Maimunatun na taya ta har ta gama bata laba

rin abunda ya faru,Maimunatu tayi mata alk'awarin in sha Allah zata yi duk k'ok'arin da zata iya ta zo ta sanar min,Hauwa tayi mata godiya suka fito tare,da ta rakota bakin k'ofa suka sake tsayawa a nan suna ci gaba da y'an maganganunsu,kafin suyi sallama

aka samu wani cikin y'an gidanmu ya kaiwa baba gulmar ga Hauwa can ta fita,babu b'ata lokaci Baba ya zo ya iske su zaure suna magana,nan d'in ma bai tsaya bin ba'asi ba ya korata gida bayan ya sauke mata kyawawan rankwashi masu shiga jiki,Maimunatu na kall

on yadda take kuka,ta fice tayi gidansu da yanayin damuwa,,bayan komawarta gida bata iya fad'awa kowa ba har Hajiya data aikata,kuma ko da ta dawo ta tambayeta ce mata tayi tana lafiya daga haka bata sake cewa komai ba,,yanayin rayuwar gidansu Maimunatu ra

yuwa ce da suke yinta a sauk'ak'e,yanayin mu'amalar su da zaman takewarsu sun kasance suna gudanar da rayuwar su tamkar abokai tsakanin iyayen da y'ay'an,idan suna tattare da damuwa iyayen suna jansu a jiki su ji damuwarsu,itama Hajiya mahaifiyar sun a lok

acin data kula da yanayin da Maimunatun ta shiga cikin kwanakin,haka ta sata gaba da tambayar lafiya take ganinta cikin damuwa.? Tana ta tambayarta da damuwa a fuskarta,tana lallab'ata saboda tana so ta sake sosai sannan taji mene ne ya kawo sauyin da aka

samu,zuwa lokacin kasancewar damuwa tayi mata yawa sai bata sake b'oyewa mahaifiyartan ba ta zayyana mata komai da yake faruwa da Hauwa,,Hajiya ta shiga damuwa ta rarrashi Maimunatu sai da ta kwantar mata da hankali,and ta bata albishir idan Alhaji ya dawo

zata san yadda tayi aka nemawa Hauwa'r sassauci,cos tana ganin lallai rayuwarta a cikin gidan akwai hatsari,sannan su da suka sani baya daga cikin hak'k'in mak'otaka kana ganin b'arna tana faruwa ka rufe baki ka zuba ido,dole tana bukatar inda zata zauna

ba tare da tsangwama ko takurawa ba,ya dace ace itama ta zauna ne kamar ko wane d'a da yake k'ark'ashin iyayensa cikin y'anci,,sun gama maganar a ranan bayan Abba'nsu ya dawo tayi masa bayanin abunda ta ji daga bakin Maimunatun,shi kansa yayi mamaki sosai

ace irin haka tana faruwa,abunda ya sanarwa Hajiya shi ne bai san yaya zai yi ya iya taimakawa ba,Hajiya ta kawo shawaran ya nemi mahaifin Hauwa suyi magana,idan ya fahimce shi,shi kenan ta san zai sassautawa yarinyar kuma rayuwarta zata samu salama,kwanak

i biyu tsakani Alhaji zakar ya samu Babanmu a k'ofar gida,bayan sun gaisa cikin mutunci kamar yadda aka saba Abba'nsu Maimunatu yana kallon Baba yace

"Malam Baba! Gurinka na zo,wata y'ar magana nake so muyi da kai,yau kwana biyu kenan ina sa rai da g

aninka Allah bai

nufa zamu had'u ba sai yanzun,ina fatan ba zaka damu da abunda zaka ji daga gare ni ba.."

Baba yana kallonsa da mamaki,murmushi kwance saman fuskarsa yace

"Toh! Alhaji Allah yasa muji alkhairi"

Alhaji zakar ya kalleshi

da murmushi shima a fuskar sa yace

"In sha Allah ma alkhairi ce."

Gyara zama Baba yayi yace "Toh Alhaji ina saurarenka,wace irin magana ce wannan d'in.?"

Sai da Alhaji zakar yayi ajiyar zuciya ya san tabbas maganar da zai yiwa Baba,idan

har bai masa kyakykyawar fahimta ba zasu iya samun sab'ani,haka kuma idan yayi shiru yaci gaba da zuba ido yasan lallai rayuwar marainiyar zata sake shiga wani halin,to amma da yake yayi nufin aikin alkhairi ne har zuciyarsa shi yasa sai ya daure yace



"Dama Malam baba magana ce nazo da ita nake son mu tattauna,Allah yasa zaka fahimce ni,dan ba akan komai nazo muyi magana da kai ba sai akan gidanka."



Baba yana kallonsa yace "Akan gida na..?"

Alhaji yace "K'warai kuwa,akan gidanka."



Baba yana binsa da wani irin kallon mamaki da rashin yarda ya sake daurewa yace

"Toh ina jinka.."

Alhaji zakar yana kallon Baba ya fara zayyana masa duk abubuwan dake faruwa a gidansa,da mugun mamakin yadda akayi ya sani Baba yake ta kallon

sa,har ya gama magana Baba bai ce masa komai ba,Alhaji zakar yayi shiru yana ta kallon baba yaji ko zai yi magana amma yaji shiru,dole tasa shi tambayar baba

"Malam Baba baka ce komai ba..?"

Baba dai yana kallonsa har lokacin da kyar ya bu

d'e baki cikin kaushin kalami yace "toh Alhaji me zance.?? Tunda Allah yasa munafukai sun fara sawa gidana ido,har sun fara yawo suna yamad'id'i da ni a gari,da tona asirin gidana.. Zance ya lalace tunda har al'amarin gida na ya shiga gari.."



"

A'a Malam Baba kada kace haka,wannan magana sam baka fahimci yadda take ba,,ni dai ka sanni kuma kasan ba mai shiga harkokin da ba'a sani bane,amma tunda kaga na tsayar da kai nayi maka magana kasan ba zai wuce na hango maka damuwa bane a cikin gidanka na

sanar da kai. Toh amma tunda har Allah yasa magana ta batai maka ba,Allah ya huci zuciyarka kuma ya baka hak'uri idan har na b'ata maka rai.."

Ajiyar zuciya Baba yayi yace "ai Alhaji wannan batun tunda kazo da shi na san bazai wuce tsaigumi aka kai m

aka ba,kuma kaima ga shi ka tabbatar min,amma tunda haka abun yake,kafin a fara zagina akan maganar yarinyar nan,dole ne tunda yake nine mahaifinta na zartar da hukuncina akanta ta

yadda babu wanda zai sake zuwa min da magana makamanciyar wannan,,zan aurar

da ita kowa sai ya huta,da ta d'auko min maganar da zata fi k'arfi na gara na zartar da hukuncin da zan kashe bakin mutane.."



Alhaji yana kallon Baba da mamaki yace "Malam Baba aure kace.?" Baba yace "Haka nace",cikin muryar rarrashi Alhaji zaka

r yace "kada kayi haka malam Baba,yarinyar nan duka nawa take da zaka ce zaka aurar da ita.? Ko a k'auye yanzun tuni an waye an daina irin wannan auren,bare mu da muke cikin birni,,ya kamata kayi tunani dai kafin ka zartar da hukuncin da zai iya kaika ga y

in dana sani a gaba."



"Alhaji ina ganin wannan hukuncin shi ne dai²,tunda har Allah yasa ka fad'i sak'on da ya kawo ka,kana iya tafiya na gode.."

Alhaji yaci gaba da kallon Baba da mamaki "Amma malam Baba ban tab'a tsammanin haka daga gar

eka ba,wannan al'amari idan har ka tsaya ka nazarce shi da kyau,na tabbata zaka gane gaskiyar da nake son ka fahimta."



"Alhaji maganar fahimta ya k'are,tunda har ka fad'i sak'on daya kawo ka,yanzun naka ido ne,,abunda nake fad'a maka a yanzun

shi ne batun auren Hauwa na gama yanke hukunci,in sha Allah cikin satin nan zan d'aura mata aure,da ma hak'k'i na ne na aurar da ita ga wanda yayi min,yadda nayi niyya haka zanyi aure babu fashi.."

Cikin takaici Alhaji zakar yaci gaba da kallon Baba

but bai sake ce masa komai ba ya mik'e da niyyar barin gurin tunda al'amarin yafi k'arfinsa,ya yiwa Baba sallama yana niyyar shiga gida,Baba dake zaune har lokacin yana kallonsa cikin d'aga murya kamar wanda aka bawa umarnin yin magana yace

"Yawwa

Alhaji ina da wata y'ar maganar nima."

Waiwayowa Alhaji zakar yayi yana kallon Baba duk da yaji haushinsa amma haka nan daga inda yake tsaye yace "fad'i maganarka ina sauraronka."

Shima Baba daga nan inda yake yace "Yawwa! Dama ina so ne na ba

ka cigiya tunda har Allah yasa nace zan aurar da ita,ba tare da samun tsayyaye ba shi ne nake son shaida maka,ko da Allah zai sa ka samu wani mai rangwamen gata kamar ta da yake buk'atar auren,dan Allah ina rok'on alfarma ka sanar masa yazo gida na ina da

matar da zan bashi sadaka.."

Cike da takaici Alhaji zakar ya bi Baba da kallon sakarci ba tare da ya ce komai ba ya juya zai shiga gida,baba yaga yayi masa magana bai tanka ba hakan tasa shi sake cewa

"Yawwa Alhaji,,nace tunda yake Allah yasa ha

r kana ganin tayi k'arama da aure yanzun,kuma kai d'in kana da ma'aikata a gidanka,shin mai zai hana ko su ne ka nemawa d'aya daga cikinsu aurenta tunda kana tausayinta tayi k'arama da aure.. Ka ga dama jihadi kake son yi.. Shi ne sai naga zaifi kyau na sa

nar da kai,sadaki ma kad'ai idan ka biya ya wadatar a d'aura musu aure,daga nan sai ka ajiyeta a gidanka,kaci gaba

da kulawa da ita ko itama ka bata aiki a gidan naka,tunda yake ni mahaifinta na yi ba dai² ba.."

Maganar ta yiwa Alhaji zakar zafi,still

bai tanka ba ya wuce gida ransa a b'ace har yaji nadamar samun Baba da maganar,shigarsa gida a cikin wannan yanayin suka yi maganar da Hajiya,yadda suka yi duka da baba ya sanar da ita tunda ita ta sashi shiga maganar tun farko,,Hajiya ta lallab'a ta kwant

ar masa hankali,followed by maganar ta akan me zai hana tunda har Allah yasa al'amarin ya zo da haka kuma Baba da kansa ya bashi damar neman auren yarinyar ga hadiman gidansa,su nunawa masa cewa maganar da yayi cikin izgili a shirye suke su tabbatar da cik

arta..??,Alhaji ya zuba mata ido yana kallo cikin rashin fahimta but yayi k'ok'arin yin magana

"Hajiya me kike son cewa..?"

Tace "so nake ka amince da batun neman auren yarinyar."



Yace "Hajiya wane irin batu kike yi haka.? Ni zan nemi

auren k'aramar yarinya kamar wannan,sa'ar y'ata fa.?? Ita kike cewa na nemi aurenta..?? Yarinya y'ar shekara sha hud'u.? "



Tace "Alhaji nifa ba kai nake nufi ba."

Yace "to waye zan nemawa aurenta.? Kin san dai bani da ikon zartar da ko wane i

rin hukunci akan ma'aikatan gidan nan cos bani ke da su ba,mu kuma ba wani babban d'a namiji gare mu ba bayan Rafeek,idan munce shi,duka shekarunsa nawa suke.? Besides yanzun yake shekara ta biyu a jami'a."

Hajiya tace "ni dai alhaji kawai kayi hak'uri

da batun shekarunsa,wannan al'amari ne da ya kamata ace munyi iya kar k'ok'arin mu wajen ganin mun taimakawa marainiyar nan,ina tausayin rayuwar yarinyar nan har zuciya ta,kallonta nake kamar Maimunatu na,idan a yanzun da muke da dama bamu taimaka mata ba

,mu yaya zamu yi a gaba..?? Kada fa ka manta taimakon maraya abune mai kyau,kamar yadda annabi (S.A.W) yace a hadisi:"Ni da mai taimakon maraya,zamu kasance kamar haka

✌

🏻

a gidan aljannah,sai ya raba tsakaninsu da wani abu,maleek (R.A) yayi nuni da yatsuns

a biyu manuni da na tsakiya,,idan ka duba duka nima bawai ina dagewa bane akan lallai sai munyi hakan zai nuna kulawarmu gare ta ba,sai dan ina ganin yin hakan shi ne zaifi bamu damar taimaka mata ba tare da anyi zarginmu ba,ni ina yi mana kwad'ayin matsay

in ne kawai,wannan ne yasa nake sake tunatar da kai,,shin a lokacin da wani namu yake neman taimako mu baza mu nemi taimakon wasu bane..? Ya kamata ka duba maganata da kyau,tamkar jihadi ne zamu yi idan har munyi nasara..!"

Alhaji zakar yayi shiru bai

ce komai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login