Showing 36001 words to 39000 words out of 58120 words
shine yana can amaryar tasa ta sami ciki, idan kuma na tuna da
ciki sai na ji na sake tsanar shi, sabida muguwar ƙarya irin tasa. Mu da muka zo kotu za a yi
shari’ah ƙarfe goma ba a fara ba sai ƙarfe sha
ɗ
aya da rabi, ina shiga
ɗ
akin shari’ar na ji gabana yana wani fa
ɗ
uwa, na ji gaba
ɗ
aya jikina ya yi evening. ‘wai yau ni ce zan tsaya gaban alƙali ina shari’ah da Turaki? Duk abinda Turaki ya yi min bai kai na
Sardauna ba, amma ban iya tsayawa da Sardauna ba sai Turaki, anya babu son zuciya nima a lamarina, anya kuwa akwai hallaci? Anya na yi tunani na mai kyau, na yi shawara da inda ya kamata, a take hawaye suka fara zubo min a fuska, bazan iya ba wallahi, baza
n iya tsayawa da Turaki na yi shari’a da shi ba, na fasa.’ A hankali na fara zame jikina ina yin baya, na dawo na sami wani benci na zauna na kifa kaina da gwiwa na fara rusa kuka mai ta
ɓ
a, zuciya kawai ni Turaki ya sake ni, amma babu zuwa gaban alƙali, Tu
raki har yanzu
ɗ
awainiya yake da iyayena da ‘ya’yana da ‘yan uwana, duk da nagama auren sa bai kamata na tsaya gaban alƙali da shi ba, bai kamata na yi irin wannan rabuwar da shi ba, muryar barrister na naji yana cewa.
“Ranki ya da
ɗ
e.”
Na
ɗ
aga rinann
u idanuna na kalleshi, ya ce.
“Mai shari’a yana nemanki.”
Na girgiza ma sa kai, ya matso kusa da ni ya ce.
“Mene bangane ba, ya yi miki barazana ne?”
Na ce.
“A’a, bazan iya shari’a da Turaki ba, bai cancanci wannan ba, ya yi min abubuwa da y
awa a rayuwa bai kamata na tsaya da shi a gaban alƙali ba da Turaki ba gaskiyya.”
“To yanzu mene abun yi?”
“Nima bansani ba, amma bazan iya ba.”
“To ki zauna anan zance baki zo ba, za a wuce shari’arku a tafi ta gaba, amma kisan ku
ɗ
in da kika bani
bazasu dawo ba.”
Na gya
ɗ
a ma sa sama kawai alamar badamuwa, ya tashi ya tafi, ni kuma na ci gaba da kukana, sai da ya kusa minti talatin da shiga, sannan na miƙe na yi waje daga kotun, kai tsaye gida na nufa na shiga ina kuka, Hajiya ta biyo ni tana fa
ɗ
in.
“Ke me ya faru kike rusa mana kuka?”
Cikin kukan na ce.
“Hajiya ni kawai ku yi masa magana ya sake ni, bazan iya shari’a da shi ba, kawai ya sake ni.”
“Au, wai da shari’a kika je?”
“Eyh Hajiya, amma ni dai ku yi masa magana, kawai ya yi
min sakina na ci gaba da rayuwata, dan Allah.”
“Nana aure fa raine dashi, ba wanda ya isa ya yanke shi sai lokacin sai ya yi, ni bazan shiga maganar raba aure ba, idan da rabu tsaf sai kika ga rabo ya kashe ni, ba zan shiga ba, kuma babu wanda zai shig
a cikin gidan nan, ki je dai ku yi yanda zaku yi a tsakaninku, amma mu dai babu mu gaskiyyar zance kenan.”
Legendspen
08129553971.
SARTSE BOOK 3
Sayyid.
(20)
Na kalli Hajiya, na ce.
“Yanzu kenan kun cire hannunku? Duk abinda. Zai faru da ni
ya faru ku babu ruwanku kenan?”
“A’a ko
ɗ
aya Nana, bamu isa mu ce mun cire hannunmu ba, amma a zancen kashe aure ba a zura kai Nana, tsakanin miji da mata ma sai Allah, yanzu da ace azaba kike sha, ko zaluntar ki yake yi to da zamu shiga, amma Nana zanc
en ƙarin aure ne, hukunci ne na zuciya, adalci da rashinsa, babu ruwanmu a ciki, yanda baza mu yi milki dole ba, to shima fa baza mu yi masa dole ba Nana.”
“To Hajiya na gaji da zaman da shi, Yayan mahaifinsa baya sona Hajiya, duk wani abu shi yake ƙull
o shi, yana namiji ya dinga abu kamar na mata Hajiya, zamana da shi wani sabon matsalal ne a gareshi Hajiya, shi ya sa na za
ɓ
i na haƙura da shi, kuma ni bazan iya zama da kishiyar da take haihuwa ba.”
“Idan kika yi wa kanki baki ai shikenan Nana, likito
ci sun tabbatar miki da mahaifarki zata iya
ɗ
auka jariri zaki iya haihuwa, kawai dan ta yi jinkiri sai ki ce haka? Allah zaki yi wa Butulci ne ko me? Da kina da hankali wallahi godiya zaki yi wa Allah, idan kika ha
ɗ
a rayuwarki ta baya da ta yanzu, Allah Ya
yi miki kyakyawan sauyi, amma duk kin kasa ganewa, kinsan da cewar shima ce masa aka yi an
ɗ
aura masa aure? Sannan
aka bashi za
ɓ
in ko ya zauna da ku ku biyun ko ya haƙura dake, duk wani abu da zai
ɗ
auke miki damuwar wannan kishiyar Turaki ya yi shi, kinsa
n da cewa ya bu
ɗ
e miki babban shagon siyar da abaya? A niyar shi idan kika dawo duk ya fa
ɗ
a miki ya nuna miki, har alfahari ya yi akam cewar matarshi na son shi kuma zata fahimci, amma Nana kin kasa fahimta, tabbas kishi halal ne, kishi da zafin zuciya gas
kiyya ne, kuma soyayya ce ke kawo shi, amma idan rai ya
ɓ
aci hankali ba ya gushewa, da kin zauna kin cire son zuciya kinyi tunani na gaske da zaki sami amsar komai da komai, amma kin kasa.”
Jikina na ji ya yi sanyi, amma duk da haka napi bari wa
ɗ
an kala
man bogin da ya shimfi
ɗ
awa su Hajiya su yi tasiri akaina, tabbas zancen shagon abaya ya bu
ɗ
e dan naga wasu irin ledojin na shago da idan ansiya kaya ake zubawa a ciki da yawa a motarsa lokacin da kafin mu tafi Saudiya, ansa NANA’S DAR, amma da na tambayesh
i sai ya ce na matar abokinsa ne take yin online bussiness a gida, shine ya sa akayi masa zai basu gudummawa, sannan kuma da muna saudiya naga yasa dp na logo
ɗ
in NANA’S DAR, amma banyi tunanin komai ba, amma dai duk haka ƙanzon kurege ne irin na Turaki, n
i sharrinsa ma tsoro yake ban, ya ƙware a yaudara.
Tashi na yi jikina babu ƙwari na tafi
ɗ
aki na kwanta, ni dai tabbas sai Turaki ya sake ni, bazan iya ba, ko da na yi niyar yin tunani akan hakan sai ma tuna wani mafarki da na yi Ni da Turaki zaune a f
alo ga yara guda hu
ɗ
u maza da mata suna zaune suna wasa, ina kallon yaran ina jinda
ɗ
i a cikin a raina, kwatsam sai wata mata ta fito daga cikim
ɗ
aki ta far
ɗ
aukan yaran, n kalli Turaki na ce.
"Habiby, kaga tana
ɗ
aukan yaran mu?"
Ya kalle ni ya yi m
urmushi, ya ce.
"Habibty ai na tane, za a hana uwa
ɗ
aukan 'ya'yanta?"
"Na ta?"
Na tambaya ina miƙewa, shima ya miƙe ya ce.
"Habibty wannan fa amarya tace, ko baki gane ta ba?"
"Banganeta ba."
Na fa
ɗ
a ina girgiza kai, sannan na sake cewa.
"Habiby yaushe ka yi aure? Rashin haihuwar tawa ne ya sa ka ƙara aure?"
Tabbas wannan mafarkin ne yake son zama gaskiyya kenan, na girgiza kai na ce. “To baza ayi haka da ni ba.” Haka na yini a kwance ina ta famam tunane tunane, duk da haka na takur
e zuciyata waje
ɗ
aya, naƙi bata damar da za ta yi tunani bayan wanda na
ɗ
aura ta kai, kawai a sake ni. Wajen ƙarfe takwas na dare muna zaune a tsakar gida ni da Hajiya sai Yaya Ridwan, daga gefe twins ne suka gama kukansu wai su wajen Papa zasu, takaici ya
kaini na dake su shine suka koma gefe suka yi fushi, wayata ce ta fara ƙara alamar kira na shigowa, ina dubawa naga Lamrah, a take na tuna dukkan abinda Big Daddy ya yi min, wani haushinta ya rufe ni baki
ɗ
aya.
“Ba kiranki ake yi ba ne?”
Na ta
ɓ
e bak
i na ce.
“Lamrah ce, ‘yar gidan Yaya Babansu Turaki.”
“Ke mutanen nan suna nemanki kina gudun su.”
Yaya Ridwan ya fa
ɗ
a, Hajiya ta ce.
“Ki
ɗ
auka mana.”
Na
ɗ
auka ina tura baki gaba.
“Hello Anty Nana.”
“Na’am Lanrah ya gida?”
“Lafiya ƙ
alau, ashe ba kya gida
ɗ
azu amaryarki tazo tana yiwa Daddy kuka.”
“Kukan me?”
“Wai Yaya Turaki baya gidan gaba
ɗ
aya, kema kuma ba kya gidan, wai ashe tun da suka yi aure bai su ta
ɓ
a magana da ita ba.”
“To ni ina zan sani, ni kawai dawowa na yi nag
anta a gidan, dan bana haihuwa shine Turaki zai yi min kishiya, to na barta mishi ta cinye duka.”
“Waya fa
ɗ
a miki? ‘Yar gidan Aminan Daddy ce fa, shima Yaya Turakin bai san da auren ba, nan Mama ta yi ta yiwa Daddy magana wai bai kyauta ba, itama sai da
ta ce matarsa zata ga kamar sabida bata haihuwa aka yi mata haka, to amma kinsan ya riga da ya yi abinda yaga dama.”
“Allah Sarki, ni kinga ina gidanmu ma, jira nake kawai ya aiko min da takardarta bazan iya ba wallahi.”
“Wallahi Mama ma haka ta ce,
wai da ‘yar ta ce bazata zauna ba, ranar sunyi fa
ɗ
a da Big Daddy sosai fa, har take ce masa gashinan yaja mana duk babu masu auren mu, ji Yaya Seemah ta girmi Yaya Turaki fa wajen shekara 40 amma bata ta
ɓ
a aure ba, Yaya Nadrah ce kawai ta ta
ɓ
a aure itama
yanzu ya mutu, shi kawai ya dinga takurawa sirinkansa dan yaga kowa yana bashi girma, Mamansu Sarauna ta ce ma Sardauna kar ya zauna da Laila
ɗ
in ina ga, tun da daman ta zo nan sunyi kaca kaca da Big Daddy, muma nan duk haushi muke ji wallahi.”
“Allah S
arki Lamrah, ku daina jin haushinsa mahaifinku ne, ni ce ba ya so kuma gashi na tafi.”
“Wallahi bake ka
ɗ
ai ba duk sirikan gidan maza da mata ba son su yake ba, gani yake kowa dukiyarsu yazo ci.”
“Allah Sarki.”
“Dan Allah ki yi haƙuri ki dawo, wall
ahi duk gidan ya hargitse in fa
ɗ
a miki.”
“Ki dai barni kawai.”
Ba yanda Lamrah ba ta yi ba naƙi bata fuska, ƙarshe ma na kashe wayar baki
ɗ
aya, ina kashe wayar hajiya ta ce.
“To kin ji dai.”
“Hajiya bakisan wannan duk tsarin Turaki ba ne? Ni fa
Hajiya yanzu tsoronsa nake ji, Allah
ɗ
aya kawai zai fa
ɗ
an na yarda, amma Turaki babu abinda zai fa
ɗ
an na yarda, duk wasu maza ma.”
“Har da mu kenan dan ubanki.”
Yaya Ridwan ya fa
ɗ
a, na yi dariya na ce.
“Banda ku.”
Miƙewa ya yi zai tafi ya ce.
“Nana adai yi tunani mai kyau dan Allah.”
“Ni dai ina kan bakana Yaya.”
Bai ce min komai ba ya fice, nima natashi na koma
ɗ
aki na kwanta, sai dai tun da na shiga
ɗ
aki maganganun Lamrah suke dawo min a raina, na hana kaina sakat ina ta faman tunani
, da gaskiyyarsu baƙin halin babbansu Ya hana su aure, kuma a cikin familin babu wata ko
wani suriki da kake jin bakinsu, nima sai da aka fara case sannan aka kira ni, amma kafin lokacin ko a family meeting ma baya baya muke zama, kuma har agama ba me ce m
ana ƙala, sai a yanzu da na yi jan wuya aka sanni, amma a wancan lokacin ma ba wanda yasan ni ko kallo ban ishe su ba, ashe gani yake kowa zuwa ya yi ya cinye musu dukiya kenan? Wani
ɓ
ari na zucuyata ya ce min. “Idan kuma dagaske take Turaki bai san komai
ba fa?.” Na yi shiru ina son na yu tunanin akan hakan, sai dai kuma wanu
ɓ
ari na zuciyata ya ce. “Ai zai iya sakinta, amma ya zauna da ita. Wannan ma a kallon da na yi mata babu makawa tana
ɗ
auke da juna biyu na Turaki.” Haka na yi ta tarawa da kwashewa a
cikin kaina kafin wani irin wahalalen bacci ya
ɗ
auke ni, wanda na dinga farkawa cikin dare, da ƙyar gari ya waye.
Washe gari bayan twins sun tafi makaranta, wajen ƙarfe sha
ɗ
aya na rana Maman Turaki da ƙannensu su Hajara suka zo, kasancewar sune suka s
an gidan, na yi matuƙar mamakin ganinsu. Bayan mun gaisa sun zauna Mama ta ce.
“Nana, ba fa aga mijikin ba.”
“Mijina kuma? Turaki ne ba agane ba?”
“Shi fa.”
Hajiya ta saki wani salati, tare da
ɗ
aura hamnu akai, ta ce.
“To ina ya tafi?”
“M
uma nan babu wanda ya sani, idan aka kirashi sai ya
ɗ
aga ya ce dan Allah a ƙyale shi, yanzu ma wayar bata tafiya.”
Legendspen
08129553971
SARTSE BOOK 3
Sayyid.
(21)
Gaba
ɗ
aya na zama kamar wata sokuwa, na shiga kallon
ɗ
aya bayan
ɗ
aya, sai nake
ganin kamar duk tsari ne abun na su, Hajiya ta ce.
“Muma nan ya kwana biyu bai zo ba.”
“Ita Nana yaushe ta bar gidan?”
Mommy ta tambaya, Hajiya ta ce.
“Ai a ranar da muka dawo.”
“Ni dai duk abinda ya sami
ɗ
ana wallahi Ismail ya ja min, ya di
nga abu kamar shine ya hallice su, haka kawai ya
ɗ
aurawa yaro aure, yanzu gashi an nemi yaron an rasa shi ko a jikinsa.”
“Haƙuri zaayi, ke Nana yaushe rabonki da shi?”
Hajiya ta fa
ɗ
a, cikin sanyi murya na ce.
“Ni an kwana biyu.”
“To ki gwada la
mbarsa ko zata shiga.”
‘Na ce masa me?.’ Na fa
ɗ
a a raina, a fili kuma na ce.
“Ai ba zata shiga ba, sabida na rufe shi.”
“Yaya Nana bai kamata ki
ɗ
auki wannan hukuncin ba, da kin tsaya kinyiwa Yaya Turaki uziri.”
Hajara ta fa
ɗ
a, Mommy ta ce.
“Gwanda da ta
ɗ
auka, ni kaina abubuwan Isma’il sun fara kaini bango, ni yanzu zan tafi idan Allah Yasa an ganshi tanan sai ku sanar da ni.”
Ta fa
ɗ
a tana tashi, duk muka fita rakata ni da Hajiya, gaba
ɗ
aya jikina ya fara sanyi na rasa gane kan al’amarin,
haka na yini duk jiki ba da
ɗ
i. Abu kamar wasa sai da aka yi sati ba a sami Turaki ba, abun tun a ganinsa ƙarami har ya girma, ni kaina tun ina ganin abun a matsayi shiri, na dawo na fara ganinshi a zahiri ya fara bani tsoro, sai da aka yi kwana goma cif s
annan aka sami labarin shi, shima ta bakin likitan asibitinsu, ina zaune a tsakar gida na yi jigun jigun kamar ko yaushe Ra’is ya shigo, yana shigowa ya ce.
“Nana.”
Na
ɗ
aga kai na kalleshi, na ce.
“Ya aka yi?
“An sami labarin Yaya Turaki, amma
kuma yana asibiti cikin halin jinya.”
A razane na miƙe tsaye, duk na tsorata na ki
ɗ
ime na ce.
“Me ya same shi?”
“A yanda Lamrah ta fa
ɗ
a min wai yaje anyi masa allura kashe ƙwayoyin haihuwa ne, shine ta haifar masa da matsala a jikinsa.”
“Kashe
ƙ
wayoyin haihuwa kuma? Kai a ina kasan Lamrah
ɗ
in? Aina kasami lambarta?”
“Ita ta yi min magana da kanta tun kwanaki, wai ina burgeta na ce mata ina da aure.”
A take na ha
ɗ
e rai na ce.
“To wallahi ka fita sabgarta, ba zakaje ka kwaso mana ‘yar wan
nam ahalin ba, ubanta ya dinga maka kallon cinye musu arziƙi ka zo yi, kuma mu a gidanmu ma ba ƙara aure. Yanzu shi yana wane aisibtin ne?”
“Ai acan Abuja ne ma.”
Jikina ƙara yin wani sanyi, na rasa me ke damuna. ‘To kenan Turaki dagaske yake akan ma
ganar? To me ya kai shi zuwa ayi masa wata allura, ko dan ya tabbatar min da cewar ni ka
ɗ
ai yake so? Amma fa namiji munafuki ne tsaf zai iya shirya abunsa, ni gaba
ɗ
aya na kasa yarda da abun.’ Idan kuma na tuna zuwan mahaifiyarsa da kuma kwanakin da aka
ɗ
a
uka ana nemansa sai naga gaskiyya ne, amma na rasa ta yanda zuciyata zata kar
ɓ
i zama da wata a matsayin kishiya a gidan Turaki, duk da idan na duba Turaki ya sadaukar da abubuwa da yawa domin ni, kuma ko sau
ɗ
aya bana fatan ace ya yi wa kansa wani abu da z
ai hana shi haihuwa, idan kuma na mutu fa? Shikenan ba zai sake aure ba ko me? Gaba
ɗ
aya jikina ya yi wani irin sanyi na rasa abinda yake min da
ɗ
i. Sai na
ɗ
auki wayata zan kira lambarsa sai na fasa, haka na yi ta faman danna waya har bacci ya
ɗ
auke ni, was
he gari ma da abinda na tashi a raina kenan, na kasa yin komai sai faman tunani, twins ma ƙarshe Hajiya ra shirya su suka tafi makaranta, babu abinda yake yawo a akaina kamar idan bayan na koma gidan Turaki amaryarsa ta haihu, tabbas akwai mazajen da basa
juyawa matansu baya, akwai ‘yan goya da zani, amma kuma akwai ‘yan iskan da ko ciki aka samu shikenan kin zama sauna, kin zama sakarya, kin zama mara daraja. Duk da bana hango Turaki da wannan halin amma tabbas ba kowanne namiji ba ne
ɗ
an