Showing 51001 words to 54000 words out of 60971 words
motar lafiyarta lau, kuma shi ba shan wani abin maye yayi ba, ba earpice a kunan sa, kuma kwakwaluwarsa lafiyarta lau kawai dai cikin biyu ne KO wani abin ya taba masa ransa KO yana Sauri ya je wani wajen ne hakan yasa ya kasa control din kansa"
Hajiya Fadimatu ta shafa fuskarsa ta ce" Ya jima yana barcin ne?"
Docter ya ce" eh toh sai da muka daidaita komai ya samu kamar awa uku muna ta neman yanda zamu sanar muku, zuwa yanzu yaci ace ya farka ma sai dai da alama yana jin dadin bacin, Muje ma'am na baku takardun da ake bukatar a cike da kuma na maganin sa"
Hajiya Fadimatu ta kali Yar Mahaukaciya dake tsaye itama tana sauraron bayanan likitan ta ce" Yata bara na dawo" ta juya ta bi bayan doctern
Da tafiyarsu Yar Mahaukaciya tayi tsai tana kalonsa sai bacinsa yake gashin idon nan nasa yayi zagar zagar a konce baki yayi lufluf da shi , bakin nan nasa tamkar ya shafa man lebe sai sheki yake namiji da shekin lebe, a hankali ta jawo kujera ta zauna daf da shi ta dago hanayenta ta dora saman cinyoyinta ta tokare habarta ta zuba masa ido tana kare masa kalo a ranta tana matukar mamakin mumurdewar hanunsa shi kuwa ba karfe yake ci ba a saninta bata taba ganinsa yana irin daga karfen nan aman hanunsa yana yan dambe da ake nunowa a tashar TL9 ,
Tana haka har wani irin baci ya kama idanuwanta ta karewa dakin kalo ba wajen konciya hakan yasa ta dan dora kanta daga bakibakin gadon baci yayi awon gaba da ita ( toh fa ke da aka barwa marar lafiya?)
Cikin nutsuwa ta turo kofar ta shiga da salamar ta , murmushi ne ya subuce mata ganin Mubasshir ya farka yana kalon Yar Mahaukaciya dake baci duk da bai ga fuskarta ba yana son sanin KO wacece ke konce kusan sa ,
Shima Murmushin ya sakar mata ya dago hanunsa irin ta karaso
Hajiya Fadimatu ta karasa suka gaisa da gudan jininta ta ce" Dan Fadimatu yaya saukin jikin?
Mubasshir yayi murmushi cikin muryar maran lafiya ya ce" maman Mubasshir i'm sorry"
Ta girgiza kai ta dora yatsarta a saman lebensa ta ce" no dan gidan Fadimatu dena bani hakuri yarona, Allah ya baka lafiya "
Yayi murmushi yana kalon hanunta magunguna ne ya dan yatsina fuska a ransa ya ce " tap gaskiya ni bazan sha maganin nan ba"
Bayan ta ajiye ledar maganin ta zo a nitse ta tana murmushi ta ce" oh Yar Fadimatu nasan bacin nan na jiya daman bai wani isheta ba , baiwar Allah gashi yanzu mun kado KO abinci bata ci ba
Gaban mubasshir ya fadi ya lumshe idanuwansa yana kalon mahaifiyarsa na kokarin cirewa Yar Mahaukaciya hijabinta dan ya shake mata wuya , yayi gagawar kawar da kansa yana kara rintse idanuwansa a ransa yana ta adu'o'i kan Allah ya kare masa idanuwansa da kalon banban muradin sa
Idanuwanta ta bude suka yi ido hudu da Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta ce" Mama kin dawo? Baci ne ke damuna
Hajiya Fadimatu ta ce" ai Dole yar Fadimatu, Konta ki hutawarki , ai likitan yace zai mabu salama aman sai dai mu tafi gida da yayanki dan nayi Kiran number matarsa ta yiwa mahaifiyarta rakiya bata nan shi kuwa baya son shan magani sai dai mu tafiyarmu gida da shi
Yar Mahaukaciya ta gyada kanta tana leken fuskarsa ta ce" Allah ya kara afuwa
Hajiya Fadimatu ta ce" Amin , sanan taci gaba da hada masa yan magungunan da likita ya ce ya sha idan ya farka sai a basu salama su je gida ya ci gaba da sha
Cikin ikon Allah likita ya salame su suka nufi gida da magungunan su, aman tunda ya farka bai yarda sun hada ido da Yar Mahaulaciya ba , koda tayi masa sanu da jiki hanunsa kawai ya daga mata a hakan har suka isa gida , inda Hajiya Fadimatu ta rasa dรฉcision din da zata dauka domin shi dai ba lafiya ne da shi ba, bazata yarda ya kwana a dakunan kasa ba , kuma dakin nasa shine Yar Mahaukaciya ta zauna, sanan tana ganin lokacin ta fada musu gaskiya yayi KO dan su dan saba da juna
๐ณ๐ณ๐ณ๐ณ๐ณ๐ณ๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐ณ๐ณ๐ณ๐ณ๐ณ๐ณ๐ณ๐ณ
.
๐ณ๐ชBelles รฉcrivaines du Niger
*'YAR ๐ง๐ป*
*MAHAUKACIYA๐น*
*_Na SAJIDA_*
54
Tana zaunen nan falon tana waya da Hajiya Hawau Yar Mahaukaciya ta fito da kwaryar fura a hanunta ta sha damu sai kanshin kayan daka da cikwui take, cikin nutsuwa ta dan zauna har Hajiya fadimatu ta gama wayar
Ganinta ta karaso ya saka Hajiya Fadimatu fadin "toh Hajiya sai kin zo zuwa yamar, sanan kar fa ki daga hankalinki da sauki jikin"
Tana gamawa ta juyo da murmushin nan nata mai tsada ta kali Yar Mahaukaciya
Yar Mahaukaciya ta taso ta nufota ta ce" Mamana ga furar yayan nan na dama nasan zai sha"
Hajiya Fadimatu ta ce" Sanu da kokari Yar Fadimatu, aman tafi ki kai masa furar yana dakina"
Yar Mahaukaciya ta juya ba dan taso hakan ba dan kuwa tunda yayi hatsarin nan tamkar ya wani tsaneta ne KO baya ji idan tayi magana dan kuwa sai dai kawai ta ga yana hararanta
Cikin nutsuwa da faduwar gaban da bata san KO ta maicece ba ta tura dakin bakinta dauke da sallama ,
Idanuwa ta zaro ganin AA Mubasshir jingine da bed ya dafe zuciyarsa ya mike kafafuwansa yana kallon kasa sanan ga wani hawaye na bin fuskarsa , bata san lokacin da ta yar da kwaryar furar ta nufe shi har tana harde kafa
Tana isa ta dire gwuiwoyinta a kasa ta saka yatsarta ta lakato hawayen kuncinsa dan tabatarwa kanta kuka yake, cikin sarkakiyar murya ta ce" Yaya Mubasshir jikin ne? Ina ke yi maka ciwo? Ka sha maganinka? Dan Allah ka dena kuka, bara na kirawo Mamana"
Ta mike da niyar FITA ta kirawo Hajiya Fadimatu sai taji an riko mata hannunta riko ba na wasa ba , riko na keta da zafi sannan aka fisgota
Dabash ta zauna domin sauran kadan ta kifo a kansa Allah ya sota, ta shiga zazare ido tana tsoron abinda ya saka ya rike mata hanu haka sanan irin yanda ya hada fuska ka rantse cewar ba AA bane , gaba daya ya zama wani abin tsoro
Nunfashi ya ja ya sauke ya zuba mata ido yana ayana abubuwa da dama a ransa sannan ya bude bakinsa yayi iya kokarinsa wajen furtawa mai raya tinaninsa mugayen kalamai inda ya ce" *I hate you* "
Da Sauri Yar Mahaukaciya ta dago idanuwanta wa'inda suka fara canza launi sai hasken mai kama da na magen da ya fara fitowa ta zuba masa su
Hakan ba karamin karayar da shi yayi ba amman sam baya jin zai iya lamuncewa zuciyarsa abinda take so ya ci gaba da fadin" *Yes i hate you, na tsani na hadu da ke, na tsani na zauna tinaninki sanan rashin lafiyata ta dalilinki ne, ke ke din nan dai ke ba zawara ba aman kinfi zawara sanin hanunki dan har kin iya yanda zakiyi ki rikitar da maza, Abdul na sonki, Abdallah na sonki, jama'a da yawa na harin cewar suna sonki , Ni....ya ja nunfashi yaci gaba karyarki ta sha karya a kaina, Ni nafi karfin nace wai ina sonki abin ba dadin ji dan haka ina mai umartar ki da kiyi gagawar tsayar da daya a cikinsu wa'inda suka zubar da girman nasu na aura miki ki kara gaba dan kuwa bana son na ringa cin karo da ke a cikin gidan nan* "
Yar Mahaukaciya dake kalonsa cikin matsanancin faduwar gaba da tarin hawayen dake zuba daga idanuwanta ta ce" *Mai yasa ka tsaneni? Shin wani laifi na aikata?* "
Mubasshir ya kawar da kansa dan kuwa hawayen nan nata ji yake tamkar ya jawota jikinsa ya saka harshen sa ya lashe su sanan ya rukunkumeta dan kar Wanda ya kalan masa ita, yayi gagawar watsar da tinanin ya ce" *kwarai kuwa kina da laifi, kin fi kowa laifi ke laifinki yafi karfin na kawar da kaina kansa dan haka ki kiyayi abinda na fada miki* "
Yar Mahaukaciya ta Mike da kyar ta juya tana tafiya , har ta kusa fita ta juyo ta dawo inda duk takun tafiyarta bugawar zuciyar Mubasshir ne,
Tana dawowa ta tsuguna kanta a kasa ta ce" *shin tsanar da kayi min ta yan'uwantakar ce KO mai?*
Kwarai tambayar ta zo masa a bazata kuma sai a sanan y'a gane ilimi ne da ita , ya kawar da kansa cikin kame kame ya ce" *ai musulmi baya tsanar musulmi banza haka, ina yi miki son yan'uwantaka wanda koda Maman Mubasshir bata yarda da ke ba dalilinki na musulma zan taimaka miki aman banda wanan son ba wani* "
Yar Mahaukaciya ta kuma cewa " *Son soyaya ne na aure baka yi min?* "
Mubasshir ya gyada kansa da alamar gajiyawa da tambayoyinta
Da mamakinsa sai gani yayi ta saki murmushi ta ce" *Har ka bani tsoro yaya, daman ni? Wacece ni? Ilimin me gare ni? Mahaifiyata Mahaukaciya ni yar bola har nayi tsamanin soyaya daga namiji kamarka? Ta yi dariya irin da mamaki ta ci gaba" ai dan gata sai Yar Gata, i'a zan fadawa Abdallah idan da gaske yake ya fito inji yayana* "
Tana gama fadar haka ta mike tayi waje da gudu da alamar jin kunyar nan ,
Mubashir yayi gagawar rike daidai zuciyarsa yana sakin wata irin ajiyar zuciya tamkar yayi tsere, ya silale nan ya konta yana kalmar shahada domin a yanda zuciyarsa ke bugawa shi yasan kawai lokacinsa ne yayi, yasan kawai shi tashi ta kare domin bai san ciwon *So* ba, ta kafa masa wuka ta barshi da tsiyayar jini a kahon zuciya,
Toh fa AA ai gwara karka bige plz ku tayani da adu'ar kar ya tafi๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป
๐ณ๐ชBelles รฉcrivaines du Niger
*'YAR ๐ง๐ป*
*MAHAUKACIYA๐น*
*_Na SAJIDA_*
55
Tana fita d'akinta ta fad'a, ta ja ta rufe ta silale jikin kofar tana mai da numfashi, a hankali ta furta" *Ya Allah , kai kayi talaka kayi mai kud'i, kai kayi mai gata da marar gata, ALLAH da kai na dogara domin kaine gatana, Allah kayi min zab'i ba zabina ba, ALLAH ka zaba mini abinda yafi zama alkhairi a rayuwata, Ya Allah* " ta rintse idanuwanta hoton Bakin AA na furta mata kalmar *I HATE YOU* tayi Saurin bude idanuwanta ta mik'e tana fadin A'uzubilahi mina shaidanin'rajim ta fada bayi ta sakarwa kanta ruwa
Bayan sallar Magarib Yar Mahaukaciya ta sauko amsa Kiran Hajiya Fadimatu a falo, ta sha Riga da Zani na atamfa ta zaya mayafi ja tayi kyau tamkar Yar Tsana duk da ba wata kwaliya ta zana ba , tana isowa ta tsuguna ta gaishe da Hajiya Fadimatu
Hajiya Fadimatu ta amsa cikin sakin fuska sanan ta ce" Yar Fadimatu ana salama da ke ina jin Abdallah ne
Yar Mahaukaciya ta sine kai ta mike ba tare da ta amsawa Hajiya Fadimatu ba dan wani irin nauyinta da take ji, ta nufi kofa
Tana FITA Hajiya Fadimatu ta sauke ajiyar zuciya a fili ta ce" astaghfrullah ya Allah ka yafe min wanan abin da nayi , Allah ka san abinda ke zuciyata Allah ka shige min gaba, sanan ta kama hanyar dakinta
Tana shiga dakinta ta tarar da Mubasshir yana zaune saman darduma yana Jan carbi , a nitse ta nufi windown dakin ta bude madubin tana lekawa
Mubasshir dake zaune yana hailala yana neman sauki wajen Ubangijin sa yayi fatiya ya juyo yana kalon Mahaifiyarsa ya ce "Maman Mubasshir ina yini? "
Hajiya Fadimatu ta juyo da murmushinta ta ce " Lafiya lau Dan Fadimatu, kaga Mamarka da tsegumi KO? Ina kalon yata ne "
Mubasshir ya ce "Yarki?"
Hajiya Fadimatu ta ce" yes zance ake kaga yanda ta ja gefe tamkar Wanda take tsoron saurayin"
Mubasshir ya zaro ido bai san sanda ya ce" What? Zance ? Kuma ita da wa?
Hajiya Fadimatu tayi masa kalon lafiyarka? Domin tambayoyin nasa a jere sanan ya mike lokaci guda har mazari jikinsa yake ,
Da Sauri ya juya ya fada bayi yana tari ya kuna pampo ya sha ruwa da kyar tarin ya sake shi ya juyo ya fito, yana fitowa ya tarar da Hajiya Fadimatu tsaye hankalinta tashe ta ce" Son jikin ne?"
AA ya girgiza kansa da yake Sara masa ya nufi bed ya konta yana rinrintse ido
Hajiya Fadimatu ta bi bayansa ta dafa shi ta ce" KO mu tafi asibitin ne? "
Mubasshir ya girgiza kai sanan da kyar ya ce" maman Mubasshir ba komai karki damu"
Zata yi magana taji ana konkwasa dakin ta taso ta bude a tinaninta Yar Mahaukaciya ce sai ta ga Hajiya Hawau
Murmushi ta saki tana fadin" Hajiya barka da warhaka , sanan ta bata guri ta shige cikin dakin
Hajiya Hawau ta kali Hajiya Fadimatu ta ce" Hajiya da wa yar tawa ke zance ? KO dai shine sirikin namu?
Hajiya Fadimatu ta ce" shine kina gani sai wani kawar da kai take," ta karashe tana kokarin kawar da fuskarta gefe dan kar ya dagota
Hajiya Hawau ta ce" ai kuwa idan ya shirya ai sai ya fito kawai ayi da shi"
Mubasshir dake sauraron zancen su a ransa ya ce" tazo ganina ne KO tazo ta karasa ni, ? A fili kuwa da kyar ya samu ya tashi ya juyo yana kalon su ya ce" Barka da zuwa Hajaju"
Hajiya Hawau ta karasa tayi tamkar yanzu ta Ganshi ta ce" Dan Aljannah ya jikin?
Mubasshir ya ce" Jiki yayi sauki Alhamdulilah, daman ina son zuwa wajen ki sai gaki kin zo"
Hajiya Hawau ta gyara zama ta ce" toh bani na sha"
Ya dan furzar da iskar bakinsa cikin kawar da kai ya ce" *Abdul ya sameni kan zancen nazo na sameki ki fadan inda Rahma take yana son aurenta , plz ki taimaka ki fada masa na yarda da son da yake mata* "
Hajiya Hawau ta kali Hajiya Fadimatu itama ta kale ta irin kalon aikin banza din nan sanan ta ce" *Ai yata anyi mata miji sai dai kuyi hakuri* "
Irin kwaruwar ta dazu ya kuma yi wanan Karin yama kasa tashi balatana ya shiga bayin ya samu sasaucin kwaruwar da yayi ta hanyar shan ruwa,
Wasa wasa tari ya tirnike shi tun yana rike daidai zuciyarsa har ya saka yana kokarin faduwa,
Da gudu Hajiya Hawau tayi bayi ta dibo ruwa inda Hajiya Fadimatu ta zauna tana rike da shi suka bashi ruwan ya sha, suka kuma bashi ya sha yana ta ajiyar zuciya
Hajiya Fadimatu ta dora kansa saman cinyarta tana shafa bayansa a hankali ta kali Hajiya Hawau da ido tayi mata maganar da su kadai suka gane abinda suke nufi sanan cikin muryar nutsuwa da kontarwa mai sauraro hankali ta ce" *Ya zakayi kokarin boyewa Wanda ta dauki cikinka ta raine ka ta shayar da kai ta juri rigimarka ta ga girman ka damuwarka? Ya zakayi kokarin yin gardama da abinda na hango a kwayar idanuwanka? Shin ka manta alkawarin mu na bazaka boye min sirinka ba?* "
Mubasshir cikin Mutuwar jiki ya dago da kansa daga cinyar Hajiya Fadimatu gabansa na ci gaba da faduwa a ransa ya ce" Kardai Maman Mubasshir ta rigayi Mubasshir sanin abinda ke zuciyarsa? Kar dai Maman Mubasshir ta gane cewar Mubasshir ya kamu da son Yar Gidan Fadimatu? Son da yake kokarin zautar da shi? Kaunar da tayi masa shigar bazata?
Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta kawar da kanta ta ce" *Idanuwanka sun nuna tsantsar tsoro da fargabar abinda na karanta a tare da kai* "
Ta Juyo ta kama kafadunsa ta ce " *YA KAKE KOKARIN KASHE KANKA KAN HALALIN KA , IYALINKA, MATARKA? SHE IS UR WIFE MUBASSHIR* "
wani irin dum dum dum maganar ke yiwa Mubasshir a kunansa , wasu tambayoyi ya juyo yayi min Wanda nima nace AO๐คท๐ปโโ
Tambaya yake shin Maman Mubasshir ta kuwa san sunan wa ta kama tace matarsa? Shin ta gane KO wanene a gabanta? Idan ta gane yaushe aka aura masa ita? Yaya zai yi da Abdul amininsa? Yaya zaiyi da ita kanta Rahmar?????????????????????????????????muje zuwa ๐ฒ
๐ณ๐ชBelles รฉcrivaines du Niger
*'YAR ๐ง๐ป*
*MAHAUKACIYA๐น*
*_Na SAJIDA_*
56
adu'ar samun sasaucin kunci da tashin hankali
*ALLAHUMA, LA SAHLA ILLAMA JA'ALTAHU SAHLAN, WA'ANTA TAJ'ANUL HAZNA, IZA SHI'ITA SAHLA*
Hajiya Hawau ya tsurawa ido yaga itama shi take kalo, ya juyo ya kali mahaifiyarsa a fuskarta ya karanci sam ba wasa a cikin bayanin ta,
Wani lalatacen murmushi ya saka yana dan juya kai cikin muryar tausayi ya ce" Eyah maman Mubasshir ba fa ni nake nufi ba, ina nufin *ABDUL* yayan Sahla ne ke son Rahma fa, "
Hajiya Fadimatu ta ce" look son, Rahma matarka ce, taya zakana hada ta da wani kuma? "
Cikin wani yanayi ya juyo ya kale su ya ce" *ku yiwa Allah ku dena hada maganar nan cos ni kunuwana suna jiyo mini wani abin daban, Wanda kuma yake impossible, Rahma dake kofa tsaye tana zance da wani saurayin, gardi, Rahamar da aminina abokina yake matukar so, sai kuma kunuwana su