Showing 57001 words to 60000 words out of 60971 words

Chapter 20 - Yar mahaukaciya complete

SAJIDA   

08 Sep 2026

24

ba dai ke ki gaji da shi ba "

Sahla ta dan yatsina fuska dan tunda ta matsa maganin nan cikinta ke yi mata wani irin ciwo kokari ne dai kawai take dan Mahaifiyarta ta fada mata anfannin maganin yawa ne da shi , ita fa a gaskiya a yanzu tsoron mazan ma take tun karfinta cause Mubasshir tamkar machine yake shi dai burinsa ya ji sa a birnin nan Wanda jirgin sa mai wuyar sauka ne (😲). " tayi kwafa kasa kasa ta ce" Ashe dai ana gajiya da ita"

Fitowa ta kuma yi da wata Babar leda a hanunta tana kokarin gyara rikonta kwalabe ne a ciki na shan ruwa masu nauyin tsiya ga tsada ga kyau , sam bata lura da mutun a falon ba tana juyowa ta gamshi zaune yana kalonta , gabanta yayi wani mugun faduwa bata san lokacin da ta saki ledar ta fada mata a kafa ba ,

Ido suka rintse a tare dan kuwa yanda ta ji azabar faduwar wanan kofofin haka ya ji a jikin sa , , wani ihu ta saki na azaba da firgici domin ta firgita kwarai da ganin ba zatan da tayi masa a falo ga kuma faduwar wanan abubuwa masu masifar nauyi murafen su masu dan kaifi har daya ya yanke ta, wani wahalalan kuka ta saki gaba daya jikinta na rawa ..

Mikewa yayi cikin zafin nama ya isa wajen ta , yayi gagawar janye ledar ya cire Wanda ya dan yankun mata , yanda jikinta ke rawa haka NASA ke yi, cikin dauriya ya Mika hanu ya daukota cimak ya nufi Babar kujerar dake tsakar falon ya shinfida ta , sai wani kakauda kai yake

Wayarsa ya janyo yayi Kiran Umairah docter matar général kadre makociyarsu dan yanda take karkarwa sai yake jin tamkar wani abin ne ya shige mata kafar,

Minti sha biyar tsakani sai gata ta shigo ta karaso tana fadin "Oh yar gidan momynta ce ba lafiya? Oya cuta baki yi mana adalci ba "

Mubasshir ya dan Mike yana fada mata ga abinda ya faru,

Umairah tayi murmushi ta kama kafar ta Yar Mahaukaciya tana dubawa ba karaya ba gocewa , jin ciwon nan dai ne , hakan ya sa ta dauko compress ta goge mata da alcool ta rubuta mata amoxi ta mikawa AA sanan ta juya ta tafi ,

Mikewa tayi a hankali tana dan rintse idanuwanta ta mika hannu zata kuma daukar ledar ta je ta kaiwa Hajiya Fadimatu ,

Mubasshir ya zubawa kirjinta ido ta tsagogin dinkin nan, gabansa ya fadi yayi gagawar hadiyar wani yawu mai wuya , ya kuma zubawa dogon wuyanta da bayanta ido ba shiri ya kawar da kansa tun kafin ya bada kansa, cikin muryar tasa ta yana hanu ya ce" ina zaki je?"

Gaban Yar mahaukaciya ya Fadi ta dago tana kalonsa cikin gargadar murya ta ce" am daman mamana ce ta ce na kai mata wa'inan wajen amsan kayan Nadiya"

Ya juyo yayi mata kalon kinyi kadan ki fita sanan ya mike a nutse ya nufo ta,

Takunsa take ji sai ji tayi ya kure mata waje, a hankali ya Mika hanunsa daya ya dan rankwafa daidai wuyanta har lumfashin sa na sauka a saman wuyan ta ya kama zub dinta ya ....... ......................... ................ ........(😅😅 oh my Hawee kinyi shiru ki ji yayi mai da zub din KO? Har kin diro, to alhana bazan fada ba 😲🤒🤒🤒🤒💃💃💃💃)

🇳🇪BELLES écrivaines Nigériennes

👹 YAR MAHAUKACIYA👹 na SAJIDA



59

Lumfashinsa na sauka a saman wuyan ta, da gangan ya kara jawota kadan hakan ya Sakata jin bugawar zuciyarsa da Sauri da Sauri, Zip din ya kama da niyar ya ja shi ya rufe sauran wajen da bai rufe bayanta ba , hakan ya baiwa hancinsa damar sauke numfashinsa a kunnanta ,

Jin wanan bakon al'amarin ya saka jikin Yar Mahaukaciya mutuwa, gaba daya jikinta ya saka ta furta " *Wayo Allahna* " tayi luuuu zata fadi

Cikin mutuwar jikin shima ya tarota suka fada saman Babar kujerar, da Sauri ya mike yana kakabe jikinsa ya dan gyara tsayuwarsa ya saita muryarsa ya ce " Kai Bariki, idan mutun ya saba da abu hakane, na tabo miki wajen dake miki kaikayi KO? Yayi kwafa ya dan duko cikin rada rada ya ce " i'm sorry da na katse miki jin dadin ki dan ba kyau bin maza a waje may be ni kadai zan iya gamsar da ke , aman da alama sai nayi da gaske dan kin fiya zalama" yana gama fadar haka ya juya yana taka mattatakalar dakin ya nufi dakin mahaifiyarsa

Da kalo ta bi bayan sa har ya shige, nanauyar ajiyar zuciya ta sauke , tabas da da ne bazata damu da maganganunsa ba , a lokacin da idan ya yi su ma bata san inda suka dosa ba , sanan da a shekaran jiya ne ma ba zasu wani mugun damun ta ba cos ba'a fada mata cewar miji yake a gareta ba , aman a yau sai ta ji ba dadi, gaba daya sai ta ji ta muzanta, shin ina laifinta dan ta wayi gari ta tsinci kanta a bola? Menene laifinta dan ta rayu a cikin bola? Ta rintse ido a fili ta furta " *Shin mijina yana yi min kalon fasika ne?* ,

Lami dake tsugune tana maganna ta ce" na'am hajiya?

Yar Mahaukaciya tayi gagawar kallon ta , sannan ta ce" Au Lami kin fito?, kinga bara na saka hijab dina mu tafi mu kaiwa mamana nassan tana ta jira"

Lami ta ce" Ai hajiya Elhaj ya ce a fada miki karki fita, mu mu tafi mu kai kayan"

Yar Mahaukaciya ta ji zancen wani iri ta dago ta ce" Elhajin ne ya fadi haka?"

Lami ta amsata cikin biyaya

Yar Mahaukaciya ta ce " ohk tohm ki dauka ku kai mata , aman kar ku ce shi ya hana ni zuwa kunji? "

Lami ta ce" to Hajiyata a huta lafiya" suka dauki kayan suka tafi abinsu

Birgima take tana ihun cikinta , fitowa tayi daga bayi ta nufota da Sauri tana fadin Sahla ke kam akoy ragwonci , matsin maganin matan ne kike yiwa wanan ihun? To da a gabansa ne sai ya san abinda kika matsa KO? "

Sahla dake rusar kuka ta cusa hannunta kasanta ta shafo lemar da take ji na binta ta dagowa Hajiya Marhaba dan kuwa bakinta ya kasa magana bale har ta furta kalmar jinnin dake binta

Idannuwa Hajiya Marhaba ta zaro sannan ta juya da gudu tana ihun a zo a taimake ta dan ta kai Sahla Asibiti. ,

Bayan kamar awa uku likitici biyu maza suka fito da nurses sun hada gumi sosai , Hajiya Marhaba ta mike tana karkarwa ta nufe su ta ce" Ya jikin y'a ta docter?

Docter Aliyu yayi gagawar fadin ki biyo ni office dina , yayi gaba inda docter Usman ya bishi da kalo yana jin haushin wanan halaya na docter Aliyu Wanda a da bai san shi da su ba ,

Suna shiga ya ja kujera ya zauna inda Hajiya Marhaba ma ta nemi waje ta zauna tana sauraron sa cikin bugawar zuciya ,

Docter Aliyu ya ce" wa ya zubar mata? "

Hajiya Marhaba ta dago tana kalonsa da alamar tambaya ta ce" ban gane inda ka dosa bâ?"

Docter Aliyu yayi murmushin rainin hankali ya ce" cikin jikinta wa ya zubar mata?"

Hajiya Marhaba ta zabura tana dafe kirjinta ta ce " ci.....ciki????? Inalilahi wa'ina ilaihi raj'une, ciki ne da Sahla ? Kuma ya zube?"

Gaba daya cikin firgici take da tashin hankali dan KO an fada mata ba zata yarda cewar Sahla har ta dauko ciki ba , abinda suke nema tamkar ransu gashi sun samu kuma sun barar da shi garin a kara mata kokarin juriyar yawan sha'awar sa , wannan ai shine kaga samu ka ga rashi, ta kuma rushewa da kuka

Docter Aliyu yayi zuru yana son sanin kukan na mainene , can ya nisa ya ce " tana da aure ne?"

Hajiya Marhaba cikin share Hawaye ta ce" da aurenta mana"

Docter Aliyu cikin jin haushin Kenan ba zai samu kudin da ya hango ba zai samu ba ya ce" Toh dole sai mijinta ya zo wajen nan dan kuwa cikin mun gano cewar matsa wani abin ne akayi dan a zubar da shi, dan haka sai ya zo KO an kawo mana takardun da likita ya saka ayi hakan saboda lafiyarta"

Hajiya Marhaba ta zaro ido ta ce" uban mai mijinta zai yi a nan? Tap KO daya ai KO mai za'ayi ayi shi iya nan docter"

Docter Aliyu ya zuba mata ido shi daman da ganinta ya san ba gaskiya a al'amuran ta shi ya sa ya gano ci a tare da ita hakan ya sa ya gabatar mata da uzurin sa inda Hajiya Marhaba cikin karkarwar jiki ta biya masa muradinsa ta baro offishin sa cike da jin haushin kanta na asarorin da suka sameta a dan kankanin lokutan nan ( wannan Kenan)

Cikin bacinta take jiyo waya na ringin ta Mika hanu ta kashe kafin ta maida hannunta ta kuma kwasan kuka hakan ya sa ta Mike tana murza idannuwanta ta nufi kofa dan bude kofar shigowar,

Tana budewa idannuwanta suka sauka kan fuskar mutanen dake Dana cl din shigowa falon nasu , kirjinta ta dafe ta kurma ihu daidai da daukewar nunfashinta tayi baya yim ta fadi kass inda suka nufota cikin kidima da tashin hankali.................'''

Shin su wa Yar Mahaukaciya ta gani????????????????????????????????

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*Na*

*Sajida*

70

Adu'a suke tun karfin su, aman jikinsa sai kara daukan zafi yake,

Hajiya Fadimatu ta daga hannunsa ta saki hannun wani irin nauyi, tayi saurin kawar da kanta ta rintse idannuwanta gabanta na mugun faduwa

Yar mahaukaciya ta ce" mama Lafiya ? Ba alamun sauki ?

Hajiya Fadimatu ta tataro dukan KOkarinta ta ce" ba komai y'ar Fadimatu,

Yar Mahaukaciya ta ce" KO na Kira Yaya Idriss ne ?

Hajiya Rafi'at ta Gyada mata kai, hakan yasa ta ajiye kansa à hankali ta nufi wayar falon ta danawa ofice dinsa Kira domin ta san kawai yana ofice

Jin abinda ke faruwa ya saka shi barin Ofice dinsa ya kwaso yan kayan aikinsa ya nufi gidan su abokinsa domin ceto ransa

Yana zuwa ya tarar still sun dukufa sai adu'a suke masa zuwa lokacin Yar Mahaukaciya kam ta fara zubar da hawaye domin hannun sa baya KO karyuwa

Yana zuwa ya shiga tambayar abinda ya faru, inda hajiya Fadimatu ta fada masa komai na idan yayi irin haka harda na Karshe da yayi bai kai hakan ba

Idriss ya ce" Mama na karshen da yayi mai akai masa yaki yin nisa ?

saï à lokacin suka tuno jawabin mahaifin Fadimatul islam (Yar Mahaukaciya) kan idan hakan ta faru à tabatar da an saka shi à ruwan kankara sosai cikin ikon ALLAH zai kawo hankali

Nan ta kwashe ta fada masa yanda Elhaj Muhammad ya fada,

Idriss ya ce" to wankan za'a yi masa ai mama

Hajiya Fadimatu, Aunty Habiba, Hajiya Rafi'at da Islam gaba daya suka zuba masa ido suna kalon sa

Hajiya Fadimatu tayi karfin hali ta ce" wankan KO ? To ya zamu iya kai shi dakin ?

Idriss ya Mike gannin yanda duk suka wani tsure ya nufi kofa yayi Kiran securitiesn suka taho suka cicibi AA suka yi dakin Yar Mahaukaciya da shi inda ta Mike ta bi bayan su domin hada ruwan wankan

Baban bokici ta cika da kankara ta shiga bayin ta zagine tana sauyewa à cikin bahon wankan Daidai nan Hajiya Fadimatu ta shigo ta kama mata suka juye kankarar,

Suna gamawa su Idriss suka shigo da shi à talafe da dan gajeren Wando à jikinsa Yar Mahaukaciya tayi gagawar lafewa à bayan Hajiya Fadimatu , suka saka shi à cikin bahon ruwan da yayi mahaukacin sanyi

Suna saka shi securities suka juya suka fita inda su Hajiya Fadimatu ma suka yi niyar fitar dan barin Idriss da AA ya zuba masa ruwan à jikin sa

Idriss ya ce" Mama ku dakata ku matso mu yi masa tare

cikin sagewar gwuiwa suka juyo islam na biye da ita tamkar jela kanta à kasa suka shiga daban ruwan suna zuba masa har à cikin sumar kansa

Basu dau wani lokaci suna hakan ba ya ja wani dogon numfashi ya bude idanuwansa tamkar gauta dan ja à fuskar mahaifiyarsa domin ita kawai ya fara tozali

ido ya rintse yana Jin yanda kankarar nan ke ratsa masa jijiyoyin jikinsa, kokarin zama yake aman sulbin abin wankan ya hana shi,

Ya damki hannun mamansa ya kafe ta da ido saï ga hawaye wasu na korar wasu

hajiya Fadimatu ta kasa jurar ganin hawayen yaronta Bata san sanda ta jawo shi jikinta ba du da tsananin sanyin ruwan nan ta ce" Hasbunnalahu Wa ni'imal wakim, Ya Salam, shin yaushe dan Fadimatu zai daina daukan bacin rai da zapi haka ? Shin yaushe zai lazumci fadin Inalilahi Wa'ina ilaihir'raj'une à duk lokacin da yaji ransa ba Daidai ba ? Dan Fadimatu irin wannan zuciya ba'asan musulmi da ita, Tunda ka yarda da kalmar La'ila ha ilalahu MUHAMMADU'rasululah salalahu alaihi Wa Salam ka gama komai, Tunda ka yarda da shi kadai ya Isa yayi kuma shi kadai ya Isa ya hana mai yasa zaka kuma saka damuwar wani à ranka ? haba dan Fadimatu yanzu fa girma ya hau kanka, Dan mai bazaka gyara shi ba ?

Kalaman mahaifiyarsa na sauka à kunan sa tamkar warware masa kalmomin bakinsa ake cikin ikon ALLAH ya fashe da kuka mai tsanani ya kara rike mahaifiyarsa yana tunanin da mugun nufin su sahala ya kasance da an halaka masa mahaifiyarsa dan kuwa bazata juri hakan ba,

yana kuka tana hamdallar Jin muryar sa domin Bata sakawa ranta zata ji muryar sa a kusa kusan nan ba, hakan yasa ta barshi yayi mai isarsa sannan ya shiga ajiyar zuciya, du wannan abin bai lura da Idriss da Yar Mahaukaciya dake zaune dirshen à cikin bayi suna nasu hawayen ba

Cikin yanayin tausayi ta ce" fada min Wanda ya bata maka haka ?

AA ya lumshe Idannuwansa, da ace zai iya da ya boyewa mamarsa wannan lamarin, saï dai Ina bashida sama da ita, damuwarsa damuwarta ce, Dan haka ya bude bakinsa yana hawaye yana fada mata gaba daya abinda kunuwansa suka jiyo masa à gidan sa wato tataunawar Matarsa ta suna da Sirikarsa

Idriss dake saurare yafi kowa firgita inda ya rushe da kuka tamkar mace ya hada kansa da garun bayin ya shiga buga kansa da garun yana tir da halayen mahaifiyarsa da Kanwar sa

sai à lokacin AA ya lura da mutane à bayin bayan mahaifiyarsa, da sauri ya Mike ya nufi Idriss ya jawo shi da hanu guda ya ce " Idriss, baka da hankali ne ?

Idriss cikin kuka ya ce" banga anfanin rayuwata ba Mubasshir, Ba yau ba nake yiwa su mama à kan duniya aman abin har ya tsalake baiwar ALLAH (Hajiya hawau) ya fito kai ? Shin Mamana Bata kaunar saduwarta da rahamar ubangiji ne ? Ta raba d'a da mahaifiyarsa, ta kyamaci nakasasu, ta wulakanci talaka, yanzu tana kokarin halaka rayuwar jama'a da dama dan kudi?

why ?

Hajiya Fadimatu ta karaso gabansu ta ce" ya ku yayana ku saurara, ku kasance masu yiwa iyayen ku adu'ar alkhairi à duk halin da kuka tsince su, Idriss tsananin ka da mahaifiyarka adu'ar shiriya da ita da kanwar ka,

Ta juyo wajen AA ta ce" ka Sani da 1 ALLAH ya kawo ka har ka tsinci wannan tataunawar ya saka da Rahama, abinda nake SO da kai shine kayi ta adu'a ba dare ba rana à duk halin da ka tsinci kanka à ciki kan ALLAH yayi maka jagora, sannan idan ta baka karka sha, ta kali Idriss ta ce" Kayi hakuri Idriss kayi hakuri Haka Taka Kadarar take, yanzu Baban abinda ya dace muyi shine mu kwatanta musu cikin nutsuwa idan da halin kubutar su cikin ikon ALLAH zaku ga sun kubuta

Idriss ya sada kansa, shi yanzu wata irin kunyar su yake ji ya zaiyi da iyayen sa ne ? Ina zai saka ransa ?

Hajiya Fadimatu ta juya jikinta à matukar mace ta nufi waje tana mamakin wannan lamari

Yar mahaukaciya ma ta juya da sauri zata fita AA ya ce" Islam dakata

Cak ta tsaya tana kalon kasa inda Idriss ya juya à nitse ya silale daga bayin ya fito matatakalar benen ya zauna yana kalon kasa

Aunty Habiba Y'ar sokoto ta kali Hajiya Rafi'at ta ce " sister banga fitowar amarya ba fa, kar aikina ya koma baya, ta karashe tana murmushi

Hajiya Fadimatu da gaba daya jikinta yayi mata nauyi ta ce" au ai mantawa Nayi na barota à dakin, please sister tashi maza ki sauko min da ita domin yaron nan sai adu'a

Hajiya Rafi'at ta Mike tana murmushi ta nufi matatakalar benen tana hawa kunuwanta na jiyo mata sheshekar numfashi inda tayi tsai gabanta na faduwa tana son gane kukan waye ?



😳 Amarya à dakin ango😳, Idriss ma yana wajen, shin kukan waye ????????????? 😄😄😄😄😄😄😄🤒

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*Na*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login