Showing 42001 words to 45000 words out of 60971 words
ki ne yake jifanta da shi?
Hankalinta ya kai kololuwar tashi da ta ga harda Fadimatu a wajen Kenan ta ji abinda ya faru ? A fili ta furta ya salam
Hajiya Fadimatu ta matso tana kalonta fuskarta cike da tausayi idanuwanta jajir jikinta ba kwari a hankali ta furta" *Tafiyar ce?*
Yar Mahaukaciya ta kara sada kanta kasa tana ta zubar da hawaye
Hajiya Fadimatu ta kara matsowa ta dago Fuskar Yar Mahaukaciya ta ce " Rahma, ki dubi girman Allah ki fada min a mai kika daukeni? Matsayina a wajen ki
Yar Mahaukaciya ta sada idanuwanta ta ce " Ke uwa ce a wajena , Wace ta karbe ni ta kula da ni ina alfahari da ke sanan zanci gaba da yi miki adu'a duniya da kiyama
Hajiya Fadimatu ta jayota ta rungume ta tsam a jikinta , haka yar Mahaukaciya ma ta rungume ta tana kuka mai tsuma zuciya tana ji tamkar ta rungume Mahaukaciyarta ne a haka
Sun kusan minti uku a haka sanan ta saketa ta juyo wajen Mubasshir dake tsaye da kur'anin a hanun sa yayi Sakai yana kalon su , ta ce " Yarona , na yarda da abinda Rahma ta fada, tabas bata taba haihuwa ba , sanan kwarai ta taba yin rayuwar bola, kuma eh lale yawan tinanin da take yi harda kuka wani likacin na tinanin mahaifiyarta ne , haka zalika yarinyar nan bata sato dan kowa ba kaninta ne dan kuwa dan mi ake satar yayan mutane? Ai dan tsafi ne da kudi a gidan nan da gangan na sha zubar da kudi dan na gwadata ta wanan fanin aman KO gyara take sai dai ta dage ta share ta mayar koma ta gewaye, sanan kafi kowa sanin a yanzu tanada ilimin yin aiki da card dinka dake wajenta ta kwashi abinda taga dama tayi tafiyarta aman bata taba kawowa a tinaninta ba , a vidion nan nasha jin ta furta Mahaukaciya aman ban san inda ta nufa ba , na yarda da ita dan baka san rayuwar titi bace , duk tsafi , duk sanyi, duk ruwa a wajen nan a nan suke, ba KO tabarma bale ayi tinanin katifa, Allah kadai ya san irin warin da suke ciki sai su kansu, dan haka ni Mahaifiyarka na karbi Rahma da hanu bibiyu zan Rayu da ita a matsayin yata koda an samu mahaifiyarta sanan ni Fadimatu ni zan aurar da ita da yardar Allah a inda zata huta dan kuwa hutu shi yafi dacewa da yata..
Mubasshir dake tsaye shi ya rasa ma mai yake ji a cikin zuciyarsa, ya rasa ta inda zai fara fuskantar wanan damuwar taya zaiyi da rayuwarsa ne ?(😳), cikin sanyin jiki ya juya ba tare da ya tofa ufan ba ya shige motarsa ya kama hanya ya nufi gidansa
Yana zuwa yau bai KO leka mutanen nasa ba , ya fice direct sai dakinsa
Yana shiga ya ajiye kur'anin a gefen gadonsa ya tsuguna a nan ya saka hanunsa ya barbaza gashin kansa ya rufe idanuwansa cikin firgici ya bude ya mike da wata irin kara ya shiga watsi da kayan dakin yana fadin no , no ,no , Mubasshir kaifa ba mahaukaci bane , kaifa ba Mahaukaci bane , mai ya hadaka kuma da wanan? Tabas duk abinda ta fada gaskiya ne, to aman idan har gaskiyar Kenan ta boye wani abin , dan kuwa bazai yiwu ta ce wai ta zauna a gidan kato har tsawon sati daya wai ya bar mata gidan a nan kasar Nigeria? Wasu mazan da kamar su warto matan a gari shi
ya samu wanan santaleliyar a gidan sa shi ba ustaz ba ,ba komai ba kuma ya zuba mata ido? No wanan ai bazan yarda ba kawai ya ciyar da ita ne ita kuwa ta biya shi, ya kaiwa table din daki duka da hanunsa
Gabansa ya kara faduwa da ta tuna harda mace ta nemi ta nemeta wai ta gudu , a yanda ya san gidan nan da matakan tsaro ita ta isa ta gudu ba tare da an Ankara da ita ba ? No bazan shanye wanan ba , kawai ta yi abinda ake so da ita ne ta samu hanyar FITA, ya rufe idanuwansa wasu zafafan hawaye suka zubo masa daga idanuwansa Wanda rabon *Honorable AA Mubasshir* da ya zubda su har ya manta wai yau gashi yana zubar da su ya furta *Ludu* Kenan ???? Inalilahi wa'ina ilaihi raj'une ya silale nan kasa yana hawaye tun karfinsa yana fadin oh my god , Ya Allah ka kawo min dauki domin wanan ciwon yafi karfina , wanan ciwon bazan iya magancewa kaina shi ba , wanan ciwon ya zarce da tinanina ya fi karfin karfina
To fah shin wani ciWo ne wanan? Sanan maiye damuwar honorable da idan ma Yar Mahaukaciya ta gamu da abinda yake zato? Zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya ne , shin honorable ya manta da wanan ne???????????????
Happy juma'at daga Yar Buzuwa yar Mutan Niger Sajida❤❤❤❤❤
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
48
A nan kasa ya yasu cikin wani irin hali marar musaltuwa ance idan mutun na mawuyacin hali baya jin sha'awar komai aman yana rufe idanuwansa hotonta da rigar barcin nan ta fado masa a idanuwansa firgigit ya kuma bude idanuwansa yana maimaita A'uzubilahi mina shaidanin rajim yana rufe ido
Daidai nan *Sahla* ta shigo dakin da salamarta ganin AA a zaune a kasa ya sakata karasawa da Sauri tana fadin *Hubby* lafiya ?
*Mubasshir* ya dago kansa ya zuba mata idanuwa yana kalonta a ransa yayi hamdallah dan kuwa da bata zo din bama tabas da shi ya je ya fitar da abinda ke damunsa
Hanu ya Mika ya jawota nan kasan inda yake zaune ya shiga yamutsata da haushi haushi abin kamar hauka tun tana ganin zata iya jurewa har ta fara kuka tun karfinta daman abin da har a lokacin ta kasa sabawa da shi kulun sai ta jure ta kai zuciyarta nesa duk irin jarabarta gashi yau tamkar ba a hayacinsa yake ba
Shi kuwa gaba daya rikide masa tayi ta koma masa macen da yafi kyankyami a rayuwarsa sanan yafi bukatar kasancewa da ita hakan yasa ya zage yayi mata horo na abinda tayi masa ( tofa sowie Sahla) bashi ya barta ba sai da yayi mata jinajina ya kai sai ta ja nunfashinta da karfi take iya fitar da shi , ya Mike a hankali ya nufi bayi ya sakarwa kansa ruwa sai da ya jima kana ya fito ya taimakawa Sahla Wace take takawa tamkar sabuwar amarya
Yana gama shiryawa ya zauna saman gadonsa ya bude kur'anin Rahma inda ya karanta sunanta *Rahma Idriss* ya dauko biro ya goge sunan Idriss din ya fara rubuta *M* kuma sai ya rufe ya ajiye ya mike ya fice daga gidan GABA daya
Wasa wasa sai da Yar Mahaukaciya tayi jinyar sati guda a gida jinya mai kama da hutu domin har dan kiba ta kara jikinta yayi wani irin freich domin wani hadin sabulai da Hajiya Fadimatu ta hada mata da kanta ga manta da take shafawa mai kara sulbin fata da kuma sheki , Hajiya Fadimatu kanta da tayi yawon kasa kasa tana sarawa kyan Yar Mahaukaciya kuma tana ji a jikinta cewar Mahaukaciya Mahaifiyarta ba Mahaukaciya bace tun haihuwa dan kuwa alamu da yawa suna nuna hakan , kulun cikin adu'a suke Allah ya bayana ta a duk inda take .
Zaune take da wata doguwar riga baka mai duwatsu jajaye da fari a jikinta kanta ba dan kwali ta saka ribom ja ta daure shi ta buda litafinta tana bitar karatun da akayi bata nan
Salama aka yi daga kofar shigowa ta daga kanta ta amsa tare da mikewa tana dafa kirjinta
Wanda ya shigo shima hakan ya zaro ido ya shigo da Sauri yana fadin beautyna kece KO idanuwana ne?
Yar Mahaukaciya ta ce " Yaya Abdallah kaine?
Abdallah yayi wata dariyar Farin ciki daidai nan Hajiya Fadimatu ta fito tana fadin tamkar salama nake ji
Abdallah yayi Saurin tsugunawa yana gaisheta
Hajiya Fadimatu ta amsa cike da sakin fuska sanan ta ce " Kun san juna ne Yar Fadimatu?
Yar Mahaukaciya ta kaleta ta ce " Lah Mama ai shine Wanda ya kaini gidansa nayi sati a can din nan
Hajiya Fadimatu ta ce " kai masha Allah na gode sosai da irin rikon da kayiwa yata Allah ya saka da alkhairi
Abdallah ya kara sine kai yana Sosa kansa ya ce " aa mama ai yiwa kai ne
Bayan sun zauna Abdallah ya dubi Maman Mubasshir ya ce " Mama daman Karin albashi muka samu gaba daya mutanen kanfanin sanan ni an kara min matsayi shine nazo nayiwa elhaj din godiya dan ban san gidansa ba kuma a office din ma sunce yayi hani da aje gidansa ya ce idan ana neman sa a zo nan kuma sai Allah yayi na taki sa'a na tardo sister a nan
Hajiya Fadimatu ta ce" eh hakane kaga yarinyata ce kwanakin baya ta samu wata jarabawar ubangiji aman Allah ya tsawatarwa abin sai dai yarona kaninta bai rayu ba
Abdallah ya zaro ido yana fadin Allahu akhbar Allah ya jikansa da rahama
Hajiya Fadimatu ta ce" amin , ya Allah , aman matar taka tayi aure?
Abdallah yayi jim yace " ai mama itama ta rasu , hatsarin mota tayi sai tokarta aka bine
Yar Mahaukaciya ta zaro ido a tare suka furta inalilahi wa'ina ilaihi raj'une
Hajiya Fadimatu ta ce" haka ne rayuwa kowa da abunda zai zamto ajalinsa sai dai muyi fatan kyakyawan karshe da kuma samun rabo mai kyau a kiyama
Gaba daya suka amsa da amin ,
Suna tsaka da labari Mubasshir yayi salama dan kuwa rabonsa da gidan tun ranar da ya koma gida yayi tafiya Australi da niyar yayi wata aman hakan ya gagara Dole ya juyo ya dawo gida
Hajiya Fadimatu ta dago kanta tana fadin ga bakin Australi sun sauko
Abdallah ya Mike da Sauri yana fadin barka da zuwa Elhaj har yana dan risinawa ya Mika masa hanu dan girmamawa
Mubasshir ma ya Mika masa suka gaisa yana fadin kaine a gidan na Maman Mubasshir?
Abdallah ya ce " Eh wly Elhaj daman zuwa nayi na kara godiya ashe baka garin ma
Mubasshir ya ce" Haka , yau na dawo , no yiwa kaine ba komai
Abdallah ya kara risinawa yana fadin " to mama zan fice sai na dawo
Hajiya Fadimatu ta ce"" sanu da kokari a sauka lafiya Abdallah , ta dubi Yar Mahaukaciya dake kalon kasa ta ce " Yar Fadimatu tashi ki yiwa dan uwan naki rakiya KO?
Yar Mahaukaciya ta mike ta dauki dan kwalin rigarta ta yafa a kanta ta nufi kofa dan rakiyar Abdallah
Hajiya Fadimatu ta juyo bayan fitar Yar Mahaukaciya daga falon ta kali AA da yayi mutuwar zaune yana kalon kofar da ta bi ta fita yana tinanin sabon al'amarin nan , ita kuwa ina ta san shi? Meye hadinta da shi? KO shima yana cikin mutanenta ne ??????????????
Hajiya Fadimatu ta ce " baka jina ne ina magana?
Mubasdhir ya juyo yana kalonta ya ce " ina zuwa Maman Mubasshir nayi mantuwa a mota ya Mike ya fice har yana kokarin bige kyauran madubin dake falon
Yana FITA gabansa ya fadi hangota da yayi jingine jikin motar Abdallah ta rufe fuskarta tana murmushi
Wani irin dumdumdum yaji a ransa idanuwansa suka rufe ya fara ganin duhu duhu ya sauko daga matatakalar kofar dakin gadan gadan ya nufo su ya................
Muje zuwa taku ce Yar gidanku ce Sajida😘😘😘
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
49
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻hhh i'm sorry fans, i'm sorry na dawo
Yana isowa da alamar basarwa ya ce" au rakiyar bata kare ba?
Abdallah ya dan risina yana fadin
Ai ni na dan tsayar da ita Elhaj, yana fadi yana dan Sosa keya irin yaji kunyar sirikin nan
Mubasshir ya hadiye wani daci a ransa sukayi salama Abdallah ya shiga motarsa ya juya cike da murnar ganin Yar Mahaukaciya duk da bata bashi amanar zata iya soyaya da shi ba yana ji a jikinsa zata amince masa
Mai dinki ne?
Yar Mahaukaciya ta dago ta kali Mubasshir sai taga tamkar ba shine yayi maganar ba hakan yasa ta juya a hankali ta nufi ciki shi kuwa ya kasa tsayar da ita gudun raini
Yana dawowa ya zauna kusa da mahaifiyarsa ya ce " Maman Munasshir yarinyar nan ta fara zuwa makaranta ne?
Hajiya Fadatu ta ce" Wace yarinya kuma?
Mubasshir ya yatsina fuska ya ce " ta gidan nan
Hajiya Fadimatu ta girgiza kai ta ce" aa sai tomorrow l'a , please kirawota ma ka kaimin ita saloon dan saboda a gyara mata gashinta saboda school
Mubasshir ya dago kansa ya kali mahaifiyarsa bai san lokacin da bakinsa ya furta Yaya kyan kura bare tayi hauka?
Hajiya Fadimatu ta ce" mai kake nufi da hakanan?
Mubasshir ya ce " Maman Mubasshir manan ki dena cewa taje saloon kar aje a gamu da ita aje a fadawa su Abdul kinga wata matsalar ce
Hajuya Fadimatu ta girgiza kai ta ce " naji ba damuwa
Haka suka wuni tare har yama tayi ya nufi gidansa ba tare da ya kuma Sakata a idanuwansa ba
Yau ta kama litinin tun karfe bakwai da rabi ta gama shiryawa ta fito fes da ita , har bakin mota Hajiya Fadimatu tayi mata rakiya tana kara jadada mata cin abinci a kan lokaci sanan banda cin abu mai sanyi
Yar Mahaukaciya tayi murmushi ta rungume Hajiya Fadimatu ta ce" Mama karki damu zan kiyaye
Hajiya Fadimatu tayi murmushin itama tana kara gyara mata hijab dinta ta shige suka tafi
Tunda ta iso Fati ke murna haka sauran yan ajinsu banda princesses Wace gaba daya wani irin haushi ya turnuke ta na ganin kanwar AA ta dawo
Zaune yake cikin office dinsa , wayar sa ta dau kukan neman agaji , wanan Kiran na biyar ne hakan ya sa ya mika hanu ya daga
Daga dayan bangaren akayi salama
Mubasshir ya amsa yana fadin ya akayi ne kabir?
Kabir ya ce " Elhaj daman yau naga Hajiya ta dawo makaranta aman dalilin kokarinta aka canza mata aji aka mayar da ita ajin wanan saurayin dan gidan minister dake sonta , nayi nayi a maido ta sun kiya sun ce wajen yafi dacewa da ita , ni kuma sunki maida ni can din shine yasa nace bara na fada maka a san yanda za'ayi
Mubasshir ya ce " What? Shi din wanene shi? Dan ubansa na minister shine zai sota ?
Kabir ya ce " ayi Hakuri Elhaj yanzu haka ina zaune ina hangenta a ajin , shi kuwa ya dawo da kujerar sa kusanta sanan yau bata saka likaf ba
Ai Mubasshir bai san sanda ya kashe Kiran ba ya mike ya kwashi makulan motarsa ya nufi kofa KO sanar da su baiyi ba inda zai nufa
Tafe yake yana nanata Mubasshir Yar Amana ce a wajenka dan haka Dole kayi takatsantsan da al'amuran ta , bazai yiwu kana ji kana gani wani dan iska ya kara lalata mata tarbiya bayan ta titi daman da ta samu, Dole ka kawo canji a rayuwarta ka fada mata karta yarda ta kula KO wani saurayi kai zaka sama mata miji idan har bata iya zama sai da namijin a kusanta ( to kaji fa Mubasshir haka ta fada maka)
Haka yayi tayiwa kansa zance tamkar sabon kamu har ya iso makarantar su Yar Mahaukaciya
Masu tsaron kofar Makarantar kansu sunyi mamakin ganin AA da kansa a makarantar gashi ba wani abu ake ba balatana suyi tinanin an gayato shi ne , KO kanwar tasa dake makarantar ce ba lafiya KO wani Abin? Haka dai suka bude masa ya nufi ciki
Yana isa ya tsayar da motarsa ya fito cikin shigarsa ta alfarma ya nufi office din director din fuskarsa da glass na rana baki ,
Yana isa sau daya ya konkwasa
Director din ya amsa da com in
Mubasshir AA ya tura ya shiga yana kokarin zare gilas din idonsa
Director ya Mike da Sauri yana fadin "kai kai kai yau baki ne damu haka?
Mubasshir ya kale shi ya ce " Asalamu alaikum, i'm sorry director kafin mu gaisa ka fito ka fito min da sisterna daga ajin da aka kaita
Director ya kale shi ya ce" AA ni kasan na san mahaifinka kafin ya rasu , Nasan kai daya ya malaka, kuma mahaifiyarka bata kara aure ba , to taya ta zama kanwarka? Ni fa abin nan na daure min kai kuma kaga dokar makarantar nan fa AA ku da kanku kuka dorata bai dace daga kanku a samu wata matsalar ba fa
Jikin Mubasshir yayi sanyi tabas ya taka doka har biyu a wanan makarantar , ta farko ya saka an karbi Rahma ba tare da takardar haihuwarta ba , a zuwan dan kawai kwakwaluwarta ta bude sai na biyu ya kawo Wanda zai kula da dukan abinda take aikatawa a cikin makarantar a matsayin dalibi shima an yarje masa, to idan yaci gaba da haka za'a samu tangardar dokar
Director ya katse masa tinaninsa ya ce " Aman fa kayi hakuri AA daman dan a dan daidaita al'amarin ne dan