Showing 36001 words to 39000 words out of 60971 words
Muhammad ya dago kansa ya gama nazartar Hajiya Hawau tabas daga ganinta ka ga tsohuwa mai kamala , sai dai ba a nan gizo ke sakar ba , shin da gaske ne abinda ta fada ?
A nitse ya ce " baba tabas na gamsu da bayananki sai dai wani hanzari ba gudu ba ,mai zai nunan shedar eh lale yarinyar nan mutuniyar kirki ce? Sanan shi yaron nan baba jininki ne kuwa?
Hajiya Fadimatu ta dauko wayarta ta ciro wata memori ta jona jikin TV daram sai ga vidion Yar Mahaukaciya tun zuwanta gidan da yawancin maganarta harda idan tana tare da kawarta Fati , da komai sanan ta ce " Yaya ka yarda da maganata ka jagoranci daurin auren nan domin yarinyar nan yar Amana ce ceton rai zamu yi , Allah shi zai bamu ladan mu
Elhaj Muhammad ya aa numfashi ya sauke Sanan ya ce " toh babu damuwa Allah ya sa alkhairi ne , yanzu su liman din suna can dakin bakin KO?
Hajiya Hawau ta amsa da eh suna can
Ya ce " sunan yarinyar Rahma wa?
Hajiya Hawau ta ce " lokacin da tazo daidai da sunanta ta manta hakan ya sa mukayi duk yanda ya dace a musulunce muka saka mata Rahma
Elhaj Muhammad ya kuma kalonta shi dai yana dan kokonto aman bashi da wani iko a nan Dole ya aiwatar da umarnin hajiya fadimatu haka ya mike ya tafi wajen su liman din da niyar daura auren Rahma da agonta ..................................................................................🤷🏻♀🤷🏻♀🤷🏻♀🤷🏻♀🤷🏻♀🤷🏻♀🤷🏻♀
🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
41
Sun jima zaune sunyi shiru kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa jiran vilowar Elhaj Muhammad suke ,
Bayan kamar minti arba'in sai gashi ya shigo da damin goro a hanunsa yayi salama
Suka amsa masa a tare suna kalonsa
Waje ya samu ya zauna ya fuskance su ya ce " cikin ikon Allah an daura aure a gaban shedu sanan kuma ga goro na samu Kiran sarki na shaida masa ya ce eh aure taya shi ake Allah ya sanya alkhairi,
Hajiya Hawau ta ce" kana nufin *Rahma* ta zama matar *Dan Aljannah*?
Elhaj Muhammad ya ce " Kwarai kuwa ni na wakilce ta liman ishak ya wakilci Mubasshir Allah ya sa alkhairi aka hada
Hajiya Hawau ta ce " Alhamdulilah Allah abin godiya tabas alkhairi aka hada Allah ubangiji ya fi karfin su Allah ya kare duk wani mugun abin da za'a jefa dan a bata wanan taraya sanan Allah ya hada Hankalinsu
Hajiya Fadimatu ta amsa da Amin ya Allah
Haka suka gama suka tatara suka nufi gidan Hajiya fadimatu
Suna shiga suka tarar da Yar Mahaukaciya konce saman doguwar kujera tana bacinta , cikin nitsuwa Hajiya Hawau ta karasa ta tataro gashin kanta ta daidaita mata shi sanan ta dora mata dan kwalinta da ya fadi a hankali ta ce " ina ji a jikina ke Yar Halak ce, sanan ke ba mutuniyar banza bace , hakan yasa na gommaci ki auri bawan Allahn nan tun kafin su saka rayuwarsa a garari, jinina ne Idriss sai dai kash bashida mahaifiyar kirki , sam bai yi dace da uwa ba , haka yar uwarsa tayo halayar mahaifiyarta Wace ta raba soyayar da da uwa,
Ni na san Ilyasu baya cikin hankalinsa shi yasa nake yi masa uzuri Allah ya yaye masa abinda ke damun sa ya haskaka rayuwarsa, kema Allah ya baki hakuri da juriya kan rayuwar da zaki tsinci kanki nan gaba
Hajiya Fadimatu dake zaune tana kalon Hajiya Hawau tayi Murmushi ta ce " Baba tabas ance zamani ya canza kana iya haihuwar yaro ka kasa tankwasa shi , na sani ne bi'izinillah gata muka yiwa Mubasshir l'a zai gode mana kan hakan , aman fa ina neman wata alfarma
Hajiya Hawau ta kaleta ta ce" Alfarmarki KO maicece fada min ita insha Allah zanyi kokarin ganin na cika miki
Hajiya Fadimatu ta ce " bana son su san an aura musu juna nafi son na kara wanke yata ta goge da ilimi ta yanda zata kwaci kanta koda za'a cutar da ita, ina son yaronki da kansa ya nuna yana so dan kar yaga an bashi kyauta yayi kokarin banbanta darajarta da ta Sahla du da ita bazawara ce aman itama mutun ce so plz hajiya ki taya ni mu boye musu
Hajiya Hawau tayi shiru ta ce " to aman hajiya kar mu taka dokar musulunci fa , kar aje ta kula wasu samarin bayan ita ga mijinta
Hajiya Fadimatu ta ce " tabas wanan shi na fara tinawa aman kuma zan saka ido sosai a al'amuran ta , l'a komai zai tafi daidai
Habiya Hawau ta ce " Toh Allah ya kama mana
Sun kusan minti talatin sanan Yar Mahaukaciya dake sheka bacinta ta farka da adu'a a bakinta tana rike dan kwalinta dake kokarin koncewa ,
Ido ta zaro ganin Hajiya Hawau zaune , ta mitsika idanuwanta ai bata san lokacin da ta tashi da Sauri ta fada jikin Hajiya Hawau ta saki kuka ta rukunkumeta
Itama kukan take na yaushe gamo sai da Hajiya Fadimatu ta ce " ya isa hakanan sanan suka sasauta
Hajiya Hawau ta talafo fuskar Yar Mahaukaciya ta ce " kiyi hakuri yata , kiyi hakuri
Yar Mahaukaciya ta girgiza kai ta ce " Haba hajiyata ki dena bani hakuri kan laifin da ba naki ba sanan wly ni na yafe har cikin zuciyata ,
Hajiya Hawau tayi murmushi ta ce " Allah yayi miki albarka ,
Ta amsa da amin sanan ta juya wajen Hajiya Fadimatu ta ce " Mamana tun yaushe kika dawo? KO tare kuka zo?
Hajiya Fadimatu cikin murmushi ta ce " Mun dan jima da shigowa kina dan hutawa shi yasa naki na tashe ki dan na san halinki sarkin aiki ta karasa tana murmushi
Haka sukayi ta labarin su har yama tayi direban Hajiya Fadimatu ya mayar Da Hajiya Hawau gida cike da kewarsu Yar Mahaukaciya
Gidan Mubasshir ,
Zaune suke saman diner suna cin abinci Sahla ta sha ado sai zuba kamshi take tana iyayi shi kuwa gangar jikinsa kawai ke tare da ita aman zuciyarsa ta tafi aikinta tinani wata can daban
Sahla ta ce " konci tashi yau har munyi kwana biyar da aure , husby yaushe zaka kaini na ga momyna?
Mubasshir ya kaleta ya ce " au har kinyi kewar gidan ne?
Sahla tayi fari da idanuwanta ta ce " eh to ba sosai ba aman momyna nafi kewa
Mubasshir ya ce " Sahla ba fa mu kadai bane a cikin gidan nan
Sahla ta tsayar da cin abincinta ta ce" eh man husby akoy masu aiki KO?
Mubasshir ya ce " no banda masu aikin akoy iyayena a cikin gidan nan
Sahla ta ce wasu iyayen naka bayan Hajiya
Mubasshir ya kaleta a ransa ya ce *Hajiya* au bazata ce mata mama ba? A fili ya ce " eh banda maman Mubasshir inada iyaye da nake kyautatawa suna saka min albarka dan gamawa da duniya lafiya kuma ina son matata ta koyi halayana na kirki
Sahla ta dan yatsina fuska a ranta ta ce lale ma har wasu bare Kenan ka yayubo min a gida tabas zanyi août da koma su waye su , aman a fili ta ce " oh ohk toh kuma a wajen ina suke?
Yayi murmushi ganin yanda bata iya boye damuwarta ya ce " ai ki gama cin abincin sai mu tafi ki Gansu KO?
Sahla ta ce " ba damuwa
To fa Sahla shin kin sans abinda mijinki ke tanadar miki? ..........'
[
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
42
Bayan ta gama cin abincinta yana zaune saman baban kujerar tsakar falon yana kalon TV ta fito da wandon nata da rigar ta ce " mu tafi husby
Mubasshir ya dago kansa yana kalonta shi bai san ana konbo da rama ba sai a kan Sahla ya girgiza kansa ya mike ya dauko mata abaya baka da mayafinta ta karba ta saka tana yatsina suka kama hanya , ita dai burinta ta ga su waye a cikin gidanta
Tafiya ta kai ta minti goma da suka yi a tsakar gidan sanan suka ISO wani wajen mai shegen kyau , abinda ya bata mamaki yanayin ginin wajen ya fi nata kyau , haka dai ta zuba ido tana biye da shi har ya tura ya shiga da salama , ta biyo bayansa itama tana wara idanuwanta
Wata irin zabura tayi abinda idanuwanta suka gane mata , wasu tsafi ne yangom a zaune a saman cafet suna cin abinci wata tsanwar miya mai warin dadawa ta doki hancinta idanuwanta suka sauka a saman miyar gogo wace sam ba hakora a bakinta abincin ma sai ta dame shi sanan take iya hadiyewa ga bakin nata gaba daya ta jamula shi da miyar wata irin tashin zuciyar ba gyaira ba dalili ta tasowa Sahla da sauri ta saka hanunta ta toshe bakinta da hancinta ta zaro
ido ganin Mubasshir ya saka hanu yana sakawa wata tsohuwar abinci a bakinta sanan ya juyo ya nuno mata sahla , Abinka da tsafi aikuwa ta Mike da kyar tana fadin Yau ga matar Yaron mu har cikin gidan mu
Sahla ta shiga baya baya dan ta lura dukan su fama suke su taba mata jiki , bata Ankara ba taji wata ta taba ta tana juyowa ta ga Gogo ce ai bata san lokacin da ta saki ihu ba ta juya da gudu ta nufi bangarenta tana rusa kuka wiwi
Mubasshir ya zaro ido ya san a rina aman bai taba tinanin abin zai kai haka ba , wai a nan ta tardo su an kimtsa su ne , da irin kafin ya tafi aiki da yake biyowan nan ne da ta suma ma dan a lokacin suka farka wasu har kashi a nan suke yin kayansu dan kuwa tsafi ne sosai ya tara yake ciyarwa da shayarwa bisa yardar hukuma da saka hanunta harma masu gatan dan kuwa irin kulawar da yake basu tafi wace zasu samu a gidan nasu
Sai da ya zazaunar da su yayi Kiran masu kula da su sanan ya juya ya nufi bangarensa
Yana shiga kakarin amai ya fara ji ya girgiza kansa ya nufi dakinsa yayi konciyarsa ya dauki waya yayi Kiran mahaifiyarsa
Daidai lokacin suna zaune Hajiya Fadimatu na gyarawa Yar Mahaukaciya gashinta dan gobe zata fara zuwa makaranta wayar dakin tayi ringin
Yar Magaukaciya ta mike ta dauko dan wayar jikinta da doguwar waya Wace za'a iya janta
Hajiya Fadimatu ta ce" daga maga mu ji kowaye?
Yar Lahaukaciya ta daga ta yi salama
Daga dayan bangaren Mubasshir ya ja wani dogon nunfashi ya kasa amsa salamar muryar nan duk da sanin mahinmancin salama haka kawai ya tsinci kansa da wani irin yaunin baki
Yar Mahaukaciya ta ce " hello , heloooooooo?
Ta mikawa Hajiya Fadimatu tana fadin Mama ai ba'a magana KO an datse Kiran ne ban sani ba ?
Hajiya Fadimatu ta karbi wayar daga hanun Yar Mahaukaciya ta kara a kunanta tayi salama
Daga dayan bangaren Mubasshir ya amsa salamar a kasalance sanan ya ce " Maman Mubsshir ina yini
Hajiya Fadimatu ta saki murmushi dan ta gane ya kasa amsa salamar ne jin muryar Rahma , ta amsa gaisuwar sa sanan ta ce " lafiya nake jin muryar taka kamar maran lafiya?
Mubasshir ya shiga kame kame ya ce" am daman aa baci ne nake ji shine nayi kira nayi miki sai da safe
Hajiya Fadimatu ta ce " To Allah ya tashe mu lafiya , am daman insha Allah tomorrow yarinyata zata fara zuwa makarantar islamiyar fa
Mubasshir ya danyi Jim sanan ya ce " Maman mubasshir plz a kula da tsaronta direba ya ringa kaita yana jira har ta fito ya daukota ya dawo da ita saboda kinga ba'a so a san inda take , sanan malaman nasu mata ne kadai?
Hajiya Fadimatu ta ce " da mata da maza ne
Yayi Jim sanan ya ce " To maman Mubasshir plz ta kula
Hajiya Fadimatu ta ce " kai ni fa na haifeka zakana kokarin koyar da ni yanda zan kula da yata? Aman ai batayi baci ba KO na baka ita kayi mata hudubar?
Da Sauri ya ce " no maman Mubasshir kiyi hakuri ba haka nake nufi ba , love u , good night
Hajiya Fadimatu tayi Murmushi a ranta ta ce zama kayi nufin hakanan din aman a fili ta ce " ohk by a gaishe min da Sahlan ta datse Kiran
Mikewa yayi zaune daga koncen da yayi ya shiga kikifta idanuwa ya ce " Maman Mubasshir plz da hakuri kika yi KO wani irin malami take da bukata sai na dauko ya ringa koyar da ita saboda kar aje rana ta baci ldriss ya hadu da ita alura ta tono garma ( to fa ka tabatar dan haka kake gudun fitarta? )
Haka yayi ta tinane tinane hardai ya yanke shawarar da shi kadai ya san kayansa ya gyara konciyarsa yana adu'ar baci ya lumshe ido yana fatan zakara ya bashi sa'a 🤔
Karfe bakwai ta gama abinda ta saba sanan ta shiga wanka tana fitowa ta zauna ta shafa mai ta daga kayan makarantar tata ta islamiya doguwar riga ce har kasa sanan hijabi shima har kasa da nikaf na matan aure da budurwar dake bukatar saka shi
Ta saka rigar Kenan tana kokarin konce hijabin dan an daure shi ne da wata yar igiya wayar dakinta tayi kara ta matsa a hankali ta daga tare da salama
Hajiya fadimatu ta ce " yar Fadimatu sauko ina jiranki yanzu
Yar Mahaukaciya ta ce" to mama
Ta ajiye wayar ta sauko da hijabin dan Hajiya Fadimatu ta konce mata daurin tana zuwa ta tarar da Hajiya Fadimatun zaune tana zuba abinci cikin faranti , ta duka tana gaisheta
Hajiya Fadimatu ta amsa tana murmushi daidai nan aka turo kofar falon aka shigo
AA ne cikin wata dakakiyar shada fara kar sai zuba kamshi yake ya shigo da salamarsa
Hajiya Fadimatu ta zaro ido ta ce " lafiya da safiyarnan? Mai ya fito da kai yau? Ka manta al'adar mu ne?
Mubasshir ya karaso yana murmushi ya kama hanayen mahaifiyarsa ya ce" Maman mubasshir i really miss u , kinga abokina ya gayaceni yau shine na biyo na ganki kafin na fice
Hajiya Fadimatu ta ce " Kenan ka karya dokar?
Mubsshir ya ce " Maman Mubasshir Al'ada ba adini ba , kinfi kowa sani , so please ki bar maganar nan kiyi murnar ganina
Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta ce" to sanunka da zuwa
Yar Mahaukaciya dake tsugune ta ce" barka da safiya yaya
Mubasshir ya juyo ya zuba mata ido ba wata kwaliya tayi ba aman har wani fizga yanayinta yake, ya ce " Barkan ki
Yar Mahaukaciya ta Mike ta mikawa Hajiya Fadimatu hijabin na hanunta ta ce " Mama na kasa kunce wanan daurin gashi lokaci ya kusan yi
Mubasshir bai san ta ina maganar ta fito ba saï ji yayi bakinsa na fadin" halan wanan rigar da ita zaki tafi makarantar ?
Hajiya Fadimatu da Yar Mahaukaciya suka kale shi a tare , da tambaya a fuskar su
Sai a lokacin ya gane cewar yana fa son ya kwafsa kansa hakan yasa cikin basarwa ya dana wayarsa yana kalon kofa ya ce" am naga kamar tayi kadan ne , am manta ,
Ya mike yana fadin Maman Mubasshir tayi sauri dan hanyata ne na sauke ta sai na fice yayi waje yana karasa zancen
To fa Malan yayadai???????
[
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
43
Ya kai minti ashirin a zaune cikin mota yana jira , abinda bai taba yi ba a rayuwarsa wato zaman jiran mutun ya fito koma waye dan koda mahaifiyarsa zai fita ta san halinsa bata barin sa zaman jira dan kuwa yanzu zai fara shiga yana fita yana takurata da Maman Mubasshir ki fito plz, aman wai yau shine zaune yana jiran fitowar wanan yarinyar da ba komansa bace , haka kawai ya ja tsaki a fili ya ce " dan na kula da amanar da na daukowa kaina ne da ba dan hakan ba da ba Wanda zai fito da ni a yau daga gidana ,
Yana tsaka da mita ya hango fitowarta ya tsura mata ido nan da nan ya ji wani sanyin dadi na ratsa shi ganin hijabinta har kasa sai dai fuskarta a bude kuma da alama da nikaf a hanunta ,
Horn ya dana hakan ya sa ta nufi motar dan kuwa ita a tinaninta ai yayi tafiyarsa tana isa ta Buda baya ta shiga tana furta barka da warhaka Musa direba
Maganar ta tsaya mata a makogwaro sanadiyar hada idanuwa da suka yi ita da Dan Aljannah
Ido ta zaro tayi Saurin dora hanunta a saman bakinta tana kikifta ido ta ce " yaya yaya kayi hakuri nayi tinanin Musa ne yake yi min horn i'm sorry ta karasa tana kokarin bude motar ta