Showing 21001 words to 24000 words out of 60971 words
yaje yi wajenta ? KO dai asirin nawa ya karye? Kam akoy matsala ,
Ta juya ta dauko wayarta ta dana kira tayi ciki ta bar Sahla zaune tana dariyar cin galaba , sanan tayi kwafa tace" da naso na barki ki dan gana da danki aman tunda kika fifita wata bare a kaina ni da ke sai dai sheri ba dai khairi ba ( Allah ya shirya mana yayanmu )
Mubasshir ya jima tsaye bata fito ba kuma yaji tafiyar Aban Sahla hakan yasa ya juyo ya fito ya yiwa Hajiya salama ya nufi gidansu zuciyarsa cunkushe da abubuwa kala daban daban,
Yana shiga yaji sautin wakar larabawa hakan yasa cikin farin ciki ya dan kara Sauri ya isa baban falon mahaifiyarsa , ai kamar jira ake yana saka kafa yaji gaba daya an shiga watsa masa tirare , ta ko'ina wasu na fesawa sai hamdallah suke , daga gefe kuwa Ashe mawakiyar ce suka zo da ita takanas sai yi take tana juyin nan na larabawa,
Mubasshir ya sada kansa kasa da kyar yake iya cira kafarsa yana dana sanin zuwansa a wanan lokacin gashi suna kokarin rikita masa lisafi ,
Hajiya Fareedah ce ta taso ta kama hanunsa ta karaso da shi kusa da mahaifiyarsa ta ce" yarona an girma, Alhamdulilah yau har zan wankeka , Allah mai kyauta da kari ,Mubasshir ya zama ango
Mahaifiyar Mubasshir tayi murmushi da taga sai kawar da kai take , tasan baya son kida yayi yawa , baya son yawon hayaniya, inda ya sha banban da ita domin ita tana mugun son mutane tana son KO wani motsi zata yi ta jita kusa da mutane ,
Ta ce" nurul'ayne mai yake damunka?
Hajiya fareeda tayi caraf ta ce" ku shiga daga ciki mana sai ya fada miki aman a nan bazai yiwu ba tunda kinga akoy mutane da yawa
Mubasshir na jin an bashi damar tashi ya Mike yayi sama , ya nufi dakin mahaifiyarsa ya konta ya lumshe idanuwansa yana fadin wacece ita? ( wai mai ya shafeka malan 😏 )
Cikin nutsuwa ta turo kofar ta shiga da salama aman bai ma san ta shigo ba , ya lula duniyar tinani ,
A nitse ta ISO ta tsaya a kansa tana mamakin abinda yake saka Mubasshir cikin tashin hankali haka tana mamakin abinda ke saka shi tinani haka , KO yana tina mahaifinsa ne? KO taron nan da yayi yawa ne yake damunsa?
Ta kai minti ashirin a tsayen nan bai san tana wajen ba hakan yasa ta matsa ta zauna kusan sa ta dago kansa ta dora saman cinyarta ta ce" mai yake damun Mubasshir da har ya kasa fadawa mama?
Mubasshir ya dago kansa ya ce" maman Mubasshir al'amuranta na mugun daure min kai
Mahaifiyarsa ta ce" Al'amiran wa fa?
Sai a sanan ya Ankara da abinda yake fada ya dago idanuwansa da suka rine ya ce"""""""",,,,,,,,,,,""""""""""
[10/3, 13:50] Umar Dalha: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
28
Wani ma yayi rawa balatana dan makadi, sisterna rabin jikina , ke din ta daban ce , wanan babin gaba daya naki ne Madame Abdul Kader *Maman Imran* love u so much
Labari
Ya dade yana wanka dan saboda sai da ya shiga ruwan zapi sosai ya wanke harda kansa ya dauro banban towel ya fito , yana fitowa ya ga Maman sa ta ajiye masa kayan da zai saka da komai saman bed
A nitse ya zauna ya busar da gashin kansa uwa na mace dan santsi da shekin baki ,ya dauki mayukan gashi ya shafa
Shi da kansa yake nanade kansa ya saka macaji ya daidaita shi yana jin haushin saurin taruwar gashin kansa kawai sai ya aske ya huta, kuma sai ya fito
Cikin nutsuwa yayi shirinsa ya gama ya dauko kayan , yana dagawa yaga manyan kaya ne gari da yar ciki da hula sun sha wani mahaukacin zubi a jikinsu hular kanta wani irin aiki ne aka yi mata sosai ta hadu , abinka da mai son manyan kaya , yayi murmushi a fili ya ce " Maman Mubasshir Kenan
Su Idriss na suna ta labari suna dariya su uku daidai suma sun sha manyan kayan su sai anuri suke abinka da ranar fito na fito
Mubasshir ya sauko cikin takun kasaita tamkar dan Sarki daidai da takalmin kafarsa na shadar nan ne haka agogonsa mai zubi ya sha hularsa , yana ganin su ya saki murmushi
Nura ya ce " waouh , waouh , waouh , wata miyar sai a makota , wai dan Allah kaine kuwa?
Mubasshir ya Mika musu hanu daya bayan daya suna gaisawa sanan cikin murmushi ya ce " angoncewa ce
Idriss ya sha kunu ya ce " kai kasan gaban manya fa kake
Mubasshir ya ce " meye manya? Yana wata yatsina
Ramadan ya ce " ya ilahi sirikinka ne fa
Mubasshir ya mike yana fadin " kunga mu yanzu mun zama masu iyali ku tashi mu nufi gidan iyayena na gaisar da kakata sai iyayen matata a al'adar chadi
Suka Mike suna murmushi , fitowarsu keda wuya wanan mawakiyar ta larabawa ta kwasa sai koda Mubasshir take , dago kansa da zai yi ya hango gimbiya Mubinah yar gidan sarkin Makah cikin shiga ta alfarma ta zuba zinari da wani mahaukacin lesh fari gata fara sai daukan ido take ,
Suna fitowa ta mike ta nufo Mubasshir Wanda sai da gabansa ya fadi a ransa ya ce " ya akayi mai martaba ya BArTA ta biyo su mai girma Barhan?
Tana isowa ta rungume shi irin gaisuwar larabawan nan sanan daidai kunan sa ta rada masa " na zo na raka mijina gidan amaryarsa da tayi min shigar wuri kafin na shigo
Mubasshir ya dan saketa ya lakaci habarta yayi murmushi sanan ya juya wajen iyayensa yayi Saurin tsugunawa yana gaisar da su
Hajiya ta taso ta kama hanunsa ta daidaita masa hularsa ta ce " Alhamdulilah yarona ya girma , Allah ya kade baki ( kunsan larabawa suna mugun gudun baki shi yasa daga sunyi magana sai kaji sun ce Masha Allah , 😁 )
Haka sukayi ta saka masa Albarka sanan suka juya inda wasu motoci kwaya hudu a jere farare tas sai sheki suke , yau yau aka fitar da su da ka gani ka san an cashi kudi a nan ,
Karar tafiyar doki naji na waiga wani ne ya taho da dokina biyu yana jaye da su da irin runfar nan ana jaye da su , sai karar kacaukacau suke sun mahaukacin sha ado na zinari sai kara suke
Mubasshir ya juya ya sauke idanuwansa saman Mubinah dan kuwa ya san wanan aikinta ne ya gala mata harara dan ta sani sarai ya tsani hawa doki KO a can su biyu suke hawa KO da ita KO da wani a gefen sa ,
Tayi murmushi cikin harshen larabci ta ce" kar a yada al'ada ka sani sarai da a can ka yarda kayi aurenka da sai ka zaga gari a saman doki dan haka ya sa na shirya wanan KO ba komai ka girmama al'adar mai martaba uba a wajenka
Da haushi haushi ya taka ya hau itama aka kama mata ta dare tamkar itace amaryar ,motocin nan suka saka su a tsakiya , mai girma Barhan ya karaso ya rufa masa alkyaba aka cire masa hular aka rufa masa ta alkyabar nan dan kuwa haka al'adarsu take
Cikin nutsuwa suka kama hanyar gidan su Sahla
Hajiya Hawau ta sha dinkinta na shada ta hade harda kafa daurin dan kwalinta sun malaya manyan tabarmi a tsakar gidansu da kawayenta tsofafi sai labari ake ana shan fura mai cukui sai kanshi take ga dadi abinka da tsohuwar da ta san darajar baki duk Wanda ya shigo Yar Mahaukaciya da kawarta Fati sai su zuba furar a cikin kwarya da ludayi su Mika masa , suma sun sha dinkinsu na shada duk da ba wata kwaliya suka yi ba dalilin ainkin da suke yi
Suna tsaka da shan dariyarsu suka jiyo karar ganga da kuma muryar mace tana ta ISO da larabci tana wakarta , ga Wanda ya iya ya san dan gata ake wakewa ga Wanda bai iya ba kuwa sai dai ya gyada kai dan dadin wakar
Fati ta kama hanun Yar Mahaukaciya ta ce" kawata ai angwaye ne
Yar mahaukaciya ta ce" mai ya kawo angwaye nan kuma a yanzu?
Fati ta ce " oho o mu dai mu shirya tarban su
Hajiya Hawau ta fado kincin din ta ce" Ramatutu ai ga Dan Aljannah nan ya ISO da tawagarsa kinga wa'incan kwaryoyin masu zane su za'a dauko a zuba musu furar , aman ai ke kinsan yanda ake dama ta dan Aljannah dan haka a dauko duka cukuii din da nonon a dame musu yi maza yar Aljannah
Yar Magaukaciya tayi murmushi Ganin irin yanda Hajiya ta rikice ta ce " Hajiya ai na dame ta tun dazu Idriss ya ce a aa zuwan su duk da nayi zaton ko wasa yake mun dai dame kuma yanda kike sonta , aman ciki zasu shigo kinga baza a bar Dan Aljannahn ki a wajeba KO?
Hajiya ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Allah yayi miki Albarka bara na sauke su a baban falon , ku kuwa ku jera furar ku kawo musu
Ta juya tana kara daure dunkunkumin dan kwalin da ta dunkuma
Yar Mahaukaciya haka kawai ta tsinci kanta da tsoron hada ido da Dan Aljannah a wanan ranar , mutun a ranar da ba ta aurensa ba ma yana mugun daukan ido bare a yau?
Fati ta ce" Malama Hajiya garin kidima har kofina take ambato 😁
Yar Mahaukaciya ta ce" Dole Hajiya ta rikice dan kuwa dan gatanta ne
Haka suka dauko kwaryoyin suka kara darwaye su , gasu kananuwa masu shegen kyau da ludayinsu masu kyan gaske suka jere a saman wani baban faranti na silba mai shekin gaske , sanan suka ringa zuba furar nan suna saka ludayin a ciki , sai da suka gama
Yar Mahaukaciya ta ce " plz my kawali ki dauko na Dan Aljannah dan Allah
Fati ta zaro ido ta ce " mai kike nufi da hakan? Yayanki ne fa kuma kin sani sarai kar na fita na zubar garin kalonsa
Yar Mahaukaciya ta san sarai zata aika hakan yasa ta dauko wani farantin dan madaidaici ta zuba furar a wata kwaryar mai murfi sanan ta dauko ludayi ta dora a gefe ta dauko mushoir ( hankici ) sabo fil fari kar ta dora shima a gefe ta gyara komai
Fati dake kalonta ta ce" gaskiya al'adar Hajiyar gidan nan na mugun birgeni , koman ta daban ne sanan ta koyawa yar Jikanlen ta
Yar Mahaukaciya tayi dariya tana dora farantin Dan aljannah a gefen sauran furar ta ce " kama mu tafi malama kar suyi tafiyarsu
Suka kamo suka fito suna tafiya cikin nutsuwarsu suna fitowa kanshin ya daki hancinsu daga fatin Har Yar Mahaukaciya suka dago suka zubawa bakin dakin kalo
Idriss da dan Aljannah sun saka Hajiya a tsakiya ita kuwa sai washe hakora take daga gefe guda kuwa Mubinnah ce sai fifitu ake yi mata ta sha kyau har ta gaji, sai su Ramadan da Nurah a wata kujerar abin gwanin ban sha'awa
Fati ta juyo ta kali Yar Mahaukaciya Wace itama kamar ta fadi dan yanayin Mubasshir ya kidimata harda Idriss abin ya mugun haduwa kawai sai taji eh lale tana iya yin soyaya da shi dan kuwa ya mugun birgeta a yau
Fati kuwa ta kidime ta haukace ta ce" kawata kina ganin zinaria ce fa a jikinsu dan Allah ki duba ki ga irin yanda AA ya zama uwa Kwaï dan daukan ido
Yar Mahaukaciya cikin rada ta ce " ki nutsu mu basu juya tun kafin na kife a nan
Su duka suka dan saki murmushi sanan sukayi salama
Hajiya Hawau ta dago kanta ta amsa haka sauran jama'ar wajen
Cikin nutsuwa su Yar Mahaukaciya suka ajiye wanan farantin a saman table din dake ajiye a tsakar dakin sanan suka shiga dauka suna mikawa mutanen dakin , har sai sun duka har kasa su Mika musu hakan ba karamin birge hajiya Hawau da kuma su idriss yayi ba
🙆🏿
[10/3, 13:50] Umar Dalha: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
29
Fati ta dauko ta nufi Mubinnah tana isowa ta dan risina ta Mika mata da Sauri mai yi mata fifitar nan zata karba Mubasshir ya daka mata tsawa " cikin harshen larabci ya ce" idan anzo waje ana anfani da al'adar su ce sanan nan gidan sirikai na kuma iyayena ne dan haka kar a kawo min batanci kin gane ?
Da sauri ta risina tana fadin Allah ya huci ran Dan Gattahn Mai Martaba mafi soyuwa ga gimbiya Mubinnah
Mubinnah duk da bata ji dadin yanda ya sacewa kuyangarta gwuiwa aman bacin ransa yafi komai daga mata hankali hakan yasa ta mika hanu ta karbin wanan kwabin da bata san KO na menene ba ta dan gyara zamanta tana shawara da zuciyarta shin zata sha ne KO aa
Su dai KO a ransu , Yar Mahaukaciya ta dauko farantin Mubasshir har a lokacin bata gama yi masa kalo ba tayi niyar bazata yarda tayi masa kalon kurula ba ,
A nitse ta nufi wajen da tafi jin kanshin sa , itama Fati ta dauko na Idriss ta nufe shi
Yar Mahaukaciya na isawa ta tsuguna har Kasa ta dago hanayenta ta mikawa Mubasshir dan farantin mai kyan gaske
Mubasshir ya zuba mata ido dan gashinta daga gaba ya dan leko kadan sanan bakinta sai sheki yake na mai mai maski da ta dan goga ,
Maganar idriss ya dawo da shi inda yake fadin" Malan kaga Karka wahalarmin da mata mana ka karba plz karka rama a kanta
Firgogit yayi dan kuwa ya fada wata duniyar tinani ya Mika hanunsa wajen karba sai da hanayensu suka gogi juna , ita kuwa Allah Allah take ta bar wajen dan jikinta har karkarwa yake jin baranbaramar da Idriss ya afka mata a gaban Hajiya harda bakin kunya sai ma da taji Muryar Ramadan na fadin" au kace kaima taka a gidan take , gaskiya kunyi mana wayo , wanan wayo har ina ? Gaskiya muma a san yanda za'ayi da mu
Da Sauri Yar Mahaukaciya ta janye hanunta ta Mike da gudu tayi dakinta tana haki
Mubasshir da Idriss gaba dayansu da ido suka bita , Mubasshir yayi dan daman bai rike hanunta ba , ji irin yanda take gudu ana kalonta ( inada tambaya , ina ruwanka hon)
Shi kuwa Idriss wata irin faduwar gaba ce ta ziyarce shi ta haka kawai a ransa ya ce " wai a nan a cikin zulumbuwar riga take lale akoy aiki a gabana ( to kaji 😏 )
Hajiya ta katse dan shirun da ya gilma ta hanyar fadin " tayi maka kyau idrissu , nace tayi maka kyau ka firgita min ya
Yayi murmushi ya ce " haba kakus ya zamu zo ki hada mû da fura ?
Ta ce " to dan nema ita ce da ni ehe 😏
Mubasshir ya ce " kyale shi hajiyata ni kadai na san darajar wanan dan haka kowama kar ya sha idan yana so
Haka sukayi ta barkoncinsu har dai Sahla ta gaji da Kiran mamanta tana fadan sun shiga wajen tsohuwar nan sun makale kar ayi mata abinda ba shi ba
Sahla ta ce " mom kiyi Kiran Yaya Idriss plz
Hakan kuwa akayi ta dana kiransa daidai zasu shigo falon nata ,
Salamarsu ta saka ta katse kiran jama'ar dakin na amsawa
Marokiyar ta rangada guda ta kwashi kirari da kuma isowar angon auta wato Sahla
Cikin nutsuwa suka tsuguna gaba dayansu kasa suka shiga gaisar da Su Hajiya Marhaba da kawayenta
Hajiya Marhaba murna kamar mai ,
Suna tsaka da gaisawa wayarta ta fara ringin
Ta dauka sai taga sunan bokanta ne inda ta rubuta hajiya bokatu ,
Tayi murmushi ta Mike ta dan matsa kadan ta daga
Daga dayan bangaran ya ce " na gama aikinki na aikawa mijinki yanzu yanzu zai aikata abinda na saka shi tunda kince kina so a cikin jama'a yanda kowa zai ganta a rana yanda ba Wanda zai so ta rabe shi KO?
Hajiya Sahla ta ce " kwarai kuwa boka yanzu ne daidai dan kuwa gaba dayan mutanen da nake so su ganta a tozarce suna wajen nan so kawai ayi aiki na cika
Boka ya ce " karfa ki manta kudin ki mai yawa ne
Ta ce " kar ka manta aikinka mai kyau ne idan har yayi kyau din ai kuwa abinda zaka samu har sai ya fi wanan
Ya bushe da wata mahaukaciyar dariya ya e " to bunsura sai na jiki , ya datse Kiran
To fa , kaka kara kaka , shin waye za'a tozarta a cikin mutane? Waye za'a wulakanta har ma