Showing 54001 words to 57000 words out of 60971 words

Chapter 19 - Yar mahaukaciya complete

SAJIDA   

08 Sep 2026

22

rinka jiyo mini cewar matata ce? Ni ?* "

Hajiya Fadimatu ta mike cikin kakausar murya ta ce" *akoy wasa tsakanin uwa d'a da , sannan akoy zancen gaskiya, Ni Mahaifiyarka ni na samu alwalinka a matsayina na mahaifiyarka da kuma Hajiya Wace ta zamto sheda kuma ta bada amanarta muka yanke wanan hukuncin, ranar juma'a ya daura aurenka da shaidu a gidansa na nan, idan kana musu kayi Kiran sa, idan kuma baka yarda da hukuncina ba to ka watsa min kasa a ido* " ta karasa cikin yanayin bacin rai, dan a ganinta Mubasshir yama raina ta ne yana so yana basarwa

Mubasshir jikinsa yayi sanyi jin furucin mahaifiyarsa da yanayin bacin rai a tatare da ita duk dan shi, da Sauri ya karasa ya tsugunna kasa gabansa na faduwa ya kama kafafuwanta ya ce" Maman Mubasshir kiyi hakuri please, ba ina nufin ban yarda da maganarki bane, KO ban yarda da zabinki ba, no abin ne ya zo min a bazata, Dan Allah kiyi hakuri"

Hajiya Fadimatu ta sauke ajiyar zuciya ta kali Hajiya Hawau dake murmushin jin dadi, a nitse ta kamo shi ta dago shi suka koma bakin gadon , cikin nutsuwa ta ce" Dan Fadimatu, zaka yi min biyaya ka rike min yata tsakaninka da Allah?? "

A ransa ya ce tamkar yanda zan rike raina da mahinmanci , a fili kuwa yayi murmushi ya ce" Maman Mubasshir koda aljana ce kika aura min dole nayi biyaya ba zancen musu " ( ehem ) ya ce GABA da fadin " damuwata biyu ce Maman Mubasshir, Abokina da kuma ita yar taki"

Hajiya Hawau ta dafa kafadarsa ta ce" abokinka ba yanda ya iya domin matar mutun kabarinsa, sanan inada kwakwaran dalili na yin hakan, dan haka kayi fatan alkhairi kawai, "

Hajiya Fadimatu ta dora da " to aman mai yasa kace da y'a ta?"

Mubasshir ya dan kawar da kai yayi kokarin kauda kishinsa sanan ya ce" kinga hanzu ma fa da igiyar aurena tana zance Maman Mubasshir , kuma kina kalo kika barta "

Hajiya Fadimatu da murmushi ta ce " Gidan ku , ta je tayi zancen"

Hajiya Hawau ta ce" aa Hajiya baza'ayi haka ba , an soke zancen"

Mubasshir ya sauke ajiyar zuciya a nitse ya Mike ya nufi bayi ya kuna ruwa ya wanke fuskarsa ya dago kansa yana kalon miror, wani murmushi ya subuce masa a saman lebensa a hankali ya furta " *Matata ce* , ya lumshe ido yana kalon kasa , sanan ya kashe pampo ya fito a ransa yana fadin "wly idan bata shigo ba zan je na dawo da ita dan kuwa ba zai yiwu ba "

Yana fitowa ya tarar basa dakin, ya sauke ajiyar zuciya sai a lokacin ya samu ya nufi window ya bude yana ta hangawa, ajiyar zuciya ya sauke ganin basa nan, ya juyo a nitse ya tada Salah saman salaya dan ya kara godewa ubangijin sa da wanan kyautar da yayi masa ba tare da wayon sa KO tashin hankalin sa ba,

Tana shigowa ta tarar da su Hajiya Hawau zaune , direct jikin Hajiya Hawaun ta je ta lafe tana dora kanta a saman cinyarta

Hajiya Fadimatu ta ce" Yar Fadimatu bakon ya tafi?"

Yar Mahaukaciya ta dan sine kanta irin jin kunyar nan bata ce komai ba ,

Hajiya Hawau ta shafa kanta cikin nutsuwa ta ce" Yar Gidana muna son yin magana da ke" ,

Yar Mahaukaciya ta dago gabanta na faduwa , badan komai ba sai dan tsoron kar ace ta koma gidan su Abdul, don kuwa KO da anyiwa Sahla aure mahaifiyarta na nan shi ma Abdul din yanzu tsoronsa take .............

Hajiya Fadimatu ta gyara zama ta ce""""""""",,,,,,,,,,,,,"""""""""""

[truncated by WhatsApp]

ⅅᝪℂႮℳℰℕᝨ ℳᗅⅅℰ ℬℽ ᗅⅅℳⅈℕ ᗅℬⅅႮℒ

ⅅᝪℳⅈℕ ℳᗅⅈⅅᗅᗯᗅ Kᝪ ℍᗅⅅᗅ ℳᗅKႮ ℒᗅℬᗅℛⅈℕ KႮ ℤႮᗯᗅ ℙⅅℱ Kᝪ ⅅᝪℂႮℳℰℕᝨⅈℕℊ Kᝪ ՏᗅKᗅᗯᗅ ℒᗅℬᗅℛⅈℕ KႮ ՏℰℂႮℛⅈᝨℽ ℂᝪⅅℰ ᗅ Kⅈℛᗅ 07068808039

ℍᗅႮՏᗅ ℕᝪᏉℰℒՏ ՏᝪKᝪᝨᝪ:

ᗯℍᗅᝨՏᗅℙℙ ℕᝪ:

07068808039

ᗯℰℬՏⅈᝨℰ:

ᗅℬⅅႮℒℳKⅈℬᗅℬ.ℍℰᝣᗅᝨ.ℂᝪℳ

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

57

Hajiya Fadimatu ta gyara zama tayi gyaran murya ta ce" Yar Fadimatu shin na isa na sakaki abu kiyi , KO na hana ki ki guji yinsa?"

Yar Magaukaciya ta yi gaggawar daga kanta jikinta na rawa dan haka kawai ta tsinci faduwar gaba a tatare da ita ,

Hajiya Fadimatu ta kawar da kanta domin sai yanzu wani nauyin tunkarar Rahma da zancen nan ya darsu a zuciyarta , ta kuma juyowa daidai Lokacin da Mubasshir ke saukowa ya canza kayan jikinsa sai zuba kanshi yake ya fesa tiraren Hajiya Fadimatu , ja yayi ya dakata yana kalon su , shi kansa a yanzu gabansa faduwa yake bai san dalili ba ( zaka sani )

Hajiya Hawau ta ci gaba da fadin " shin kin dauke mu a matsayin iyaye? Wa'inda suka isa da ke , wa'inda zasu iya yanke hukunci dan inganta rayuwar ki? Wa'inda zasu guji ganin kin halaka sai inda karfin su ya kare? Shin a yau idan muka zo miki da wani hukunci da muka yanke a kanki zaki yarda da shi? "

Zuwa wanan lokacin Yar Mahaukaciya ta gama jika da gumi, domin KO ba komai ta san wanan zancen mai matukar mahinmanci ne, tabas wanan zancen mai mahinmanci ne tana rokon Allah ya sa alkhairi ne, idanuwanta ta dago wa'inda suka kara girma na tashin hankalin da ta shiga ta sauke su a fuskokin su hajiya , wani irin kwarjinin su ya daki kwayar idanuwanta da Sauri ta sada kanta kasa cikin gargadar murya ta ce" Mamana, hajiyata, iyayena, kun yanke hukunci a kaina shine kuma kuke yi min shawara? Wacece ni? No a duniya banda mahaifiyata sai ku gareni , kun isa da ni , Ko mai kuka yanke a kaina ni na san alkhairi na ne dan haka bani da musu KO ja da maganar ku"

Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyoyin su, kaunarta da Karin ganin darajarta da kunyarta suka darsu a zuciyoyin nan uku,

Hajiya Fadimatu ta sauke ajiyar zuciya da ido ta yiwa Hajiya Hawau nuni da ta fadawa Yar Mahaukaciya abinda suka yi ,

Hajiya Hawau ta kara gyara zama ta ce" *Daman ranar juma'ar can da ta shige aka daura miki aure ke da Dan Aljannah* "

Bugawar zuciyar Yar Mahaukaciya daidai da kiftawar idanuwanta, domin kwatakwata idanuwan ta kasa tsayar da su sai kikifta su take, jikinta gaba daya rawa yake, kafafuwanta dake tankwashe ta samu ta hau saman su ta yi tamkar zaman rakumi a hankali cikin rawar jiki ta dauko hanunta guda ta tokare habarta , hawaye wani na bin wani

Jikin Hajiya Fadimatu yayi sanyi, ta taso a nitse ta kamo Yar Mahaukaciya ta dora kanta a saman cinyar ta tana shafawa tana gyara mata gashin kanta da shi kansa ya jike wajen hudodin, har a lokacin jikinta rawa yake sanan bata furta komai ba,

Ta kai minti goma a haka , zuwa wanan lokacin shi kansa ji yake kafarsa ta kasa daukar sa, a hankali ya cire hular kansa ya jinginu da jikin abin hawa benen, ya dora hanunsa na dama daidai zuciyarsa yana irga bugawarta ,

Can kamar an tsikare ta ta zabura ta sauko kasa ta hada hanayenta biyu kamar ta zo neman gafara ta ce" *Mamana ki yi min rai, kar ki saka ya kore ni daga inuwarki, shi ya fada min da bakinsa cewar na fitar da miji cikin satin nan ya aurar da ni ya huta da gani na, yanzu idan ya ji cewar an aura masa ni ai har ya hadiyi zuciya ya mutu daman ba lafiya gare shi ba , dan Allah dan Annabi a kashe auren nan tun kafin ya ji ya kore ni mama Dan Allah, kinga sai Abdallahn yayi ya fito daman yanzu ya gama fadar hakan* " ta karashe zancen tana rushewa da kuka , ta mike da gudu ta nufi hanyar dakinta

Daidai zata hau ta ganshi nan tsaye gabanta ya yanke ya fadi ganin irin yanda yake da kyau haka gashi da alama fuskar sa tamkar ransa a bace, gabanta ya kuma yankewa ya fadi , a ranta ta furta *wutsiyar rakumi tayi kadan ta taba kasa*

Shi ma gabansa ya yanke ya fadi domin idanuwansa sai suka hango masa tsanarsa a kwayar idon Yar Mahaukaciya, nan take kalmar *I HATE YOU* da ya furta mata nan da yan awanni suka dawo masa , ya bi bayanta da kalo har ta shige dakin ta rufo

Hajiya Fadimatu ta mike da niyar bin bayan yarinyarta , Hajiya Hawau ta dakatar da ita ta ce" kar ki bita a yanzu, ki barta ta gama shawara da zuciyarta , "

Hajiya Fadimatu ta koma ta zauna jiki bâ kwari ta ce" tabas idan Yar Fadimatu ta ce bata son Dan Fadimatu zan raba auren nan , dan kuwa bazai yiwu ni da kaina na aurawa yar Amana abinda bata so,

Muryar Mubasshir suka tsinta yana fadin" *NO MAMAN MUBASSHIR BAZA'A RABA AUREN DA BA'A TARE SHI BA MA , BA KYAU* "

Hajiya Hawau da Hajiya Fadimatu suka zuba masa ido irin yanda jijiyoyin hannun sa suka mimike,

Hajiya Hawau ta kawar da kanta tana kokarin danne dariyarta dan kuwa da ka kali fuskar Mubasshir zaka karanto tsantsar tsoron kada a raba shi da abinda yake matukar so, ta kali Hajiya Fadimatu ta ce" *wanan aure mun hada shi ne da niya mai kyau, sanan shi aure raine da shi, kuma wanan karamin dalili ba zai saka mu raba auren nan ba saï da kwakwaran dalili, Rahma na cikin tsoro ne da fargabar yanda Dan Aljannah zai karbi maganar, bayan shi ban karanci tsanarsa a kalamanta ba, ki barsu su sasanta kansu ya nemi soyayar matarsa da kansa ki zira ido hakan shi zai kawo alkhairi ba wai a raba auren ba* "

Mubasshir ya gyada kai uwa shi ake fadawa ya ce " yawa Hajiya , ai shi kansa sakin ba kyau ana yinsa"

Hajiya Fadimatu ta zabga masa harara ta ce" ai Dole ka fadi haka bayan ka gama fada mata tayi ta fitar da miji kai ka gaji da ganinta KO? Kai ga dadynta, to sai kayi kokarin fahimtar da ita kaine mijin idan ba haka ba kuwa ,i'm sorry sai dai ka sakar min y'a "

Tana gama fadar haka ta Mike ta nufi kicin dan samawa Hajiya Hawau wani abin Marar nauyi ta ci...

Da ido suka bita sanan a tatare suka sauke ajiyar zuciya , Mubasshir ya kali Hajiya Hawau ya ce""""""""__,,,,,,,"""""""""""""""",,,,_______"""""""""""""

🇳🇪BELLES écrivaines Nigériennes

'YAR 👧🏻

MAHAUKACIYA👹 na



58

*Tabas soyaya ita ke sakawa a damu da mutun idan an ga shiru, idan na ce zan tsaya zano ku wly sai mu cika page din bamu gama bâ, Alhamdulilah Allah na gode da ka bani ikon rubutu tabas alkhairin rubutu shi na samu ba sharin sa ba, sisters godiya marar addadi , tsakanina da ku sai fatan alkhairi, daga taku yar Mutan Niger*

Mubasshir ya zubawa Hajiya Hawau ido , yana matukar son ya kara fada mata kar ta yarda Maman sa ta raba auren sa , aman ina ai da kunya KO ba komai kakar Sahla ce, Dole ya ji kunyar wani abin, Hakan ya sa ya Mike yana kokkarin FITA daga dakin dan bai ga ana marhabun da shi a cikin gidan ba

Cikin murmushi irin nasu na Manya ta ce" dawo ka zauna Dan aljannah,"

Mubasdhir ya juyo yana tafiya kansa a kassa ya dosanu ya zauna stil yana kalon kassa

Cikin nutsuwa ta ce" ni na jajirce da taimakon ubangiji aka daura maka aure da Marainiyar Allah,

Cikin firgicci ya dago yana kalon ta,

Hajiya Hawau ta ci gaba" kwarai kuwa , abinda ya saka ni aikata hakan dan ina tsoron aurawa wani yarinyar amanna ya cutar min da ita, tabas na san bazawarra ce aman idan kayi hakuri ta fi budurwar dadin zama ,"

Mubasshir ya kuma dagowa ya kara kalon ta a ransa ya ce " Ai fa ni ba dadin zamanta nake so ba, dan kuwa na sani Sahla ta FITA dan ta FITA kama kai,duk da haka ga yanda na same ta ballatana Wace ta waye a harkar? Ni kawai hutu na aura sai kuma ina dan tausaya mata,

Hajiya Hawau ta ce" ka bani amsa, shin zaka iya kular min da yarinyata? "

Mubasshir ya danyi murmushi ya ce " ai KO da ban sanki ba girman ki ya isa na girmama abinda kika hango ballatana na yarda da zabin ki, insha Allah zan yi kokarin adalci a tsakaninsu

Hajiya Hawau ta amsa sa cikin farin cikin girmamata da darajata da Dan Aljannah yayi

Bayan ta salamce salar walahar ta ta juyo a nitse ta karasa inda Gajiya Fadimatu ke zaune da abinci a cikin assiete tana jiran ta gama sallar, tsugunnawa tayi har kassa fuskarta da dan murmushi ta ce" Mamana ina kwana, an tashi lafiya? "

Wani sanyin dadi ne ya ratsa zuciyar Hajiya Fadimatu ta ajiye plat din abincin ta kamo Yar Mahaukaciya ta zaunar da ita saman bed din tana kalon ta, can ta ce" jiya kinyi baci baki ci abinci ba Yar Fadimatu,"

Yar Mahaukaciya tayi murmushi ta ce" kawai sai da na farka na ganni ina baci kuma sai tsoro ya Hanna ni FITA na debo abinci, "

Hajiya Fadimatu ta ce" Tsoron mai?"

Yar Mahaukaciya tayi gagawar dukar da kanta ta ce " ba komai mama"

Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta dago habar Yar Mahaukaciya ta ce" idan na ga auren nan cutuwa ne a gare ki believe me ba inda zai da izinin Allah, sanan a yanzu haka idan kika kafe kan bakya so zai sawake miki duk da shi din yana so"

Yar Mahaukaciya ta zaro idannuwanta bata san sanda ta ce " Yana so?

Hajiya Fadimatu ta ce " Yes, yana so"

Yar Mahaukaciya ta dan sadda kanta da matsanaiciyar kunya tana tir da wanan baki nata, a zuciyarta kuwa tasan wacece ita harda AA Mubasshir zai so auren ta? (Haka)

Mikewa Hajiya Fadimatu tayi ta bude werdrob din Yar Mahaukaciya ta ciro wata doguwar riga ta atamfa, rigar taji dinki daga sama ta matse sai ta bude daga kasa, da dan tsaga tsaga a sama daidai kirjin rigar sannan zub din bai hau har sama ba, hanun rigar daya dogo ne daya gajere , jar atamfa ce mai ratsin baki baki kalar fararen fata 😅🤷🏻‍♀,

Ta mikowa Yar Mahaukaciya dake zaune sannan ta ciro mata dan kwalin rigar ta miko mata ta ce" tashi Yar Fadimatu ki shirya mu tafi amsar kaya na nadiya nan makota,"

Yar Mahaukaciya ta dago atamfar, dinki ya hadu iya haduwa sai dai kunyar dinki ta saka ta kasa sakawa, sai dai a yanzu bazata taba iya musantawa Hajiya Fadimatu ba , Hakan ya sa ta dauka ta nufi gaban mirror dan ta dan gyara fuskar ta dan Hajiya bata son ta FITA bata saka kwali ba ,

Zama tayi ta yi dan adonta iya lips dinta da idanuwanta ta Mike ta dauki bras dinta ta saka ta saka pant dinta sannan ta dauko rigar har wani kara karan zub din take dan KO tafiya kake zub din na motsi suna Jan hankalin mutun, , cikin nutsuwa ta saka ta ja zub din sannan ta dauko dan abin hannunta baki siriri ta saka , ta dauko dan kwalinta zata daura Hajiya Fadimatu ta shigo tana fadin " Yar Fadimatu ki fito sai su dauko miki wa'inan bol din , hajiya Karima ce ta ce a zo mata da su saboda wajen mijin Nadiya gidan sarauta ne ita kuwa bata tanadi wanan ba , dan haka bara nayi gaba sai ki biyo ni da sauran

Yar Mahaukaciya ta ce " To mamana , ki bata kar ta manta"

Hajiya Fadimatu ta ajiye ta karbi bakin ribom din ta tatara gashin kan Yar Mahaukaciya ta hade waje guda ta saka mata ribom din sai gaba daya ya zubo ya rufe mata wajen da rigar bata rufe ba daga baya sanan ta dauko bololin ta nufi hanyar gidan Hajiya Karima makociyar su,

Bayan ta gama shiryawa ta dauko tirarukan dake saman table din dakin ta yiwa jikinta barin sa ta bude wajen takalman ta ta dauko wani plat mai igiya baki ta daura a kafafuwanta sannan ta fito cikin nutsuwa da mayafinta baki mai shara shara irin mai dan duwatsun nan tamkar sange ,

Cikin nutsuwa ta sauko direct ta nufi kicin tana kwalawa ma'aikatan gidan kira dan ta ga an fitar da kayan ita kawai suke jira

Da ido ya bita sauran kadan ya kware , yana waya da Sahla tana ta magiyar ya amsata yayi mata shiru , cikin sarkewar murya ya ce" Sahla ina zuwa ,"

Kafin ta bashi amsa ya katse Kiran ta kali mahaifiyarta dake zaune tana sauraron labarin nasu ta ce " Mama kinji fa ya kashe, ni gaskiya sai na kara kwana biyu na kara hutawa dan wly so yake ya kashe ni sam bai san gajiya ba a rayuwarsa "

Hajiya Marhaba ta ce " ai shiyasa na amso miki magungunan nan sai kiyi ta anfani da su yanzu haka Wanda kika matsan nan kinga dubu hamsin na siyo shi dan karfi ne da shi, sai dai yayi ya gama har ya gaji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login