Showing 18001 words to 21000 words out of 60971 words
caje Jakarta aka rage litatafan aka ware na ranar abinda zasu yi sai wani litafin aka saka mata dan saboda karatun da zata ringa dauka da wasu malaman bayan aji .
❤
🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
20
Haka Yar Mahaukaciya ta shiga cikin makarantar ta nufi office din da aka nuna mata taje ta ja ta tsaya ta shiga rapka salama ta kai wajen minti biyar a nan a tsaye sai da wani dalibi ya zo ya dana wani jan abu sai taga kofar ta bude ya shige ta kwalalo ido tana nan tsaye ya fito yayi tafiyarsa ta lumshe ido tayi bismillah hanunta na karkarwa ta dana jan abun kofar ta ce wani guiui ta bude ai uwa an hankadata ta fada sai zazare ido take tana kifkif da ido
Mutumin dake zaune ya hakimce da shigar manyan kaya a jikinsa gefensa kuwa da wasu mutane sai dadana computer suke gaba kadan da shi kuma jerin wasu mutanen ne suna observing dalibai a computer ita dai tayi tsai tana kalon su yayi gyaran murya ya mika mata hanu da nufin ta bashi takardarta Wace idan tazo zata gabatar a kaita aji a nuna mata komai
Ai gaba daya takardun hanun nata da litatafen da jakar ta ajiye masa saman table din nasa na glass ta ce" wly sun caje ni kosan ma yaya ya juya da shi KO karyawa banyi ba
Nan da nan suka shiga kalon juna , banban na zaune Wanda ke hakimce ya ce" ur name?
Yar Mahaukaciya tayi Kifkif da ido tana kalonsa fuskarta bayane da tsoro kafin tayi magana téléphone din saman table din yayi ringin ya Mika hanu ya daga
Daga dayan bangaren ya ce " tazo KO?
Abdallah mai kula da makarantar ya ce" aa dalibai dai suna ta shigowa har yanzu bamu ga mai sunanta ba aman ga wata tsaye inajin bata iya turanci ba ma
Mubasshir ya ce" what? Na fada maka yar gidana ce kuma akoy abinda ya tsayar da ita ba'a kula da karatunta ba kayi mata hausa idan tazo shine zakana cewa baka sani ba ? Look idan kaga bazaku kula kan karatunta ba na tura a dauko mini ita , karatu KO a Wace kasa take so sai na kaita kuma KO wani kalar malami sai na sama mata ya koyar da ita
Abdallah ya ce " kayi hakuri abin du bai kai nan ba yaya sunanta ne?
Mubasshir ya zaro ido yayi Saurin rufe kan wayar ya kali idriss da ya saka shi a gaba kan a kula kar su banzatar da ita ya ce" kai sunanta fa?
Idriss ya dane dariyarsa ya ce" *RAHAMA IDRISS*
Mubasshir ya yatsina fuska ya kara a kunan sa ya ce" Rahama idriss
Abdallah ya tambayi Yar Mahaukaciya dake tsaye da hausa ya ce" kece Rahama Idriss?
Da Sauri ta gyada kanta ta ce " eh Nice
Abdallah ya ce" sir itace a kara hakuri zata samu kyakyawar kulawa
Mubasshir ya ce " ohk thx ya datse Kiran
Abdallah da kansa ya mike ya raka Yar Mahaukaciya aji Sanan yayiwa malamin bayanin idan ya gama ya nuna mata office din hajiya Amina , ya juya ita kuma ta samu waje ta zauna ta shiga kalon Malan yana ta gwaranci toh gwaranci mana domin ita dai ba abinda take ganewa a cikin abubuwan da yake fada tana dai kalonsa har ya gama ya kaita wajen Hajiya Amina inda ta kwashe awa uku tana koya mata A B C D ......Z, sanan taje wajen cin abinci inda ta sha mamaki kamar ba a cikin makarantar yake ba kuma gaba daya sai daukan ido wajen yake nan taga manya manyan yan mata da samari kowa yana harkokinsa wasu suna ta selfi wasu suna buga gem , wasu suna ta labari, wasu suna zance, wasu kuwa suna jiran abincin su kai wajen ba dai tsaruwa ba ,
Cikin tsoro ta nufi wani table mai shegen kyau Wanda taga ba kowa samansa sanan harda wani rubutu a farar takarda ta nemi waje tayi zamanta da bismillah tana dan yarfe hanunta domin ba komai a hanun ta mugun gaji ne da rubuta A B C din nan , tana zama bata ma gama hutawa ba taji muryar wata cikin turanci na fadin tayi ta tashi ga princess nan zuwa table dinta ne ,
Abinka da Wanda bata san mai take cewa ba kawai sai ta dan sakin mata murmushi ta waiga dan taga inda zata kai katin ta a zuba mata abinci ta ci ta koma masalaci ,
Bata Ankara ba sai ji tayi an daki table din ta dago kanta da sauri tana kalon wace ta buga table din , wangalau tayi da idanuwanta tana kalonta batada KO dan kwali a kanta ta sha kananan kitso na atash sun mugun yi mata kyau , ta kara girar ido sunyi zako zako ta sha lips dinta mai sheki gwanin kyau gata fara kar ta budi baki cikin turanci ta ce " ke yar gidan uban waye harda zaki zo ki dora tsumakaran duwaiwanki a saman kujerarr da ni nake zama?
Yar Mahaukaciya bata kauce idanuwanta daga kalonta da take ba ita mamaki take Kenan ana zuwa makarantar babu hijabi KO dan kwali?
Ita kuwa ganin kalon da take yi mata da idanuwanta kamar na mage kuma ta ki yi mata magana yasa cikin zafin rai ta saka hanu ta ja hijabin Yar Mahaukaciya tana fadin shegiya mai acuci bari na tona miki asirin abinda kike boyewa a hijabin yanzu haka wani kurji ne da ke daidai lokacin gaba daya daliban wajen sunyi ca suna kalonta dan kowa yasanta da rashin mutunci yar gidan embasader ce table dinta ba mai zama mutun daya take shayi shi kuwa yayi kwana uku bai zo makarantar ba shi yasa take taka rawarta yanda take so a makarantar, kuma taga bakuwar fuskar nan tana kokarin kawo mata raini dole tayi maganinta
Da karfi ta idasa Jan hijabin Yar Mahaukaciya harda ribom din da ta daure kanta da shi ya biyo hijabin gaba daya gashinta ya barbazu har gadon bayanta cikin gigita ta Mike tsaye ai kaf wajen suka kwashi waouh domin sai da ta Mike dirinta ya fito ita kuwa baiwar Allah kokarin ganin ta kame kanta take suna tsaka da wanan rigimar chef din cafetariar ta fito itama ta sha ado da masarar Riga a daure a tsatsonta ta fito cikin turanci tana tambayar mai yake faruwa?
Princess da gaba daya jikinta yayi sanyi domin sai da ta raina kanta duk irin tarin adon nan da ta sha kuwa sai taga tamkar wata banza a Yar Mahaukaciya ga kalar gashinta kalar blonde kuma gashinta ne ba atash bane ga tsahi da gareshi ga shegen santsi ga yanayin jikinta da ka ganta ka san daga gidan hutu ta fito ,
Wani daga cikin daliban ya ce" aunty wanan mai kyau ce ta zauna a table din princesses shine princesses take fada
Aunty ta kali Yar Mahaukaciya ta ce" ina katin ki yarinya ?
Yar Mahaukaciya jin an ce kati ta gane na cin abincinta ake tambaya ta juya nan kasa inda ya fadi ta dauko ta mikawa Auntyn ,
Aunty ta zaro ido ta ce" kai princesses kin san da wa kike magana kuwa? Kinsan du wanan gyaran da muke tunda safe na tarbanta ne ? Kinsan KO yar gidan wacece?
Gaba daya suka bada hankalinsu wajenta har Yar Mahaukaciya domin yanzun da Hausa tayi magana don kuwa ta tsorata kar wanan yar masefar princesses din ta ja musu asara dan an hau shegen table dinta , ita kuwa yar mahaukaciya tambayar kanta take to ita kuwa Yar gidan waye harda za'a yiwa yar gidan ambasader fada dan ta taka ta ???
Nima ina son sanin amsar wanan tambayar???????????????????????????????????
🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
23
Tunda garin Allah ya waye jama'a ke kai kawo manya manyan mata masu ji da kansu kawayen Hajiya Marhaba , tayi wanan gayar ne dan kawai a tsayar da shagulgulan da za'ayi mawakan da za'a dauko har na wajen diner , da sauransu
Sahla ce ta fito daga dakinta tana waya , Hajiya Marhaba ta ce" beby ina kuma zaki je haka?
Sahla ta juyo ta ce" mom zan je na zabo kalar Wanda zan dora , tayi kirana ta ce ta kawo su jiya
Hajiya Marhaba ta ce " Ohk karfa ki yarda ki jima, sanan ki san da kinyi lulubi saboda kin san ya hane ki fita so ki kula
Sahla ta amsa mata tayi gaba abinta
Idriss ya dago kansa ya kali mahaifinsa ya ce" ina yaro ban taba ganin mutun mai biyayar iyaye kamar ka ba abanah, aman tunda na kawo shekara goma sha uku a duniya sai naga ka fara janyewa da Hajiya , Abanah karka manta Hajiya kai kadai gareta danginku duk babu, Abanah yar uwarta daya ba mai aure a nan bace bata da labarinta ma , shin Abanah idan ka samu dan lokaci na ka zauna kadan da kakata bazaka je ka gaisheta ba ? Tana matukar nisa rashinka a cikin zuciyarta kuma nasan bata barci Haba Babana karka manta fadar Allah ce mu maza mu bi iyayenmu matayenmu kuwa su bimu dan samun tsira a gobe kiyama, a kulun idan muka zauna da ita sai na bata hakuri sai tayi murmushi ta ce ba komai , ya hade hanayensa ya ce" kayi min rai Abanah ka gyara koma meye tsakaninka da Hajiya ka koyar da mu kulawa da tamu mahaifiyar 😌
Mahaifin Idriss , Ilyas ya kare masa kalo gaba daya jikinsa ba kwari ya ce " Idriss please tashi ka bani guri ina bukatar tinani
Idriss ya mike yana adu'ar Allah ya sa mahaifin sa ya gane
Bayan fitar Idriss Elhaj Ilyas ya mike ya har wani juwa yake yana mamakin kansa, mai yake sha'afar da shi da mahaifiyarsa? Yaushe rabonsa da ya kai mata abinci ya zauna ya bata ta ci yana yi mata hira? Mai ke damunsa? Cikin Sauri ya juya daga office dinsa ya shiga motarsa ya nufi gida , yana zuwa ya bar motar a kofar gida gudun kar Marhaba ta Ganshi ya dawo yanzu
Cikin Sauri ya fada bangaren Mahaifiyar sa , sai da ya lumshe ido domin Hajiya ba dai kanshi ba , kulun cikin zambada tiraren huta take na hayaki kalakala , ga tsakar gidanta sai ka yarda Abu ka dauka ka cinye, kai ba dai tsafta ba Allah ya bata abinta ,
Cikin faduwar gaba yake takawa a hankali yana dosar dakin bugun zuciyarsa na tsananta , kuma wani bangare na zuciyarsa na korarsa ya rasa meye wanan, aman a yau kaunar ya ga Hajiya ta rinjayi kin ya ganta,
Sautin dariyarta ya tsinkaya tana fadin" kai aman akoy aiki kwabin fulawa wajen yan mata kadai ta isa ta saka bawa ciwon ciki dan dariya
Yar Mahaukaciya da ta takarkare zaune a saman tabarma ta saka Roba baba tana kwaba fulawar da zasu yi fanke na mutanen hajiya tunda Hajiya ta zuba mata kilo biyu ta kasa kwabeta sai nishi take ita kuwa Hajiya ta ce ai kuwa sai ta koya
Salama yayi inda cikin zabura Hajiya ta dago kanta ta zubawa fuskar gudan jininta ido , kasa amsa salamar tasa tayi dan tsananin mamaki ,
Suna yin ido hudu ya dauki sauki ya je da Sauri ya tsuguna ya dora kansa saman ciyoyinta ya rike kafafuwanta daga kasa ya saki kuka kamar karamin yaro
Yar Mahaukaciya dake zaune ta waigo ta zaro ido , tunda tazo gidan nan yau kadai Allah ya taba hadata da mahaifin Idriss daga kamar ta gane cewar mahaifinsa ne , da Sauri ta Mike ta basu waje
Ya kusan minti goma yana ta kuka a saman cinyar Hajiya Hawau , Wanda kukan ke ratsa duk wata gaba ta jikinta , ta rasa ya zata yi sai ta daga hanunta zata shafa kansa sai ta kasa , ji tayi an daga hanunta an dora saman kan Elhaj Ilyas ta dago kanta tayi ido hudu da *Mubasshir* ya sakar mata wani lalausan murmushi sanan yayi mata nuni da ta kula baban, baiyi magana ba gudun kar ya ganshi a haka ya shige a hankali dakin Hajiyar .
Cikin nutsuwa Hajiya ta ce" mai yake damunka Dan gidan Hajiya?
Da sauri ya dago kansa ya kuma rushewa da kuka yana fadin dan Allah ki yafe min , wly ban san abinda yake damuna ba , na rasa nutsuwata na rasa abinda ke damuna , na rasa farin cikina Hajiya ki yafe min
Hajiya Hawau ta share hawayenta ta ce" kulun cikin yi maka adu'a nake Dan gidan Hajiya , ka sani Allah yana tare da mai gaskiya kuma ka kara riko da adininka Allah ya baka lafiya
Elhaj Ilyas ya ce" Amin na gode Allah ya kara tsawon kwana da lafiya , nan fa tsakani uwa da Da suka shiga hirar su
Mubasshir na shiga ya tarda Yar Mahaukaciya zaune saman wata kujera mai tsayi tana kalon madubi da macaji ( masarci) a ganunta tana caje gashin kanta da kyar sai nishi take dan kuwa daga ta caje sai ya koma ya nanade kansa haushi ya kamata ta wurgar da macajin tana fadin wly sai na askeka gaba daya ma na huta , haka kawai
Mubasshir dake tsaye yana kalonta yau dai yayi niyar sai ya san wai atach ne take sakawa KO kuwa haka kalar gashinta yake ,
Yayi gyaran murya ,
Da Sauri Yar Mahaukaciya ta kale shi , sam bata ji karar shigowarsa ba , kuma tirarensa da ya zama KO da yaushe yana gidan sai ya kasance kanshin tiraren KO yaushema jinsa take a hancinta hakan yasa KO yanzun da tana caje kanta ta dan ji kanshin bata wani kula ba , tana ganinsa ta shiga neman hijabinta da a tinaninta saman bed din Hajiya ta ajiye shi , da Sauri ta bude akwatinta ta dauko na makarantarta ta zumbula Sanan ta shiga kikifta ido,
Mubasshir shi abin nata dariya ma ya bashi wai kariya bayan bugu , aman sam bai daran ba ya ce" menene kike kokarin rufewa tamkar naki bayan kin loda gashin doki KO na matacen mutun a kanki ?
Yar Mahaukaciya jin an ambaci ta loda gashin matacen mutun a kanta ya saka ta kwalalo ido waje ta ce" karde aje gashin nan na matacen mutun din ne?
Mubasshir ya kaleta a ransa ya ce zata raina min hankali , a fili ya ce" ya zanyi miki tambaya kiyi min ni ma?
Yar Mahaukaciya tayi kalar tausayi ta ce" wly kaga gashin mutane duk baki ne, gashin Fati ma baki ne, haka na princess da su Tina su Mariam duka baki ne, kaga kuma ance idan mutun ya mutu gashinsa fari yake zama, kuma ni tun ina yarinya yara idan suna bina sai suna cewa Yar Mahaukaciya mai farin gashi matata, ...... Maganar ta tsaye mata a makogwaro lokacin da ta ambaci sunanta a gaban Dan Aljannah da Sauri ta rufe bakinta ta tura bayi tayi shigewarta
Mubasshir dake tsaye yana sauraronta gaba daya zancen ya shige masa duhu mai take nufi da yara na kiranta da *Yar Mahaukaciya*? Mai hakan ke nufi?
Sahla dake labe tana sauraron su ta jiyo gaba daya abinda suke fada ranta ya gama baci ya mijin da zata aura ya zo yana magana da wanan banzar? Kuma taji Ashe ma ita din *Yar Mahaukaciya ce*, ai kuwa zata fadawa momy tun wuri ayi maganin wanan abin tun kafin a jaza mata bala'i
Wayo Yar Mahaukaciyata
🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
24
Sahla na fita ta ficewarta ta nufi cikin gidan su, tana zuwa ta shige dakin mahaifiyarta tana haki,
Hajiya Marhaba na ganin yanayin yar Tata ta Mike ta nufi dakinta tana fadin tana zuwa, tana shiga ta tarar da Sahla tana ta haki ta ce" Beby lafiya?
Sahla na ganin mamarta ta fashe da kuka har tana buga hanayenta jikin bed tun karfi
Hajiya Marhaba ta je da gudu ta rike hanunta tana fadin Beby wa ya taba miki zuciya haka? Fada min uban wa ya taba min ke? Idriss ne KO?
Sahla ta shiga sauke ajiyar zuciya ta ce" mom ni fa kawai a kori yarinyar nan daga gidan mu , gaskiya ta fara fice Gona da iri ,
Marhaba ta ce" wace yarinyar?
Sahla ta ce " wanan mai kalar fatar zabaya mana,
Hajiya Marhaba ta ce" toh mai tayi ?
Sahla ta dago kanta ta ce" kinga irin yanda Yaya Idriss ke kashe mata kudi kuwa? Sanan yarinyar uwarta Mahaukaciya ce , tana nan tana hauka kina son samun sirika Yar Mahaukaciya ne? Kuma duk da Mubasshir ya tsaneta hakan baya hana shi zama inda take, kinga tun wuri kiyi maganinsu dan kuwa yau naga dad a wajen Hajiya .
Hajiya Marhaba ta zabura tana dafe kirji ta ce" what? Dadyn naki ne ya tafi wajen Hajiya? To mai yasa bai fada min ba? Mai