Showing 24001 words to 27000 words out of 60971 words

Chapter 9 - Yar mahaukaciya complete

SAJIDA   

08 Sep 2026

18

kowa ya gujeta? 🤷🏿‍♀🤷🏿‍♀🤷🏿‍♀🤷🏿‍♀🤷🏿‍♀🤷🏿‍♀ taku har kulun yar mutan Niger 😘😘😘😘

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

30

*Jiki Alhamdulilah sisters na gode da adu'ar ku gareni love u*

Cikin takunta tamkar ba ita ce ta gama wayar ba ta juyo ta zauna , tana zama idanuwanta suka sauka kan Mubinnah Wace ita har ga Allah da farko bata ganta ba , gabanta taji ya fadi abinka da mai sakin magana idan ta raya mata ta kali Mubasshir wanda ya kagauta su tashi su bar dakin irin yanda matan nan kowace ta zuba musu ido ga uban surutu an cika su da shi ga wasu hotuna uwa Wanda aka gayace su gidan TV shi kam duk a takure yake

Hajiya Marhaba ta ce" Mubasshir wanan fa? Ban Santa ba

Mubasshir ya kara sada kansa kasa dan kuwa KO bai dago ba ya san da Wace ake magana

Idriss ya kaleta ya ce" Mom Wanan fa itace Mubinnah daya daga cikin yayan sarki

Hajiya Marhabah ta ce" wani sarkin?

Idriss ya ce" na Makkah mana mom

Hajiya Marhaba ta washe hakora ta shiga yiwa Mubinnah barka da zuwa jama'ar dakin ma haka , sanan kasa kasa sai surutu suke suna tambayar Kenan harda iyalan sarkin sun zo? Gaskiya Hajiya Marhaba ita tayi dace ,

Wani irin ihu suka jiyo , gaba dayansu suka yi tsit , suka kuma jiyo wani ihun da Sauri suka Mike Idriss ya ce " a nan ne

Mubasshirr ya kama hanyar fita shi da Idriss inda matan suka yi cirko cirko suna raraba ido dan kuwa kowanen su tsoron FITA yake ayi ba shi

Suna fitowa suke jin ihun daga wajen bangaren Hajiya Hawau ne Harda Alamar koke koke

Idriss ya sha gaban Mubasshir ya ce cikin haki" Malan dakata , mu fara Kiran yan sanda kafin mu shiga cikin gidan nan wa ya san Abinda ke faruwa a ciki, idan fa yan boko haram ne?

Mubasshir ya gala masa harara ya ture hanunsa ya ce" KO yan a rayu haram ne Allah ya jikana ya juya ya nufi cikin gidan

Da shigarsa abin mamaki ya tarar Wanda ya kasa gaskatawa idanuwansa abinda suke gani , haka kunuwansa suka kasa yarje masa abinda suke jiyowa, nan da nan wata nadama da dana sani suka darsu a zuciyarsa domin wanan ba halin datako bane, sam wanan abin datijon kirki ba zai aikata shi ba

Cikin sauri ya FITA ya saka akayi gida da Mubinnah domin idan ta ga wanan abin shi aka tonawa asiri ba kowa ba ,

Cikin mutuwar jiki ya juyo ya dawo inda wajen ya zamana tamkar ana kida dan kuwa har dan gewaye su aka yi ana kalo , ba kowa bane face *Elhaj Ilyass* sai Jan kafar *Yar Mahaukaciya* yake yana mugayen kalamai a kanta kamar haka

*Ashe Hajiya Mahaukaciya ce kika tare min a gida? Ashe kortuwa ce yarinyar nan ? Idan ka ganta luplup tamkar mutunuyar arziki ashe ita kuwa munafuka ce?*

Hajiya hawau cikin tashin hankali da kuka tana Jan Yar Mahaukaciya , Elhaj Ilyas na jan ta ta ce" Haba , haba Ilyasu dan girman Allah ka cika min yarinya ka cikata mu bar maka gidan ka domin wanan yarinyar ni shaida ce kan mutuniyar kirki ce , KO wa ya fada maka abinda ya fada maka karya ne domin wanan yarinyar marainiya ce sanan ni ni na daukota lokacin da danta ya rasu harma akayi masa sitira a nan , Haba Ilyasu wanan wulakanci har ina, ya kake so nayi da raina ne?

Elhaj Ilyass ya ce" Hajiya wly kinji na rantse ba inda zaki sanan yarinyar nan a yau yau din nan zata bar min gidana domin ni ba mazinaci bane sanan ba zan lamunci ta bata min suna ba da sunan iyalina , ke kuwa ni kika Haïfa ba ita ba dan haka ita kadai zata bar min gidana

Hajiya Hawau ta juya wajen kawayenta tsofafin dake tsaye suna al'ajabin wanan lamarin da hanu daya ta fara rokon a taimaketa a tafin mata da Yar Mahaukaciya kafin danta ya gane yayi kuskure ta maidota

Aman ina kowa sai ya silale domin da ace ma jinin hajiyar ce aman haka kawai haduwar rana tsaka a zo da wanan zancen gashi daga an ganta bata shigen yayan hausa ga ido irin na kyanwa aje tsakar dare ta farka ta cinye mutun,? Gaba daya kowa tsoron Yar Mahaukaciya ya darsu a zuciyarsa

Mubasshir na rakube jikin garu yana kalon yanda da daya daya jama'ar suka fara fashewa suna tafiyarsu sai yan tsirirai su hajiya Marhaba da sauransu , muryar Idriss ta dawo da shi inda ya ce" Aba ka kontar da hankalinka ka cikata haka ni zan fitar da ita

Da hajiya da Mubasshir a tare suka kali Idriss jin furucin bakinsa

Elhaj Ilyass ya ce" Yawa yaron kirki fitar min da anoba daga gida

Yar Mahaukaciya da ta zamto tamkar mutun mutuni , a da da farko tayi tinanin zuwan wanan ranar , aman ganin irin yanda ta samu zama sai tinanin ya kau daga ranta, tabas ta saba da wulakanci, da cin zarafi aman bata taba zaton a wanan ranar haka zata faru da ita ba , furutin Idriss shi ya fi komai daga mata hankali bata san lokacin da wani karfi ya zo mata ba ta Mike daga yashen da take cikin karaji ta ce " Ya isa ,

Ta juyo da idanuwanta da sauran farin ya koma ja, tsakiyar kuwa yake haske haske cikin dakakiyar murya ta ce" *Idriss ba sai ka fitar da ni ba , zan FITA da kaina, ta juya wajen Hajiya ta tsuguna ta kama kafafuwanta ta ce" Ni ba mazinaciya bace , aman kuma ban san ba KO ni mayiya ce KO aljana ce, abu daya na sani nima mutun ce, sanan ni YAR MAHAUKACIYA CE, kiyi hakurin rashina , karki damu da inda zan kwana na saba da wahala, kar kiyi fushi da danki haka Allah ya so , na gode sosai da tarbiyar da kika bani harma kika nuna min nima inada daraja*

Tana gama fadar haka ta jawo hijabinta na makaranta dake rataye saman igiya ta juya cikin nutsuwa ta fito daga gidan su Idriss inda take yi masa kalon karshe

To jama'a ina Yar Mahaukaciya zata nufa? Muje zuwa😁😁😁😁

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

31

Tafe take bata san inda take jefa kafarta ba , gata dai da ganinta ka san yar banban gida ce KO yanayin jikinta da yanda take haske sai dai fuskarta a mugun hade tamkar hadarin gabas

Mutane sai kalonta suke suna al'ajabin wanan mai ke damunta? Wasun kuwa har tambayarta suke , aman ina ita ba ta tasu take ba

Tun da ta fito yake biye da bayanta a hankali yana son sanin inda zata je , tafiyar yaga ba mai karewa bace hakan yasa ya samu ya shiga gabanta da motarsa daidai wani dan karamin gida na laka

Kasa take kalo ganin mota ta shiga gabanta ya saka ta juya ta fada cikin kofar gidan nan ita duk a tunaninta hanya ce

Da Sauri ya sauko yana kokarin cire Babar rigarsa domin ji yayi kwatakwata tayi masa nauyi , cikin nutsuwa ya kutsa cikin gidan nan inda ya tarar da Yar Mahaukaciya da wata mata tana yi mata tambayar wa take nema , ita kuwa kawai ta tsura mata ido tamkar sabuwar halita

Cikin nutsuwa ya karasa yana fadin " salam kiyi hakuri kanwata ce bata tayi ne

Matar nan ta ce" oyo sanu kinji kiyi hakuri ga yayanki

Yar Mahaukaciya ta dago idanuwanta ta sauke su a fuskar *MUBASSHIR* Wanda shima a lokacin ita yake kalo , suka yi ido hudu da shi

A hankali ya furta " mu tafi yana nuna mata kofa

Tamkar wata karamar yarinya Yar Mahaukaciya ta make kafada tana nufin ba inda zata je

Mubasshir ya hade rai yayi iya yinsa aman firr ta kafe ita fa ba inda zata tafi

Matar nan ta fito itama ta saka baki ake baiwa Yar Mahaukaciya hakuri kan ta shige su tafi aman kamar da kurma suke magana

Mubasshir ya hade rai tamkar bai taba yin dariya ba ya umarci Yar Mahaukaciya da ta fice su tafi , aman ina abinka da Wanda bai iya fushi ba , ita duk gani take idan fa ta bishi za'a koma ne a kuma ci mata mutunci kamar yanda akayi mata yanzu KO ma fin hakan , shi yasa sam ta kasa daga kafarta kuma bata ga abinda zai Sakata daga kafar tata

Mubzsshir ya lumshe ido a ransa ya ce" Ya Allahna ka yafe min taimako zanyi ka fini sanin ba dan wani abin zan tabata ba ,

Kawai sai gani nayi yana tatare hanun rigarsa ya CIRA Yar Mahaukaciya sama ya nufi motarsa da ita , Wace ta zaro ido tana wutsil wutsil din ya sauketa tana yakushinsa tamkar sabon kamu

Shin ina Mubasshir honorable zai nufa da Yar Mahaukaciya? Zata amince ne KO aa? ❤❤❤

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

32

Tunda ya sakata cikin motar ya zagaya ya shiga ya dauki hanya ita kuwa tsananin tsoro ya hanata dagowa ta kale shi balatana ta tambaye shi inda zai kaita dan haka kawai sai ta hade kanta da gwuiwar ta tana ta sheshekar kuka

Tafiyar da sukayi ta kai ta minti talatin gaba dayanta ta hada zufa domin du ta dababaye jikin nata da katon hijab dinta na makaranta ,

Ji tayi ya ja ya tsaya ta kasa dago fuskarta kawai jiran jin duka take KO wulakanci dan tasan gidan su Idriss din ne kawai ya maidota , ta kai kamar minti biyar a zaune bayan tsayuwar motar tana ta sheshekar kukanta , wani sanyi kamar na busawar iskar Allah du da hijabinta sanan taji wani lalausan hanu wanda da ba dan taji yatsitsai ba da KO ya za'ayi da ita ba zata yarda cewar hanu ne ba , cikin Sauri ta dago kanta dan ganin wanda ya dora hanunsa saman kafadunta

Hajiya Fatimatu Mahaifiyar Mubasshir ce tsaye sai kyali take , ga kwaliya ta sha ga sarka mai kyanli, ga farar fata ga kuma hasken gari hakan ya hadu ya haska fuskarta a idanuwan Yar Mahaukaciya Wace nan take ta gane wanan mata KO ya take ta hada alaka da Dan Aljannah da tsabar kamar da suka yi har ta baci , aman sam bata kawowa ranta cewar ta haife shi ba saboda ita bata da banban jiki sanan du da daga fuskarta zaka gane ta manyanta aman hutu ya hana a gane shekarunta ,

Hajiya Fadimatu ta katsewa Yar Mahaukaciya tinaninta ta hanyar sakar mata murmushi sanan ta kamo hanayenta cikin nutsuwa ta ce " Marhababiki yata , ta juya fuskarta cike da fara'ar da Mubasshir har ya fara kishi ta ce " Son kaga Adu'ata ta karbu KO Allah ya bani ya daidai lokacin da na aurar da dana ,

Mubasshir yayi Murmushin shima ya ce" Maman Mubasshir aure fa kika yiwa Mubasshir ba mutuwa yayi ba , dan haka kar a maye gurbin Mubasshir a zuciyar Maman Mubasshir dan kuwa ba zai taba yarda ba

Mahaifiyar Mubasshir tayi murmushi ta lakaci Hancin Mubasshir ta ce " Kishi? Au kishi kake? To ka zage dantse dan kuwa aiki ya sameka jan aiki kuwa , ta kama Hanun Yar Mahaukaciya wace KO takalmi babu a kafarta sanan jikinta yayi busu busu da kura ta bi wani lungu da ita saboda taron jama'ar gidan ta nufi dakin Mubasshir da ita dan kuwa ita bangarenta jama'ar sunyi yawa sosai

Suna shiga wayar dakin ta fara ringin ta daga tayi salama

Mubasshir ya ce " Maman Mubasshir hajiya ce tayi kira na hadaku kuyi magana tace tana son sanin idan har da gaske kin karbi sha lelenta

Hajiya Fadimatu tayi murmushi jin yanda ya karasa maganar sanan ta amsa Kiran Hajiya Hawau , sun jima suna zantawa sanan hajiya Fadimatu cikin wani irin farin ciki ta ce" Haba , haba Hajiya ai yarda daya ce , da kuma na kowa , sanan tunda ta zamto musulma koda yayanta ashirin ai bai haramta ba , dan haka ina so insha Allah kiyi kokari nan da kwana uku ki zo mu hadu da shi Aban tun kafin ya juya sai ayi KO?

Hajiya Hawau cikin Hamdallah da godiyar ubangiji ta ce " Allah ya saka miki da mafificin alkhairin dake nan gidan duniya da kuma na kiyama, Allah ya sa ki gama da duniya lafiya, Yanda kika kudurci aikata Alkhairi a kan marainiya Allah ya jibanci lamuranki

Hajiya Fadimatu tayi saurin fadin" Amin hajiya aman plz ki dena Gode min na fada miki yiwa kai ne na yarda da ke da zuciya daya , haka suka datse Kiran su dukansu suna farin cikin abinda suka yanke Wanda a tinaninsu hakan shine banban gudumuwar da zasu yi dan taimakon marainiyar Allah wato Yar Mahaukaciya

Cikin nutsuwa ta juyo wajen Yar Mahaukaciya Wace gaba dayanta take tsorace da wanan dakin, ita tunda ta wayi gari ta ganta a gidan duniya bata taba , no bata taba kawowa kusan ranta cewar wai a nan gidan duniya za'a iya tsantsara wanan tsarin haka , Dakin ciki daya ne wani wawakeke sanan du madubi ne ya gewaye dakin sai gadon dake tsakiyar dakin kasan ba kafet jikin tils din kasan hoton Mubasshir ne aka zana da sajensa yana murmushi gaba daya wata kunya ta kamata gani take kawai kalonta ne yake ta kuwa tatare siket dinta ta matse ita kar yaga jikinta ( lol ) aman kuma mamakin da take Wai ina bayi? Sanan ina wajen kaya? Ita tsoroma ya mugun kamata da ace ita kadaice da ba abinda zai hanata ta zare a dakin nan

ℍᗅႮՏᗅ ℕᝪᏉℰℒՏ ՏᝪKᝪᝨᝪ:

ᗯℍᗅᝨՏᗅℙℙ ℕᝪ:

07068808039

ᗯℰℬՏⅈᝨℰ:

ᗅℬⅅႮℒℳKⅈℬᗅℬ.ℍℰᝣᗅᝨ.ℂᝪℳ

Hajiya Fadimatu ta kamo hanunta cikin nutsuwa ta jata saman gadon Mubasshir suka zauna a gefen gadon sanan cikin sanyinta da kwarewa wajen kontarwa da mutun hankali ta ce" Rahma, Rahmatullah, mai yayi zafi da aka manta Kiran inalilahi wa'ina ilaihi raj'une ake kukan nan? Shin kin manta fadar Ma'aiki idan ka ga abinda ya kayar maka da gaba KO ya bata maka rai kayi ta maimaita sunayen Allah kana tazbihi kana kusanta da ubangijinka dan samun saukin zuciyar ka ? Domin kinsan ita zuciya a jikin dan Adam Mugun nama ce idan har zuciyar Dan Adam ta baci to fa ba mutun, sai ki ga mutun yana aikata abubuwa irin Wanda KO daba ba zai aikata ba dan kuwa cikin aikinsa tsabar kin Allah zaiyi yawa a ciki , shi kuwa wanan Halaka ne Rahma Tabas Halaka ne

Cikin nutsuwa Yar Mahaukaciya ke kalon Bakin Mahaifiyar Mubasshir wata irin nutsuwa taji tana ratsata wace bata taba jinta cikinta ba hadi da kunya Wace ta rasa ta maicece, da sauri ta sada kanta kasa tana dan murza yatsuntsanta tana raurau da ido

Hajiya Fadimatu tayi murmushi ganin Yar Mahaukaciya tana da kunya ta dago kanta ta ce" Ni sunana Nana Fadimatu sanan ni Mahaifiyar Mubasshir ce kuma ina son zama mahaifiyarki , shin zaki bani wanan damar?

Idanuwan Yar Mahaukaciya suka ciciko da kwallah tana kokarin zubar da hawayen shaukin wanan kalma ta Mahaifiyar Mubasshir

Hajiya Fadimatu tayi Saurin girgiza mata kai ta ce " AF sanan idan abu ya faranta ranta kayi hamdallah ba kayi kuka ba

Ta cire hijabin Yar Mahaukaciya ta dora kanta saman cinyarta a hankali tana yi mata labari har barci mai dadi yayi awon gaba da Yar Mahaukaciya cike da farin cikin wanan rayuwa sabuwa tare da adu'ar Allah ya sa mai dorewa ce

To fa shin mainene abinda su Hajiya Hawau suka yanke ne? Muje zuwa 😘

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

33

Sosai take bacin ta hankali konce harda ajiyar zuciya, Hajiya Fadimatu ta gyara mata konciya ta Mike a hankali gudun kar ta tashe ta ta koma wajen bakin ta

Bayan wanan tarzomar kowa ya watse aka bar Hajiya Hawau ita kadai domin gaba daya bakin nata sunyi tafiyar su gudun kar a makala musu Yar Mahaukaciya

A boye ta samu wayarta har tayi magana da mahaifiyar Mubasshir , bayan ta gama ne ta fito dan ta tatare tabarmin da ta shinfidawa bakin ta , tana fitowa ta tarar da Fati kawar Yar Mahaukaciya rakube kanta a kasa tana ta tinane tinane

Hajiya Hawau ta karaso a hankali ta zauna kusa da ita ta ce" Fati tinanin mai kike?

Fati ta dago kanta ta kali hajiya sanan cikin gargadar murya ta ce"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login