Showing 27001 words to 30000 words out of 60971 words

Chapter 10 - Yar mahaukaciya complete

SAJIDA   

08 Sep 2026

27

shin Hajiya ina sister ne? Hajiya dan Allah ki cireni daga cikin duhu cos ina cikin duhu ta karashe zancen da kuka

A hankali hajiya Hawau ta dafa kafadarta ta ce" RAHMA ba mazinaciya bace , sanan mafaifiyarta ba mahaukaciya ba ce, kuma ita marainiya ce sanan ni kakarta ce, Kuma Dan Aljannah yayanta ne , wanene baki fahimta ba a ciki?

Fati ta ce" Kenan AA jikanki ne shima?

Hajiya Hawau kawai ta daga kanta alamar eh

Fati ta sauke nanauyar ajiyar zuciya sanan ta ce" yanzu tana ina Ita din?

Hajiya Hawau ta ce" Tana gidan su Mubasshir dan haka ki mike kiyi wanka zan saka a rakaki wajenta , ki tafiyan mata da kayanta gaba daya kin ji?

Fati ta daga kanta tana farin cikin jin Rahma na gidan su AA Mubasshir ,

Hakan kuwa akayi Hajiya Hawau tayi kira ta shaidawa Mubasshir yayi Kiran securites ya shaida idan za'a kawo wata budurwa baka mai dan tsayi da kaya a shiga da ita ta baya , sanan ya shaidawa Mahaifiyarsa , ita kuwa sai murna ta karu dan Hajiya Fadimatu akoy son yaya mata shi yasa kulun adu'arta Allah ya bata kafin rasuwar mahaifin Mubasshir to bayan rasuwar tasa ma bata daina ba tana fatan Allah ya baiwa Mubasshir sai a bata ta rike sai gashi yau Allah ya bata ya mai kyau haka tayi murmushi tana adu'ar Allah ya tayata riko

Cikin bacinta taji an kankame mata jiki firgigit ta farka tana zare ido domin bata san tayi baci har haka ba , idanuwanta ta shiga murzawa dan gaskatawa kanta Wanda take gani

Fati tayi dariya ta ce" ni ce sis

Yar Mahaukaciya tayi musrmushi ta ce" wa ya kawoki? Ya akayi kika zo ? Kinga abinda ya sameni ko ? A ina..........cikin sauri Fati ta ce" ke ki dan huta da tambayoyin mana , Hajiya ta fada min komai dena daga hankalinki haka kinji

Yar mahaukaciya tayi shiru tana tinanin mai Hajiyar ta fada mata , aman sai ta share bata ce mata komai ba ,

Suna nan zaune Mahaifiyar Mubasshir ta kuma shigowa ta ce" Yar Fadimatu kin farka? A taso ayi wanka domin yama tayi

Yar Mahaukaciya ta ce " ohk mamana tana murmushi

A hankali Mahaifiyar Mubasshir ta nufi daidai wani madubi ta mika hanunta a nitse ta dan shafa wani farin abu , abin mamaki kofa ta bude daga Yar Mahaukaciya har Fati da kalo suka bi Hajiya Fadimatu baki sake uwa zararu sanan ta kuma taba wani bayi biyu suka bude a cikin dakin cikin nutsuwa ta taho ta kuma taba wani abin sai dirowa ta bude ta zaro tapi ta nufi wajen tiraruka ta dauko kala uku du ta zube musu ta ce" kuyi wankan ga salaya, ga kuma wanan kafin ku gama kimtsawa za'a kawo muku kayanku ku saka

Su duka suka amsa mata

Har ta kusa FITA ta dawo ta ce" zaku tafi diner ne?

Fati ta ce" Eh

Yar Mahaukaciya ta ce" aa

Suka kali juna a tare

Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta ce" Kuyi shawara idan kun yanke shawarar sai na turo mai shirya ku

Suka amsa mata da to ta juya ta fita

Tana fita Fati ta zarowa Yar Mahaukaciya ido ta ce " hey😳, for what zaki ce ba zamu tafi ba?

Yar Mahaukaciya ta ce" ki gane sisi idan na tafi kinga abinda ya faru da safe bana so ya kuma faruwa

Fati ta ce" auren yayanki ne , auren gidanku ne, dan kawai wata nonsence bata sonki a wajen sai ki ki tafiya? Sis harda mai shiryamu fa waouh har ina tinanin yanda zamu dawo idan aka shiryamu plz ki amince mu je muma

Haka dai suka zauna suna ta musanyar yawu kan su je KO kar su je

Eyah fans shin Su je din ne KO kar su je??????🤷🏿‍♀

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

34

Wanka suka shiga kowace ta dau lokacinta , ita dai Fati tana gamawa ta dauro alwalah ta zo ta gabatar da salar Magarib, tana nan zaune tana lazumi Yar Mahaukaciya ta fito ta nufi Jakarta ta buda ta dauki pad ta juya cikin bayin ta saka ta kuma fitowa kanta daure da tawul karami ta lulube jikinta da hijabinta

Sai da Fati tayi sallar Isha sanan ta mike daga saman dardumar ta ninke ta ta tsaya ta zubawa hoton Mubasshir dake zane saman terrace din

Yar Mahaukaciya ta ce" mai kike kalo?

Fati ta ce" sis kinsan Allah gaskiya banga laifin matan da suka yanyanka hanayensu lokacin annabi yusuf , ki duba ki ga irin kyan AA fa sis ni KO da AA kadai aka barni sai nayanyanke hanuna

Yar Mahaukaciya ta bushe da dariya ganin yanda Fati tsakaninta da Allah take bayaninta har cikin zuciyarta yanayin yanda take fitar da zancen

Ta ce" sisi kinsan wani Abu? Ni sam kyan mutun baya rudata wly ke wani lokacin nafi son mutun mai bakar fata cos yafi kyau

Fati tayi mata kalon kin raina ni sanan ta ce" to tayaya kyau zai rude ki ? Ai dan kinsan kina da shi shi yasa , da baki da kyan nan da garin kalon mai kyau har sai kin fadi , sis dan AA yayanki ne shi yasa kyansa baya baki tsoro

Yar Mahaukaciya a ranta ta ce na fiki tsoron kyan bawan Allahn nan domin ina daya daga cikin wa'inda suka Ganshi yana zubawa mahaifiyarsa shagwaba , da a lokacin kika Ganshi da sai kin suma ma ina jin , aman a fili ta ce" idan kin gama ki zo mu kimtsa plz

Suna tsaka da kimtsawa Fati ta dage ta gyara zama tana tsantsarawa Yar Mahaukaciya kwaliya mai shegen kyau da tsari ta caje mata girar ta domin girar kalar gashin kanta , ta dauko tana kokarin zabar mata jan bakin da zata shafa Hajiya Fadimatu ta shigo fuskarta dauke da murmushi

Tayi musu salama

Suka amsa suna gaishe da ita

Ta amsa su tana ta zuba murmushi ta ce" kuyi hakuri yayana na barku ku kadai, kunsan bakin ne da yawa sai yanzu na samu na kufce

Yar Mahaukaciya ta ce" lah ba komai mama

Hajiya Fadimatu ta karasa tana fadin zaku tafi ne wajen dîner?

Fati ta ce" No mama ba zamu je ba

Hajiya fadimatu ta ce ohk ba damuwa , daidai nan wata mata tayi salama da wata jaka a hanunta ta tsuguna har kasa tana gaishe da su fati , suka amsa suna kalonta

Ta juya cikin murmushi ta ce" ma'am wacece kanwar ogan?

Hajiya Fadimatu ta nuna Yar Mahaukaciya ta ce" kin ganta nan baki ga kama ba?

Wace aka nunawa mai aikin bangaren Hajiya Fadimatu ce ta ce" kai masha Allah , Ashe ta warware ma , Allah ya raya mana ita ( uwa wata beby? )

Hajiya Fadimatu ta amsa da Amin Ya Allah sanan ta karbi jakar ita kuwa ta juya ta bar dakin

Hajiya Fadimatu ta bude jakar wasu abayoyi ne a ciki da kuma wasu mahaukatan less farare tas anyi dogayen riguna da su gwanin ban sha'awa da ribon na less din ta ce" kunga wajen ango ga abinda zasu saka nan wanan less din , tunda bazaku tafi ba sai kuyi shigan arabian ku fito dan saboda hotuna da za'ayi mana da ango kafin ya tafi diner

Yar Mahaukaciya ta ce" An gode mama,,,,,.....kafin ta karasa Hajiya Fadimatu ta rufe mata bakinta tana fadin no kar naji godiyar nan , dan mamanki tayi miki kyauta sai ki kama gode mata? No kiyi hamdallah ya wadatas sanan ta Mika hanu ta dauko wani Jan baki kalar pink ta Mika mata ta ce" wanan shine daidai da kwaliyarki

Yar Mahaukaciya tana murmushi ta karba ta dan goga pink ne Wanda bai ciza ba sanan bashida man lebe a hade da shi ta fito tsaf da ita

Hajiya Fadimatu a ranta ta ce" Allah yayi halita a nan , Allah ya kade hau da bakin duniya , a fili kuwa ta ce" Yar Fadimatu kinyi kyau har kin gaji masha Allah

Yar Mahaukaciya tayi murmushi sanan ta sada kanta , Hajiya Fadimatu ta kali Fati ta ce" takwara kuyi Sauri ku fito fa kunsan al'adar mu da banbanci

Fati ta ce " toh mama i'a gamu nan fitowa

Ta juya ta fita , tana FITA Yar Mahaukaciya ta cire tawul din dake nanade da gashinta ta saka macaji baba ta caje kanta sanan ta dauko ribom ta daidaita gashin tsakiyar kanta ta daure ta warware abayar bata san lokacin da ta furta masha Allah ba ta juyo dan nunawa Fati sai taga ita har ta saka

Fati ta ce" kawai ki rage mamaki yan Mata dan kuwa haduwa mun hadu saka nayi miki roling mu tafi ,

Yar Mahaukaciya ta saka tata Fati ta nada mata mayafin Abayar ta fito tamkar balaraba ga hasken da idanuwanta ke bayarwa idan ta kaleka abin ba'a cewa komai ,suka dauki takalmansu mai shegen kyau suka saka , Fati ta dauko wayarta ita kuwa ta kama hanyar fita cikin takunta na nutsuwa da daukan hankali

Fitowa suka yi suka tarar da matar nan ta dazu tana tsaye tana jiran su , ta ce " Hajiya mu je na kaiku falon da ake salamar angon

Yar Mahaukaciya ta ce" salamar ango kamar yaya?

Amina ta waigo ta ce" Eh ai haka al'adarsu take yanzu angon ya fito tun dazu ana ta hotuna tamkar baza'a daina ba , idan aka gama sai a barku ku uku tunda Hajiya ce yar uwarsa ta jini da Mahaifiyarsa , Mahaifiyarsa tayi masa nasiha sosai da sosai shi Kenan sai ya tafi daga wajen dinern gidansa zai fice da matarsa shi Kenan sai jibi da auren zamu ganshi shima gasuwa zata kawo shi idan ya koma sai bayan sati guda kuma shikenan ya zama magidanci shima

Fati ta ce " waouh wanan tsarin ya tsaru ya birge ni sosai tsarin nan , ta juya kan Yar Mahaukaciya ta ce " sister al'adar ku tana birge ni

Yar Mahaukaciya tayi murmushi tamkar wata sakara ta dan juya kanta a ranta ta ce " nima yanzu na ji ,

Daidai nan suka karaso wani falo Wanda fadin haduwarsa bata lokaci ne , ya hadu ya hadu yayi karshen haduwa , cikin nutsuwa Yar Mahaukaciya ta saka hanunta ta bude tana kalon Fati dake yi mata magana , sai gani tayi Fati ta zama tamkar robo kikam tana kalon ciki

Cikin faduwar gaba ta juyo a hankali idanuwanta sukayi arba da jama'ar dakin ta furta ya salam ta lumshe idanuwanta dan faduwar da gabanta yayi

Hajiya Fadimatu ta mike cike da murmushi ta tarota ta kamo hanun Yar Mahaukaciya da Fati ta ISO har tsakiyar jama'ar dake hahakimce ana ta daukan hoto domin Mubasshir a zaune yake saman wata kujera mai ruwan ash da baki baba gaba daya idanu aka zuba mata ganin wanan yarinyar mai shegen kyau a tare da ita ,

Hajiya Fadimatu cikin Murmushi ta ce" Asalamu alaikum

Gaba dayansu suka amsa mata salamarta kanan ta ce " Ina mai gabatar muku da Yarinyata Rahma , da kuma kawarta mai sunana , Kanwar Mubasshir ce she is my daughter my lovely Girl ta karashe tana sakarwa Yar Mahaukaciya Murmushi

Gaba daya dakin suka kwashi dan surutu suna fadin waouh,

Hajiya Halima ta taso ta karaso gaban kawarta tana murmushi ta Mika hanayenta ta kamo na Yar Mahaukaciya tana murmushi ta jata jikinta suka yi irin gaisuwar nan ta larabawa sanan ta jata gaban sauran kawayen Hajiya Fadimatu suna gaisawa cikin raha kowa yana mamakin daman yayanta biyu?

Bangaren Mubasshir Hajiya Fadimatu ta nufa tana nazartar yanayinsa , lokaci guda du ya wani dan daburce yana kalon kasa gashi Mubinna ta rumgume shi ana daukan su hoto aman sam hankalinsa baya kan daukan hoton

Hajiya Fadimatu na isa ita ma ta shiga aka dauke su da Mubinnat sanan ta yafito Yar Mahaukaciya , sai da gabanta ya fadi ta mike kamar wace Kwaï ya fashewa kaza a ciki ta nufe su , Allah ya taimaketa kafin ta isa Mubinnat ta daga waya tayi waje ,

Cikin nutsuwa ta isa abin mamaki kanshin tiraren da ta fesa shi ne a jikin Mubasshir , shima yana jin kanshin ya dago suka hada ido daidai ta ISO kusa da shi

Cikin Sauri ya kawar da kansa yana ajiyar zuciyar da bai san KO na mainene ba ,

Hajiya Fadimatu ta kara matsota sosai jikin kujerar kamar yanda itama take ta ce " Yar Fadimatu ki saki jikinki mana sanan kiyi murmushi ayi mana hotunan mu

Mubasshir ya dago kansa ya kali Mahaifiyarsa da alamar shagwaba a fuskarsa ya ce" Yar ?????🙁

Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta ce " yes

Mai hoton ya dauke su ya kai kala biyar sanan Hajiya Fadimatu ta ja Yar Mahaukaciya ta zaunar da ita a gefen kujerar sanan ta dora hanunta na dama saman kafadarsa kasa kasa ta ce" wai ba zaku saki jikinku ba ana kalonku fa

Mubasshir da yayi sumar zaune ya kuma dago da kansa da cikin muguwar kasala ya bi dayan hanun nata da kalo Wanda ya sha kunshi yayi mugun kyau a ransa ya ce Au Ashe sai da tayi kunshin , a fili kuwa ya sakar mata murmushi itama ta mayar masa inda mai hoto ya dauki abinsa tamkar itace amaryar yanda take wani annuri

Haka dai akayi ta hotunan nan har lokacin nasiha yayi , gaba daya mutanen suka bar dakin harda Fati kawar Yar Mahaukaciya ,

Hajiya Fatima ta nemi waje ta zauna ta kali Yar Mahaukaciya dake kalon kofa tana son fita kuma ta rasa ya zata yi

Hajiya Fadimatu ta ce" Yar Fadimatu zo nan ki zauna mu yiwa Yayanki gargadi KO?

Mubasshir ya zaro ido Yar Mahaukaciya ma ta zaro ido nima haka cos wanan gargadi harda abinda yaro ba zai ji ba , ita kuwa Mahaifiyar Mubasshir an fada mata Yar Mahaukaciya bazawara ce , shi yasa zatayi maganar ta a gabanta , shi kuwa gani yake sam bai dace ba karta raina shi dan kuwa KO da ta taba aure har ta haihu hakan ba yana nufin za'a yi masa galgadi a gabanta ba dan yarinya ce , ita kuwa mugun tsoron sa ne ya Sakata firgici jin za'a yi masa gargadi a gabanta

Hajiya Fadimatu ta ce"""""""""""''''"'''''"""""""""""""""'

Muah

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

35

Hajiya Fadimatu ta kare musu kalo sunyi wani cirko cirko suna kalon ta ta ce " yar Fadimatu matso kusa da ni ki zauna KO kema kina jure tsayuwa ne?

Yar Mahaukaciya ta kifta ido tamkar ta juya ta fice take ji aman kuma bazata iya yin hakan ba , cikin nutsuwa ta karasa ta zauna a kasa daidai kafar Hajiya Fadimatu , inda shima ya karaso ya zaunan

Gyaran murya tayi sanan ta fara da adu'a , wato haka al'adar su take idan kayiwa yaron ka aure sai ka zaunar da shi ka tinatar da shi cewar da da yanzu ba daya bane , ka kara jadada masa irin nauyin dake kansa a yanzu Wanda idan yayi wasa da su tabas gobe kiyama yana cikin garari tsirar sa sai wani ikon Allah , hakan Hajiya Fadimatu ta dage wajen kawowa danta kwaya daya misalai da ayoyin da suka zo mana da mahinmancin iyali da yanda zaka kula da su , tana tsaka da yi masa wanan jawabin gaba daya ya nutsu maganganunta na ratsashi duk da ya san duk abinda take fada masa kamar ana kara yi masa bita ne aman kwarai yana ratsa shi kuma yana ji a jikinsa cewar dole ne ya kula da iyalinsa, jin mahaigiyarsa tayi shiru ne ya saka shi dago da kansa , aman mai zai gani *Hawaye* take sharewa daga idanuwanta

Cikin kidima ya mike tsaye ya dare saman kujerar da take zaune har hanunsa na rawa ya dan karkato fuskarta , kwarai hawaye Mamanda ke zubarwa , cikin wata irin murya ya ce " Kuka? Hawaye daga idanuwan Maman Mubasshir? Shin mai ya batawa Maman Mubsshir rai haka? Mai ya daga mata hankali haka?

Hajiya Fadimatu tayi lalausan murmushi a ranta ta ce' ina kaico da rashin sa'ar mata da kayi shi ya saka ni kuka aman a fili ta ce" Ina mamakin girman Mubasshir ne , yau da gobe sai Allah

Yar Mahaukaciya ma da ta mike tana kalonta sai taji hawayen maman Mubasshir na shigar mata zuciya tamkar Mahaukaciyarta , haka kawai taji zuciyarta ta tsinke wani irin kuka yana kokarin zuwar mata tayi iya yinta ta dane shi aman sai da hawaye ya zubo mata tayi saurin sharewa

Hajiya Fadimatu ta Mika mata hanu ta matso itama ta zauna suka Sakata a tsakiya a hankali taci gaba da jawabinta Wanda wani har kunya yake baiwa Yar Mahaukaciya , wasu abubuwan sai yau ta taba jin wai a aure akoy su kuma Dole a kiyaye , ita kam tata ta sameta koda yake Wanda ya nuna yana son nata ya fasa son nata kenan bata da wata damuwar tinanin idan fa bata yi biyaya ba itama zata hadu da fushin ubangijinta

Sosai ta kwashe lokaci tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login