Showing 39001 words to 42000 words out of 60971 words
fita sai karkarwa hanunta yake sanan motar taki buduwa
Sai da ya gama kalonta a yanayin tsoro son ransa sanan cikin dakakiyar mirya ya ce " ba'a tsayar da ni jira , wanan ya zama na farko kuma na karshe cos hakan na bata min rai ba kadan ba , ki dawo gaba dan ni ba Musa direba bane
Wani iri yake saukan mata a jiki yanayin maganarsa gaba daya tamkar tayi tsere haka take jin zuciyarta nayi mata lugude da kyar ta samu ta bude motar ta fito tana ta adu'a ta bude gidan gaba ta shiga kanta a kasa sanan ta kama yar karamar yatsarta tana ta murzawa da karfi tamkar ita tayi mata wani laifin
Tafiyar kurame ne suke domin ba Wanda ke cewa dan uwansa ufan sanan KO saukar numfashin su ba mai ji sai yatsarta da ta koma jajawur dan azabar murzata da take tunda suka fito tsawon tafiyar minti arba'in Kenan dalilin gosulo , suna isowa makarantar ya shiga direct har cikin kofar baban office din malamin mai suna ustaz Mu'azu ya faka
Cikin nutsuwa ta dago kanta sai taji ya ce " ina zuwa
Fita yayi ya shiga office din bai wani jima ba sai gashi ya fito da wata malama a bayansa ta karaso wajen Yar Mahaukaciya ta bude motar ta fito
Tana fitowa ta tsuguna ta gaisar da ita , ita kuwa sai washe hakora take ta kamata ta mike sanan ta ce " muje madame
Sai da ta sada Yar Mahaukaciya da ajinta sanan ta dawo wajen Mubasshir AA
Tana zuwa ta ce " an gwada mata kuma insha Allah za'a kiyaye , aman fa dalilin bazata zaman jiran malaman mu maza ba zatana sauka a lokaci daban daban dan haka dole mu dauki nimber wayar ka idan ta tashi da wuri muyi kira kazo ko ka turo a mayar da ita gida
Mubasshir ya ce" wanan duka ba damuwa idan dai har za'a kiyaye wanan , sanan komai akeda bukata ni za'a kira ba ita ba so ya mika mata takarda ya ce ganumberna personnel koda yaushe kika kira zan daga
Malamar mai suna Husnah ta karba tana godiya ya juya ya shige motarsa yana hamdallah a cikin zuciyarsa
Tafiya yake wayarsa ta fara ringin sai da tayi har sau uku sanan ya mika hanu ya dauko dan ganin KO waye ke kiransa da safe haka
Number Hajiya Marhaba ya gani hakan ya sa ya nemi waje yayi parking ya daga tare da salama
Hajiya Marhaba dake haki ko tsayawa amsa salamarsa bata yi ba ta ce " Mubasshir ina gidanka ina jiranka yanzu
Mubasshir ya ce " am Hajiya Gidana kuma? Ni ai ina gidan Maman Mubasshir fa
Hajiya Marhaba ta ce " ohk mu hadu a can din
Kafin ya bata amsa har ta datse kiran a hankali ya furta ya Salam sanan ya tada motarsa ya juya kanta ya nufi gidan mahaifiyarsa
😘😘😘😘😘😘😘😘😘
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
45
Kamar yanda suka zo haka suka koma tafiyar kurame suna isowa ta kama kofar zata bude ta fita
Mubasshir da ya kasa hana kansa magana ya ce ji mana
Yar Mahaukaciya ta jiyo tana kalon kasa dan koda wasa bata iya kalonsa cikin ido
Mubasshir ya mika hanunsa ya karbi nikaf din dake hanunta ya daga yaga eh lale nikaf din ne
Ya ce " mai yasa ke bakya saka shi ne?
Yar Mahaukaciya ta dago ta kale shi , idan bata manta ba wataran ta taba riskar hirar su da Hajiya Hawau yana fada mata cewar ya tsani yan matan nan masu saka nikaf din munafurci dan abinda suke aikatawa gonda gagarumar karuwa da su yawancinsu aman yau kuma ya tambayeta mai yasa ita bata saka ba?
Tambayarki nake , Muryar Mubasshir ta dawo da ita daga duniyar da ta fada ta ce " Am daman ance na matan aure ne , yan mata sai idan mutun yana da ra'ayi ne zai saka idan kuwa baka ra'ayi to karka saka
Mubasshir yana sauraronta sam bai so maganar ta tsaya daga nan ba ya lumshe ido ya ce " aman ai zawarawa ma na iya sakawa KO?
Yar Mahaukaciya ta dago idonta suka yi ido hudu ta kawar da kanta ta ce " eh
Ya Mika mata ya ce " toh ki ringa rakawa duk inda zaki je tunda zawarawa ma na iya sakawa kinga kina layi KO?
Yar Mahaukaciya ta karba ta daura a fuskarta idanuwanta kadai ake gani ba'a ganin sauran fuskarta , ta dago ta sauke idanuwanta cikin nasa ,
Wani irin yar yaji a jikinsa harma yayi nadamar Sakata daura nikaf din , dan da ta daura kawai sai kyan idanuwanta suka fito ba kadan ba har wani walkiya suke balatana na tsakiyar nan mai kama da na mage , Saurin kawar da kansa yayi yana fadin kina iya tafiya
Yar Mahaukaciya ta kama ta bude kafin ta fita a hankali ta ce " Allah ya saka da mafificin alkhairi sanan ta fice tana tafiyarta da ta saba
Ba shi ya bar wajen ba sai da yaga eh lale ta shiga falon sanan ya ja yayi gaba yana mai jin haushin kansa irin yanda yake mantawa da ayukansa masu mahinmanci wajen tinanin gyara rayiwar yarinyar nan , dan ba dan ya daukarwa kansa alkawarin kulawa da ita da bazai tsaya batawa kansa lokaci a kanta ba , aman insha Allah zai nema mata miji Wanda ya san zai kula da ita domin Allah a daura musu aure KO yayi abinda zai fishe shi ( toh fa )
Tana shiga Hajiya Fadimatu na amsa waya ta zauna sai da ta gama ta gaishe ta
Cikin murmushi take amsawa ta ce" ah Yar Fadimatu ya akayi kika saka nikaf din?
Yar Mahaukaciya tana cirewa ta ce" Mama ai yaya ne yace na saka kar na kuma fita babu shi
Hajiya Fadimatu a ranta ta ce toh kaji shi da ya tsani saka nikaf yau kuma shine da kansa yake cewa a saka ? Lale yau kam ta gama yarda da abinda take zargi aman zata gwada shi tayi murmushi ta ce " toh ki ke kiyi wanka sai ki sauko mu ci abinci
Yar Mahaukaciya ta amsa tana mikewa ta nufi dakinta
Konci tashi har Hutun su Yar Mahaukaciya ya kare sun koma makaranta inda wanan karin da wani irin gata take tafiya wanda wataran direba ya kaita wataran Maman Mubasshir kanta kawai sai ta shirya wai rakiya zata yi mata har cikin makarantar ba wanda bai Santa ba sanan yanzu idan bata son zuwa ta ci abinci har inda take ake kawo mata cikin mutuntawa
Yau ta tashi a lati dan kuwa mura ta hanata baci sai daidai asuba ta samu ta rintsa jikinta zafi rau da zazabi
Hajiya Fadimatu ta fito karfe bakwai da rabi ta zauna tana jiran saukowar Yar Mahaukaciya abin mamaki har karfe takwas tayi bata sauko ba , a fili ta ce" lafiyar Yata kuwa? KO ta tafi ne? No bazata tafi bata sanar da ni ba dan ba dabi'arta bace
Hakan yasa ta mike ta nufi dakin Yar Mahaukaciya tana fatan Allah yasa lafiyarta lau
Tana shiga ta hangota konce lulube cikin bargo tana karkarwa , Da sauri ta karasa ta dan yaye mata bargon tana fadin Yar Fadimatu lafiya?
Yar Mahaukaciya dake barin sanyi har hakoranta haduwa suke da kyar ta iya furta mama can cikin kasan makoshinta sanan ta maida idanuwanta ta rufe
Ai da gudu Hajiya Fadimatu ta juya tana rarumar wayarta ta danawa doctern su kira ta fada masa yarinyarta ba lafiya kuma sosai ne jikinta yayi zafi sosai
Doctern ya ce " To Hajiya Zan karaso nan da Awa biyu dan makocina ya rasu muna wajen jana'iza
Hajiya Fadimatu ta ce " Eyah Allah ya jikansa ta datse Kiran ta shiga neman lambar Mubasshir dan kuwa bazata iya zubawa yarta ido a haka ba har tsawon wani lokacin
Lambarsa ta wajen aiki take kira dan tasan a wanan lokacin yana office aman secreteria dinsa ta dauka tace bai karaso ba
Tana kokarin Kiran numbersa ta gida duk ta rude taji takun hayowa matatakalar dakin nasu
Da Sauri ta leka ta ga Mubasshir ne ya shigo ai bata san lokacin da tace " Yarona maza karaso Yarinyata ba lafiya plz
Wani irin faduwar gaba ya tsinci kansa da ita ya kara Sauri ya haye saman ya nufi dakinsa na da Wanda Yar Mahaukaciya ta zaune shi ya tura ya shiga ya karasa saman gadon da Hajiya Fadimatu ta yaye mata rufar tana kokarin daure mata gashin kanta ta kamata ta mikar da ita daga koncen da take
Saurin kawar da kansa yayi dan kuwa irin doguwar rigar barcin nan ce mai sulbin gaske duk da tsayinta aman lafewa take a jikin mutun , idanuwansa ana mike ta suka sauka saman mamarta dake tsaye tsai tamkar su tsole ido hakan ya mugun kayar masa da gaba da dana sanin kalonta
Hajiya Fafimatu ta ce" wai zaka kama min ita ne na saka mata hijab mu kaita asibiti KO kalon kasa zaka tsaya yi yarinya na galabaita?
Mubasshir cikin inda indar da bai san yana da ita ba ya ce" mmmmamar Mubasshir bara na dauko docteur Halima a haka bazata iya jiran harkar asibiti bâ
Kafin ta bashi amsa ya fita ya figi mota ya nufi office din Docter Halima tana tsaka da aikinta ya daukota ya kawota
Tana zuwa ta shiga gwaje gwaje nan ta gano mura ce ke damun Yar Mahaukaciya ta rubuta magunguna suka Fito da AA dan ya Mayar da Ita wajen aikinta
Bayan ya ajiyeta ya nugi pharmacie dan siyan magungunan da aka rubuta
Bayan ya siya ya kaiwa Hajiya Fadimatu ya dawo falo ya zauna ya kuna TV aman ina hoton dazu ya fado masa a idanuwansa a fili ya furta " A cikin nan yaro ya konta kuwa? Dan cikin gonda nashi na namiji dake shafe da nata , a shafe yake tamkar bata cin abinci KO haka halitarta take???
I dn kw
[
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
46
Shi kadai yana zaune tamkar sabon kamu yana magana da kansa daidai Hajiya Fadimatu ta sauko daidai ya ce" To kai Mubasshir mai ya shafeka idan ma ba nata bane?
Hajiya Fadimatu ta ce" Lafiya kake magana kai kadai?
Mubasshir ya mike yana dan murmushi ya ce" No maman Mubasshir ba komai ina dai tinanin wani abin ne,
Hajiya Fadimatu ta ce" toh Allah shi kyauta
Mubasshir ya ce" Maman Mubasshir ya jikin Yar taki?
Hajiya Fadimatu ta ce" ah yanzu da sauki har baci ya dauke ta
Ajiyar zuciya ya sauke sanan ya ce Allah ya kara lafiya
Hajiya Fadimatu ta amsa da amin
Ba ita ta farka ba sai gabanin la'asar domin maganin nata na mura mai saka barci ne , tana farkawa cikin ikon Allah da karfin jikinta ta farka ta shiga bayi ta wanke jikinta ta wanke bakinta ta dauro alwalah ta fito ta dauko Zani da Riga na atampa ta saka ta kabarta sallah
Tana gama salolinta ta mike ta cire hijabin ta koma dan kuwa har a lokacin barcin bai saketa ba ta ja zif dinta tayi konciyarta dan bata son saka rigar da ta dan kama ta kuma ta konta da ita , baci yayi awon gaba da ita
Cikin nutsuwa ya turo kofar ya shigo da yar salamarsa shirun da yaji ne ya saka shi idasa shiga dan ya san kawai tana barci
Hangota yayi ta hade kafafuwanta tana bacinta rigingine aman gashin kanta gaba daya ya rufe mata fuska ,
Gaba daya ya tataro courag dinsa ya nufi gadon yana adu'ar Allah ya sa bacin take dan ya ga ta canza kayanta ne ma ya saka shi nufar inda take ,
Yana zuwa ya dan dakata daga nesa da ita yana kalonta , jikinta daidai da ita , fuskarta ta yara ce , yanayin jikinta bata sha fama ba , to aman wacece ita? Yaron da ya rasu wanene shi? Mai dinta ne ? A ina ta samo shi? KO dai sato shi
tayi? Idan ba sato shi tayi ba to dan waye ? Da ita ta haife shi da jikinta ya nuna duk da akoy matan da idan sun haihu cikinsu na komawa ya lafe aman wanan ai a shafe ne yake daga ganinsa
A fili Ya furta no bazan iya ba , bazan ci gaba da zuba miki ido a haka ba aje ki cutar da ni, a yanzu haka na gaji da irin cutar da ni din da kike dan haka hakurina yazo karshe yau bazan kuma hakura da hakan ba
Gadan gadan ya nufeta yana tatare kafar wandonsa
Hanayensa biyu ya saka ya tayar da ita daga konce
Cikin tsoro ta buda idanuwanta ta sauke su cikin nasa wanda yayi iya yinsa dan ya hada idanuwan da ita
Bakinta ta buda cikin karkarwar baki ta ce " Yaya mai akayi? Lafiya?
Mubasshir ya ce " who are u?
Yar Mahaukaciya ta zuba masa ido jikinta ya fara karkarwa gabanta na dukan uku uku tsoro ya darsu a zuciyarta
Cikin karaji Mubasshir ya ce " da ke fa nake bazaki bani amsa ba ?
Yar Mahaukaciya tayi Saurin fadin wayo Mahaukaciyata ta fashe da kuka ta hade kanta da gwuiwarta , sosai take kuka har jijiyoyin wuyanta sunyi rako rako
Wani irin tausayinta ya darsu a zuciyar Mubasshir a hankali ya sauke hanunsa daga kafadunta cikin dakakiyar muryarsa ya ce " wacece Mahaukaciya?
Yar Mahaukaciya ta dago kanta ta sako daga Saman bed din cikin sarkakiyar murya ta ce" Mahaukaciya itace Mahaifiyata , bansan kowa ba ban san komai ba , Mahaukaciya da ita na fara bude idanuwana , ita na fara gani , mu ci abincin mu mai tsami , mu sha ruwa a bola , Mahaukaciya tana cikin Hauka aman tana nemo abinda zamu ci da cikin mu , Mahaukaciya koda an taba ta tayi min duka tana dawowa ta rungume ni muyi baci,
Ta silale kasa cikin kukan mai tsuma zuciya ta dago ta hade idanuwanta da Na Mubasshir Wanda ya zamto tamkar mutun mtuni ta kwashe gaba daya labarin rayuwarta ta fadawa Mubasshir dake zaune yana kalonta
Bayan ta gama bashi labarin Hajiya Fadimatu dake rabe tana sauraron su ta kara kasa kunenta
Mubasshir ya kare mata kalo ya ce " Karya kike Rahma, Karya ne , shin taya zan yarda da ke? rahma kina nufin neman mahaifiyarki ne ya saka kika baro bolarku? Taya ma zan yarda da ke duk irin yanda Hajiya ta kula da ke ta daukeki tamkar yar cikinta aman kika watsa mata kasa a ido kika yi mata karya? Ni wanene da bazaki yi mini ba ? Ki fada min gaskiya Rahma wacece ke ?
Yar Mahaukaciya ta lumshe idanuwanta , tabas ta san akoy ranar kin dilaci aman ta so sai ta hadu da mahaifiyarta sanan hakan ta faru , mikewa tayi a hankali ta nufi saman drewernta ta dauko alkur'aninta ta zo ta zauna gaban Mubasshir ta lumshe idanuwanta ta dora hanunta a saman kur'anin ta ce " Na Rantse da ,,,,,...... Kafin ta karasa fadin abinda yake bakinta Mubasshir ya Mike ya karbe kur'anin cikin zaro ido ya ce " *Baki da hankali ne?*
Yar Mahaukaciya ta Mike itama cikin karajin ta ce " *Ka barni na rantse Mubasshir , ka barni na rantse maka da alkur'ani mai girma duk da irin yanda mutun da gaskiyarsa yayi rantsuwa da shi yake samunsa ka san duk jahilcina na san idan bakada gaskiya ka rantse da shi ka halaka*
Ta kuma fuskantar sa ido cikin ido ta ce " *Tabas ni Mahaukaciya ce dan kuwa Mahaukaciya ta haife ni* sanan na boyewa Hajiya ne dan ina mace , macen ma mai rauni marar gata , ina gudun idan hajiya ta koreni ina zan dosa, ina gudun wani abin ya kuma tunkarata, ina gudun fadawa wata halakar , aman a kulun cikin bakin cikin biyewa Mama ta gidan nan nake , domin a kulun na kali darajarta da kimarta sai nayi kuka na karyar da nake yi mata , aman a yanzu alhamdulilah tunda Allah yayi kafin na bar gidan nan kun san KO wacece ni , na gode da kulawarku gareni Allah ubangiji ya biya ku ranar gobe kiyama
To fah , shin Yar Mahaukaciya zata kara GABA ne ? Ya aurenta da Mubasshir zai kasance? Zata ga mahaifanta ne KO yaya?
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
47
*Happy Juma'at, Allah ya karbi ibadun mu, Ya kyautata karshen mu, ya sa Aljana ta zama makomar mu dan nabiyin Rahamati*
Tana gama fadar haka ta juya cikin mutuwar jiki ta nufi akwatinta dake ajiye sai a lokacin ta tina zip din rigarta a kunce ta kama ta ja sama , ta buda akwatin ta zaro hijab dinta fari kar tana dagowa ta ga Hajiya Fadimatu ta harde hanayenta tana kalonta shima Mubasshir din ita yake kalo inda ta kasa fasara kalon kyama ne KO na